Chapter 04
SANADIN HIJIRA🐫
by
💞Ummu Fadeela💞
Chapter 04...
Malam Bulama Gana mai turare, mutumin asalin jihar Borno ne a garin Bama. Allah ya azurtashi da y'ay'a Maza guda Biyar, Modu, shi ne babba a cikinsu sai Aisami, Abbagana, Baana, sai autansu Bamaina. Bulama da Mau mai dakinsa sun yi matukar kokarinsu na ganin yayansu sun taso da tarbiya da kuma hadin kai.
Alhamdulillah da taimakon Allah kuwa hakan ta kasance, kamar yadda muka sani jihar Borno tana daya daga cikin daulolin musulunci a wannan nahiyar dan haka yaran gaba daya sun samu ilimi na addini, inda bayan sun fara zama samari mahaifinsu a ajiyesu ya ce kowa na da damar fita ya nemi kudi, wanda kuma ke da burin zama ga fili nan ya yanka ya gina, ya fada yana nuna kafcecen tsakar gidanshi. Cikin sa'a gabadayan su babu wanda ya nuna sha'awar fita neman kudi sai Autansu Bamaina, haka ko akayi Bulama ya bawa kowa jari Modu dai ya ce irin sana'ar mahaifinshi zai yi wato sai da turare, saura kuma kowa ya kama sana'ar da ta kwanta mishi a rai. Bamaina ko ya tattara ya tafi birnin Maiduguri domin fara kasuwanci.
Sannu a hankali sana'ar turare ta karbi Modu, tun yana bin kasuwanni dashi a basket,har ya fara zuwa kasuwanni yana kasawa a teburi. Wasa wasa sai ga shi ya bude babban shagon saida turare mussaman Oil perfumes wanda mutanen yankin sukafi amfani da shi, haka Allah ya dinga daukaka shi har ya zama kaftanin yankin babu wanda ya kai Alai Modu shigo da turaruka, tare suka fara gini da kaninshi mai bi mashi Aisami inda Alai modu ya gina gidan sama, a wancan lokacin ba karamin mai kudi bane ke samun zarafin yin gini irinshi Aisami kuwa ya gina nashi daidai shi a gefe a rana daya sukayi aure bisa matsawar iyayensu Modu ya auri Uwani yar kawunshi ta wajen mahaifiyarshi wacce ake kira UWA, Aisami ko ya angwance da masoyiyarshi Bintu haka rayuwa take cigaba da tafiya shekara daya da rabi da aurensu Bintu ta haifo santaleliyar yarta nan fa hankalin Uwa ya tashi dama tana daga mata hanci cewa mijinta yafi na ta kudi,nan ta bazama neman maganin haihuwa ko ta halin kaka ne amma shiru, wani ikon Allah yar da Bintu ta haifa bata kai wata guda ba a duniya ta koma, nan fa hankalin Uwa ya dan kwanta.
Saidai bayan shekara daya ta kuma haihuwa shima dan bai zo da rai ba haka dai sadda Bintu ta yi haihuwa Hudu duka basa zama kafun ana biyar ta haifi danta *ALMUHAJIR*...Sosai hankalin Uwa ke tashe dan har lokacin shiru babu labari, a time din ne kuma ABBAGANA ,DA BAANA,suma suka yi gini a cikin gidan kowa ya yi aure,daga kan Almuhajir kuwa Allah ya barwa Bintu da suke kira Amma, sai da ta haifi yaya takwas cif a gefe guda kuma matan Abbagana da Baana suma suna ta hayayyafa gida ya cika makil da yaya amma Babu na babban yaya Modu, sosai shima hankalinshi ke tashi ga arziki ga komai hakan yasa shi tunanin karo aure amma Uwa ta yi tsalle ta dire ta ce bai isa ba idan dai tana raye,hakan kuwa ya hakura dan dama tun farkon aurensu Modu kamar yana tsoron Uwa duk abun da tace shi ake yi a gidan sauran matan kuma sami'ina wa aɗana dama suke binta dan itace matar mai kudi a cikinsu kuma itace uwar adashe idan ka mata rawar kai yanzu ne zata hanaka kuma ta tsaneka, idan ta tsaneka kuma sauran yan gidanta suma kaff janye maka za suyi yaran kuwa tsoronta suke dan masifarta shi sa kowa ke binta sau da kafa amma ban da Almuhajir.
