SANADIN HIJIRA

Chapter 05

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA🐫

                        By

              Ummu Fadeela



      



Chapter 05...




Gudu ya ke sosai duk da tashin hankalin da yake ciki hakan bai hanashi kiyaye dokokin driving ba, parking ya yi ya fito da sauri ya bude Entrance ya afka cikin gidan (mafi akasarin gidajen turawa babu katanga babu get haka nan suke abun su) 

Ba kowa a dan matsakaicin palon wanda babu wasu tarkace sosai a ciki kitchen ya leka nan ma ba kowa, da gudu ya haura sama ya dinga dube dube amma wayam wani babban labule da ya cinye bango guda na falon saman ya bude, door glass ne ya bayyana a wajen wanda shine madadin ginin dake wajen, a can kasa ya hangosu cikin garden a gefen Swimming pool Mom tana rungume da Elisha sai kuka ta ke yi.


Da wani sassarfan ya kuma saukowa ya nufi backyard na gidan tun bai karaso ba yake fadin, "Mom! What's wrong with Lisha?" Ya fada yana zaman yan bori a wajen ya kamo kan ta dake jikin Mom ya mayar zuwa cinyar sa yana tattara dogon gashin kanta zuwa baya cut face dinta ya zubawa idanu tsawon minti daya sannan ya dago yana kallon Uwar da gaba daya bata a hayyacinta, yana shafa gashin Elisha zuwa fuskarta yace.

"Mu wuce hospital kawai Mom, wai ma ya aka yi ne?" Ya fada yana ciccibar ta a kafada ya kamo Mom da kusan suman wucin gadi ta yi itama ta mike. a backseat ya kwantar da Elisha da har lokacin idanunta ke rufe, ya budewa Mom frontseat, maimakon ta shiga sai kawai ta fada jikinshi ta saki kuka.


"Ohhh no, first love stop it plsss komai zai dawo normal, kawai muyi saurin tafiya asibiti." 

"Do something Jack! ka yi wani abu plsss kar in rasa ya ta. Ka je ko ina ne ka samar mata lafiya, idan ba za ka iya zuwa ba ni zan je ko da ina ne matukar Lisha ta zata samu lafiya. This is thrice time take kokarin hallaka kan ta Jack help a innocent soul plsss plsss and plssss". 


Mom ta fada tana hade hannayenta waje daya bayan ta dago. Kar ki damu Mom, kawai mu wuce hospital din kar mu bata lokaci, za ta warke na miki alkawar......"Shiru ya yi a take kamar wanda aka dannawa pause da remote control yana bin gefe daya da kallo baki agape, jin ya yi shiru Mom ta baza idanu itama dan san gano abun da ya dauki hankalin dan nata a take haka. Arba ta yi da wata kyakkyawar budurwar baturiya fara kal mai murjejjen jiki sanye cikin wani riga wanda da kadan ya wuce mazaunanta daga kasa daga sama kuma hannun breziya gareshi hakan ya taimaka wajen bayyanar halittar kirjinta cikakku dam wanda rabinsu ke bayyane tarwai a waje. 

Jikinta mai maiko sai walkiya yake da daukan idon mai ganinta babu alamar gashi ko kadan a jikin nata kamar an mata wankan inji, kafarta sanye da kamvas fari sai gashin kanta da ya sauka har gadon baya.

"Hii Mom!" ta fada tana dagawa Mom hannu lokacin da ta iso garesu, kana ta rungume Jack da bashi wani dogon Kiss da ya sanya Jackiyarsa dagowa a take, wani irin yawu ya hadiye mukut ganin tana kokarin wuce gona da iri gashi suna sauri, da kyar ya yakice ta yana nuna mata Elisha dake kwance bayan mota da yatsa dan ya kasa iya furta ko kalma daya. Mom da tuni ta shige motar ta ke kara sanar mishi ya yi sauri, da dan gudu Nancy ta je bayan motar tana tattaba Elisha,

"Sorry Lisha, you will get well soon. Haka ta dinga babatu kamar rediyo Jack dake kokarin gyara zaman Jackiyarsa ya matso yace ta shiga part nashi ta jirashi suna dawowa yanzu, key's da yake mika mata ta amsa shi kuma ya shige motar yana ci gaba da gyara zaman wandonsa da hadiyar yawu.

Jugum jugum su ka yi dukkansu a gaban likitan dake cigaba da zayyano musu jawabin halin da elisha take ciki da idan ba'ai gaggawar daukar mataki ba komai ka iya faruwa.

