Zumar Hamada 🍯 🏜️

Embarrassed

by @zahrabmrs02


Bacci mai daɗi ya ratsa Tadala, ba ta farka ba sai da sautin kiran sallar Magriba dake tashi daga masallacin dake cikin gidan . Ta tashi da sauri, ta sake watsa ruwa ta ɗauro alwala, sannan ta canza kaya zuwa wata tsohuwar doguwar rigar material ta zaman gida. Ta  idar da sallah ke nan, sai ga Sadiya da su twins sun tura ƙofar ɗakin sun shigo.

"Mts, na shigo dazu naga kina ta baccin gajiyar tsiya, kamar daga china kika zo " Sadiya ta faɗa tana zama a gefen gadon cikin isa.

Tadala ta ɗan sauko daga kan gadon cikin girmamawa, "Eh, Anty Sadiya. Amma alhamdulillah, yanzu gajiyar duk ta tafi." Tadala ta miƙe ta fara buɗe akwatinta dake ajiye a gefe, ta ɗauko kulli na fari, "Yauwa Anty Sadiya, gashi inji Uma ."

Sadiya ta amsa a wulaƙance, ta kalli kullin tana ɗaure fuska, "Nagode. Ajiye nan, Bintalo zata kai min store ɗin personal kitchen ɗina. naji ƙamshinsa kamar da man shanu, kuma kinsan shi da wari sosai! Mutanen can dai ba zaku taɓa wayewa ku bari wannan kazantar ba."

Shiru Tadala ta yi, gabanta ya yi wani irin duka. Lalle Sadiya abun da mahaifiyarta  ta sha wahala ta daka ta haɗa mata tun daga agadaz , shi take wa wannan tarbar. Zuciyarta ta yi zafi amma ta daure, ta sake mika hannu ta ɗauko ɗayan kullin, "Gashi, wannan kuma na Mama adizatu ne

Safa ta matso ta taɓe baki, "Gross! What is this? Wannan menene haka datti-datti?"

Marwa ta tabe baki itama, "I doubt grandma zata so abun nan. Anyways, za a bata .Tadala ki shirya nan da minti goma, Bintalo zata zo ta miki jagora zuwa dining."

Bayan fitar su, Tadala ta zauna a gefen gado ta dinga mamakin yadda girman kan Sadiya ya ninka na da. Ta share ƙwallar dake neman zubo mata, ta faɗa a ranta cikin harshen Faransanci dake cire mata zafi: ‘Mon Dieu, la vie est difficile! (Ubangijina, rayuwa akwai wuya!) Wai yau Sadiya ce ke kiran kayan iyayenmu da kazanta?’ Tana nan zaune cike da tunani, Bintalo ta tura ƙofar ta shigo ta ce: "Wai  Mami tace ki biyo ni zuwa dining table, lokacin cin abincin dare ya yi."

Tadala ta gyara mayafinta, ta fito ta shigo babban falon a sanyaye, kanta a ƙasa, hannunwanta duka sun cure waje ɗaya saboda tsabar fargaba. Falon ya canza mata gaba ɗaya, ta sami ɗaukacin iyalin gidan sun hallara a kan dogon teurin cin abincin na alfarma.

mai gidan Alhaji Kamal (Dad) ne zaune cikin kwarjini na manyan masu kuɗi.

"Sannun ku..." Tadala ta faɗa da muryarta dake ɗauke da ainihin harshen Hausarta ta ƙasar Nijar wadda ba ta fita daidai ba.

Sadiya (Mami) ta ɗago da sauri ta kalli Tadala, take fuskarta ta canza saboda ganin tsohuwar rigar material dake jikin Tadala, 

"Wani irin shiga ne haka Tadala?!" Sadiya ta faɗa da wata irin tsawa da ta sa gaba ɗaya mutanen wajen tsagaitawa da abin da suke yi. "Baki da wasu kayan ne na kirki da zaki fito gaban mutane haka ?"

