SANADIN HIJIRA

Chapter 07

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA

                  

  By

Ummu Fadeela        





Chapter 07...




_Cikin kasa da minti biyar Hajja Fanta ta hadawa Thaufeeq duk wani abu da zai bukata a cikin trolley din ta zugeshi tana ajiyewa a gefe.

"Wai bazaka fito bane Thaufeeq?" Ta fada tana knocking bathroom door din tamkar yaro dan shekara bakwai ne a ciki.

"Ka hanzarta ka san Abeey bai son jira" ta fice daga dakin, zaune ta samu Abeey yadda ta barshi bayan ta koma ya zuba tagumi alamar ya fada duniyar tunani, "Yallabai tunani is not good for your health you know!" cewarta tana zama kusa da shi. Dan muskutawa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, "Haka ne Fanta, amma wasu abubuwan suna fin karfi ne, ko da kayi niyyar ajiye su gefe amma sai an samu akasin da wani abu zai kawo tarnaki a kasantuwar lamarin, dole in yi tunani shekaru tara muka kwashe muna neman business din ya tabbata ni da Mukhtar sai gashi kwatsam yanzu mun samu amma babu Mukhtar a duniya, ya sha wahala ashe bazai ci gajiyar wannan wahalar ba. Anyways, ga wannan"..Ya fada, yana mika mata takardun da Al'ameen ya gama signing."Na sa Aminullahi ya sanya hannu a kai, takardun asibitin da ya dage sai ya kai Safeenatu ne, amma ni a nawa ra'ayin na fi bukatar mu gwada na gargaijiyar nan amma kun dage, ki adana su wajenki idan na dawo by then ta kammala using magungunan da na kawo sai muyi shirye shiryen kaita asibitin."...

"Wani irin dadine ya mamaye zuciyar Ummah, cike da zumudi ta ce, "Allah ya kara girma Yallabai".


Suna zaune saman dining Ummah na serving Abeey breakfast Thaufeeq ya fito jaye da trolley nashi, daga kasa Abeey ya fara ganinshi, yana sanye da wani booth shoe mai girman gaske, sai crazy jeans da ya sanya gabadaya jikin wandon a bubbule kuma ya zazzago kasa har kana iya ganin boxer nashi dake ciki, sai farar shirt na kamfanin polo, fuskarshi makale da black space."I hope dai kanka kalau ko Thaufeeq?you mean ni zaka bi da wannan banzar dress din?" Abeey i though Germany zamu je, this is normal a...." katse shi Abeey yayi da tsawa, "wuce ka sauya kaya my friend". Juyawa ya yi yana kunkuni, wannan dalili yasa bai son bin Abeey ko nan da can.

Mikewa Abeey ya yi yana cirar tissue bayan ya kammala cin abincin, Thaufeeq da ya canzo kaya yana zaune cikin kujera sai faman danna waya yake yi duk yadda Ummah ta so ya yi breakfast ya ki ya. Dakin Ummie Mahaukaciya Abeey ya tunkara, kamar Ummah zatace wani abu sai kuma ta fasa ta bishi a baya, a daidai lokacin Saudat da Badar suka sauko daga sama, "Haan kai ba ka shiga duba Mahaukaciyar bane?" Saudat ta yi tambayar tana duban Thaufeeq, "Ahh rufamin asiri Anty, idan ki ka ganni a lahira to kai ni a ka yi, Ita wannan Ummien fa babu ruwan ta da sanin da tai maka yanzu ne zakaji shaka k......"Tsitt yayi jin footstep da kuma kamshin turaren da ya shako..

Sanye cikin kakinsa na soja ya fito, "Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen" Badar ta furta tana bin Al-ameen da kallo tamkar ta lashe shi ko zata huta da yanayin da take ji a jikin ta, ko bangaren da suke bai duba ba, gaisuwar da Thaufeeq ya jefo mishi ma da hannu ya daga fuskar nan a daure tamau kai kace a filin daga yake ba a gida ba.

