SANADIN HIJIRA

Chapter 03

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA🐫

  By


Ummu Fadeela


Chapter 03






Cike da mamaki Badariya ta bi kofar da Al'ameen ya rufe da kallo. Dan kwafa ta yi hade da murmushi a fili ta ce, 

"Hali zanen dutse, da kanka za ka nemo ni ai"


Daga haka ta juya ta sauko. Bata sa mu Ummah a palon ba sai ma'aikata dake ta jigilar kwashe kayan da mahaukaciyar ta farfasa hakan ya sa ta  kuma hawa sama direct bangaren Hajja Fanta ta wuce, a cikin tsararren palon da ke saman ta samu Hajjah Fanta da ke goye da hannayenta a baya sai faman zagaye palon ta ke kamar soja a fagen daga, Saudat da gaba daya jikinta ya yi tsami da dukan da ta sha tana daga gefe sai faman cika take tana batsewa.


Shigowar Badariya ya sa ta fadin, "Small Mom mu je ki shafe ni da mentholatum, gaba daya jikina ciwo ya ke, na rantse da Allah wannan munafukar mahaukaciyar ba ta ci bulus ba idan ina numfashi a gidan nan." Ta karishe gami da juyawa zuwa balcony da dakunansu ke jere a wajen.

Da kallo Hajja Fanta ta bi su kawai tana girgiza kai. A dai dai lokacin ne kuma ta ji karan bude get da dirin mota, da sauri ta iso jikin window ta zuge curtains din hadi da lekawa,


Wani kyakkyawan farin dattijon balarabe ne ya fito daga bayan motar kirar royce rossey 2022. Sanye cikin shiga ta kamala da dattijantaka, farar shadda ce sol riga da wando da malum malum sai hula kana da takalmar fata a kafarshi, a kallon farko zaka fahimci tsananin kamar da suke yi da wannan Soja da aka kira  da Al'ameen. Alhaji FADLALLAH ALMISRY ke nan, hamshakin dan kasuwar da babu kamarshi kaf fadin yankin Africa mazaunin Nigeria, dan asalin kasar EGYPT (MASAR)

Curtains din ta sake ta na sauke ajiyar zuciya da nufar hanyar kofa ganin Alhajin ya tunkaro entrance na shiga. Kallo daya ya yiwa palon da ma'aikatan da ke ta jigilar fitar da kaya ya girgiza kai dan ya fahimci yau kuma an samu akasi a gidan nashi, ya na amsa gaisuwar da masu aikin ke mashi ya haura saman benen da zai sadaka da sama, babban bene ne mai fadin gaske a shimfide yake tamkar kwalta. 

Tafiya ya yi mai dan tsayi ya iso mararraba in da hanyar suka yi hannun riga, daya yabi dama can ne zai kaika side na Al'ameen da Thaufeeq, mazan gidan kenan wanda ya kasance bangare mai girman gaske babu abun da babu na more rayuwa a cikinsa, daya kuma yabi bangaren hagu, in da zai kai ka bangaren Hajja Fanta da yayanta mata,yayin da daya kuma ya cigaba da mikewa dodar direct zai kaika hawa na biyu inda nanne bangaren mai gidan a dama dashi akwai bangaren uwargidanshi Hajiya Safeenatu kafin ta samu lalurar tabin hankali bisa dole aka maida ita downstairs.


A daidai junction din suka ci karo da Alhajin, "Barka da shigowa yallabai" cewar Fanta, 


"Barka dai Hajiya yau kuma gidan ya hargitse mana ko?" ya tambaya still walking. Ba tace komai ba ta bi bayanshi har cikin hadadden falonshi mai kama da aljannar duniya. Kan daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun da suka kawata falon ya zauna yana cire hular kanshi hade da ajiye wani fancy leda da ya shigo dashi kan center table.


Gaban fridge ta je ta ciro bottle water guda daya ta bude wani glass cupboard dake wajen ta fitar da glass cup ta matso gareshi ta na zama a kujerar da ya ke, sai ta zama tamkar an ajiye gawayi ne kusa da farar auduga tsabar hasken dattijon balaraben        


"Sannu da hanya my yallabai, kun sha tafiya, ina fatan dai an dace?".

Ta yi tambayar tana mika mashi ruwan da ta tsiyaya cikin cup din. Amsa ya yi ya kai baki ya yi sipping biyu sannan ya yi gyaran murya, 


"Naga kamar motar Ameenullahi a parking space, yaushe ya shigo?" Ya jefa mata tambayar ba tare da ya bata amsar tambayar da tai mishi ba. Daidaita nutsuwarta ta yi ta na dan murmushi ta ce, "Bai wani jima da shigowa ba, da taimakonshi ma mu ka shigar da Safeenatu dakin ta".


