SANADIN HIJIRA

Chapter 9_10

by @ummufadeela01

*SANADIN HIJIRA*



Chapter 9/10.


Koda kowa zai gaza fahimtar sa ya san Fanne itace mutum ta farko da zata fahimce shi.

Har ya iso bakin kofa sai kuma ya tsaya yana contemplating anya zan iya fita kuwa? Ji ya yi kamar duka kunyar duniya aka tattara bisa kanshi sai yanzu abun da ya faru yake dawo mishi, ya tabbata babu wanda zan iya hada idanu dashi a gidan.
Saman katifarshi ya dawo yana kwanciya ba dan yana so ba, sai dan bashi da za'bi face hakan...!


Na dade kwance jikin maahh zuciyata tana radadi da kuna, da haka har bacci ya d'auke ni ban sa ni ba, saukar numfashi na dake alamta na yi bacci shiya ba Maahh sassauci tana ta addu'a a zuciyarta dan shi kadai ne gatan da za ta yiwa Fanne a yanzu, kullum damuwarta shin wane hali zata bar Fanne a ciki bayan kasa ya lullube idanun ta? Ita bata da kowa a yanzu, dama iyayenta yan cin-rani ne suka samu wajen zama a Bama kuma ita kadai suka haifa, mamarta lokacin haihuwarta ta rasu, babanta ko bayan aurenta ba jumawa shima ya ce ga garinku, yadda take rayuwa ita kadai cikin kunci a yanzu haka take hango rayuwar yarta abar alfaharinta a nan gaba....Kaico Maahh ko wanne bawa yana tafiyane akan zanen kaddararsa. Idan Allah ya hukunta wanzuwar wani abu akan wani bawa, babu makawa sai wannan abu ya kasance, sai dai addu'a ta kan rage kaifin tasirin mummunar kaddara...!


Har suka fito nan tsakar gida Baba Bamaina bai daina fada da hargowa ba duk cikin yan uwansu yafisu zafin zuciya, sai da kyar Baba Modu ya bashi baki yayi shiru sai kuma ya fara basu labarin yadda yan ta'addan B*k* H*r*m suka yi kaca kaca da garinsu suka kona gidaje da shaguna suka kwashi dukiya da yan mata, yanzu haka garin babu wani mahaluki da ya rage dan sun karbe garin har sun kafa tutarsu a ciki nan da kuka ganmmu daga mu sai rayukanmmu muka tsira, cikin jama'ar dake wajen babu wanda hankalinshi bai tashi ba da jin kalaman Bamai. 

"Yanzu Bamai kana nufin yan ta'addan ke da iko da garin yanzu?" cewar Abbagana. "Sufa yaya, ai hatta sojoji wasunsu gudu sukayi, kowa yana ta kansa abun ya wuce yadda duk kuke zato. A dakuna uku dake kasan Baba Modu aka budewa su Bamai dama babu kowa a ciki tun yana da arziki ake jibge amfanin gona a cikinsu...!


"Kin rufemin wannan shegen bakin naki mai kama da kofar gari ko sai na ciremaki hakora?" cewar Uwa a mugun fusace tana kallon Yaganah dake ta kuka tana sharbar majina, "Munafuka ina ce sai da na ja kunnen ki da kina bashi ki juyo, amma dake kunnen kashi ke gareki ki ka maida ni shashasha wacce bata san abun da take ba, to wa gari ya waya?"


"Ni dai gaskiya Uwa ki barni, ai ba haka kema mukayi dake ba, cewa kika yi maganin da zai soni ne amma kawai ni daga bashi sai ya turmusheni yana niyyan yi min fyade,ai ba haka kikace min...." Rufe min baki nace" Uwa ta katsawa Yaganah wani mugun tsawar da ya fi na farko tana goya hannunta a baya ta fara fareti a dakin,(me hakan ke nufi, ya naje kyamis na sai maganin karfin maza musamman dan in bashi ya lalata Fanne amma abun ya koma kai na) Uwa take yiwa kan ta tambayar tana cigaba da zagaye dakin.. tura baki gaba Yaganah ta yi tana kwanciya saman gadon gami da nade kafafunta, duk ta tuna abun da ya faru sai ta matse hannunta a kirji tana tamke idanu, kwafa Uwa ta yi ta fita daga dakin...!