"Sojana!" 

Ta kuma fada yana binshi da dan sassarfa ganin shima ya durfafi dakin Ummie.

A ciki kuwa time da Abeey da Ummah suka shigo cirko cirko suka yi ganin abun da Ummie ke aikatawa, ta sauke mattaress dake saman gadonta ta watsar da bedshets da pillows din a gefe bedside duk an yi daddaya dasu, tana tsaye gaban mazubin kayanta sai diba take tana watsar wa a fusace take fuskar nan kamar garwashin wuta dan jan da yayi.

"Subhanallahi, Safeenatu me kike aikatawa haka yau kuma?" cewar Ummah tana nufar Ummie, suuuuuuuu wani irin santsi ya kwasheta da masifar karfi ji kake garab, ta bugu da katakon gadon dake watse, "Hasbunallahu Fanta!" Abeey ya kira sunanta da karfi yana nufarta cike da rudani, juyowa Ummie ta yi ta yiwa Ummie kallon second biyar sai kuma ta girgiza kai ta juya tana cigaba da watsi da kayayyakin.

Da kyar Ummah ta mike har goshinta ya fara digar jini, da dingishi ta bar dakin, bata san me yasa ba duk sadda zasu hadu da Safeenatu sai ta yiwa rayuwarta lahani bata ji ba bata gani ba.

Tana fita Al-ameen yana shigowa tare da Badar dake binshi a baya kamar jela, da karfi ya rumtse idanu ya bude ya kuma saukewa a kan su, Abeey na tsaye kikam gaban Ummie ita kuma sai dukanshi take da duk abun da hannunta ya rarumo amma ko gezau Abeey bai ba, sai ma sanar da ita da yake zai yi tafiya yanzu jirgin su ya kusa tashi.

Temper na shi ne ya fara haurawa take idanunshi suka fara komawa ja jijiyoyin wuyarshi da na kanshi suna tashi, makogoronsa na hawa da sauka ganin yana tunkarar rasa control na shi kuma bai son yimata ihu kawai ya juya da wani irin karfi saura kadan ya bangaje Badar ta yi tsalle ta koma gefe, ya bar dakin.

Abeey sai da ya tabbatar ya gama mata jawabin zai yi tafiya sannan ya bar dakin.

Gabadayansu su ka mike a palon dan yiwa Abeey rakiya, a parking space suka sameshi yana zaune cikin mota a driverseat, kafafunsa duka biyu suna waje, "Aminullahi baka wuce bane?" Abeey yai mishi tambayar, "Zan sauke ku airport".

Jin abun da ya fada Badar ta yi tsagal Abeey zan maka rakiya airport, ta wutsiyar ido Al-ameen ya kalleta amma bai ce komai ba har Abeey da Thaufeeq suka shiga backseat Badar ta shige gidan gaba suka bar compound din, motar tsitt babu mai cewa komai har suka isa filin tashi da saukan jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, isar su da kamar minti takwas jirgin su Abeey ya daga,Al-ameen da Badar suka fito yana harba motar kan babban titi bai yi wani nisa ba ya gangara gefen titi yana kashe motar, "Sauka ki samu abun hawa".

Zaro ido Badar ta yi, "What? Sojana! taxi fa? haba inaa ba wannan maganar, kamar ni matar Regimental Medical Officer a ganni a taxi? haba mana Sojana wannan ba girmanka bane wannan gagarumin abun kunya ne a gareka a ganni cikin taxi".Ta fada cike da shagwaba da iyayi....Ta gefen ido ya kalleta, "Yaushe aka daura?" ya furta saman labbanshi.

"Ba'a daura ba amma an kusa ai, idan ba kai dake jan kafa ba ma ai da yanzu muna renon danmu na biy....."Wayarshi ce ta dauki tsuwa hakan ya dakatar da ita daga zancen da ta dauko."Elmustapha" sunan dake yawo gaban wayar.