Umma ta ɗago kai ta kalli Tadala, ta saki  murmushi ta kalli ameenatu , sannan ta kalli Sadiya tace, "Haba amarya , kiyi haƙuri mana. . ay kinga bakuwa a hankali zata saba   ,Kuna da  ameenatu suka yi murmushin raini ƙasa-ƙasa.

Gaba ɗaya kowa na kan table din ya juyo yana kallon Tadala. Safa da Marwa suka sake ƙunshe dariya, Tadala ta ji wani irin daci da kunya kamar ƙasa ta tsage ta rife ta. Ta matse yatsun ƙafarta a cikin takalmin robar dake ƙafarta.

Ganin yanayin da aka jefa ta, Ahmad ya ji tausayinta ya kama shi. Ya tashi da sauri daga kan kujerarsa, ya taka ya jawo mata kujera ta kusa da shi, yace, "Zauna a nan Anty Tadala."

Sadiya ta daure fuska, amma ganin mijinta ya ɗago kai, sai ta washe baki ta kalli Alhaji Kamal tace, "Daddy, ga cousin ɗina Tadala ."

Tadala ta tattaro ragowar jarumtarta, ta kalli Alhaji Kamal da muryarta dake ɗan rawa tace, "Ina yini Daddy... mun same ku lafiya?"

Alhaji Kamal ya gyara zaman farin gilashinsa. Ya kalleta cikin sanyin murya da mutunci ya ce, "Lafiya lau Tadala, ya hanya? Ya mutanen gida?" Ya amsa mata cikin mutunci, amma hankalinsa sam baya kanta; a lokacin yana tunanin wata babbar harkar kasuwancinsa dake neman tangarda.

Bayan ya amsa, mommy dake zaune cikin cikar kamala da girma, ta kalli Tadala  cikin karamci tace: "Sannun ki da zuwa Tadala. Ya ƙasar ta ku? Fatan dai baki sha wahalar hanya ba?"

Tadala ta sunkuyar da kai, a hankali bakinta ya subuce ta amsa da yaren da ta saba dashi Non, ça va, merci..." Da sauri ta dawo da tunaninta ta gyara cikin Hausa, "A'a, hanya akwai lafiya. Nagode."

Su Safa suka kalli juna suna tabe baki, yayin da umma ta girgiza kai tana murmushin da ita kadai tasan maanar sa 

Daga nan aka fara cin abincin dare baki ɗaya cikin natsuwa. Tadala loma kaɗan kawai take iya kaiwa saboda nauyin zuciya da kuma yadda ta ga kowa na kallonta kamar wata baƙuwar duniya.

Bayan an kammala dinner, gaba ɗaya iyalin suka dawo babban falon alfarma (Main Living Room). Tadala tana zaune a sanyaye a kan wata kujera a  gefe, tana kallon yadda gidan yake ta sheƙi.

Amal ta matso kusa da ita ta zauna, ta kalli fuskarta dake ta annuri ta ce cikin gaskiya da murmushi: "Anty Tadala, kina da kyau masha Allah! Fatarki tana da kyau sosai."

A daidai lokacin, Ameenatu ta juyo ta watsa wa Tadala wani irin kallo na wulaƙanci da raini, daga sama har ƙasa.

Ta taɓe baki cikin gadara da takama, ta ce da ƙarfi yadda kowa na falon zai ji: "Kyau kuma Amal? Wannan ai kyan ƙauye ne! Duba fa kiga kalar kayan jikinta... gaskiya akwai aiki a gaban Mami na wayar da ita kafin ta tafi makaranta

Mommy  ba ta ce uffan ba, ta ci gaba da danna iPad ɗinta saboda ba ta shiga shirkin yara, yayin da umma  ta saki dariya a hankali . Sadiya (Mami) kuma ta ɗan murmusa ta kawar da kai ta nuna kamar bata San Tadala ba 

Daddy kam AirPod ne ma a kunnensa Kamar waya yake 

Tadala ta sake jin wani irin daci ya taso mata har maƙwarwato. Ɗaya bayan ɗaya suka fara mikewa suna nufin respective bedrooms ɗinsu, har aka bar Tadala da Sadiya kaɗai a falon.