Bacci ya daukeni har ya fara nisa, ba zato ba tsammani na ji saukar ruwa a jikina, zabura na yi na mike, Maahh da itama bacci ya fara fizgarta dan taji dadin karin ruwan da akai mata ta bude idanu, "Munafuka har kina da lokacin zuwa ki kwanta kenan? Na ce kina da lokacin hutu a gidan nan? wa kika barwa jibgin wanke wanke dake zube bakin kwararo?" cewar Uwa dake tsaye a kanmu rike da kofin ruwa da alama ita ta watsa mana, ina share ruwan da ya jikamin fuska na ce, "Ban san bacci ya daukeni ba Uwa". Na fada ina zuro dogayen bakaken kafata kasa. 

"Kina kammalawa ki share gidan nan tas ki dauramana sanwa, ni ba baiwar Uwarki bace tana zube kamar jidali sai dai a dafa a bata. "cewar Uwa tana kaimin bugu a bayana, da hanzari na fice ina hango Maahh bakinta yana motsi kamar tana yiwa Uwa magana ne, wani dadine ya lullubeni dan tun jiya kenan da ta fado bata yi magana ba sai yanzu.!


Cike da kuzari nake wanke wanken da la'asar ta wuce sosai, wanke wajen nayi bayan na gama na shiga madafar mu dake can gefe na hura icce da hawar da tukunyar tuwo kana na dauki tsintsiya na fara sharar tsakar gidan, idan ka ganni a lokacin zaka dauka ni baiwace ba yar gidanba.!
                      *Almuhajir*
Tun da ya koma ya kwanta yake ta sake-sake a ranshi, gefe guda kuma wani irin matsanancin ciwon kai yake ji, wasa wasa zazzabi mai zafi ya rufe shi har yana kakkarwa, bargo yaja ya rufu dashi. Duk yadda ya so yin bacci kasawa ya yi tsaki ya ja a karo na barkatai ya ce, "Ko me ya kawota daki na ma?"

Yana cikin wannan halinne ya jiyo karar tsintsiya ana shara, ita kadaice ke sharar gidan a irin wannan lokacin, zuciyarsa ta fada, bai damu da halin da yake ciki ba ya mike doguwar jallabiya ya zura yana fitowa, ko dar bai ji ba yanzu bai damu da wani ya ganshi ba, matukar Fanne zata fahimceshi to kaso sittin na damuwarshi ta kau.!


Na gama share tsakar gidanmmu saura bakin rijiya wanda yake a tsakiyar mu da bangaren su Ya Muhajir, durkushe nake ina sharar bakina dauke da tilawar karatun alqur'ani cikin suratul Furqan na ji an damko hannuna, cikin kiftawa da budewar ido ya shige dani bangarensu, da karfi na bude baki zan kwaka ihu yayin da ko ina na jikina ya dauki rawa. Ya yi saurin sanya tafin hannunshi daya ya toshe bakin daya kuma ya tokare gini dashi hakan ya bashi daman yimin rumfa da jikinshi.

Babu inda baya makyarkyata a jikina, idanuna sun kwalalo a waje. Ganin na tsorata sosai yasa shi sakin bakin nawa,

"Dan Allah kada kayi min komai, ka dubi darajar Allah na rokeka kada ka rabani da mutuncina kada kaci zarafina". Na fada a gigice cikin fitar hayyaci, babu abun da ya dawo min a rai sai hoton incident nasu da Yaganah. Zaro ido Almuhajir ya yi jin abun da ta fada, Subhanallah, kallon da Fanne ta ke min ke nan, "Kada ki fahimce ni baibai Baby, magana nake so muyi nasan k.....Bai gama ba na kara bude baki zan zabga ihu yayi saurin dannewa da hannunsa, "me kike yi haka Baby,idan wani ya ji fa?" 

"Ni dai ka sake ni na ce ka sake ni,duk na fita a hayyacina a tunanina irin abun da ya yiwa Yaganah shi zai mini. Cikani ya yi kana ya koma jikin ginin shima ya jingina yana harde hannayensa saman kirji, lips nashi da suka bushe kamas sukayi wani fari dasu kamar mai jinya ya kamo na kasa yana ciza da karfin gaske, yana sakeni ban yi wata wata ba na kwasa a guje ban tsaya ko ina ba sai cikin madafa na tsaya ina maida numfashi kirjina na dukan tara tara, sai a lokacin wani kuka ya tahomin. Na sha kukana mai isata na wanke fuska sannan na cigaba da aikina duk zuciyata babu dadi.