Kwantar da kanshi ya yi jikin headrest na motar yana lumshe idanun wayar a kare kunnenshi. Tsurawa labbansa idanu Badar ta yi tana hadiyar yawu yadda yake maganar yana daukar hankalinta, "Heyy kana fa jina amma kamin banza" wanda ya kira wayar ya fada jin ya kwashe sama da 20second yana magana amma Al-ameen bai ce dashi komai ba, "Are you with me?" 

"Yeahh"

Al-ameen ya fada yana kuma gyara kwanciyar kanshi, "amma kai banza ne ya mutum zai bata lokaci yana maka magana amma ka kasa amsawa"

"Look Musty, kasan dai ni ba likitan mutane bane ko?"...Da sauri Musty ya ce, "Ehh na dade da sanin cewa kai likitan aljanu ne, itama kuma aljanar ce hurry up plss ka zo ka dubata, its urgent." yanke wayar ya yi yana wani murmushin gefen baki yai wa motar key suka harba titi.

Badar dai sake baki kawai ta yi tana kallonsa, direct Wuse zone ll suka wuce inda a nan gidan Musty childhood friend na Al-ameen yake, tare su ka yi komai a rayuwa tun matakin primary har matakin da suke kai yanzu, amintaka ne a tsakanin su na sosai har ta kai idan daya ya hana daya abu to ya hanu ke nan har abada shima Musty soja ne yayin da Al-ameen ya kasance Soja kuma Dr. 

Sabanin Al-ameen Musty ya yi aure shekaru biyar da suka gabata saidai Allah bai basu haihuwa ba sai kwanan nan matar tashi ke laulayi shi ne yanzu ma ya kira Al-ameen dan ya dubata.

Horn ya yi mai gadi ya bude mishi get ya danna hancin motar ciki, bai shiga parking lot ba a nan compound ya ajiye motar suka nufi cikin gidan Badar tana ta daure fuska kamar wacce akayiwa dole sai ta zo gidan, a palo suka samu Musty yana ta fama da matarshi Zeenat dake ta kwarara amai tun safe, duk abin da ta ci baya zama a cikinta.

Musty ma daure fuska ya yi ganin Al-ameen ya shigo tare da wannan matar da ya mugun tsanar ya gansu tare, abun babu tsari ko kadan duk da kasancewar Al-ameen yana da cikar sura, amma idan ka gansu tare zakayi zaton mamarshi ce ko yayarsa. Zama ta yi bisa kujera tana daura kafa daya kan daya 
Al-ameen kuwa ya nufi Zeenat dake kwance ranga ranga duk ta yi laushi, ta ba jikinta ya yi da sauri ya dauke hannunshi, 

"Her tempreture is high, me yasa ka barta a gida"...Ta ce bata son warin hospital i don't know what to do shi sa na kiraka"...Takarda da pen da ya gani saman center table ya janyo yana prescribing mata drugs da ya kamata ta sha. "ka samar mata wannan idan ta yi using na su for three days jikin bai sauki ba ku wuce asibiti."

"An gama likitan Aljanun jeji, yanzu muje ka kaini pharmacy in samo drugs din motata ta na wajen makaniki, dayar kuma tana barack". Komai bai ce ba sai nufar kofa da yai yana fadin "Allah kara lafiya madam" kada kai Musty ya yi yabi bayanshi, tsam Badar ta mike itama tabi bayan su.

"Miskili ka fi mahaukaci wuyar sha'ani" Musty ya fada a zuciyarshi yana bude gefen mai zaman banza dan tuni Al'ameen ya shige driver seat, hango Badar ta nufosu ne Musty ya ce, "Ga can yar lukutar ka, ni na rasa gane shin me ka gani a jikin matar can da har kake dating na ta Bro" ...Ba tare da ya kalleshi ba ya ce, 

"Ra'ayina"

Daga haka bai kuma cewa komai ba har Badar ta iso suka bar gidan, a wani Babban pharmacy ya sauke Musty sukuma suka wuce, sai a lokacin Badar ta fara mishi surutu kamar yadda ta saba dan itama yadda Musty ya tsaneta haka ta tsaneshi kawai sanine bai ba. 

