SANADIN HIJIRA

Chapter 08

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA*         


                  By

  💞Ummu Fadeela💞


Chapter 08...









Wani irin sarawa kan Al-muhajir ya yi lokaci daya ya saki kofin shayin dake hannunsa ya dafe kan, "Ya Ilahil-alameena". Ya furta yana kaiwa kwance saman katifarsa rub da ciki ya kwanta kanshi na cigaba da sarawa, wani irin feeling ya ke ji da tun da ya mallaki hankalinsa a matsayin cikakken Namiji bai taba tsintar kanshi a irin yanayin ba.

Karan bude kofa ya ji hakan ya sashi rumtse idanu da karfin gaske, "Subhanallahi, Ya Muhajir! Ba ka da lafiyane?"

Yagana da ta gama aikin wanke bayin ta fito ganin halin da yake ciki take tambayarsa lokaci daya tana daura hannunta saman keyarshi... Wani irin shock ya ji tamkar ta jona mishi electric a sassan jikinshi. "Ya Muhajir ko in kira Ammah? in kira Baba ne, baka da lafiya,Ya Muhajir ka tashi mana".

Tamke idanu yake yi da karfi dan har cikin kwakwalwarshi yake jin muryarta na mishi amsa kuwwa. Sosai Yaganah ta tsorata, ganin yadda yake ta mutsu mutsu saman katifar. "Ya Muhajir cikin ka ke ciwo ko, bari in kira Ammah da Baba" cewarta lokaci daya tana mikewa da ga durkuson da tayi....Tsakanin yaganah da Almuhajir babu wadda yasan me ya faru, kawai ji yayi wani abu mai kama da mayen karfe ya sarkafe hannunshi ya janyo Yaganah da ta fara tafiya rijibb ta fado saman katifar. "Help me Ba.....B..Bby, i am going to die helpme.Hel...P", shi da kanshi bai san me yake furtawa ba bare yaganah da gabadaya wutar jikinta ta dauke ganin Almuhajir ya koma kamar wani zaki ihu take son yi amma kamar wacce aka zarewa lakka haka ta zama saboda wani irin damka da ya mata yana lalubeta ko numfashi bata iya shaka da fesarwa, lokacin da ta samu dama kadan ta wage baki zata zunduma ihu aka samu rashin sa'a ya kame bakin da nasa, babu inda baya rawa a jikinsu baki daya sai dai na Almuhajir hadda fitar hayyaci.

              *FANNEH*

A nutse na mike har lokacin raina makale da damuwar halin da na ga ya Almuhajir a ciki dazu, sam baya cikin nutsuwarsa bana raba daya biyu da akwai abun da ke damunsa Drip dake makale jikin Maahh na leka saura kadan ya kare hakan yasa na nufi kofa domin kiranshi kamar yadda ya sanar dani cewa idan ruwan ya kusa karewa in kirashi ya cire mata. Kusan karo mukayi da Uwa, ina fita tana shigowa namar fuskarta har tana rawa ta ce, "Ina zaki je, ruwan ya kare ne?". "Ya kare Uwa, Yaya zan kira ya cire mata yanzu". Jiki na rawa Uwa ta waiga ta duba bayanta da gafe da gefenta sai da ta tabbatar da babu kowa ta ce, "Yi hanzari to, hanzarta kada ruwan ya kare ya fara zukar jininta, ki yi da jiki mana".Ta fada da dan tsawa ganin Fanne na tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki. Ta saman benen Uwa ta leka kanta tana lekowa taga kamar Yaganah ta na shiga sashen Baba Aisami. Ajiyar zuciya ta yi tana dafe kirji ta koma dakinta tana magana ita kadai, "Wato ita yaganah akan ta dawo ta sanar min abin da ya faru ta gwammaci ta shige yawonta wajen su Bintu, to ai shi ke nan tunda dai shegiyar ta tafi." gajab ta zauna bakin gadonta tana jin tsanar Maahh da ahalinta na kuma mamayar zuciyarta kamar wutar daji...A bakin kofar part na mazan na yi clash da Ammah rike da karamin flask na tea da kofi saman wani faranti, "Yawwa yar albarka ungo nan maza ki mikawa Yayanku, ya sa Fandau ta dafa masa shayi sai yanzu aka samu suga ita ko tana bayi maza mika masa, ya jikin Maah kuwa?"...

