Chapter thirteen
by @aysharano22
Bude idanun yayi a hankali jin yanda zuciya da kwakwalwarshi keta kokarin lallai sai sun maida tunanin nashi can baya domin ya sake tunawa da kalar kyautatawa da sadaukarwa da Lee yayi a gareshi wai ko mantawa yayi.
Bai tsaya gardama da tunani ko kwakwalwar nashi ba, don yasan ba iya dakatar dasu zaiyi ba don haka kawai ya bada kai bori ya hau.
Nan take kuma tunanin nashi ya koma can baya tunma kafin haduwarshi da Lee.
TUNA BAYA.
Cikakken sunanshi Ayaan Agnihotri, shekarunshi 26 ciff a duniya amma bazai taba ce yasan wani abu dangane da iyayenshi ba face abubuwa guda biyu…na farko shine sunayensu sai kuma kasancewarsu Indians.
Mahaifinshi Dr Prakash Agnihotri da mahaifiyarshi Nandini Agnihotri sun kasance ‘yan asalin garin Mumbai dake Maharashtra state of India…maybe for their unkonwn selfish reason suka zabi su haifeshi ta hanyar SURROGACY bayan kasancewarsu ma’aurata da zasu iya haifanshi da kansu amma suka zabi su sama wata mata cikinshi ta haifeshi madadin ace mahaifiyarshi ce ta dauki cikinshi ta haifeshi da kanta.(NB:Surrogacy wata hanya ce da couple ko kuma ince matan da basu son daukan ciki su haihu da kansu kuma sunada buqatar samun yara sukebi don samun ‘ya’ya na kansu…kmr yanda ake IVF haka surrogacy yake saidai banbancin dake tsakaninsu shine, shi IVF idan an kammala fertilization na sperm din namiji da egg din mace ya zama embryo, zaa sanya shi wnn embryo din a cikin mahaifar uwar yaron wacce akayi amfani da egg dinta wajen fertilization…kenan zai zama biologically wnn dan ko ’yar da aka samu nata ne tunda anyi producing nashi da egg dinta snn ita aka sama cikinshi tayi rainonshi wata tara har ta haifi abunta while in surrogacy shi kuma in an gama fertilization madadin a sama uwar ’dan ko ’yar wacce ta bada egg dinta kenan, sai a samo wata mace daban wacce ba da egg dinta akayi amfani ba a saka mata a mahaifarta ta dauki cikin tsahon wata tara ta haifa kenan biologically wnn babyn ba nata bane tunda bada egg dinta akayi producing nashi ba shiyasa ake kiransu SURROGATE MOTHERS).
So this is the same procedure da akabi aka samar da Ayaan Agnihotri aka Mr India…ma’ana asalin mahaifiyarshi daban snn wacce ta dauki cikinshi ta haifeshi itama daban.
Surrogate mother dinshi sunanta Haj Madina Auwalu Aleiro ta kasance ‘yar asalin jihar Kebbi ce karamar hukumar Aleiro…tanada shekaru 23 ta auri wani babban dan kasuwa anan cikin Kebbi wande ke yawan fita kasashen waje don harkar business dinshi kuma India ta kasance daya daga cikin kasashen da yake yawan mu’amalar kasuwanci dasu…shekararsu wajen shida da aure Allah bai basu haihuwa ba amma suna zamansu lfy don ba wani dangi ke gare mijin nata ba balle su sa musu ido ace ya zauna da matar da bata haihuwa.
Ana haka watarana ya tafi da ita India kasancewar ta dade tana mishi naci kan ya tafi da ita tanaso taje taga ya garin yake…tunda take bata taba tsayawa ta zurfafa tunanin wace irin sana’a mijin nata keyi ba dukda bata sani ba amma bai taba bata dalilinda zaisa tayi zarginsa ba so ta yadda da kayanta dari bisa dari.
Koda suka isa India suna sauka Mumbai airport tunma kafin a gama clearing kayansu da su kansu kawai sai ganin custom da immigration officers dinsu na can sukayi sun zagayesu wai sun samu tip din cewa suna daukeda miyagun kwayoyi…tun daga yanda taga hankalin mijin nata ya tashi har yana kokarin guduwa tasan zaiyi wahala ace karya suke mashi…ilai kuwa suna duba kayansu suka tsinci dami dami na wiwi da cocaine har a cikin suitcase dinta da batasan yaushe yayi planting mata su ba…haka custom suka kamasu suka tafi dasu akaje akayi locking dinsu a cell akaita gana musu azaba kan sai sun fadi abokan harkallarsu na nan cikin india don wanda ya basu tip din ya tabbatar musu cewa sunada abokan harkallah a nan cikin kasar tasu amma mutumin nan kememe yaki bude baki yayi mgn, haka tanaji tana gani akayi labelling dinta as criminal aka kuma yita azabtar da ita amma mijinta koda wasa bai fada musu gskyr lamarin ba ita kuma tace batasan komai kan harkokinshi ba batada hannu a ciki sukace bazasu saketa ba sai sun kammala bincike tunda itama sun kama kayan a jikin jakarta.