Ba ni na kammala aikin ba sai ana kiran sallar maghriba. Dakin Uwa na shiga na sanar mata na gama itace zata raba abincin, ko da ta raba a dan kwano karami ta yafa mana ni da Maahh kamar wanda za'a ba jinjiri tuwo da miyar duk a waje guda...
Loma biyu Maahh ta saka a bakinta ta tura min kwanon, "Ki cinye da sauri kizo in baki wani labari". Cewarta tana kallona.!


A tsakar gida aka shimfida babbar tabarma kamar yadda al'adar gidan yake gaba daya iyayenmu maza a nan suke cin abincin dare su duka hudu ana kawo Abinci daga sashensu, yau ma bata canza ba suna zaune dukkansu harda Baba Bamaina bayan sun gama cin abinci yana ta basu labarin yadda yan ta'addan suka watsar da garinsu dama sauran garuruwan dake makwabtaka dasu duka sun kwace suke da iko dasu yanzu.
Baba Aisami ne ya muskuta ya ce. 

"Lallai Almuhajir ya shigo mana da bakon lamari a gidan nan, dukkanku kunyi shiru babu wanda ya ce wani abu"..."Jira nake mu gama da wannan Aisami, bana son muzo muna yanke hukunci cikin fushi a samu akasi," cewar Baba Modu yana kwadawa Bulama dake wucewa kira. 

"Kira min yayanku yanzun nan kace ina bukatar ganinsa".
A bakin kofar dakinsa Bulama ya rafka Sallama, Almuhajir dake kudundune cikin bargo maganar Fanne ya dawar mishi da wani zazzabi sabo fil ya amsa da kyar, "Yaya Su Baba suna kiranka a wajen cin abinci". "Karfin halin mikewa ya yi yana fadin. "To" Jallabiyar da ya cire ya mayar jikinshi ya fito.
A tare suka amsa gaisuwar da ya miko musu kanshi a kasa bai yadda ya hada idanu dasu ba...

"Wannan shi ne karo na nawa kana tarayya da yar mutane cikin gidanmu kafin yau dubunka ya cika muka ganka Almuhajir? Baba Abbagana ya watso mishi tambayar da ya sanyashi jin wani irin faduwar gaba da bai taba jin makamancinsa ba. "Kayi shiru fa ana tambayar ka" Babanshi Aisami ya fada a fusace, still Almuhajir bai dago ba bai kuma ce komai ba, sai dai karara zaka fahimci bacin ran dake tattare da fuskarsa har wasu jijiyoyi sun fito a saman goshinsa. 

"Akwai sa'anka a nan ne muna magana kayi shiru?"...Still bai ce komai ba ba don bashi da abun fada ba sai dai ji yayi kamar an kulle mishi baki da superglue ne.
Baba Bamaina ne ya maida kallonshi kan yan yayyunsa ya ce. "Wannan yana nuna mana cewa ya dade yana aikata hakan wanda kuma ko kadan ba tarbiyar wannan gidan bace, can ya samoshi watakila a yawon bokon da ya yi, bayan haka ya maidamu yan iska muna magana ya yi banza damu, dole a yanke mishi hukunci domin ya zamo izina ga sauran kannensa na baya, dan haka nan da sati daya za'a daura maka aure da ita yarinyar dake lalatawan sai kaje ka cigaba da ga inda ka tsaya dan babu wadda zaka barwa sauranka.Wannan shine karshen magana ta shi ka bamu waje mutumin kawai gobe idan Allah ya kaimu za a Mata gwajin ciki".
Tun da ya fara magana kan Almuhajir ke kasa yana furta kalmar aure ya dago a rikice yana zuba rinannun idanunsa kan Bamaina, "Aure kuma baba? Aure da yaganah?" kalmar ta subuce daga bakinshi fuskarshi tana bayyana tashin hankalin da yake ciki.

"Ita fa ko ka dauka dama kaci banza ne zaka yasar da ita ka auro wata fresh ko? to ba'a gidan nan ba ba za ka mayar damu kananan mutane ba.".


