GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 27

by @nusybee143

Page 27



Kallonsa ɗan sandan da yake yi mata bayani kawai take yi numfashinta yana ɗagawa sama-sama, dishi-dishi ta hango ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin buga mata handcuff,daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba

A hankali ta fara buɗe idanunta,tana rufewa tana buɗewa, lokaci guda kuma komai da ya faru ya dawo mata fes 

Labari aka kawo mata na cewa mijinta Arnold ya mutu,kuma ana zargin da saka hannunta a mutuwarsa,a firgice ta yunƙura zata diro daga kan gadon, ƴar sandan da take tare da ita ta dakatar da ita gudun kar ta illata kanta, ga cikin da yake jikinta 

Kuka sosai ta fashe da shi mai ban tausayi, duk yadda likitocin suka so ta kwantar da hankalinta ta daina kukan hakan ya gagara,ba wai mutuwar Arnold ce kawai ta taɓa ta ba, sai tonuwar asirinta, ina ma a yanke mata hukuncin kisa a ce ita ta kashe shi,ina ma ta zo haihuwa ta mutu,ina ma zuciyarta ta buga ta bar duniya,irin tunanin da ta rinƙa yi Kenan tana rera kuka cikin tashin hankali da gigita 

Kwananta biyu aka sallame ta,kuma kai tsaye aka nufi station da ita,a can ta wuni,duk irin tambayoyin da aka yi mata ta kasa ba da amsa

Diego shine ya tabbatar da cewa Arnold giya ya sha,a buge yake lokacin da ya yi hatsari,kuma tabbas hayaniya ta haɗa su da matarshi Fatima shiyasa ma ta gudu ɗaki,sai dai ba ita ba ce ta ji masa ciwo,kamar yadda suke tunani, sunanta kuma da yake ambata yana da alaƙa da kewarta da yake yi ne 

Da wannan bayanin Diego ya samu ƴan sandan suka saki Shaheeda,gashi kuma dama ba a son ransu suke riƙe da ita ba saboda cikin jikinta da kuma kukan da take yi, wanda duk wanda zai ganta zai tabbarwa kanshi na baƙin ciki ne

Diego shine ya cigaba da kulawa da Shaheeda har ta samu sauƙi,da farko ya kan zauna ma ya yi ta ɗebe mata kewa,ya kawo mata abinci,ya hana ta shan ƙwayoyin da take sha cikin dabara da hikima, don sun fara illata ta da ɗan cikinta,daga baya ma sai ya kawo mata ƙanwarshi Martina don ta rinƙa ɗebe mata kewa 

Shaheeda ta yaba da karamcin da ya yi mata sosai,har hakan ma ya rage mata raɗaɗi mai yawa daga zuciyarta,ta yi iya ƙoƙarinta ganin ta rabu da damuwa kamar yadda Diego yake so 

Kwanan Arnold tara da rasuwa mahaifiyar Mrs. Andrea Lambert ta iso ƙasar Spain,a ranar Shaheeda ta ga wulaƙanci ta ga tozarci, Arnold shi kaɗai ne ɗa a wajen Mrs. Andrea Lambert,kuma a saboda Shaheeda ya gudu ya bar gida,babban abin da ya fi yi mata ciwo ma shine kasancewar Shaheeda musulma,hakan ne ya sa ta sake zargin eh tabbas ita ce ta kashe mata ɗa

A ranar ta kore ta daga gidan,duk da halin jinya da kuma nauyin ciki bai saka ta tausayawa Shaheedan ba,haka tana kuka ta ɗauki iya abubuwa masu muhimmanci da zata buƙata ta bar gidan, zuciyarta cike da tunanin inda zata je,don lokacin Martina tana makaranta,gashi bata san gidansu ba

Haka ta yi ta gararamba daga wannan titin zuwa wancan,gaba ɗaya hankalinta ba ya jikinta, tunani kawai take yi yadda zata bar Spain, don ko kuɗin abin da zata ci bata da shi ballantana na jirgi 

Tana tafiya tana bin gefen titi sai jin wani mahaukacin horn ta yi,tsabar gigita ma sai ta rasa yadda zata yi,a wajen ta durƙushe jikinta ko'ina yana karkarwa, wadanda suke cikin motar suka fito da sauri suka nufo inda take suna dubawa ko ta ji ciwo

Sai dai kafin su ƙaraso juriyarta ta ƙare,tuni ta silale a wajen ta kwanta,suna zuwa suka ɗauke ta suka sanya ta a mota suka nufi asibiti 

Ita dai Shaheeda bata samu kanta ba sai washe gari,da matar da ta kusa kaɗe ta ta fara haɗa ido bayan ta dawo hayyacinta,ta ga kulawa sosai,suka ba ta labarin sun je ɗauko yaransu daga makaranta ne a hanya suka ganta 

Suka tambaye ta labarinta,daga ina take?bat gaya musu komai ba,kawai ta ce musu tana son komawa Nigeria ne,amma bata da kuɗin Flight,hakan ya sa suka ba ta shawarar ta zauna tare da su kafin mijin ya samu yadda zai yi ya saka ta a jirgin Nigeria 