Ita kuwa a duniya babu wanda take shakka kamar shi duk da kankantar shekarunsa ba dan kuma yana mata wani abu ba sai irin kwarjinin da Allah ya bashi....Babu wanda ya kara daga zancen karin auren Modu, ashe Allah ne bai saukar ba, lokacin aurenne bai ba da Allah ya ce za'ayi wata rana yaje wani daurin aure da aka gaiyacceshi aka samu tankargada bangaren maza suka ce sun fasa nanfa hankali ya tashi uban Amarya ya rikice ga jama'a an tara, kamar da wasa Modu ya mike jiki na dan rawa ya ce shi yana so a daura da shi abun ka da rantsewar rabo nan take aka daura auren Modu da Aminatu bisa sadaki da tsarin shaidu, sai da aka gama daura aure hankalin Modu ya dawo jikinshi ya fara tunanin yadda zai tunkari Uwa da zancen ya kara aure, ga shi yanzu babu manya dan iyayensu duka sun rasu zuwa lokacin.
Haka nan ya yi kundubalar sanar mata, babu shakka an gudanar da yakin duniya na uku a lokacin dan gaba daya zaman lafiya ya kauracewa gidan tun ma ba da Uwa ta kyallara ido ta ga Aminatu ta fita da komai ba gata yarinya kyakkyawa yar shuwa, iya kayan dakin da aka jere mata ma abun kallo ne. Nan Uwa ta kara daura damara ta damke kowa na gidan da kyau ciki kuwa harda amarya da angon ta rike ko ina sai baza mulki take yi, kowa rusuna mata yake.
Abun da ya kara dagula lissafinta shine bayyanar ciki jikin Aminatu, duk wani abun da ya kamata ta yi dan wannan ciki ya fita abun ya faskara Allah ya ce sai tazo, bakar wuya da izayar da take karba wajen Uwa bai hana Aminatu ta haifi kyakkyawar diyarta mai kama da ita sak kalar shuwa ba sai dai ta dauko kalar fatar babanta har ma ta d'ara shi a baki tun a jaririyarta, ranar suna yarinya ta ci suna Fad'ima ana kiranta Fanne. Wuya iya wuya Fanne da mamarta suke sha a wajen Uwa amma babu mai iya cewa ko uffan a kai, a dan tsakanin ne kuma aka bata kyautar yar dan uwanta mai suna Yaganah ta yayeta daga haka ta zama ya a wajen Uwa, wani tashin hankali kuwa shine na arzikin Modu da ke komawa baya baya tun bayan aurenshi da Aminatu abun bai kara ta'azzara ba sai da wutar nefa ta kama a store nashi wanda a daren ranar aka kawo kaya daga Saudia, tashin hankalin da ba'a sa ka masa rana hauka ne kawai Uwa ba tayi ba ta dinga tsinewa Aminatu da yarta, a cewarta FARAR KAFA gare Aminatu, cin mutunci kala kala take mata da kiranta da mai farar kafa ta zo ta janye mata arzikin mijinta(Wa'iyazubillah) Allah shi kadai ke ba da arziki ga wanda ya so a kuma lokacin da ya so.
Rayuwa ta yi wa Aminatu da Modu tsanani, dan a hankali duk wani abun da ke mallakinshi yake karewa har ya zamana abun da zasu ci ma sometimes wahala ke musu, nan fa wasu daga cikin yan uwa da dangi suka fara aminta da zancen Uwa cewa Maahh tana da farar kafa, inba haka ba mai yasa kafun ya aurota bai fada cikin wadannan iftila'in ba(Ya Salam Allah ka rabamu da jahilci).