"That's good, kira mini shi ta waya" 


Cewarsa yana janyo ledar dake gabansa.




Tun da ya dakatar da Badar ya sanyawa kofar shi makulli bai tsaya a palon ba direct bedroom na shi ya wuce, dakin ya tsaru iya tsaruwa, mai karatu ya kwatanta irin dakin da za'a samu a gidan hamshakin dan kasuwar da babu kamarshi a Africa baki daya, komai na cikin dakin ash colour ne kama daga kan round royal bed, mirror, sofa, centercarpet,da curtains gaba daya ash ne mai daukan hankali. 


Rigar Kakin dake jikinsa ya fara cirewa, Subhanallah wani irin murdadden damtse ne dashi da ya kara fito da zallar kyawun surarshi. Ga wasu six packs kawance Wanda ya kara fitar da faffadan kirjinsa mai cike da gargasa kwance yala yala. Ko ba a fada ba lallai jikinsa yana shan training. zama ya yi bakin bed din ya fara kwance igiyar takalmanshi cikin kasa da minti biyu ya cire gaba daya kayanshi ya rage daga shi sai boxer, bare skin nashi ya bayyana fari kal mai kwantattun gargasa lub lub da zafin nama ya fada toilet, bai jima a ciki ba ya fito daure da bathrobe kalar sky blue da wani karami yana goge saman kanshi da babu yawan suma zuwa fuskarsa bacci ne fal idanunsa dan kwana hudu kenan a jere basu samu bacci a wajen aiki, wannan ne dalilin dawowarshi gida dan ya dan runtsa kadan tun da ya samu free time. Allah Allah kawai yake ya iso ya kwanta sai ga abun da ya tarar a gidan da ya dagula mashi brain gaba daya ya yi fatali da illahirin baccin da ya kwaso. 

Yana cikin wannan tunanin ne wayarshi dake saman glass table na gaban sofa ta yi kara, ya tako cikin izza ya kai hannu ya daga ganin sunan Ummah na yawo saman sikirin din ya sashi kamawa ya kara a kunne sai dai bai ce komai ba,


"Dan Albarka Abeey dinku ya shigo yana bukatar ganinka" cewar Ummah jin Al'ameen bai da niyyar yi mata sallama balle ya ce wani abu, 

"Ohk" kawai ya ce tamkar bai son maganar ya yanke wayar. 


Sabanin three quater da armless rigar da ya fitar zai sanya kawai ya kuma fadawa closet na shi a gaggauce ya zura jallabiya milk colour mai shaking bayan ya sanya undies ya dan goga turaren ko mai bai shafa ba ya fita zuwa part na Abeey.


Zaune ya same su saman kujera Abeey yana fitar da wasu bottles na swan amma kamar magani ne a cikin su, saman rug ya zauna hadi da tankwashe kafafu ya ce, "Barka da warhaka Abeey" 

"Barka ka dai our RMO, likitan fagen daga" 


Abeey ya amsa da kalar tsokana,kara tsume fuska Al'ameen ya yi " Ah'ah ko allurar ta motsa ne soja marmari daga nesa?

"Ummah ta amshe zancen ganin ko murmushi  gogan bai ba yasa ta ja bakinta itama, komawa serious Abeey ya yi ya na daga bottles din da ya fitar daga ledar, 


"Wannan magani ne mai muhimmanci da na niki gari na yi tafiya mai nisan zango wajen karbar shi, duka na sha ne sau uku a rana za'ake bata, sai dai unfurtunately wata tafiyar kasuwanci ta gaggawa ta kamani a gobe zuwa Luxemberg dan haka Ameenullahi zan bar wannan magani a wajen ka, ka kula wajen ganin ta sha shi a kan ka'ida".


Da hanzari ya dago kai tun da aka fara maganar bai ce komai ba sai yanzu, "But Abeey she's under medications ai, bai kamata a bata irin wadannan abubuwan ba, I always say that matsalar Ummie na hospital ne ba gargajiya ba Abeey, dura mata these herbals zai iya mayar da hannun agogo baya a kokarin da muke yi na samun lafiyarta".