Ta ji daɗin zama tare da su na tsawon kwanaki biyu,yaransu masu suna Ana da Mia suna ɗebe mata kewa sosai,sai dai bayan kwanaki biyun ta buƙaci zata koma inda ta fito kawai,don hankalinta ya koma ga iyayenta 

Tilas ba don sun so ba suka bar ta ta tafi,don duk shawarar da suka ba ta bata saurarensu, hankalinta da tunaninta kacokam suna gida wajen iyayenta 

Kai tsaye ta koma unguwar da suke zaune ita da Arnold, abin baƙin ciki ta samu gidan a kulle,haka ta zauna a ƙofar gidan tana rera kuka mai ban tausayi 

Sai dai kuma ta yi ƙatuwar Sa'a, saboda ɓullowar Martina da ta gani,babu shiri Martina ta taho da gudu ta rungume ta tana tambayarta 

"Muka neme ki muka rasa,yayana yana ta so ya mayar da ke Nigeria amma ba mu same ki ba"Shaheeda ta yi saurin cewa "to yanzu ki gaya masa,zan koma Nigeria Please"babu musu Martina ta ciro wayarta ta danna masa kira,bugu biyu ya ɗauka, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar masa abin da yake faruwa 

Kai tsaye ta ce su jira shi,a nan suka zauna suka yi jugum-jugum bayan ta kashe wayar,ita dai Shaheeda fargaba da razani ba su bar ta ta fahimci komai ba

Babu jumawa Diego ya zo, cikin kuka Shaheeda ta kora masa bayanin komai na yadda mahaifiyar Arnold ta tozarta ta,kuma ta kore ta daga gidan saboda tana zargin ita ta kashe mata ɗa,ya ɗan yi shiru, kafin cikin ƙunar rai ya ce "babu komai,dama ai tun farko bata so auren bane shiyasa ta yi haka,amma babu komai,na bincika yanzu,akwai jirgi mai tashi zuwa Nigeria,sai na yi miki boarding ɗin sa"babu musu ta yiwa Martina sallama,suka rabu cike da kewa,Diego ya ɗauki Shaheeda a motarsa suka nufi airport 

Ya yi mata komai na jirgin, sannan ya ba ta yan kuɗin da zata rike hannunta,ya dube ta cikin tausayawa ya ce "to shikenan tafiyar ko?
Ina yi miki fatan alkhairi,sai watarana idan da rabon za'a sake haɗuwa,kuma kar a manta da mu please"ya juya ya tafi,ita kuma tana ta yi masa godiya amma sam bai juyo ba ballantana ya ba ta amsa

Har Shaheeda ta shiga jirgi jikinta a sanyaye tana ta kuka,a wannan lokacin ji take yi inama Allah ya ɗauki ranta ta huta da wannan bala'in,don ta gama fitar da rai da rayuwa,ga taraddadin tashin hankalin da zata je ta riska a Nigeria sakamakon guduwar da ta yi ta bi Arnold,ga cikin da zata koma da shi,da baƙaken labarin kasancewar Arnold bai musulunta ba,da kuma mutuwarsa,da korar da uwarsa ta yi mata 





💫

Roxy tana zuwa nan a labarinta ta kasa cigaba da labarin kukanta yana tsananta,ita kaɗai ta san irin ciwon da take ji da baƙin ciki na rayuwarta ta baya,a hankali ta yi ƙasa da kanta tana shashsheƙar kuka mai tsanani,shi dai Haisam kallonta kawai yake yi,ya kasa iya ce mata komai,kai a ƙasa tana girgiza kai ta ce "ba zan iya ba,watarana kawai na cigaba"daidai lokacin maasu kula da prison ɗin yake tabbatar musu da cewa tun ɗazu lokaci ya wuce, Haisam dai yana zaune kamar an dasa shi yana bin kowa da kallo kamar mutum-mutumi aka shigar da Roxy zuwa inda aka fito da ita

Da kallo kawai ya bi su, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake,shima ji yake yi kamar ya fashe da kukan kamar yadda take yi,a hankali ya miƙe tsaye jiki a sanyaye ya fice daga wajen yana tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki,tausayin Shaheeda ya kasa barinsa, tabbas laifinta ne,amma kuma ɗaukar irin wannan hukunci a gare ta da ƙananan shekaru ba abu ne mai sauƙi a gare ta ba

Daga nan orphanage ya wuce inda ya kai Mubarak,don ya san abu ne mai wahala Roxy ta samu fitowa saboda laifukan da ake tuhumarta da su,amma zuwa yanzu ya fara nazarin yadda zai yi ya fito da ita ko ta halin yaya ne

Signing ya yi na karɓar Mubarak gaba ɗaya,ya samu ya karɓe shi ya saka shi a mota suka bar wajen zuwa gida 

Yana zuwa gida kai tsaye part ɗin sa ya shiga yana rungume da Mubarak da ya yi shiru yana kalle-kalle,tausayin yaron ya kama shi sosai, gaba ɗaya bai san menene jin daɗin rayuwa ba,bai san menene farin ciki ba, rayuwarsa cike take da ƙalubale a sanadin kuskuren da iyayensa suka aikata 

Ranshi ya sake ɓaci lokacin da ya ga Nimra a sashensa ta yi ɗaiɗai tana kallon TV tana cin porpcorn,wata sexy dress ce a jikinta,tana ganinsa ta tashi da gudu ta faɗa jikinsa tana yi masa oyoyo,a fusace ya ture ta gefe yana faɗin "ba kya kula ne?