"But baba bana son ta ni Fanne nake so kowa ya sani kuma an tsaida magana dama ana jiran su kammala boko ne, ni Fanne nakeso, ita nake so ita ce zan aura ba Yaganah ba...Abun da ya faru dazu ban san ya aka yi ba, i just don't know what came over me, ban ....." 

Rufe mana baki my frnd, (luran saro sai sha lorisa nimiya, fanima na, wanɗe am sinana ro anda gonime.) Wllh sai ka aureta bazaka (mai damu kananan mutane ba).'Bamaina ya fada cikin harshen kanuri cike da masifa, dama shi din mafadacine. Tashi ka bamu waje ka fara shiri kuma nan da sati guda, ita kuma Fanne Allah ya bata mijin da ya dace da ita ba irinka ba lusari kai baka kare mutuncin kannen ka ba kai ne mai haike musu, Allah wadaran wannan hali naka" Cewar Babanshi shima cikin fushi, kuma rikicewa Muhajir yayi tashin hankalinshi na karuwa jin kalaman Allah wadarai da Babanshi ya jefeshi dasu, duk yadda zai musu bayani a yanzu baza su gane ba, dan haka ya tashi yana hade hanya dafe da goshi ya koma dakinsa da niyyar zuwa safiya zai musu bayani yasan yanzu suna cikin fushi ne. 

Allah sarki Almuhajir kayi ganganci, me yasa baka musu bayani yanzu ba? Wannan shiru da kayi baka sani ba watakila ya zamo igiyar zaren da zata mike dodar ta sada ko wannenku da kaddararshi tsakanin kai da Fanne.
**********
       *Abuja*

Zaune ya ke bisa office chair dinshi guiwar hannayensa suna saman desk daga sama kuma ya harde yatsunsa cikin na juna habarshi daure bisa yatsun, kakinsa na soja ne sanye jikinshi as usual, Macbook dake gabanshi ya kafe da idanu tsawon mintuna goma ke nan yana kallon abun da aka tura mishi fuskarsa tana bayyana madaukakin bacin rai. Landline dake saman desk din ne ya Yi kara, da sauri Aminullah ya daga yana karawa a kunne gami da mikewa ya kame kyam daga daya bangaren a kayi magana, "yes sir" ya fada yana sarawa kamar yana a gaban mai shi. Macbook din ya janyo da hanzari ya rufe bayan ya ajiye kan wayar, da hanzari ya fita yana nufar ofishin MG da ya kirashi yanzu, tafiya yake amma kamar wanda yake gudu tsabar yanda ya samu training a kan aikin shi. Sai da ya yi knocking a ka bashi izini sannan ya tura kofar ya shigo, makeken ofishi ne da tsayawa fasaltashi bata lokacine, daga gaban desk din ya tsaya kyam ya daga hannu daya zuwa gaban goshi daya hannun kuma ya makale shi jikin cinyarsa,

"Sir!"

Ya fada daga makwogoransa." Have a sit capt." Mutumin da alama zai kai shekaru hamsin ya fada. sauke hannu Al'ameen ya yi ya janyo kujera yana zama.
Tafkeken desk PC dake saman teburin MG ya dan karkato dashi gefen Al'ameen, kallon second biyar ya yi ya ce cikin bacin rai har jikinsa ya fara rawa alamar allurar sojojin ta motsa" Shi nake kallo yanzu sir, and abun ya bani mamaki kamar nig....."...daga mishi hannu MG yayi ya ce, "You know nothing capt, just stay quite dan umarni aka bayar daga sama."

"Al'ameen was shocked and speechless, kawai sai ya hangame baki yana kallon MG da ya cigaba da bayani "Zaka jagoranci bataliya ta tamanin da daya (81 Batallion) karkashin operation Kuka Zaki zuwa Borno State, lallai ka tabbata kun kwato duk wani garin da ke hannun y'an ta'addan nan, this is a command. Mikewa ya kuma yi ya Sara mishi da karfi ya ce

"Yesss Sir." A hada duk wasu kayan aiki yanzun nan,"..yes sir" Al'ameen ya kuma fada kafun ya fice daga Office din, duk wani soja dake karkashin bataliya ta 81 ya samu labarin tafiyarsu Jihar Borno, take Barikin ya kaure da hayaniya baka Jin komai sai dirin motoci kirar igwa masu sulke da sauran samfurin motocin ya'ki, a bangare guda kuma sai jibga kayan ya'ki Ake a cikin wasu doggin motoci masu kalar kakin sojoji daga sama kuwa wasu jirage ne masu sauk'ar ungulu ke ta shawagi a sararin samaniyar Barikin don tabbatar da tsaro kana wasu sojoji sun ja layi sai fareti suke yi da takensu na sojoji (NO GOING BACK).





