Chapter fourteen
by @aysharano22
Bayan kwana biyu batasan meya faru ba kawai sai ganin wata mata tayi wacce bata samu ganin fuskarta ba sbd rufeta da tayi ta dawo mata da jaririn ta kuma ce mata muddin bata hada kayanta ta koma kasarta ba saita tabbata Case din da aka rufe nata an sake budeshi don saita san duk yanda tai tayi convincing customs cewa harda ita cikin deal din drugs da akeyi kan mijinta daga nan kuma bazata sake shaqar iskar ’yanci ba don zata dawwama ne a prison idan ma baa yanke mata hukuncin kisa ba…jin wnn batu ya daga hankalin Madina sosai don bazata taba manta azabar data sha hannun Customs din nan ba don haka ta hada kayanta tsaf kmr yanda ta bukaceta ta dauki jaririn data dawo mata dashi tabar gidan amma maimakon ta tafi saita koma gidan Magret don bazata iya tafiyar mashi da danshi ba…washegari taje asibitin Dr Prakash don maida mashi da danshi ta kumayi masa bayanin dalilin bacewarta daga gidanshi sai aka ce mata yayi tafiya…haka ta koma gida jiki a sanyaye still kuma har snn bataji zata tafi mishi da ’da gari ya garara har Africa ba, African ma Nigeria…haka taita sintirin zuwa nemanshi ana ce mata bai dawo ba a takaice har lokacin tafiyarta yazo don ta riga ta siya ticket dinta…ganin haka nefa hankalinta ya sake tashi har tana tunanin ko zuwa zatayi ayi mata rescheduling ticket din a dan kara mata kwanaki har zuwa sanda zata ganshi ta maida mishi da danshi kawai kwatsam sai ganin wnn matar tayi wnn karon hadda ’yar rakiya da itama bataga fuskanta ba sunzo har gidan Magret din sun sake jaddada mata kodai ta tafi can inda ta fito ko kuma ta shiryawa zama na har abada a gidan yari…haka tana kuka tana komai suka sanyata a gaba ta hada kayanta dana jaririn da tace zata barma magret shi inyaso idan babanshi ya dawo saita maida masa dashi tunda tasan inda zata sameshi nan ma sukace sam basu yadda saidai ta tafi da yaron…itama kuma Magret tace bazata taba sa kanta cikin wnn Case din nasu ba don da ganin wayan nan mutanen tasan ba abinda bazasu iya aikatawa ba tunda ta fuskanci da gaske ba son yaron sukeba ita kuma idan suka makala mata sharrinda zaa rabata da india ina zata koma?…haka tayi rejecting tace ita sam bazata amsa yaron ba.
Daga karshe dole Madina ta hakura ta tafi da baby don basu bata wata dama da zata sake neman mafita ba, da kansu suka kaita airport sukasan yanda sukayi sukai cuku cukun yanda bazata samu matsala ba wajen tafiya da yaron sukayi masa duk abinda ake buqata har saida jirginsu ya tashi snn suka bar airport din.
Ita kuma Madina dama kafin ta tafi ta bar number waya da address dinta wajen magret ta yanda idan mahaifinshi yazo nema ta bashi ta kuma roqi data sanar dashi yanda aka tilasta mata tafiya dashi don kar yaga laifinta.
A takaice wnn shine dalilinda yasa ta dakko Ayaan ta taho dashi Nigeria ta kuma raineshi tsakani da Allah tamkar itace biological mother dinshi sbd son da take mashi dukda yanda dangi da ’yan unguwa suketa gulmarta wai duk yanda akayi baban yaron ba indiye ne tunda dai ga kamanni nan yaron ya nuna bayan daga ita har mijinta kuma kowa yasan ba indiyawa bane…bata damu da cece kucen mutane ba da yan kudaden data dawo dasu ta fara business dinta cikin ikon Allah kuma ta kafu sosai.
Bayan shekaru biyu ta koma Kano gaba daya da zama sbd yanda har snn baa daina gulmarta ana kuma tsangwamar Ayaan ba ana kiranshi da suna shege..dama business din nata yafi karfi a Kano kowa kuma yasan dama Kano garin kasuwanci ne so kafin kace kobo business dinta ya sake bunkasa har ya zamana ta fara order kayanta da kanta ba sai tana siya wajen ’yan kasuwa ba.