Kiiiiii ta ji ya taka burki ya gangara gefen titi, "Sauka ki wuce gida" But Sojana nan..." .."I said get down" ya fada da karfin da ya sanya Badar balle marfin motar ta sauka babu shiri, tana gani ya ja motarshi ya wuce Barrack na su, dole sai waya ta daga tana kiran Saudat ta zo ta dauketa.


                       **********

                       FANNEH

Zaune ta yi gaban Maahh ta buga tagumi, ita kanta bata san abun da take tunani ba, jira take ruwan ya kare ta kira Yaya Al-muhajir ya cire mata kamar yadda ya tabbatar mata ba tare da Sallama ba Uwa ta fado dakin hannunta rike da wani leda mai dan girma taana mikawa Fanne cike da mazurai ta ce, 

"Tashi ki mika wannan gidansu lami yanzun nan"...Jiki yana rawa Fanne ta mike da ace zata iya, cewa za ta yi Uwa ta yi hakuri har ruwan da aka daurawa Mahh ya kare, amma tasan ko giyar wake tasha bata isa fadin hakan ba.

Hijab ta sanya tana karbar ledar gami da satar kallon gefen da Maahh ke kwance ta fice a dakin. A haraba ta hadu da Baba yake tambayarta inda ta tafi, "Na hana wannan yawon Fanne, kin san dai yadda yanayin garin nan yake ba sai an fada miki ba, kowa cike yake da tsoro sannan mutanen nan yan mata suke diba irin ki dan haka a kiyaye yi maza ki koma ciki."

"Uwace ta aikeni gidan lami Bab..." tun kafin in karisa ya katse ni da sauri "Oh to to yi maza ki hanzarta kije ki dawo, kada ki bata lokaci a hanya Allah ya yi miki albarka".

"Ameen baba" na amsa ina hana kaina tunanin dake son bijiromin akan mai yasa baba ya canza shawara daga jin cewa uwace ta aikeni.

Garin shiru babu hayaniya ko kadan kafin in fita daga layin namu na jiyo sawun mutum dab dab kasancewar babu zirga zirga sai hakan ya darsa tsoro a zuciyata, sauri nake zabgawa kamar zan kifa dakasa har na iso gidan da Uwa ta aikeni, sosai lami ta dinga fada akan me yasa za'a barni in fito yanzun nan, ni dai bance komai ba na juyo ina wani saurin har Allah ya kawoni gida ban hadu da ko tsuntsu ba balle ran dan adam. Kusan karo muka yi da Ya Muhajir ina shiga yana fita. 

"A rikice yake gabadaya, "Ina kika tafi a halin da gari ke ciki Fanne? ko mu dake maza kinga mun fitane, baki da hankaline? nace baki da hankaline?"

Ihu yake min sosai duk ya firgice, hakan yasa jikina ya dauki rawa wasu hawaye suna ballemin kamar bakin famfo.

A ta ke kuma jikinsa ya yi sanyi ganin yadda nake hawaye bance komai ba, hannayena duka biyu ya kama ya rike cikin nashi yana kallona, "Sorry Baby, bai kamata in miki ihu ba, but why zaki fita yanzun nan uhmmm? Ina tsoron kar wani abu ya sameki Fanne, I felt bad these days, bana ganewa kaina amma zan iya jure komai na sani banda rasaki bazan jure rasaki cikin rayuwata ba Fanne. (Nyiya dina man kolgin ba Fanne.) kema kada ki barni dan Allah.

Wani irin sanyi jikina ya kuma yi tamkar an watsa min ruwan kankara, kamar kadangaruwa haka nake kada mishi kai dan gabadaya kalmomi sun kauracewa bakina.