*SANADIN HIJIRA*









Chapter 11/12.




Sai da komai ya kammala Al'ameen ya Koma cikin office na shi, tab ya bude ya yi wasu y'an danne danne, zuwa minti biyu Badar ta bayyana gaban tab din tana zaune bisa kujerar dining kan ta babu hula sai guntun gashin ta da ya sha gyara dake bayyane.

"Hiii Sojana" ta fada tana daga mishi hannu daga inda take, "kamar ka san tunanin ka nake yanzu haka, ji nake tamkar in yi tsuntsuwa in ganni a gaban ka, how are you doing?". Lumshe idanu ya yi ya bude, "Ban hana ki zama kai bude ba? "ya fada a can kasan makoshi.

"Awwwn sorry Sojana a cikin gida nake fa shiyasa but kada kaji haushi bari in saka yanzu" ta fada tana janyo hularta dake gefe. 

Wayarshi dake burarin neman agaji ya kalla ganin mai kiranshi ya ce, "I will call you later" daga haka ya katse vidcall din yana picking call din Musty.
"Hey Capt. Abun da ka turamin gaskiya ne or you are kidding me?".. Dan murza goshinsa ya yi, yace, "About work issue zan maka wasa? Oya get ready mr man" karfe shida na safiyar gobe ne tafiyar." Cewar Al'ameen yana tattare fatar goshinsa waje daya.

"Gosh. ka san halin da Zeenat take ciki fa, tana bukatar kulawata ta musamman you know shekara d'ai-d'ai har biyar mukayi muna jiran wannan lokaci yazo kuma zan shiga daji in barta cikin taraddadin ta yiwu in dawo ko kuma an rabu kenan har abada!.Cewar Musty yana bata fuska

"Sosai maganar Musty ta doki Al'ameen yaji shima ya kamata yaje yaga Ummie even though ba lallai hakan ya kasance ba amma dan kar ya karyar mishi guiwa yana daure fuska yace, "Ka yi alkawarin kare rayukan al'umma a kowane mataki, so NO GOING BACK. Zeenat kuma da izinin Allah zata haihu lafiya, inyeee wayaga su Musty Daddy amma zaka min kara ka sanya sunana ai ko? "Ya fada da barkwancin da Musty bai saba ji daga gareshi ba sai abun ya mishi wani bambarakwai, yana dariya ya ce,

"Wannan alkawari ne Amin, matukar Namiji ta haifa mai sunanka ne, idan kuma mace ta haifa sunan Ummie za'a sanya Safeenatu, amma idan Namiji ne kai zaka yo mana farautar Giwa a dajin Borno mu yanka mu rakashe a jeji". Cewar Musty dariya dauke saman fuskarshi dan tuni Al'ameen ya kawar mishi tunanin da ya fara na halin da Matar shi ke ciki.
********
Da dare misalin karfe takwas Al'ameen ya dira a gida unexpected kawai suka ganshi, Badar da Saudat ne zaune a palo suna kallon tashar Zeeworld suna kallon wani Drama (Age is just a number). sai Humaira yar Saudat din dake zaune gefe tana assignment na makaranta,

"Sannu da zuwa Uncle A"Cewar Humaira, Hannu ya daga mata yana nufar bangaren dakin Ummie dan sauri yake yi. Badar ta biyo bayanshi da sassarfa. 

"Sojana kai dai ka iya mana dirar mikiya, why not ka sanar damu ko dan turare ai zan shafa maka ko?" Ta fada cike da gwalli, sosai ta bashi dariya yadda tayi din, amma sai ya kanne yana fadin zan shiga wajen Ummie". Baya tayi da sauri dan yau kuma jikin na Ummie ya motsa mata sosai Ladi mai aikin gidan taci duka.