A bangaren Ayaan kam babu wanda yasan ba danta bane tunda basu san labarinta ba snn kuma tsananin soyayya da shakuwar dake tsakaninta dashi bazaka taba cewa ba jininta bane domin shi kanshi Ayaan din bai sani ba…haka suka cigaba da rayuwarsu da kudaden da take samu na business dinta take kulada kanta da Ayaan da har yayi wayo ya shiga school, a wani bangaren kuma tana cikeda mamakin dalilinda yasa har yanzu mahaifinshi baizo nemanshi ba…kodai basu hadu da magret bane?…ko kuma number waya da address din nata ne bata bashi ba don tasan da ace ta bashi to tabbas da tuni ya dade da zuwa ya dauki dansa dan son da taga yana mishi ba dan kadan bane amma sai gashi har yanzu shiru kmr an shuka dusa…koda ta bar Kebbi tasan indai yaje address din data bayar a bashi to zaa kira a fada mata don address din gidan iyayenta ne kuma har yanzu akwai mutane a gidan shiyasa koda ta dawo bata damu ba don tasan idan yaje can kmr ya sameta ne.
Ayaan nada 6 years ta samu wani mutumi ya fito yana sonta yanada yara mata biyu matarshi ta rasu ta barshi dasu shine yake son yayi aure don ya samu mai kula masa dasu…shima babban ma’aikaci ne a Kano wanda yafi karfin duk wasu buqatu nashi dana ‘ya’yanshi harma yakan iya taimakawa dangi…bata boye masa komai dangane da Ayaan ba ta fada mashi ba biological son dinta bane don idan tayi karya ma tasan dole watarana gsky zata bayyana kanta…shima bai qita ba saima tausayin yaron da yaji ya kamashi ganin yanda shi Kuma kaddara ta baroshi da motherland dinshi ta kawoshi har Africa Nigeria…alkawari yayi mata zai kulada Ayaan tamkar danda ya haifa a cikinshi tunda dama ba da namiji gareshi ba nan kuma itama tayi alkawarin kula da nashi yaran tsakani da Allah ba tareda wani cutarwa ko zalunchi ba…haka kuwa akayi domin har bayan aurensu kowa yayi sticking to promise dinshi sun hada kan yaran sun rike gaba daya bazaka taba cewa ba ‘ya’yansu bane duka.
Bayan shekara daya ta haifi ‘yarta itama mace, bayan wasu shekaru ukun ta sake haihuwar wata macen ya zamana yaransu hudu kenan mata, biyu nata, biyu kuma na marigayiya matar mijinta sai kuma Ayaan da daga ita har mijin nata suke bala’in ji dashi kasancewarshi kadai ne namiji a cikin yaran…sbd tsabar so da kaunar da suke nuna mashi bai tashi sanin cewa ba sune suka haifeshi ba har saida ya gama primary, shima ta hanyar sunan da yake amfani dashi wato Agnihotri don koda Umma ta sashi a school bata canxa surname dinshi ba tace gara yayi amfani da surname din babanshi tunda taga su can indiyawan haka sukeyi..sai kuma yanda duk wanda ya ganshi ke cewa baiyi kama da kowa daga cikin ’yan gidansu ba.
Tun abun bai damunshi har ya fara damunshi, nan kuma iyayen suka yanke shawarar sanar dashi gsky don bai kamata su barshi a cikin duhu ba…kasancewar akwai yarinta a tattare dashi abun bai wani dameshi ba tunda dai ba wani banbanci suke nuna mishi ba dukda kuma bawai ya saba da ainihin iyayen nashi bane so sam bai damuba amma ita Madina da a yanzu yaran suke kiranta da Umma bata taba cire rai da ganin mahaifinshi yazo daukanshi ba amma har ya kammala secondary school babu shi babu alamarshi.
Wnn dalilin yasa tayiwa mijinta mgn ya shiga ya fita ya sama mashi scholarship da gomnatin kano ke bawa dalibai a lokacin shima yayi saa yana daya daga cikin wanda zaa dauki nauyin karatunsu zuwa Shri Mahatma Gandhi University dake babban birnin New Delhi a can India…tayi haka ne bisa yakinin cewa wata kila Allah ya hadashi da iyayenshi a can dukda ita so tayi ma ace makarantar a Mumbai take tunda tasan iyayen nashi ’yan can ne amma New Delhi dinma babu laifi tunda at least dai yana cikin kasar kila idan da rabo Alla ya hadasu da juna, lokacin shekararshi 19 ne kacal a duniya.
Haka sukayi masa dukkanin wasu shirye shirye ya tafi India bayan sunsha kukan rabuwa shida Ummanshi harma da sisters dinshi da suke bala’in son juna kmr siblings din gaske, basu san cewa wnn tafiyar ce zata bude wani sabon babi cikin rayuwar dukkaninsu ba.(Wnn knn)
6 years back, Shri Mahatma Gandhi University, New Delhi, India.
500 ne kacal zuwa 0013569116 Aisha Ahmad Tijjani Jaiz Bank sai tura receipt ta ***.