A bangaren Uwa kuma sana'a take yi babu kama hannun yaro kuma sosai Allah ya sanyawa abun albarka ta ko ina kudi shigo mata suke yi,a wannan yanayin Fanne ta taso cike da rayuwar tsangwama mussaman kasancewarta mai bakar fata sosai duk duniya mutum uku ke kaunarta a zahiri,daga Maahh wacce tun akan fanne itama ko batan wata bata kara yi ba sai Babanta sai kuma yayanta farincikinta Almuhajir. Sau uku Fanne ke fita tallah na kayayyakin da uwa ke siyarwa a rana, a rayuwarta babu abun da ta sani daga tallah sai tallah and tallah again. Na safe daban rana daban haka ma dare.A wani dawowa da Almuhajir yayi daga makaranta inda yake karatun Digiri a gaban Baffansa Bamaina a Maiduguri ne ya sauya fasalin ya sanya ta a boko kana ya sanya ta a islamiyya ta hadda inda sauran yaran gidan ke zuwa, wannan ne ya kawowa Fanne sauki a rayuwa.
Maahh da Baba kuwa suka dinga sanyawa Almuhajir albarka Uwa kuma ta cika ta yi famm sai dai babu damar magana dan tsoronsa da shakkarsa ta ke.
Kwanci tashi asarar mai rai har Fanne ta fara zama yan mata ita da Yaganah dake kusan sa'arta, sai dai ita Yaganah a sangarce take, kana babu abun da ta mance bata dauko ba a halayen Uwa. A gaban kowa Almuhajir ke nunawa Fanne soyayya, tun bata maida hankali a cewarta tsokanarta yake mai zai yi da mummuna irinta, har ta fara sakin jiki sannu sannu soyayyarsa ta kafa rassa da jijiyoyi a jikinta ya zama ko wanne bugun numfashinta tare da soyayyarshi take bugawa, a yanzu haka ya kammala digirinshi na biyu a fannin larabci a jami'ar Maiduguri kuma ya dawo gida amma babu aikinyi, sanin kowa ne yadda aiki ya zamto a kasar nan daga wa ka sani? wa ya san ka? Sai nawa ka mallaka da zaka sai aikin dashi?.
Yanzu haka kasuwanni yake bi shima yana sana'ar turare kamar dai baban Fanne kafin ya samu karayar arziki.
Su Fanne kuwa sun yi candy sun yi saukar kur'ani. Soyayya suke yi mai tsafta ita da yayan nata, a bangaren Yaganah ma wani irin mahaukacin so ta ke yiwa Muhajir tana zama cikin dare ta yi ta kuka, tun uwa bata dau lamarin da gaske ba har abun ya fara bata tsoro, ganin da gaske Yaganah ke yi ta kwantar mata da hankali da fadin zata yi wani abu a kai, sai sannan Yaganah ta dawo nutsuwarta.
Har bayan shekaru goma sha shida kowa ya fitar da tsammani kwatsam sai ga wani ciki ya bayyana jikin Aminatu, wohoho ina wuta Uwa ta jefata ciki ko ta huta, amma wani irin mugun laulayi da Maahh ke yi wanda ya hadar mata da ciwon kafa haka kawai sai kafarta ta yi ta kumbura har ya zam ko sauka bata iyawa kullum tana cikin daki yanzu haka cikin yana a matakin wattanni shida zuwa bakwai ne.
______________________________
CIGABAN LABARI....
Da wani irin gudu Fanne ta fada kan Maahh dake kife a kasa ko motsi bata yi wani irin ihun kuka ta ke tana jijjigata da fadin,
"Ki tashi gani nan na dawo maahh, ki tashi in fada miki abun da ya faru, ki tashi maahh.(Nyiya raakina maahh). Cidakk taji an yi gefe da ita Baba da Baba Aisami da Ya Almuhajir ne suka daga Maahh dake kwance kamar babu rai a jikinta zuwa daya daga cikin dakunan kasa da babu kowa a ciki, ruwa aka fara shafa mata da nufin bata taimakon gaggawa tunda babu yadda za'ayi a fita a halin da garin ke ciki. Sai bayan kusan mintuna goma har sun fara fitar da rai sai ga Maahh ta kawo wani dogon numfashi sai dai idanunta basu bude ba sai bakinta dake rawa alamar tana son furta wani abu amma ta kasa.
