SANADIN HIJIRA

Chapter 02

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA🐫
               


                 By 

    💞Ummu Fadeela💞.



               *Chapter 02*

*AR-RAHMAN*





________Cike da nutsuwa take takawa sai faman kare jikinta ta ke da hijab din ta wanda ya sha jiki ya kode sosai, ruwan bula ne mai haske amma sai da ya koma fari tsabar yadda yake shan wanki.


A gefe guda kuma wani dattijo ne da bazai gaza shekaru sittin ba, dama dashi wani saurayine da shima bazai haura shekaru ashirin da takwas ba ke ta faman murmushi, farin ciki ya kasa boyuwa saman fuskokinsu tunda aka kira sunan Fanne Modu Bulama.


A can tsakiyar fili kuwa ko da Fanne ta iso microphone aka mika mata ta fara karatu cikin zazzakar muryar da Allah subhanahu wata'ala yai mata baiwa dashi, ita din mummunace kamar yadda da yawan mutane suka dauki wanda fatarshi take baƙi cewa mummunane ko da yana da wani sirrin kyau. Wannan baƙar fatar ta kan ɓoye bayyanan hakan, amma Allah ya mata baiwar murya da ko waye kai idan tana magana sai ka nutsu ka saurareta balle kuma idan tana karatun Qur'an.

Zazzakar muryarta ya karade illahirin wajen dama wajajen dake kusa inda iska ke kadawa yana daukar karatun da take yi cikin SURATUL-IBRAHIM, cike da kwarewa da bawa ko wanne harafi haqqinshi take rero karatun tana tuna fassaran ko wacce aya a ranta, ta ke Imani ya shigeta a hankali muryarta ta fara rawa shauqin Alqur'ani ya fara dibarta,(Malaman tafsiri sunce duk wadda aka karanta da fassarawa suratul Ibrahim amma baiji Imani a ranshi ba ko zuciyarshi bata rusuna ba, ya kamata a bincika imaninsa).Ba bu abun da kakeji a wajen sai Allahu Akbar, Masha Allah,Alhamdulillah ne ke tashi a bakin jama'ar dake wajen.
 

Tun tanayi muryarta tana rawa har kuka yaci karfinta, cike da rashin sanin abun yi kawai ta kama raira kukanta ta cikin loudspeaker din, sosai hakan ya yi tasiri a zukatan wadanda suke sauraronta, mai jawabi ne ya yi saurin amsar mic din daga hannunta tana share hawaye da bakin hijab ta koma wajen zamanta, Fanne ta Burge jama'ar dake wajen  ciki kuwa harda babanta Modu Bulama da yayanta ALMUHAJIR dake zaune a wajen.


Haka aka dinga kiran dalibai daya bayan daya suna gabatar da karatu, bayan kammala karatun kuma manyan malamai suka gabatar da laccoci masu matukar fa'ida kana aka bawa ko wanne dalibi da daliba satifiket da ke nuna shaidar sun haddace Alqur'an akayi addu'oi sannan aka fara gudanar da liyafar cin abincin da ko wacce daliba ta kawo manyan kuloli daga gidansu.

Tana zaune cikin kawayenta ana ta rabon abincin da ta tabbata idan ba don Allah ya sa tare da yar uwarta YAGANAH suka kammala islamiyyar ba ko tsinke bazata kawo ba, amma dalilin Yaganah an musu kyakkyawar waina da miya ga kuma white rice da stew da ya sha naman rago da yayansu ya kawo...

Tsaye ya ke jikin machine na shi mai kafa uku (Keke napep) ya harde hannu a kirji, sai kallonta yake with smile on his face.


Baki ne dai shima sai dai bai kai Fanne duhun fata ba, yanayin skin na shi kamar ka hada bakin shayi ne ya ji bournvita fiye da madara,a cikin yankin da yake idan za'a hadashi da wasu mazan, zamu iya kiranshi da kyakkyawa ajin farko kuma dan kwalisa. Zagayayyen fuska ne dashi mai manya manyan idanu girarshi cike take da gashi mai yawan gaske, yana da suma mai yawa da alama ya barshi ne dan gayu, yana da cikakken saje wanda ya taso daga kanshi har ya hade da gemun gayu da ya tara,bakinshi mai fadi ne yayinda lebenshi suka kasance bakikkirin kamar na mai shan taba/sigari,sai dai shi ko warin hayakin icce bai so balle na sigari,hallita ce kawai ta ubangiji.