"Na yi wannan tunanin kafin yanzu Ameenullah, but ganin yadda condition din  ta yake kara zama worst yasa dole mu hada da na gargajiyar bamu san ta inda Allah zai dubebmu ya bamu waraka ba. Bata wannan magani ba wai yana nufin zamu daina using na asibitin bane, a hada duka biyu dan haka ka rike wajenka dan tafiyar safe zan yi gobe idan muna da rai". 


Ya fada ya na mika mishi ledar, rikewa Ummah ta yi tace, "Amma yallabai ba'a kyauta min ba, yanzu ko da ace zaman gaba muke da Safeenatu ni ba zan iya kula da maganinta ba tunda baka nan har sai ka ba Al'ameen mai tafiya wajen aiki? Balle ma zaman amana ne a tsakanina da ita" ta karishe fuskarta dauke da madaukakiyar damuwa.


"Banaso a takura miki ne Hajiya, naga abubuwa sun miki yawa, amma tunda kin ce haka sai ki barshi a wajenki ki kula da bata shi a kan ka'ida  Allah ya saka maki da alkhairi na kular da kike da ita." 


Ba komai Alhaji lalura ce tana iya fadawa kan kowa, Allah dai ya bata lafiya". Rumtse idanu Al'ameen ya yi ya bude yana jin wani irin daci a zuciyarshi na ciwon da Umminshi ke ciki. "Zaka iya tafiya Ummarka ta ce zata kula da maganin Allah yai maka albarka". 


"Ameen Abeey Allah ya huce gajiya ya kara girma" ya fada  a saman labbansa yana mikewa ya bar part din, walking slowly kamar ba wannan soja mai zafin namar ba ya koma bangarenshi, gabadaya baccin da yake ji ya gudu sai wani irin yunwa da tai mishi dirar mikiya a palo ya zauna saman kujera ya mike dogayen fararen kafafunsa bisa center table dake kusa da kujerar wayarshi ya dauka ya hau daddanawa kafun ya kara a kunne.



Sosai Saudat ta gasa jikinta da ruwan zafi time da suka shiga dakin. Ta fito daure da towel a kirjinta zuwa guiwa rub da ciki ta kwanta saman gado ko ina yana mata ciwo dan ba karamar duka ta ci ba a hannun Ummie, 

"Small Mom make sure duk wani lungu da sako dake jikina kin shafa masa man zafin nan kuma ki ballar min paracetamol, ina tabbatar miki idan na samu karfin jikina sai wannan matar ta gane shayi ruwa ne wallahil-Azeem bazan barta ba " ajiye wayarta datake ta faman daddanawa Badariya ta yi ta wuce kan mirror gami da dauko kwalbar Mega mentholathum ta fara yiwa Saudat massage da shi. A daidai lokacinne kuma wayar da ta ajiye ya fara tsuwwa kafun ta yi wani yunkurin dauka Saudat ta rigata kyakkyawan hoton Al'ameen ne tsaye cikin kakin soja hannunshi rike da bindiga ya yi pointing wani abu kamar zai yi harbi sai sunan "SOJANA" dake yawo saman screen din.

Wani irin dogon tsaki Saudat ta ja bakin ciki na turnuke ranta a kufule ta ce, "Dan jaraba, bazaki dau wayar nan ba, ni ban san me kike samu a wajen wannan mai fuska kamar an sulala karas din ba, dan iska mai zubin munafukai".


Wafce wayar Badariya ta yi daga hannunta a kufule itama ta ce, "Ah'ah gaskiya babu ruwanki da harkata ban shiga gonarki ba a lokacinda ki kayi aure har kika ajiye kwai a duniya wacce za'a gani a tuna dake bayan baki dan haka kar ki shiga tawa gonar a lokacin da nake tsaka da bukatar yin shuka a cikinta"


Cikin zafin nama Saudat ta mike ta yo kan Badariya kamar mayunwaciyar zaki ta ce, tana nunata da yatsa, "Karya kike wallahi, babu wanda ya isa in....." Cakk maganar tata ta katse sakamakon yatsar da badariya ta daura mata saman lip ta ce, "Shhhhtt, kada ki daga murya idan ba haka ba sai in sake ta fashe kowa ma ya rasa, kin san wannan kadan ne daga aikina".


Shirun kuwa ta yi Badariya ta janyo hular ta dake saman gadon ta bar dakin tana danna kiran Al'ameen da ya katse, a bangarenshi ma sai da kiran ta kusa yankewa ya kama "Food" kawai ya furta ya yanke kiran ba tare da ya jira jin abin da zata ce ba.Murmushi ta yi ta nufi hanyar downstairs domin hada mishi abincin.