Alhamdulillahi da aka dinga ambata daga cikin dakin ne ya sanya Fanne dake rusar kuka a waje mikewa da gudu ta nufi shiga dakin,da azama Uwa da ta gama jikewa da zufa ta cafko hannunta tana zare idanu ta ce, "Ina kika nufa munafuka annamimiya, ni dai naga jarabar duniya anan, uwarki ta talauta mini miji ke kuma kina kokarin ganin bayan tattalin arziki na, to baki isa ba maza maza ki fice ki dauko min kuli kuli da jarkar man gyada ta yanzun nan dan ban amince da kirga asara da wannan daren ba ehe".
Ba Fanne kawai ba illahirin jama'ar dake wajen sai da kirjinsu ya harba, sai dai an rasa ko mutum daya da zai samu kwarin guiwar cewa wani abu.
"Kin wuce kin kwaso min arzikina ne ko kina kallona tukuna?" ta kuma fada ganin ko motsi Fanne ba tayi ba sai ma idanunta masu kama da na mujiya ta bakin Uwa da ta zuba mata with shock, da kyar ta yi gathering courage ta ce, "Uw...U...Uwaaaa bindiga fa ga duhu".
"A'a atilare ne ba bindiga ba, na ce makaman kare dangi ne ba bindiga ba ja'ir..." Hada idanu da suka yi da Almuhajir da ya fito daga ciki ne yasa ta tsaida maganar tata. Ya tako har gaban Fanne ya tsaya ya zuba hannayensa duka a aljihun wandonshi.
"A ina kika zubar da kayan?" Kusancin da suka samu sosai ya hanata iya furta komai shi kuma kamar babu ruwanshi ya kuma tambayarta.
"Me kake nufi da ina ta zubar Muhajir?" cewar Mamarshi da suke tsaye cirko cirko suma.
"Xan dauko ne Ammah, bai kyautu a matsayinta na mace ta fita a halin da'ake ciki ba"
"Kaima baza ka fita yanzu ba ai rai bai fi rai ba Muhajir".
Nanfa Uwa ta juya ta dinga surfa bala'i daga karshe dai sai muhajir da babansa ne suka hada suka biyata kudinta dan Ammah ma taki yarda dan ta ya fita, sai da Uwa ta karbi kudin ta kirga sannan ta kalmashe su a bakin zani ta wuce dakinta. Wuff Fanne ta fada dakin da Maahh ke kwance.
Da daddaya matan suma suka koma sashen su fargabar dake ran kowa na dada ninkuwa.
***************
*ABUJA*
A cikin wani dan madaidaicin gidan dake wani anguwa da babu yawan kafa ta yankin. Mafi akasarin gidajen dake wajen sababbi ne, wata macece zaune cikin palo waya kare a kunnenta ,gyara zama ta yi jin ta samu wacce take nema a waya,
"Yauwa barka dai Hajiya Turai mun wuni lafiya? Dama akan maganar kayan nanne kunyi magana da Hajiya Babba kuwa dan gasu sun cika daidai yadda ake bukata kuma kowanne daga cikinsu cike yake har ya tumbtsa full options ne wallahi."
Dan shiru ta yi kafin daga bisani ta ce.