Jikinta ne ya bata ana kallonta dan haka ta daga kai saitin inda take jin idanun na yawo a kanta caraff idanunta ya sauka a kan shi, murmushi ya sakar mata itama murmushin ta mishi a lokaci guda kuma ta mike ta nufi inda yake.

Duk takun da ta yi haka jikinta ke rangaji tamkar reshen bishiya a yanayin damuna. Da yawan mutane suna ganin tamkar da gangan take juya jikinta idan tana tafiya basu san itama Fanne bata son wannan yanayi ba kawai dan babu yadda ta iya ne da hallitar Allah.


"Ndaah Dubdi Ya Almuhajir," (Barka da yamma yaya Almuhajir).  Bai amsa mata gaisuwar  da ta mishi ba sai kafe ta da idanu da yayi,,, "Ya Muhajir!" ta kuma fada murya a shagwabe.

Firgigit ya dawo jin muryarta, "Uhmmm" ya fada sannan ya sake hannayenshi dake harde ya dan taso daga jinginan da ya yi da napep din yace, "You make us proud today, kin yi karatun da babu wacce ta yi kamarshi you did good recite with your golden voice keep up the good work dear,".sai kuma ya yi kasa da murya yana dan rankwafowa kanta kadan yace, "Na tabbata yayanmu ba za su taba samun matsala ba wajen karatun addini i swear".


Da sauri ta sa hannu tana rufe fuskarta dan sosai ya bata kunya yadda ya yi a karshen maganar.

"Wangina Ya Muhajir" (banaso)"! ta fada da muryarta dake kara narkar da shi da sake dulmiyashi cikin kaunarta... "Nikam ina so, kuma lokaci kadan ya rage mana da zan yi kaca kaca da wannan kunyar taki" 

A bazata naji maganar ta shi dan haka na dago a dan zabure, jinjina min kai ya yi alamar 'yesss'. Fakam fakam ta iso wajen kamar zata tashi sama, fuskarta a murtuke murtuk tana kallon Fanne a kasan ranta take ayyana wani abu da ita kadai ta sanshi, murmushi ne ya subuce mata tana dan kaiwa duqe kadan tace, "Yaya Almuhajir ko ka neme ni, bayan kasan kannenka biyu ne sukayi sauka yau din". Cewar Yaganah tana kallon cikin idanun Almuhajir.

Yaganah kyakkyawace sosai a fuska fara tas sai dai fuskarta cike take take da zane irin na kanuri akalla zasu kai guda tara gefe da gefe da kuma saman goshi manya manya. jikinta kuwa tamkar an daurawa tabarya zani tsabar rashin kumari, daga sama har kasa daidai suke bata da shape ko kadan sai tsawo.

"Oh sorry sister, kinsan idan ina tare da ita mance komai nake yi. So ya saukar kema kin yi kokari sosai amma ina fatan zaki kara zage damtse wajen gyaran tajweed na ki, ko idan mun koma gida Fanne ta dinga gyara miki ohk? Kun sakamu farin ciki sosai yau din muna alfahari daku". Zuwa lokacin Yaganah ta cika ta yi fam kamar zata fashe har idanunta ya fara kawo ruwa dan haka ta juya kawai ta bar wajen cike da takaici.


Bayan kammala ciye ciye hotuna suka daddauka saboda tarihi sannan kowa ya kama gabanshi.

Fanne da Yaganah suka shiga bayan machine din Almuhajir Babansu kuma da sauran tarkacen kanne da suka zo saukar su ka shiga wata tsohuwar motar Baba Modu kirar akori kura su ka koma gida.