"Da sauki Ammah". Na fada ina amsar flask da plate din, na nufi ciki direct dakin Ya Muhajir na dosa sai dai bansan dalili ba kirjina na ji na bugu fat fat fat, dan dakatawa na yi ina shakar iska da fesarwa a lokaci daya sannan na cigaba da tafiya akan takalman Yaganah dake zube bakin kofar idanuna suka fara sauka, me ya kawo Yaganah nan har da shiga dakin Yaya? Na yi wa zuciyata tambayar dan ka'idarshi ce babu mai shigar mashi daki a yan matan gidan ciki kuwa harda ni, duk abun da kake bukata a bakin kofa zaka tsaya kayi sallama idan yana free ya fito. Tunanina bai gama sauka ba kunnuwata suka fara jiyo min wani irin gurnani mai hade da sambatu, kana a gefe guda kuma kuka da wata shakakkiyar muryar dake nuna an danne muryarce da karfin tuwo. 


Ban bawa kaina wata ga'ba ta yin tunani ba kawai na afka cikin dakin cikin rawar jiki duk a zatona Yaya ne bashi da lafiya, still na yi a wajen  tsakanin labule da kofa. Ya zage iya karfinsa da baiwar da Allah yai mishi ta mazantaka sai lalubar Yaganah yake bakinsa kuma yana cikin nata ihu take tana neman agaji amma baya fita zaka gane hakan ne ta yanayin yadda kafarta ke motsi, Almuhajir ya fara nisan da bai jin komai babu komai a gabanshi yanzu kamar ya iso inda yake da muradi ko zai samu ya rage abun da yake ji cikin Manhood dinshi.

"Yayaaaaa"

Sunan ya kufce daga bakina  a lokacin da flask dake hannuna ya fadi kasa ji kake tasss tusshhh fashewar flask din ya bada sauti tare da faduwar farantin dake dauke da kofi. Jikina yana mazari tamkar ana kada mini gangi wani irin zafi ya sauka saman kafata kana duhu ya fara mamaye gani na, tamkar daga bakina kamar kuma daga nesa dani sosai naji wani irin kara mai sautin gaske yana fasa ihu da kiran Yayaaaaaaaaaa! 

Gabadaya illahirin gidan lungu da sako babu kusurwar da bata dauki muryar Fanne ba na ihun da ta takarkare ta zabga ba tare da ita kanta ta san daga gareta ihun ya fito ba, tsaye take kikam kamar statue ta kasa gaba balle baya.


Har cikin zuciyarsa yaji lokacin da ta ambaci Yayaaa a hankali da kuma karan faduwar abu,sai dai duk yadda yaso rabuwa da Yaganah ya kasa ji yake kamar kuran karfene ke kara hade su, babu zato ya kuma jin wani irin azababben ihu still da muryarta wanda ya kusa balla mishi dodon kunne amma ya kasa jaye jikinsa daga na Yaganah balle ya samu damar gane abun da ke faruwa. 


Cike da razana Ammah da ta baiwa Fanne Flask bata kai ga isowa sassanta ba ta jiyo firgice rubuce saman fuskarta, zabura Uwa dake zaune saman gadonta har lokacin tana jiran fashewar tayar tayi ta kamo hanyan waje a tamanin har tana hada kafar bene bibbiyu. Wani irin bugawa zuciyar Maahh dake kwance ko yatsarta bata iya dagawa yayi da karfi  gaske, dan har cikin kunnuwanta taji ihun na Fanne.!
abun duka ya faru ne a cikin kasa da minti daya...!


