Chapter 06
SANADIN HIJIRA
By
Ummu Fadeela
Chapter 06....
Bude kwanon Almuhajir ya yi bayan shigar sa dakinsa, ya dade yana kallon soyyayiyar naman dake ciki kusan yanka goma an badesu da yaji sai tashin kamshi su ke yi, a ranshi yana mamakin yadda nama mai yawan gaske har haka ya fito daga hannun Uwa, kawar da tunanin ya yi yana daukar yanka daya yayi bismillah ya kai baki, dama shi nama ne fav na shi a rayuwa, kafin ya ankare kuwa ya ci yanka shida yana kokarin daukar wani ne kaninsa ya yi sallama ya shigo dakin ya bashi sakon da ya aikesa tun jimawa mika mishi kwanon da sauran naman yayi ba dan ya isheshi ba sai ganin yadda yaron ke bin kwanon da ido.
Ya goge hannunsa da hankici sannan ya kama aikin daddana wayarsa. Bayan a kalla mintuna talatin Dr Girema da ya kira dan duba Maahh a gida ya shigo suka rankaya saman Maahh din, har lokacin Fanne na a zaune gabanta tamkar mai neman gafara, dube dube likitan yayi sannan ya mata karin ruwa da magungunan da ya ce zai hado mata a pharmacy na shi.
**********
*SPAIN*
Bayan likitan ya gama yiwa su Capt Jack bayani ya mike Jack yabi bayanshi dan zuwa a diba jininshi kwalba biyu da ake bukata yanzu dan daurawa Elisha.....A hankali yake driving maganganun likitan suna dawowa cikin kwanyarshi tas tamkar yanzu yake sanar dashi luumshe idanu ya yi ya bude yana dukan steering da karfi da fadin "Gosh". Da haka har ya iso gida, direct bangarensa ya wuce, babban bangarene a upstair,idan ka cire palonshi, komai dake bangaren kama da bedroom da toilets,kitchens da sauransu duk da Glass akayi su babu alamar gini a wajen komai glass ne, idan kana cikin bangaren nashi ji zakai kamar a cikin kwalba kake,wajen ya hadu iya haduwa, irin Glass dinnanne da duk wadda ke ciki zai iya ganin duk abun da ke waje,amma na waje babu abun da zai iya hangowa a ciki.
A palon babu wasu tarkace sosai,daga setin kujeru sai babban tvn bango,daga dama da tvn akwai wani shelf da akai na musamman a jikin gini da katako mai kalar gold, a cikinshi kyaututtukan karramawar da ya samu ne a wasanni mabambanta da ya halarta a rayuwarshi,ciki har da ballon d'or guda biyu kyauta mafi kololuwar daraja kenan a wajen ko wanne dan kwallo,Jack ya yi nasarar lashewa har sau biyu,sai sauran manyan gifts daya samu dake rataye a wajen a kalla zasu kai talatin da bakwai,kama daga Danyar gold,azurfa,tagulla.Daga daya gefen kuma hotonshi ne makale a wajen tun yana yaro dan kimanin 11years,Idanunshi ruwan toka su zasu fara bayyana maka shidinne,tsaye yake a filin wasa irin na cikin anguwa sanye da jessey,ya daure rigar jessey din daga gefen hannunshi na dama, yana rike da ball a dayan gefen sai Mom a gefenshi rike da Elisha kana wani baturen mutum da alama mahaifinshine dukkansu suna dariya. Daura dashi kuma wani hoton ne wanda a tsaye ya kusa rabin mutum Still Jack ne tsaye tamkar ka kirashi ya amsa cikin kayan yan kwallo rike da kofin duniya ya dan sunkuya kadan yana sumbatar kofin wanda suka yi winning shekaru hudu da suka gabata.
"Hiii" Nancy dake fitowa daga kitchen hannunta rike da coffee dake ta turiri ta fada ganin Jack yana tsaye rike da waist na shi yana karewa palon kallo, "Take this" ta fada tana mika mishi cup dake hannunta, tsurama ta idanu ya yi kafin ya dage kafada yana nunata ya ce, "You first". "Really?" ta tambayeshi. Bai ce komai ba sai dagata da yayi ya nufi hanyar bedroom na shi, "Hello Jack, its hurting" sai a lokacin ya lura da cewa kofin dake hannunta ya zubar mata a jiki, hannu daya ya sanya ya buge kofin ya tarwatse a kasa ya sa kai cikin hadadden bedroom din nashi da yaji komai na more rayuwa......
**********
Washegari kamar yadda Abeey yace jirgin karge sha daya na safe ne zai wuce da su Luxemberg, za su yada zango a Germany kafin su karasa can, karfe tara da rabi ya gama kimtsa komai yana zaune gefen gado wasu takardu yake shiryawa, Hajja Fanta ce ta fito daga closet jaye da dan madaidaicin trolley bag ta jingine jikin bedside, "Wai yaron nan bai fito ba har yanzu hajiya?"