Babbar anguwace da galibin mazauna wajen masu rangwamen karfi ne, sai dai ba a rasa daidaikun gidaje da masu hannu da shuni ke dashi a anguwar tsilli tsilli. Gaban wani gida su ka tsaya gidan yana da kyau ba laifi, tsarin gini ne irin na masu kudin shekarun baya, akwai get baki amma ya kwashi zamani dan haka garkame yake da katon kwado sai ta karamar kofa ake bi.

Cike da farin ciki su ka shiga gidan amma ban da Fanne dake dan raƙubewa a gefe zuciyarta na ɗan bugawa kadan kadan dan ta tabbata yau UWA bazata barta ba, ta san hukuncin yau mai tsauri ne a gareta.


Babban gida ne sosai mai dauke da sassa daban daban, direct sashinsu suka nufa wanda ya kasance ya fi kowanne sashi girma da kyau a gidan harda gidan sama yake dashi amma irin ginin da sosai. duk ya kode ya kukkuje, da dan hayaniyar su ta farin ciki yaran su ka shiga saboda sanɗar da Fanne ke yi hakan ya sa ta shigo a karshe. Caraff kuwa idanunta ya fada cikin na UWA dake zaune da wani shirgegen daron silba cike da ƙuli ƙuli da kuma jarkar farar mai a gefe sai faman karkaɗa ƙafa take yi. Suna hada ido gaban Fanne ya bada wani irin sautin bugu Dammmm, a lokaci guda kuma cikinta ya ƙulle ji ta yi tamkar ta juya  da gudu ta koma inda ta fito tsabar bala'in da ta hango a idanun UWA. Sai dai babu yadda ta iya,haka ta tako cikin sanyinta cikinta yana hautsinawa ta iso gabanta.

Gabadaya jama'ar dake wajen sun taru ne ana jiran dawowarsu dan taya su murnan sauƙa, amma ko tari babu wadda ya yi suna jiran ganin yau kuma wane irin tijara Uwa zata sauke a kan Fanne?.

"Na dauka daga wajen sauƙan ƙauyensu uwarki zaki koma ai munafuka mai baƙar fuska da baƙar zuciya. Wato baƙin cikin abun  da zan samu na cinikin yau ki kai min ko? To don kaza kazanki sai kin fitar da ƙulin nan yanzun nan sannan kar ki yadda ki dawo min da ko guda ɗaya cikin gidan nan, idan ma sata za kiyi ki kawo min kuɗina kawai na sa ni. Kin wuce kin ɗauka ne ko sai kin gama ƙare min kallo da idanunki kamar na mujiya a wajen?".

Durƙusawa na yi saman guiwata daga inda nike tsaye haɗe hannayena na yi duka biyu na ce, "Dan girman Allah Uwa ki barni in je Maaah ta sanya min albarka yau na yi sauƙa kafin in wuce tallar dan Allah Uwa!" na karishe hawaye suna sauka saman fuskata.

A hasale ta miƙe kafun ta iso gareni na tashi da sauri, dan nasan matuƙar Uwa ta damƙe ni yau sai na ya ba wa aya zaƙinta.

Baya baya na fara jikina na rawa ina cigaba da roƙarta, duk jama'ar dake tare a wajen yawanci matan ƙannen mahaifinane amma babu wadda ya samu liver ɗin cewa wani abu.

Hannuna naji an riƙe ta baya kafin muryar shi ta furta," Ala ro ri yi ne Uwa" (ki ji tsoron Allah Uwa). Cewar mahaifinmu da shigowar shi ke nan. Kwafa kawai Uwa ta yi ta koma wajen zamanta. Ba don mutanen dake tare wajenba ta tabbata sai ta sauƙe masa kwandon rashin mutunci. Modu Bulama kuwa jan hannun Fanne ya yi har jikin kafar tsohon benen dake wajen wanda zai kaika sama, a saman akwai ɗakuna guda uku,daga ƙasan benen kuma akwai ɗakuna uku suma, har lokacin jikin Fanne bai daina rawa ba,a bakin ƙofar ɗaki na farko ya sake ta, wufff ta faɗa shi kuma ya shige ɗaki na tsakiya.