Kitchen ta shiga kafun ta fara hada tray ta jiyo footstep da alamar magana kasa kasa, store ta shige da hanzari a daidai lokacin Ummah ta shigo kitchen din hannunta rike da bottles na maganin da Abeey ya bata na Ummie, "Shi yallabai duk yadda ka so ya fahimta ba zai fahimci in da duniya ta sa gaba ba.

Ga shi dai dan albarka Aminu yana ta kokarin fahimtar dashi illar wadannan magungunan akan rashin lafiyar safeenatu amma yayi kememe yaki yarda tun da dai tana kan magungunan asibiti ba zata sha wannan ba salon komai ya koma mana baya alhali ta fara samun sauki" Ummah ce ke magana ita kadai kamar zararrah lokacin da take bulbule gaba daya magungunan a cikin sink dake kitchen din,sai da ta tabbatar ta dauraye gorunan duka sannan ta debi coffee spoon uku ta dura a goran farko ta cika da ruwa kana ta jijjigeshi mai kyau ta ajiye a gefe,sai gashi ya koma sak kalar maganin dake ciki tun farko, haka ta yiwa sauran gorunan duka ta debe su ta fice daga madafar tana ta bambamin masifa kamar mai aljanu, fitowa Badariya ta yi tana share zufar dake tsatstsafo mata a fili ta ce, 


"Aunty Fanta,what are you up to ne?" abincin ta shirya a kan tray yadda ta san yana bukata ta wuce sama a hanya suka yi clash da Ummah, Ummah a ranta ta ce , "Oh ni fanta ina ganin talatar rayuwata, ina auren Uba,kanwata ta dage sai ta aure d'a".




Har lokacin yana zaune kafafunshi duka daure saman table hannunshi rike da remote yana kallon News a zahiri sai dai a badini hankalinsa ya yi nisa a tunanin halin da mahaifiyar shi ta ke a ciki, yana ganin wannan karon dole kawai ko Abeey bai so ya fitar da ita kasashen waje."SOJANA the food is ready, Ko anan zan kawo maka?" 


Ta tambaya tana pointing inda kafafun shi su ke, bai motsa ba kuma bai ce komai ba, a fahimtar yarenshi da ta yi hakan yana nufin 

"yess"


Dan haka ta koma saman dining da ta ajiye abincin first ta yi serving na shi komai ta kawo inda yake. 

"Sorry sojana, wannan tun breakfast ne, abincin ranar Ummie ta....."

Kallon da ya watso mata babu shiri ne ya sanya maganar tata katsewa ta koma kujerar dake opposite nashi ta zauna, ita tun da take bata taba ganin miskilin mutum irin Al'ameen ba, zaku iya zaman good two hours ba tare da ko tari ya yi ba, harde hannu ta yi a tsakanin cinyoyinta ta matsesu sosai kamar mai jin sanyi, zuba mishi ido ta yi tana kallonsa kamar zata cinye shi danye haka take ji.


"An sauya ni ne?"ta tsinkayi muryar shi a bazata. 


"Kai ai kullum cikin sauyawa ka ke kamar mai wanka da ruwan zallar gold". "Whats this Badar?" ya kuma tambayarta ba tare da ya maida hankali kan abun da ta fada mishi ba. Dube dube ta fara yi a gefenta don san gano abun da yake tambayarta akai amma wayam bata ga komai ba, kallonshi ta yi irin na son karin bayani ." 

A tsarin rayuwata banison farar mace as mata, abun ya yi yawa ni fari, Ummie fara, Abeey fari and my wife fear also? No i don't like it at all. Your darkness skin ya taimaka wajen falling in love with you, but yanzu na ga you've totally change daga Badar din da na sani zuwa something else".....

"Sojan..."Katse maganar tata ya yi ta hanyar daga mata hannu at the same time ya na sauke kafafunshi daga saman table din ya janyo abincin ya fara ci, bai kuma bi ta kanta ba,itama tasan bazai kara magana ba, ya ma yi kokari da ya mata magana mai tsayi har haka. Tana zaune har ya gama cin abincin ya zari tissue dake wajen ya mike gami da nufar bedroom na shi, wani irin hawaye masu dumi Badar taji suna kokarin kwaranyo mata amma ta yi ta maza ta mayar dasu a ranta ta tsinewa Saudat ya fi cikin carbi, ita ta zugata ta fara bleaching a cewarta me za'ayi da bakar mace, yanzu kai ya waye gashi tun ba'aje ko ina ba wanda ta yi domin sa ya ce bai so.

kwashe kwanukan ta yi ta bar part din cike da nazarin neman mafita.