In takaice muku dai saida tayi three weeks a hannunsu kafin finally su gano babu sa hannunta a ciki ta hanyar asalin wanda yayi tipping dinsu don haka sukayi releasing dinta bisa sharadin cewa bazata bar India ba har sai an gama shari’a tunda har an samu kayan cikin kayanta dole watarana bincike zai iya biyowa ta kanta…haka ta tafi Allah ya taimaketa ta hadu da wata mata itama ’yar Africa ce zama ya kaita India, ita ta taimaka mata da wurin zama dukda cewa ita dinma ba wani sarari ne da ita ba amma dai at least tanada inda zata tsuguna kafin komai ya lafa tasan inda dare yayi mata.
Saida tayi kusan wata tana jinya kafin ta warke daga wancan wahalar da tasha hannun Customs, har snn kuma baa bata izinin komawa kasarta ba…dole ta shiga neman sana’a don ko kudin siyan ticket da zata koma gida bata dashi gashi lokacin waya ma ba wadata yayi a Nigeria ba snn ba wasu shaqiqan dangi ko iyaye ne da ita da idan ta kira zasu iya taimaka mata ba don haka ta fara neman aikinda zata dan dinga samun na kashewa harma ta tara kudin siyan ticket idan lokacin komawarta yayi.
Matar da take tareda ita mai suna Magret tayi mata introducing irin sana’ar da takeyi wato SURROGACY.
Koda tayi mata bayanin yanda Surrogacy din yake sam hankalinta bai kwanta da abun ba musamman da take ganin kmr bazata sake wata biyar bama a kasar balle har ta yarda asa mata cikinda sai yayi wata tara kafin ta haifeshi amma daga baya sbd tsananin buqatar kudi da takeyi dole ta amince zatayi nan kuma suka shiga yawon asibitoci suna neman couples dake neman surrogate mother…a yawon asibitocin ne kuma watarana Allah ya kaisu wani asibiti a nan cikin Bandra duk cikin Mumbai din mai suna Saraswati Fertility Hospital…nan ma dai shiga ciki sukayi suka fadi buqatarsu sai aka hadasu da mamallakin asibitin Dr Prakash…shima har yace suyi hakuri sai kuma yana ganinsu yaga sunyi mashi kala da Africans nan take ya canxa shawara ta hanyar ce musu suje bayan kwana biyu su dawo…haka kuwa akayi kwana biyu nayi suka dawo nan ya tambayi wacece surrogate mom din Magret da nuna masa Madina ba bata lokaci ya kira lab suka dauki jininta yace aje ayi dukkanin tests da akeyi wa surrogate Moms…kwana biyu nan ma ya sake basu yace idan result ya fito su dawo…bayan dawowar nasu ya tabbatar musu da cewa gwajin da akayi ya tabbatar da batada wata matsala don haka zaiyi planting mata babynshi na kanshi sbd yanason yara matarshi kuma batada lafiyar da zata iya rainon ciki amma bisa sharadin zata bar duk inda take ta koma inda zai kaita don yanaso yayi watching dinta sosai sbd bazaiyi risking rayuwar danshi ba tunda ba saninta yayi ba plus abune da zaiyishi a sirrance ba tareda sanin ko matar tashi ba sbd wani dalili…ba musu ta yadda da qudurinshi cikin kankanin lokaci kuwa ya canxa mata wurin zama tareda ajiye mata komai na bukata tunma kafin ayi procedure din…yayi amfani da kasancewarshi likita yayi taking eggs din matarshi da dama ba lfy ne da ita ba batareda saninta ba yahada da sperm dinshi yayi fertilizing har saida ya zama embryo snn yayi planting dinshi cikin mahaifar Madina.
Bayan sati hudu yayi mata pt aikuwa saiga ciki radau a jikinta ma’ana dai ivf din nasu yayi sbd ba kowane lokaci nema akeyin saa yayi lokaci daya ba…haka Madina tacigaba da zama gidan daya sama mata tana kulada cikinta shima kuma yana sa mata ido sosai kuma yana yi mata duk wani abu da mai ciki ke buqata da gani ba karamin so yake yima cikin ba dukda bama ko yaushe yake zuwa ba yafi aika mata wani da batasan alakar dake tsakaninsu ba.
Ciki na shiga wata tara yayi mata Cs da kanshi ya ciro ’danshi mai zubin indiyawa sak kuma mai kama dashi…fadar farin cikin da yayi na samun dan ma bata baki ne, da kanshi ya saka mishi suna AYAAN don yana son sunan sosai…bayan haihuwar dan sai ya shiga zullumin ta yanda zai sanar da matarshi cewa sun samu da ta hanyar surrogacy sbd yafi kowa sanin yanda ta tsani surrogacy duk akayi zancenshi har cewa take duk dan da bai zauna cikin mahaifarta ba kuma ba ita tayi labour ta haifeshi ba to bazai taba zama danta ba…shi kuma yayi hakan ne sbd wani dalili da zakuji a gaba…haka dai ya biya Madina kudade masu yawa hakan kuma yayi daidai da lokacinda akayi releasing dinta daga wancan case na mijinta don haka ta fara shirye shiryen komawa kasarta Nigeria bayan ta samu da kyar mijin nata ya saketa, yayinda shi kuma Dr Praskash ya karbi danshi ya tafi dashi.