Da sallama ta shiga dakin ta samu mahaifiyarta da take kira da Maah a saman wata yar yololuwar katifar da ta sha jiki hannunta rike da carbi tana lazimi, da gudu ta karasa wajenta gami da fadawa kanta tana dariya mai hade da kuka.Rumtse idanu Maah ta yi jin irin yadda Fanneh ta cukuikuyeta. 

Tsawon minti daya tana rike da ita tana dariya hawaye na sauka bisa kumatunta kafin ta dago, zaro idanu ta yi ta sake Maahh da sauri ta koma gefenta ganin yadda ta rumtse idanu, sai a lokacin ta tuna halin rashin lafiyar da Maahh din ke ciki. "Ki yi hakuri Maahh farin ciki ne ya mini yawa". Cikin murmushi da murya irin ta marasa lafiya Maahh ta kamo hannunta duka biyu ta rike cikin nata ta ce, "Nima ina cikin farin ciki mara adadi Fannetu nah ta haddace Alqur'ani mai girma. Ina rokon ubangiji da ya baki ikon aiki dashi ya kuma hadamu a cikin wannan alkhairi na babbar baiwa da ya yi miki ke da sauran dalibai, a duk inda kika samu kan ki Fanneh duk yanayin da rayuwa ta juya maki kada ki kuskura ki mance da alqur'ani, ki karanta shi kana kiyi aiki da ayoyin dake cikinsa Fanneh ina ji a jikina tamkar cewa rayuwata ta zo karshe ina ji a jikina na kusa tafiya in barki, zan barki cikin wahala da rashin mai kula amma ina farin ciki cewa Fannetu na jaruma ce, ina da yakinin cewa bazata taba yin kuka bayan babu ni ba zata tsaya akan kafafunta don haka nasihar da zan maki wadda na ke ji tamkar ita ce ta karshe Fanne duk tsanani kada ki kusanci zina. Ki kiyaye kan ki da zuriyarki Allah yai wa karatunki albarka Allah ya miki albarka kema, ya hada ki da sanyin idaniyar da za ki yi murmushi Ko babu ni".

Wani irin gunjin kuka Fanne ke yi tana sauraron Maahh, sai da ta kai aya Fanne ta rike hannayenta da karfi tana girgiza kai, 

"Maahh bazaki tafi ki barni a cikin wannan duniya mai cike da ababen tsoro ba, ke ka dai na sani ke na budi idanu na gani a matsayin kawata aminiyata baza ki mutu ba Maahh idan ba ke rayuwata zata zamto tamkar shuka ce da ba'a bata ruwa, kin ga ke nan bushewa zatayi karshe ta mutu ,da izinin mai sauke mana ruwan sama zaki haife wannan cikin lafiya nima in samu abokiyar shawara, dan Allah ki daina irin wadannan maganganu Maahh".

Murmushin da ya fi kuka ciwo Maahh ta yi ta ce, "In Sha Allah......"Kafun ta daura da maganar tata aka banko kofar dakin nasu, Uwa ta shigo rai a hade, "To uwar kinibibi da kwainane,me kika ajiyeta a daki kike kitsa mata munafuka dangin farar kafa dangin jaraba, ai ni naga jaraba tun da aka auroki a gidan nan muke ganin masifu da jarabta kala kala komai ya kare kamar an yi ruwa an dauke, kin talauta min miji to ahir dinki wllh ni kam nafi karfin ki talauta ni kuma kurwa ta kurrr haka zaki ganni ki kuma barni,"..

Ke kuma yar banza kin mike kin fitar min da sana'ata ne ko sai na babbalaki na zubar da banza?". Tun ba ta kai karshe ba Fanne ta mike jiki na rawa ta nufi waje kafin ta kai mata bugu dan karamin aikin uwa ne ta mata dan banzan duka kuma duk girman gidan babu wadda ya isa ya karbeta sai in tayi sa'a Yaya Almuhajir yana nan. 