Bai yi zaton da mutum a dakin ba dan haka ya shiga kansa tsaye sallamar ma a zuciya yayi ta ba zato ba tsammani Hajja Fanta dake tsaye jikin mirrorn dakin ta juyo a rikice jin sound na bude kofa abun da ke hannunta ta fara kokarin boyewa a bayanta ganin Al'ameen ne ya shigo.

"Ahh lale maraba da dan albarka, yanzu ko nake zancen ka a zuciya ta ashe kana tafe" Ta fada tana yaken dole a gefe daya kuma jikinta na dan rawa tana cigaba da boye hannunta a baya.

"Barka da dare " Kawai ya fada kai tsaye yana tunkarar bakin gado inda Ummie ke zaune kanta a kasa, gashin kan nata yayi biji biji da datti kana ya sauko ya rufe har saman fuskarta, hannunta daure da chains hakama kafarta, rigar jikinta ta yayyage har ana iya hango gefen mamanta.

Ganin bai mai da hankali a kanta ba yasa Hajja Fanta saurin fitar da abun da take boyo, maganin Ummie ne da dr ya kawo dazu, ainahin na cikin container din ta juye tana kokarin musanyawa da wanda ta kawo Al'ameen ya shigo, da hanzari ta juye nata ta kwashe na dr din tana zubesu a bakin zaninta...
Rumtse idanu yayi da karfi yana juyowa a fusace ya ce, "What the heck is this, waye ya daure mata hannu da chains bayan na kafarta,? "Ba Ummah kawai ba hatta da su Badar da ke Palo sai da suka tsorata da irin tsawar da ya doka.

"Amm ehh dama Ba jimawa Dr Shettima ya shigo sakamakon kiran da Abeey dinku yai mishi, shi ne ya daure mata hannu, ya kuma yi mata injection ga nan ma sabbin drugs da ya taho mata dashi yanzu na ke shirin bata su, jikin nata ne ya dan motsa mata shi ya sa" Umma ta fada cike da rawar murya tana mikawa Al'ameen maganin da ta musanya. Jikina rawa ta fita cikin kasa da minti biyu ta dawo dauke da bottle water a hannunta.

Yana tsaye yadda ta barshi sai huci yake idanunshi kamar zasuyi aman wuta, tana mikamishi ruwa da drugs din ta fita bakinta alekum dan tasan shi ne kawai mutumin da zai iya bata maganin cikin salama.

Takowa yayi gaban Ummie dake duke har lokacin gabadaya jikinta ya yi weak, "Dr Shettima" yake ta nanatawa a ranshi, wato wannan mugun injection din yau kuma ya yiwa Ummiena? sau nawa zan fada ciwonta bai kai matsayin da zai mata wannan allurar ba? Kwafa yayi yana zama ya dan dago kanta kadan, 

"Ummie" Ya fada a hankali kamar ba daga bakinsa kalmat ya fito ba. Lumsassun idanunta da suke nuna halin galabaitar da take ciki ta dago kamar taji kiran da yai mata, suna hada idanu ta fara kyakyacewa da dariyar da zai tabbatar maka cewa lallai ita din sha tarace, "Stop it!" ya fada da dan tsawa dan yasan shi ne kawai mafita idan ta fara irin haka, aiko ta tsorata nan take jikinta ya fara makyarkyata hawaye ya soma gangarowa saman kuncinta. Da wannan damar Al'ameen ya yi amfani wajen bata maganin hadi da ruwa, hannunta ya kama yana kwance chains din, a hankali ya fara magana kamar mai rada.

"Ina bukatar sanyawar albarkar ki kamar ko wanne d'a Ummie, gobe zamu tafi yaki can wani yanki dake gabashin kasar nan ban sani ba ko wannan shine gani na karshe da zan miki tafiyace ta ko a mutu ko a yi rai. Ina fatan Ubangiji ya amshi rokona ya baki lafiya. A daidai lokacin ya gama kwance mata hannu ya dago kai bisa mamakinsa ta yi shiru hatta rawar jikin da ta keyi na tsawan da yayi mata ya tsaya sai kallonshi take kamar mai fahimtar abun da yake fadi, sai dai tunaninshi bai sauka ba ya ji ta fara sambatu tana daukar pillows dake saman gadon ta fara jifanshi da su, ta janyo bedsheet nan ma ta jefa