Hankali a tashe Jack ya ce, "Mene ne mafita yanzu dr,?"dan muskutawa likitan ya yi yace, "Lallai dole a mata aiki cikin gaggawa kamar yadda nake sanar dakai kullum amma kun kasa daukar mataki. Idan ka fita zuwa AFRICAN COUNTRIES zaka samo maganin Elisha cikin sauki ka kawo mu mata aiki thats it!".Ba yau Jack ya fara jin wannan kalmar a bakin likitan nasu ba kusan kullum sai ya sanar dashi zai samo maganin cutar Elisha a Africa. African da bai taba zuwa ba babu country daya da kafarshi ta taba takawa a can, dago ash colour eyes na shi da suka koma brown tsabar tashin hankali ya yi yana kallon likitan ya ce, "But dr. Where in Africa? I know nothing about Africa, I even don't know where i am going to start?".

Ya fada da damuwa saman fuskarshi. Kuka Mom ta fashe da shi mai karfin gaske tana rawar baki ta ce, "Idan bazaka ba ni za ni, just tell me dr wanne kasa zanje a africa and ya zan yi in fara neman abun da ya kai ni". 


"Oh no first love, I don't mean to hurt you, iam just confused ne" "Yeah Jack dole ka zama confused tunda kai womanizer ne kana tunanin yadda zaka rayu a can babu girlfriend da zaka ke hutawa da ita ba,"ta fada tana zaro mishi ido, devilish smile ya yi, "You cought me well Mom," ya ce yana tura hannun cikin tarin gashin da ke kan shi.

Mom ta mishi farin sani, ba ya iya rayuwa babu mata ya riga da ya zama addicted to it, mata sune rabin rayuwarshi yayinda Ball da Mom and Elisha suka maye gurbin sauran rabin, shi idan ya ga macen da ta burgeshi sometimes ko da ba su samu kusanci ba sai Jackiyarsa ta mike. Wani yawu ya hadiye still yana lashe pinklips na shi tuna Nancy dake gida tana jiranshi....." Ki Ke NIGERIA Madam Mareyya i think zamu da ce, dan a can akwai mutane daban daban masu abin mamaki. Nayi imanin za mu samu wanda zai maye mana gurbin Elisha a can. Kawai kudi ki Ke bukatar tafiya dasu masu yawan gaske" Muryar dr ya dawar da Jack daga duniyar tunanin da ya afka."No, Dr ni zan je. kawai ka bani duk wani details da ya kamata".Cewar Jack cikin rawar harshe. Kasa kasa Likitan yayi da murya ya fara bashi bayani.........(A mana aikin gafara turawa ne ke magana,amma dole ayi maganar da Hausa saboda mu samu saukin fahimta) 


__________'''''__________'''''__________

Washe gari su Fanne suka tashi garin tsittt baka jin hayaniyar komai, kasuwanni, shaguna, makarantun boko da na islamiyyu da kuma tsangayu duk a kurkule, asibitoci kyamis kyamis duk a rufe hakan ya kara munana halin da jama'a ke ciki,sai a labaran safe a gidajen radiyo suka samu labarin ai sojoji sun yi nasarar kora yan ta'addan sun koma cikin jeji, duk da haka bai sa garin ya dawo normal ba harsai wajajen yammaci masu shaguna suka dan bubbude saboda jama'a.

Fanne na zaune gaban Maahh dake kwance bata san wanda ke kanta ba har lokacin bata a hayyacinta, ga asibitoci duk basu bude ba hakan ya kara ta'azzara yanayin halin da Maahh ke a ciki. Kuka ta ke yi tamkar ranta zai fita fararen idanunta sun yi jawur da su tamkar gautar da ya sha rana.

Ya roki Allah a zahiri da badini akan ya daga mata kafadun Maahh dinta. Kamshin turarensa na mussaman da shi kadai ta sani da irinsa duk fadin duniyar nan ta fara shaka wanda hakan ke alamta mata cewa duk inda yake to gab yake da karasowa gare ta, lumshe idanu ta yi ta bude a lokaci daya daidai time din da ya dage labulen dakin ya shigo bakinsa dauke da sallama, bashi da shamaki da ko wanne bangare na gidan hakan yasa yake shiga ko ina kanshi tsaye.

Da sauri na dauke kaina daga kallonshi duk kuwa da yadda zuciyata ke kara ingizani ga kallon nashi, tabbas Ya Almuhajir dan gayu ne, babu abin da yake daukan hankali na a gareshi kamar wannan black lips din nashi da kuma suman da ya tara bisa kanshi hannayenshi zube cikin aljihun jeans dake jikinshi idanunsa duka suna kan Maah.

"Har yanzu bata farfado ba?" Ya yi tambayar yana dawar da idanunsa a kaina. Kamar jira nake kawai na kuma fashewa da kuka harda sheshshseka, hannu ya daura saman goshinsa ya dafe yana furta, "Ya Allah, me aka maki kuma? daga tambaya sai kuka baby? Oya taso ki fadamin abun da ya sa me ki" ya kuma fadi yana zaro dayar hannun daga aljihunsa da mikomin wai in kama. Makale kafada na yi ina kuma mayar da kai kasa. "Ohk, ta so to ki sameni a waje ina jiran ki".