Ba ki ga yaro a hannuna bane?ko sai kin buge shi?"

Ja baya ta yi, cikin rashin damuwa ta ce"oh sorry!

A ina ka samo shi?so cute little boy

Kai what's your name?"shi dai Mubarak da alamun babu cikakkiyar lafiya a tare da shi kanshi yana kwance akan kafadar Haisam yana kallonta, Haisam ya ja tsaki ciki-ciki ya wuce da shi ya kwantar akan kujera,ya gyara masa kwanciya sannan ya wuce banɗakinsa don ya yi freshen up

Kafin ya kammala shiryawa Nimra ta gabato masa da nau'ikan abincin da ta shirya masa wanda ta san yana matuƙar so,sai dai ko kallo biyu bai yi musu ba ya shiga kitchen don ya dafa musu noodles shi da Mubarak 

Nimra ta biyo shi tana shagwaɓe fuska, cikin sanyin muryarta ta ce"ba ka son abin da na dafa maka ne kake ƙoƙarin boiling noodles?"

Bai kalle ta ba ya ce"a'a kawai dai I'm craving noodles ne, shiyasa ma ban yi takeway ba"

"To ka kawo na yi maka mana"ta faɗa tana ƙoƙarin karɓar girkin 

Murmushi ya yi ya ce"No kin wahala akan wancan girkin, thanks ba sai na sake wahalar da ke ba,ki je ki taya yaron can zama da muka zo tare ki yi masa hira, I'm sure you will like him, idan kika yi haka I'm okay with it"

Kallonsa ta yi kamar mai nazari,sai kuma ta juya ta fice daga kitchen ɗin ba tare da ta yi magana ba

A parlourn ya same su a zaune,ta taƙarƙare tana ta yi wa Mubarak hira,shi dai kasancewar ba shi da saurin sabo kallonta kawai yake yi daga inda yake kwance 

Haisam bai kula ta ba ya ɗaga shi zaune,ya fara ba shi abincin yana nazartar yadda yake a nutse, Nimra da ta gaji da pretending ta ce"yaya Haisam wannan yaron fa?

Ina ka samo shi?"

Kai tsaye ya amsa mata ba tare da ya kalle ta ba"ƙanin Amna ne"

Take fuksarta ta sauya,ranta ya fara sosuwa, Amnan da take so ta san yadda zata yi ta sa ya tura ta ga mahaifiyarta shine za'a ɗauko wani ƙaninta,dama tana da wani ƙani?

Ranta a ɗan ɓace ta ce"to amma meyasa ba ka bar shi a hannun mahaifiyarsa ba?

Kalle shi fa,har Amnan fa ya dace a ce suna gaban mahaifiyarsu, meyasa ka ɗauko su?".
Kai tsaye ya ce"ra'ayi, dukkansu za su zauna tare da ni,shi dai wannan da yiwuwa ya koma hannun mahaifiyarsa amma Amna tana hannuna"

Nimra ta ce "to me yasa ba za ka mayar da amnan ba sai shi kaɗai?"

Haisam da ya fara gajiya da tambayoyin ya ce "saboda shi ba ba ni na haife shi ba,amma shima idan mahaifiyarsa ta so zan rike shi a hannuna"

"To menene alaƙarka da shi da za ka rike shi?

Babu wani mai rike shi ne sai kai?"

Banza ya yi mata,sai da ya tabbatar Mubarak ya ƙoshi sannan ya rungume shi da kyau ya dube ta ya ce"ni zan riƙe ɗana,ban ce wani ba, ballantana ke"yana kai wa nan ya miƙe ya fice daga sashen don ya kai wa Nanny ɗin Amna shi, Nimra ta bi shi da kallo zuciyarta tana raɗaɗi,tana jin dole sai ta raba shi da yaron nan






*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*


Ƙaton katafaren parlourn gidan ya ɗauki shiru tamkar babu wani mahaluki a ciki, ba'a jin komai sai ƙarar AC da shashsheƙar kukan Arfa da ya karaɗe parlourn, Alhaji Yusuf da yake zaune a inda ya saba zama ya yi shiru yana kallon Arfa da take ta kuka,tun da aka kawo masa maganar sakin da Muyassar ya yi mata yake cike da tsananin mamaki

Gashi an kira wayar Muyassar ɗin ba'a samun sa,da alamu ma ba ya ƙasar tunda ya aikata abin da yake so 

Gyaran murya ya yi, ilahirin matansa da Hajiya Sa'adatu da Hajiya Salma da da sauran ƙannensa maza suke zaune suka mayar da hankali kanshi don jin abin da zai faɗa,gaba ɗaya jikinsu a mace




#Nusy_bee