A tsakar gida Ammah ta ci karo da Baba Modu da kuma Baba Aisami sai fuskar da batayi zato ba a lokacin wato Bamaina kaninsu Modu da shi kadai ya fita neman kudi a gidan sai matanshi biyu da tarin yaya kusan goma sha biyu dukkansu suna jaye da tafka tafkan ghana must go dake cike da kaya, kana ganinsu kaga YAN GUDUN HIJIRA, dan gabadaya jikinsu ya yi kaca kaca da datti da kuma alamar rashin nutsuwa dake tattare dasu da yanayinsu..!
Babu mai bukatar karin bayani dan duk sun ji ihun kuma sun ji daga inda ihun ya fito dukkansu. Rufawa Ammah baya kusan Kowa ya yi zuwa bangaren..!


"Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, Allahumma ajjirni fi musibati, wa'akhlifni kairan minha" shi ne addu'ar da na dinga nanatawa a raina kafin gani na ya fara washewa, dakyar na daga kafata da ta daskare a wajen na fara laluben inda labule da kofa suke..!
Baba Bamaina ne ya fara shigowa dakin sai Baba Aisami kafin Ammah sai Baba na, dukkan su hankali a tashe suka shigo amma gaba daya suka ja tunga kowa yana shiga rudani abun da idanunshi ke gane mishi. Uwa ce ta shigo a karshe tana zunduma ihu da fadin, "Me ya samu Fanne, me aka mata Innalillahi," har tana bangaje ni na yi taga taga zan fadi amma na turje ina dafe bango da karfi.


wani irin fizga Baba Bamaina ya yiwa Almuhajir da ke kwance jikin Yaganah har lokacin sai dai kwance yake kawai ya kasa motsi kamar matacce, akan kafafunsa ya tsaida shi kasancewarsa mutum mai zafin gaske bai yi wata wata ba ya kifawa Almuhajir wani irin mari, tun bai dawo daidai ba ya kuma kifa masa wani wannan karon sai da yaga gilmawar taurari a idanunshi, wani marin ya kuma sauke mishi take hancin Almuhajir ya fara tsiyayar da jini. 

Ihu Yaganah ta yi ta rungume Uwa da tayi mutuwar tsaye a wajen kwakwalwarta na kokarin tantance mata shin abun da idanunta suka gani gaskiya ne ko dai a duniyar mafarki take.?
Bangon da na dafe na fara bi ina takawa a hankali ina laluben hanya har na yi katari da kofa ba tare da na kuma musu kallo daya ba na fice daga dakin. Akan idon Almuhajir na fita ya juyo sakamakon marin da Baba Bamaina ya kifa masa ta daya gefen, idanunshi sun yi jajur, kamar zasu yi aman wuta, black lips na shi sai kakkarwa suke alamun ran Maza ya baci, fuskarshi sai digar ruwa yake dil, dil, dil, shi ba hawaye ba baza kuma a kirashi zufa ba dan yawansu!


Bana iya gane meke faruwa na dai ga jama'a da yawa tare a kofar shigowa bangaren su Ya Almuhajir, uku uku nake gani kamar wacce ta shawu ina layi na haye samanmu. Gaban Maahh na zube bisa guiwata abun da nake ji cikin zuciyata na kuma hauhawa kuka na ke son yi amma hawaye sun ki fita, tabbas abu  ya sameka ka zubar da hawaye ma ba karamar rahama bace, duk yadda muminar zuciyata ke lissafo min in yiwa Ya Muhajir Uzuri, karamar kwakwalwata ta kasa bani hadin kai, turmi da tabarya na kama su, wannan wacce iriyar bakar rana ce, tabbas da ina da iko da na gogeta daga cikin zanen kaddarata, kamar mahaukaciya na kamo hannun Maahh dake kwance ta zuba min idanu tana son tambayata me ya sa me ni amma ba baki sai idanu kawai, drip din na yi kundunbalar cire mata ganin ya kare cak har ya fara janyo jininta.


Kamar wacce aka tsikara na mike zuwa gaban mirrorn dake dakin tsayawa na yi ina karewa kaina kallo daga sama har kasa, "Dama yaudarar kan ki ki ke Fanne, me mutum kamar Almuhajir zaiyi da ke, jibe ki mummuna dake kamar a kife ki da kwarya, ga dai yaganah farar mace kamar ka saceta". Zuciyata ta fada sai a lokacin naji wani irin kuka mai karfi ya taho min, hannu nasa ina danne bakin da karfi, tabbas ya muhajir daman wasa yake min ni kuma na dauka gaskiya ne ashe ma wasa yake da zuciyata. 