Hawaye ne suka cika idanun Maahh na tausayin yar ta da wannan farar maghribar za'a daura mata tallah kuma tana gani babu yadda ta iya, ga yanayin gari babu tsaro kullum al'umma da fargabar yiwuwar yan ta'adda za su iya kawo attack su ke kwana su hantse. Haka tana gani Fanne ta fita Uwa ta bi bayanta.



Tafiya ta ke ta na sharar hawaye kan ta dauke da babban daron silba cike da kuli kuli, hannunta rike da jarkar mai. Cikin rashin sanin inda ta nufa ga maghriba ta kawo kai gaf ake da fara kiraye kirayen sallah.

Kamar almara ta fara jiyo karar harbe harben bindiga masu tsananin razanarwa gami da firgita duk wani mahaluki da ya ji wannan kara, cikin kiftawar ido gaba daya garin ya turnuke da kura kasancewar yankin kamar sahara ta ke, duk ta inda Fanne ta juya jama'a ne kawai ke gudun ceton rai kowa ya miki gabas sai ihu da kiran Ubangiji masu imani ke yi wasu kuwa tsabar firgici babu abun da suke fadi sai.

"Sun shigo sun shigo. Sun kawo hari Innalillahi sun kawo mana hari"

Abun kamar wasa karar harbe harbe sai karuwa yake yi ganin haka ne ya sa Fanne sakin daron da ke kanta itama ta runtuma a guje tabi ayarin masu gudu, dan zuwa lokacin ta fahimci yan ta'adda masu ikirarin jihadi a arewa maso gabas ne suka kawo musu hari kamar yadda su ke jiyo labari sun kai  hari a garuruwan da suke makwabtaka, yanzu haka ma garin na su cike yake da yan gudun hijira. 


Gudu kawai su ke yi, kowa ta kan shi ya ke haihata haihata, yayin da karar harbe harbe ke kara kusanto cikin garin, babu mai tuna komawa gida kowa daji ya durfafa cike da tashin hankali.



                ***ITALY*** 


*Leonardo da Vinci-Fiumicino Airport Rome city Italy*. 


Kasaitaccen filin tashi da sauƙan jirage na ƙasa da ƙasa dake birnin Rome a ƙasar Italiya, jirgin da ya taso daga birnin Barcelona na kasar Sifaniya (spain)ne ake bada sanarwar sauƙar shi. Ba bu jimawa bayan ya daidaita a kasa fasinjoji suka fara sauƙa, da yawan su yan ƙungiyar wasar ƙwallon ƙafa ne da suka zo buga wasan sada zumunci tsakanin Spain da Italy don fara shirye shiryen kofin duniya da za'a buga ba da jimawa ba, sai magoya baya da yan kallo da jirgin ya kwaso.

Shine ya fara sauƙowa, sanye cikin jessey (kayan yan ball) red and yellow kalar tutar kasar Spain,kasancewar rigar mai karamin hannu hakan ya bayyana zanen TATTOO daya cika ko wanne bangare na hannunshi daga sama har ƙasa babu masaka tsinke, kafar shi sanye da wasu shegun takalma irin na ƴan ball, fari ne tasss kamar babu jini a jikinsa irin dai farin turawa na asali, dogo sosai mai kakkarfan jiki, yana da faɗin kirji da manya manyan damatsa wanda ya taimaka wajen bayyanar da kirar majiya ƙarfi da Allah ya ba shi, ya na da dogon fuska mai ɗauke da manya manyan idanu kalar ash, wato baƙin cikin sun yi kalar toka toka da zara zaran lashes kamar mace da dogon karan hancin da ya sauko har kan zagayayyen pink lip na shi, gashin girarsa kuwa kaɗan ya hana su haɗewa da juna gashin kansa mai yawa ne sosai a tsatstsaye amma gefe da gefen an saisaiye shi daga tsakiya kuma a cike kamar za'a kitsashi, kyakkyawane ajin farko kana ganinshi kaga baturen asali. Captain JACK Smith Edward, Captain ɗin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Spain ɗan wasan gaba mai sanya riga lamba 7. 