Sadiya ta miƙe tsaye, , "Haba Tadala! Ya zaki zo gaban kishiyoyina da wannan tsofofin  kayan? Salon ki ja min raini ? Shi yasa ma tun farko bana son kowa daga Nijar yazo   gidan nan, saboda yanzu sai a jawo min abun gori!"

Tadala ta sunkuyar da kanta, hawaye ya kwace  mata, "Kiyi haƙuri, Anty Sadiya. Ni ban zaci kayan basu yi ba, naga dare ne kuma a cikin gida ne, shi yasa." Sadiya ta huri iska ta juya ta bar falon cikin bacin rai.

Bayan Sadiya ta bar Tadala a falon ƙasa, ta nufi babban kicin dinta . Kullen tadala ta dauko , can cikin zuciyarta ta san cewa  Hajjo kwararriya ce a fannin sarrafa sirrin dake riƙe miji  a hamada.

Ta buɗe kullin, man shanu dake gauraye da zafafan ganyayyakin gyaran jiki na asali ya daki fuskarta. Sadiya ta ɗan ja tsaki a hankali saboda ba ta saba da abubuwan gargajiya ba, amma hakan bai hana ta dibi tsabar dakan ba, ta shiga banɗaki ta shafar wa kanta a matsayin gyaran jiki kafin ta fito.  Tasha na sha da madara Bayan ta watsa ruwa, ta feshe jikinta da tsada-tsadan turarukan  Chanel, ta sanya wata doguwar riga ta bacci mai taushi ta siliki (silk) wadda ta fito da siffarta, sannan ta nufi sashen mijinta.

Sadiya ta tura ƙofar ƙatafaren sashen Alhaji Kamal (Master Bedroom). Ɗakin babbane mai cike da daula da sanyin AC, ga ƙamshin turaren wuta na Oud dake tashi. Ta sami Alhaji Kamal yana zaune a kan gadonsa mai faɗi, sanye da fararen kaya na alfarma, yana duba takardun kamfaninsa a kan iPad ɗinsa.

Sadiya ta taka a hankali cikin salon kissa , ta zauna a gefen gadon, muryarta a sanyaye tace, "hubbi , har yanzu ba a yi baccin ba? Gashi dare ya yi sooai."

Alhaji Kamal ya ɗago kyakkyawar fuskarsa , ya gyara zaman gilashinsa, ya kalleta sannan ya sauke numfashi. Ya ajiye iPad ɗin gefe yace,  sweetheart , ina duba waɗannan takardun ne na harkar Oil & Gas dake neman tangarɗa a Port Harcourt. Zuciyata ba ta ba ni baccin ba baki ɗaya."

Sadiya ta matsa kusa da shi, ta sanya hannunta tana ɗan matsa masa kafaɗa cikin lallashi tace, "Hubbi tunda lokacin hutu ya yi, kamata ya yi ka ajiye duka waɗannan takardun a gefe. Ka huta, ka rage wa kanka nauyin tunani."

A take, yayin da Sadiya ke magana cikin wannan kusancin, wani irin daddadan ƙamshi ya bugi hancin Alhaji Kamal. Ba ƙamshin turaren Chanel ɗinta na kullum ba ne; wani ɓoyayyen ƙamshi ne na asali, mai haɗe da zafin hamada da ganyayyaki dake ratsa jini. Alhaji Kamal ya ɗan dube ta, gira a dage, ya ji wata irin natsuwa da sha'awa daban ta fara dukan zuciyarsa wadda ya daɗe bai ji irinta ba Takardun dake hannunsa duka suka fita a kansa.

ya ajiye gilashinsa, ya janyo Sadiya zuwa jikinsa domin su amsa kiran juna a wannan daren .