"Magana zaki min ba gyada kai ba Baby banason haka, da kyar na tattaro yawun bakina ina jin yadda kallonshi ke kokarin kassara garkuwar jikina na ce, "Nima bazan taba barinka ba Ya Muhajir, kai din rabin rayuwata ne idan ka rabu dani sauran bazai yi amfani ba, kai na ke so! da sonka na rayu zuciyata bata san kowa ba a duniyarta sai ka...." 

Makalewa sauran maganar ya yi ina wangale baki ganin abun da Ya Muhajir ke yi, wani irin kiss ya ke bawa bayan hannuna dake rike cikin nashi a bazata kuma a karon farko ciki rayuwarmu. A bangarensa kuwa ba dan ya san haramcin hakan ba babu abun da zai hanashi rungumeta a jikinsa dan yadda yaji maganganunta suna tasiri a ranshi.

Da karfi na janye hannuna, "Ya Muhajir Me haka?idan aka ganmmu fa".

Jajayen idanunshi ya dago yana kallona bakinshi na rawa, "Plsss Baby ko sau daya ne, only for today ki barni in rungumeki na yau kawai, yau kadai don't say no plsss" Ya fada a rikice yana tunkaroni, tabbas ya bani tsoro, wannan ba Ya Muhajir din da na sani bane ba, this is someone else. Yaganah dake makale tana kallonsu ne ta kwasa a guje tana kuka kamar ranta zai fita ta wuce dakin Uwa.

Ganin da gaske ya Muhajir yake yasa na shammace shi na gudu, dafe kai yayi, "Ouchhh Ya Ilahi, what came over me ne?" ya tambayi kanshi jin wani al'amari da bai san da shi ba yana taso mashi.

Kuka kawai Yaganah ke yi kamar wacce aka ce uwarta ta mutu, "Za ki yi shiru ki min bayanin abun da ke faruwane ko in wuce sabgogina". Cewar Uwa da Yaganah ta kwakume tana ta zabga kuka.

Cike da sheshsheka ta ce, "Ko ba Yaya Almuhajir bane na ganshi.......Gaba daya abun da ya faru ta zayyanewa Uwa har da kari.

Wani murmushi Uwa ta saki, "Ka da wannan ya dameki, hakan yana daga cikin shirina ina son ganin yadda zuciyar Aminatu zata buga ta fadi ta mutu a lokaci daya, maza ga wannan" ta fada tana mika mata wani karamin flask shayi ne mai dauke da sinadari, cikamakon naman da ya ci, wuce ki kai dakinsa ki ajiye, na ji yana tambayar Bintu shayi dazu ta ce babu za ai mishi anjima ki tabbatar kina ajewa kin fito kada ki bari yasha kina dakin."

"To Uwata abun alfaharina" ta karba ta wuce bangaren da dakunan mazan gidan suke, dakinsa ta shiga yana zaune bakin katifa dafe da kai, har lokacin idanunsa basu dawo daidai ba... "Yaya Ammah ta ce a kawo maka, "dago rinannun idanunsa yayi ya sauke a kanta take ya ga ta rikide ta koma masa sakk Fanne, murya a shake ya ce, "Zuba mini kadan,".

Da hanzari Yaganah ta kai duke ta fara tsiyaya mishi shayin dake ta tiriri cikin cup, "Ga shi nan yaya". Da hannun hagu ya karba hannun damar kuma yana rike da kanshi still.

"Shiga bayina ki wanke min" Ya kuma fada still bai dago ba wani irin dadi ne ya mamaye zuciyar Yaganah yau Muhajir yana mata magana harda sanyata aiki, tuni ta manta da hudubar Uwa na cewa ta na kaiwa ta dawo. Ta shige dan karamin bayin dake makale da dakin nashi ta fara wankewa with happiness.

Cup na shayin ya kai baki batare da ya damu da zafin da yake dashiba, a hankali ya lumshe idanu yana jin dadin kamshin sinadaran ginger, garlic, da kuma clove da akai using wajen dafa shayin suna ratsa harshensa har zuwa cikin makwogoronsa, kafin ya ankare ya shanye ya kuma tsiyayar wani ya kai baki.......