Jikin Maahh na koma ina kwanciya a gefen ta na daura hannuna saman tirtsetsen cikinta. Rumtse idanu na yi da karfi ina bawa kaina karfin guiwa wasu hawaye masu zafi suna gangaro min a karon farko, yadda kirjina ke bugawa haka na ke iya jiyo na Maahh yana bugawa da karfi karfi.


A can dakin Almuhajir wani marin Baba Bamaina ya kara yunkura zai kaiwa fuskarsa Baba Modu ya yi saurin rike hannun na shi, "Ba'a hukunci da duka Bamai, kuma ba'a hukunci cikin fushi, Annabi salallahu Alaihi Wasallam,ya ce,'(kada kuyi fushi, kuma kada ku yanke hukunci cikin fushi") ka samu nutsuwa tukunna Bamai, mu bi komai a hankali".


Juyawa Ammah ta yi tana share hawaye ta fita daga dakin, wannan wacce irin abu ne haka ke faruwa ga dan ta kamar a shirin film,Almuhajir dinta mafi soyuwa cikin zukatan kowa a gidan shi ne aka samu kwance saman wata mace? Innalillahi take nanatawa har ta fito, bata bi ta kan taron matan gidan da yaya har da su Yakura da taron iyalansu da shigowar su gidan ke nan al'amarin ya faru ba ta wuce sashenta tana matsar kwallah.


Fitar Ammah ne ya dawar da Uwa daga duniyar suman wucin gadin da ta afka. Zabura ta yi tana rike hannun Yaganah sosai ta ce, "Na shiga uku Allah ka dube mu, wanne sababi nake gani haka ni Uwa? iskanci da rana tsaka Muhajir? kuma a kan yata? lallai idan ka saba lalata yayan mutane ka zauna lafiya to yau ka tabo inda ya fi karfin ka. Na ce ka tabo inda ya fi karfin ka Muhajir!.


Ta fada da wani irin sound mai karfin gaske, kafin jama'ar dake wajen su ce wani abu ta figi hannun Yaganah suka bar dakin bakinta har yana kumfa tsabar bala'i.. "To munafukai algungumai wadanda ba za su ji kamshin aljannah ba, me kuka taru kuke min a nan? na ce kuna me anan matsiyata kawai ohh na gane, kun zo...." "Uwa!" Baba modu da fitowarsu daga dakin ya ambaci sunanta a hankali ganin yadda gabadaya ta rikice.

A fusace ta juyo ta fara balbale shi da bala'i tun tana magana da hausa har ta koma kanuri duk ta fice a hayyacinta wani irin zafi take ji mai yasa abun zai koma kan Yaganah bayan akan Fanne ta ci burin ya kasance?.


Simi-simi taron mutanen dake wajen suka fara watsewa don duk cikinsu babu wadda batayi haddar rashin mutuncin Uwa ba. Fuuu ta kuma figan hannun yaganah dake ta rusa kuka suka haura sama still bata daina karanto bala'i da jifa'i daga bakinta tana mulmuloshi kasa ba.


Yarafff Almuhajir ya koma da baya ya fadi saman katifarsa hannu yasa ya shafo jinin dake tsiyaya bisa hancin sa a lokaci daya kan shi yana wani irin matsanancin sarawa still wannan feelings dake yamutsa jininsa bai barshi ba, ji yake kamar ya ci Babu.
Pillow ya dauka ya matse a tsakanin  cinya da cikinsa ko zai samu sassaucin abin da yake ji." *Fanne*" Zuciyarshi ta ambato sunanta, zabura ya yi yana mikewa ihun da ta kwala dazu yana dawowa cikin kunnensa as fresh as new, tabbas yaga gilmawarta lokacin da take fita, dole ya je ya gan ta ko kowa zai juya mishi baya yasan ita za ta fahimce shi. Da wannan tunanin ya nufi hanyar fita...!


#Redlips
#Blacklips
#Pinklips