              *Borno State, Bama*

Gudu kawai su Fanne ke yi ba ji ba gani, har sun fara fitar gari suna hango jeji yayin da majority ma sun shige cikin jejin suka hadu da convoy na sojoji cikin shirin yaki da motoci masu sulke, nan fa hankali ya kara tashi ciki ya duri ruwa wasu har sun fara jika wandunansu duk a zatonsu yan ta'addanne dan al'umma suna da labarin yadda suke tare mutane a hanya su sace su hade da basu training cikin dazuka a hada su da makamai, matan kuma suna maidasu matansu ta dole su dinga yi musu ciki suna haihuwa, mayar da jama'a sojojin suka fara yi zuwa cikin gari suna sanar musu ba nanne aka kawowa hari ba, garin da suke makwabtaka ne aka kaiwa hari kowa ya koma gidanshi ya kwanta saboda ana iya samun missing bullet ko ka shiga jeji ka hadu da wani abu mai cutarwa, kai yan ta'adda basu maka illah ba ka yiwa kan ka da kan ka illah.


Da taimakon sojojin jama'a suka yi ta dawowa cikin gari. Garin ya yi difff, ko kukan tsuntsaye baka ji kowa ya shige gida ya rufe ba abun da ke tashi daga nesa sai karar bindugu na batakashin da sojoji ke yi da yan ta'addan da suka shiga garin da ke kusa da na su Fanne. kwata kwata tsakaninsu bai fi naira dari ba a kan abun hawa wannan ne ya sanya aka ji kamar anan din suke.


A cikin gidan su Fanne kuwa gabadaya hankula sun tashi ta ko wanne bangare, kusan duka jama'ar gidan suna a tsakiyar gida babu abun da ke tashi sai muryoyi ana magana da yaren kanuri, daga tsakiya Alai Modu ne baban Fanne sai Mala Aisami Kanin Modu baban Almuhajir, sun rike Almuhajir din sai janshi suke shiko yana turjewa da fadin, 


"Baba ku barni in fita in nemo ta, za su kashe ta, zasu sace ta, jeji za su tafi da ita idan sun kama ta ku barni in nemota na ce," Sai fada yake yana nanatawa a bar shi ya fita ya nemo Fanne daga gefe kuwa mata mussaman mamar Almuhajir sai kuka take tana fadin kar ya tafi za su kashe shi yayinda Uwa ke gefe sai hada zufa take har wani kakkarwa jikinta ke yi, ita ba damuwar ta rayuwar Fanne ba a'a ita kuli kuli da mangyada dinta take yiwa rawar jiki.


Daga ciki kuwa Maahh kuka take tana ihu da ambaton sunan Fannetu, shi ke nan fannetu na na ra sa ta  na rasa Fannetu na duk yadda ta so ta mike dan ta fito hakan ya faskara sakamakon ciwon da kafafunta ke yi ga kuma ciki babba wanda ya hadu da manyantaka da kuma ciwo tun kan Fanne bata kara haihuwa ba kwatsam sai ga ciki ya bayyana a jikin ta, ja da duwawu ta farayi gwanin tausayi tana yi tana kuka ta fito bakin kofarta yadda zata sauka daga benen kuma ya zama tashin hankali, a daidai lokacinne kuma aka fara buga kofar gidan a hankali, cakkk dukkansu suka tsaya daga abin da suke yi hadda Almuhajir mai turjiyar a barshi ya fita kowa kirjinshi na dukan tara tara kar ma Uwa ta ji labari.


"Maahh, Babaaa, Yayaaaa". Zazzakar muryarta ta doki kunnuwansu daga waje,a sukwane mazan suka nufi kofa jiki na rawa Muhajir ya zare sakatar ya sanya hannu ya damkota da wani irin karfi ya dannawa kofar sakata, Fanne! ya fada wani dariya na subuce mishi, Alhamdulillah gaba daya jama'ar dake wajen suka ambata banda uwa wacce ta kamo zaninta dake kokarin faduwa kasa tsabar yadda zuciyarta ta tsinke ganin Fanne babu daro babu jarkar mai, a zabure ta nufesu amma karan da suka ji daga saman bene yasasu juyawa a rikice ganin Maman Fanne na gangarowa daga kafar benen sai tambul take yi gaba daya suka nufi wajen a guje, kara Fanne ta saki da fadin Maaaahhhhhh daidai lokacin da maahh ta fado kasa rib akan cikinta ko shurawa ba tayi ba......