A gaskiya, ta fuskar love making, babu wani sabon abu ko armashi na bajinta da ya faru. Sadiya ta kasance cikin ainihin salonta na kullum; sanyi, babu wani motsi na kissa, babu explore na zamani, kuma babu wani rikitaccen salon da zai gamsar da namiji ɗari bisa ɗari. Komai ya tafi ne a kan tsari guda ɗaya na tsohuwar al'ada da suka saba, inda ita dai kawai tana kwance tana karɓar buƙatar mijinta ba tare da wata bajinta ko dabarun motsa sha'awa ba.

Amma duk da rashin armashin da salon nata yake da shi, wani abu na ban mamaki ya faru a daren nan saboda tasirin dakan da ta yi amfani da shi. Alhaji Kamal ya ji wani irin zazzafan canji daban a jikin Sadiya wanda  ya dade ba ji hakan daga gareta ba , jikinta ya sake yin wani irin laushi, dumi, da sanyi na musamman dake riƙe namiji. 

Bayan sun kammala, Alhaji Kamal yana kwance yana maida numfashi, fuskarsa cike da mamaki dake haɗe da gamsuwa, ya juyo ya kalleta cikin sanyin murya yace: "Maman Twins... Yau gaskiya naji ki daban sosai. Wanne irin sirri kika canza ne haka a daren nan? Ko akwai wani sabon abun da kika fara amfani da shi ne?"

Sadiya ta gyara zaman rigarta, ta gyara kwanciyarta tana mai lula cikin farin jin kalaman sa Ta saki wani daddadan murmushi , ta ce: "hubbi ... babu wani sirri fa. Kamar kullum ce dai amaryarka Sadiya, soyayya ce kawai ta motsa a daren nan."


Duk da tsananin laushin ƙatafaren gadon da aka sauƙi Tadala a kai, gami da daɗaɗan sanyin AC dake huri a cikin ɗakin, baccin sam ƙara gudu yake yi a idanunta. Wani irin nauyi da dacin kalaman da aka jifeta da su a wajen dinner ya dawo mata sabo fil a rai. Tunani da fargabar irin zaman da zata yi a gidan ya hanata natsuwa, can kuma zuciyarta ta tafi Agadez... Tana hango fuskokin yan gidansu .

Ganin daren ya tsala , Tadala ta tashi da ƙyar ta nufi banɗaki. Ta sake watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito. Ta shimfiɗa dadduma ta ta da sallar dare domin ta kai ƙukanta ga Ubangijin da Yake ji kuma Yake gani.

Bayan ta idar da sallah, ta zauna a kan daddumar, ta ɗaga hannuwanta biyu sama, idanunta cike da hawaye dake kwarara a kan kyakkyawar fuskarta, ta shiga addu'a. Ta fara ne cikin natsuwa da harshen Faransanci a hankali don kada wani yaji ta:

"Ya Allah... Ne me laisse pas seule, mon Dieu. (Ya Allah... Kada Ka bar ni ni kaɗai, Ubangijina). Ka ga zuciyata, Ka fi kowa sanin abin da ke ciki. Ubangiji Allah Ka buɗe mini ƙwaƙwalwata da basirata ta yadda zan fahimci dukkan karatun da zan fuskanta a jami'ar nan ta Base University. Ya Allah, Ka haɗa ni da daukacin alherin dake cikin ƙasar Najeriya. Abin da na zo nema na neman ilimi da dukiya don na canza wa iyayena rayuwa, Ya Allah Ka tabbatar mini da shi. Kada Ka bar ni da ikona ko wayona, Ubangiji Ka kare mini mutuncina a gidan nan, Ka ba ni juriya da haƙurin zama da Anty Sadiya da mutanen gidan nan baki ɗaya."