        *THE STADIO OLIMPICO*

Filin wasan stadio olimpico,a yaren italy,ko Olympic Stadium a turance babban filin wasane mai girman gaske,shaƙe yake maƙil da yan kallo a ƙalla 70,000 yan wasan spain da italy ne ke fafatawa, sai dai har bayan minti talatin da farawa babu ƙasar da tayi nasarar jefa ƙwallo ko guda a raga. ko wanne bangare ya galabaita bayan dawowa daga hutun rabin lokaci amma babu nasara, yan kallo sun cika wajen da ihu kowa yana karawa kungiyarsa karfin guiwa, cikin haka ne Allah ya bawa Jack ikon karbe kwallo daga kafar wani, nan ya fara lilata yana wani irin juyi a wajen cike da kwarewa da sanin sirrin kwallo cikin kasa da minti daya ya yi baya baya ya fara kamar zai kwanta a kasa still ball din tana kafarshi, wani irin shoot ya bawa ball din ta mike dodar sai cikin ragar yan Italy ta shiga ta bugi raga ta kara fitowa daidai Jack ya kawo kafarshi kenan ya kuma bugunta da wani irin karfi, fiit ta kuma shigewa ciki duk yadda goalkeeper dinsu ya so tareta hakan bai samu ba.

Ihu magoya bayan spain suke yi iya karfinsu ganin cikin minti daya an sha kwallo har biyu. A tsakiyar fili kuma wani irin tsalle Jack ya yi yana bankare kirjinsa gami da hade babbar yatsarshi da kuma yatsar tsakiya, daya hannun kuma ya ware yatsu guda uku ya tankwashe biyu,yana bude baki da yin wani irin ihu mai karfin gaske, gaba daya jijiyoyin jikinsa suka mimmike yayin da ake iya hango har cikin makwogoronsa. Wannan shi ne sign na shi duk sadda ya ci kwallo, bare ma irin wannan ci biyu a bugu daya. Tuni wadanda su ka fahimci abun  da ya yi suka fara kwaikwayonsa su na ihun murna da fadin,' Jackie,jackie jackie'. Haka wasan ya yi ta gudana har aka tashi ba tare da daya bangaren sun rama ba.

Da wannan nasara ta ci biyu da babu 2:0 tawagar su Jack su ka samu wucewa kofin duniya.



Joseph  tarradellas barcelona-el prat airport spain.


sabanin tafiyarsu sanye da jessey, dawowar su ko wanne dan wasa cikin kayanshi normal ya dawo, filin jirgin cike yake makil da magoya baya sai daga musu hannu ake yi kowa burinsa su gaisa da yan wasan mussaman Jack da ya kasance captain kuma fuskarsa sananne ne a kowacce nahiya ta duniya, sanye cikin wasu riga da wando pencil farare sol sai wata bakar jacket da ya daura a kai ba tare da ya zuge zip na ta ba hakan ya bayyana rubutun dake gaban rigarshi da manyan baki kalan black an rubuta HANDSOME, kafar shi sanye da wasu arnan sneakers samfurin gucci kalar baki,hakama tsintsiyar hannunshi daure da wata makeken agogon azurfa itama samfurin gucci din daya hannun kuma daure da bracelet na maza mai kyau kirar Diamond wuyarshi makale da wata chain na zallar diamond ya sauko har kan kirjinshi sai walwali ta ke yi, gashin kansa ya sha gyara a tsatstsaye daga tsakiya, ash colour eyes nashi tarwai akan magoya baya sai daga musu hannu yake yi fuskarshi tamkar gonar auduga dan fara'a, da haka har suka isa jerin gwanon motocin da ya zo daukarsu zuwa club center na su dan halartar liyafar da aka shirya musu na murnar nasarar da suka kawo gida....














Ga dai Sojanmu mai Redlips, da kuma Captain namu mai pinklips, ga kuma Yayanmmu mai Blacklips,mu cigaba da bin alkalamin Uwar Fadeela don jin wanene Kaddarar Fanneh ke makale da tashi😍...
Follow this link to join my groups ***