"To babu damuwa idan kunyi magana yanzun kya sanar min"daga haka ta yanke wayar tana taunar cingam kas kas kas kas. Daga bangaren wacce aka kira da Hajiya turai ma cikin sauri ta shiga neman Hajiya Babba, bugu biyu kuwa aka daga kamar dama jiran kiran ake,
"Hajiya Babba barka da, ya gida da iyali,?" lafiya lau Turai,ince dai ko akwai bayanine najiki cikin farin ciki"...Ai babban bayani kuwa Hajiyar Allah, yanzu Abu dilalliya ta ke sanar min kayan nan ya cika yadda ake bukata umarnin ki kawai ake jira hajiyar Allah".Ta kare tana murmushi...Ajiyar zuciya Hajiya Babba ta sauke kafin ta ce,
"Turai akwai matsala,inaga this time saidai a turasu Qatar ko Jordan ko kuma Bahrain or any Arabian country dai kawai, ina fadi maki mun samu problem a Italy na wadanda muka tura na dai sanar da agent cewa duk rintsi kada sunana ya fito to dama kinsan Spain ne target namu this time amma yanzu muna wanted any slight mistake zai iya sanyawa mu samu matsala, so is better a wuce dasu yankin larabawa yafi zama safety idan yaso next order su wuce can Spain din by then komai ya lafa".
"An gama ranki ya dade duk yadda kika ce haka za'ayi" cewar turai, Abu dilalliya ta kira bayan sun yanke wayar ta sanar mata duk yadda suka yi da Hajiya Babba, ta roketa alfarmar ta kara musu wasu kwanaki kafun azo a kwashi kayan, "A'a turai bama yi haka ba, sai dai a kara price, kin san dai zaman kaya a kasa kara raunata tattalin arziki yake yi"..."Baki da problem Abu idan na shigo zamu gama ne". Da haka suka yanke wayar kowa ranshi cike da murna.
**SPAIN**
A kalla ya zagaye wajan kusan sau takwas, babban filin wasa ne wanda ke dauke da daidaikun mutane dake ta kaiwa da komowa suna exercise duk da yanayi na azababben sanyin da ake ciki bai hanasu aikin dake gabansu ba.
Sanye cikin wasu bakaken tractsuit riga da wando na kamfanin Adidas wandon ya kai har kasa baki da dogon layi ja a gefe da gefe kana rigar tana da dogayen hannu da kwala kirar na sanyi itama da dogon layi ja a bisa hannun, kafarshi kamvas ce itama ta kamfanin adidas hannunsa sanye cikin aljihun rigar yake gudu a wajen yayin da gashin kan shi da aka yi wa askin tsakiya ke tashi yana kwanciya a duk motsin da ya yi. zufa ne keta wanke mishi fuska duk kuwa da sanyin da ake yi a kasar.
Ya zagaye wajan a kalla sau takwas amma ba shi da niyyan tsayawa. Wayarshi dake kuka a aljihun wandonsa ya sanya hannu ya fitar ganin Mom na shi ke kira ya sashi dan sassauta gudun da yake yana Sassafras ya yi picking ya kara a kunne, da muryarshi mai dauke da accent na turawa ya ce,
"Hii first love, good morning?" Sai mutum ya maida hankali sosai kafin ka fahimci abun da ya fada.
Daga daya bangaren Dattijuwar baturiyar itama ta mayar mishi cike da damuwa a muryarta "Hello,where're you Jack?" cakk ya tsaya daga sassarfar da yake jin yanayin Mommyn tashi.
"Whats happen Mom? Is there any problem?" still da damuwa ta ce,
"Just come back home as soon as possible, its Elisha she's try to commit suicide" ta karishe tana sakin kukan da ya kwace mata. Zaro ash colour eyes na shi ya yi da karfi ya ce, "Whatttt" ya yanke wayar ya nufi motar shi a dari da sittin, bangaren mai zaman banza ya bude gami da zuge wata jaka ya fitar da bottle water guda biyu sai small towel, dan tsuggunar da kanshi ya yi ya fara tuttula ruwan daga tsakiyar kanshi har saman fuskarshi sai da ya juye duka sannan ya sanya towel din ya hau gogewa daga bisani ya fada motar shi kirar yan gayu mara rufi daga sama ya bata wuta ya bar wajen kamar zai ta shi sama dan gudu.......
💞Ummu Fadeela💞
#Almuhajir
#Ameenullahi
#CaptJack
#2023