"Sorry yallabai bara naje na duba shi kasan jiya har around 10pm ya shigo daga bikin abokinsa shi ya sa na matsu ka daura Thaufeeq akan harkokin companies dinnan Yallabai amma kamin banza, tun da shi dan uwanshi yana can wajen ceton kasa da rayukan jama'a shi kuma ya kamata ka daurashi bisa harkokin kasuwancin girma ka ke kara yi ya dace ka samu mai taimaka maka a cikin harkokinka".
Tsaida shirya takardun da yake ya yi yana zuba mata idanu da nazartar kalamanta kafin ya ce "Taso shi yanzu, na bashi just ten mins ya shirya mu wuce tare".
"As you say Yallabai" daga haka ta juya, tana fita Al-ameen yana shigowa, gaishe ta ya yi ta amsa cike da fara'a tana tambayarshi lafiyarsa ta wuce, dakin mahaifin nashi ya shige sakamakon kiran da yai mishi, a gefe ya zauna ya ce, "barka da safiya Abeey" "Barka ka dai Ameenullahi, ga wannan ka mini signing exactly irin na Safeenatu yanzun nan, i know kai kadai ne zaka iya," cewar Abeey yana tura mishi wasu tarin takardu gabanshi, sosa kai Al'ameen yayi yana dan tabe baki ya fara.
Yana signing din Abeey yana bashi labarin wani harkar kasuwanci da za su yi tare da wani kamfani dake sarrafa tumatur a Luxemberg, "Shekaru tara mu kayi muna neman wannan damar Aminullahi, sai yanzu Allah ya nufa suka ne me mu"....
Dago kyawawan idanunshi ya yi ya sauke kan fuskar Abeey, wani bangare na ranshi yana sosuwa a hankali ya motsa labbansa "Allah ya baku nasara a harkar Abeey".
"No Aminullahi!,ba wannan na ke son ji ba,so nake na ji ka ce zaka bar wannan aikin naka da ka tilastawa kan ka yin sa ka dawo ka taimaka min a lokacin da girma yake dada tunkaroni"....Sadda kai kasa Al-ameen ya yi ya ce, "A min afuwa Abeey". Daga haka bai kuma cewa komai ba, ajiyar zuciya Abeey ya sauke ya san ba zai ce din ba kuma yasan how this work meant for him dan haka ya ce, "Allah yai maka albarka, ya kare ka a duk inda ka shiga". Ameen ya furta a daidai lokacin da ya mike bayan ya gama signing din, "Let me freshen up Abeey, before ka gama kimtsawa, a fito lafiya" ya sa kai ya fice Abeey ya bishi da idanu.
*********
Sai da hajiya Fanta ta yi knocking wajen sau goma amma babu alamar za'a bude mata, tura kofar ta yi, luckily ta jita a bude dan haka ta sa kai cikin palon, ko ina na palon kaca kaca babu kyan gani, kada kai kawai ta yi ta wuce bedroom din da shima babu bambanci da palon komai a watse kawai daga saman gado yana kwance sai bacci yake yi kamar dan shi ya zo duniyar,a fusace ta jaye duvet din da karfin gaske, a firgice ya mike jin an ja kafarshi,idanunshi dake cike da bacci ya bude ya sauke kanta, "Ohhh Ummatah,kin yi kewata ko?". Ta shi dan Allah kafin ka fara yimin shirmen ka mara kan gado"..."Allah Ummah bana jin cin komai yanzu, just bacci kawai ki barni plss sai anjuma zan sauko in yi breakfast din".
"Oya get up joor" ta daka mishi tsawa, mikewa ya yi tsaye Ummah ta fara binshi da kallo, saurayine ba zai haura 26years ba, farine sol dogon gaske, bashi da auki ko kadan tamkar zai karye yanada doguwar fuska mai cike da kyau kana gashin kanshi mai yawane dake hade da beard har zuwa kan gemun shi na yan gayu da idan zaka kirga bazai fi guda ashirin ba.
"Ka wuce ka kimtsa cikin two mins Abeey dinku yana jiranka zaku wuce Germany yanzun nan, "What, Germany Ummah, no way aradu, ke Ummah kinsan irin takurar dake tattare da tafiya foreign countries da Abeey kuwa? matsala ke nan".Ya fada yana dan rankwafowa kanta kana yana jan gemunshi. "Ka wuce ka bani waje ko sai na yi kuli kuli da kai yanzun nan, kai babu abun da ka sani a rayuwar ka sai sharholiya, this trip is for your own benefit amma ka tsaya kanamin shashanci, yanzu kai yayanku baya burgeka? na ce baya burgeka?" ta fada daidai lokacin da take turashi bayin da karfi ta ce, "I just gave you two minutes ka fito" ita kuma ta juya saman wardrobe na shi ta sauke trolley bag ta fara shirya mishi kayan sawarshi a ciki........