A kan second to the last step na staircase na hango shi zaune ya na latsa wayarshi samfurin samsung, har na zauna a dan gefenshi kadan da kusan minti daya sannan ya rufe wayar Yana mikewa ya mayar da wayar aljihu yaba harde hannayensa saman kirji. 

"Ehmmm me ya samu Baby na ta ke kuka haka, dubi kiga yadda kika bata min wadannan kyawawan idanun masu digon zaiba a cikinsu da wannan kukan mara dalili".

Da sauri na rufe idanuna dan sosai ya bani kunya yanda yai maganar yana dan rankwafowa da leka fuskata.

"Banaso Ya Muhajir". Na fada da muryar da ban san ina da ita ba."Allah kinaso Baby" shima ya fada yana katse min tawa maganar. Ganin a take har na dan sake ina dariya ne ya kuma gyara tsayuwa yana komawa serious ya maida hannayensa cikin aljihu which's dabi'arshice hakan ya ce, 

"Fannahhh!"dasauri na dago sakamakon wani irin bugawa da kirjina ya yi at the same time kuma gabana ya yanke ya fadi da wani irin karfi, ban taba jin ya ambaceni da hakan ba shi ya sa abun ya zo mini a ba za ta...

Fannah this life is too short, rayuwar nan ta duniya gajeruwace kuma cike take da abubuwan ban tsoro,mamaki,da kuma dadi atimes....." "Ah ni bana so Ya Almuhajir, ka daina dan Allah ba na so, haka ma Maahh ta fara fadamin gashi tun lokacin bata sake yimini magana ba ta na kwance, plssss Ya Muhajir ka da ka barni kaima, my heart can't take it anymore plssss" 

Na hade hannayena idanuna suna tsiyayar da hawaye."Ohk na ji bazan barki ba Baby wife, zamu yi aure ki haifo min yaya masu kama dake right?" ya tambaya yana dage min gira daya, ai da sauri na rufe fuskata ina murmushi tuna irin subul da bakar da na yi. "Thats amazing Baby, hakan na nufin na fara nasarar yaki da wannan kunyar taki a gareni...

Uwa ce ta fito daga dakin ta wanda shine a karshen jerin dakunan da suke a sama,daga na Maahh sai na Baba sai nata,dan leko da kanta ta yi dan jin kamar ana magana daga kasa,caraf idanunta suka sauka kan Almuhajir da ke harde da hannaye saman kirji ya zubawa Fanne da ke rufe da fuska da tafukan hannunta ido alamar suna cikin farin ciki. Da dan sassarfa ta koma dakin ta, wani dan kwanon silba mai kyau dake rufe ta dauko harta kai kofa ta kuma fasawa ta dawo dakin tana bubbuga kafar Yaganah dake ta sharbar bacci kamar matacciya,

"Kai Uwa! mutum yana bacci sai ki wani kama tashin sa, me zan miki kuma?" Yagana ta fada tana zumbura baki da goge gogen idanu har da turje kafa. "Dalla malama rufe mini baki, ke naga alama ma bakya kishin kan ki ni kika bari da wahala. Maza tashi ga can yayanku a kafan bene da wannan bakar jarabar, ki kai mishi wannan kuma ki tabbata ya ci....' 

Ai tun ba ta kai aya ba Yagana ta wantsalo daga saman gadon tana washe baki, jiki na rawa ta nufi gaban dirowar gado inda take jere kayan kwalliyarta turare ta dauka irin yar duwala dinnan na duri ta shashshafa a jikinta sannan ta karbi kwanon salalo salalo babu ko gyale haka ta fito tana ta gyara fuskarta,  

'Sannu da hutawa Ya Muhajir" cewar Yagana bayan ta iso garesu, "Ga wannan inji Uwa a baka rabonka ne dama ya rage" tana mika mishi kwanon."Tanks" kawai ya fada ba tare da ya kalli gefen da take ba, "Ko in kai maka dakin ka?" "No barshi zan wuce dashi"ya sa hannu ya karba. tunga Yagana taja ta tsaya cikin rashin sanin abun yi,wrist watch na shi ya duba kafun ya dago ya dubi Fanne ya ce, "Baby nan da awa daya dr Girema zai shigo ya duba Maahh, make sure kin shiryata ohk" daga haka ya juya rike da kwanon silban ya wuce sashensu, fam yagana ta cika kamar zata fashe ta koma dakin Uwa. 

Bayanshi na bi da kallo har ya bacewa ganina sannan na mike na koma dakin Maahh raina fal damuwar da ban dan dalilinshi ba........



Ko me Uwa ta ba Almuhajir?ni fa ba wai na gama yadda da wannan Uwar bane😒







💞Ummu Fadeela💞