Zumar Hamada 🍯 🏜️

Silken smile

by @zahrabmrs02

 

Ta jima tana Addua  cikin kuka, kafin ta shafa addu'ar, ta miƙe ta naɗe dadduman.

Ta koma kan gado ta kwanta, amma tana kwanciyar, sai hoton abin da Sadiya ta mata a dining table ya dawo mata. Ta tuna yadda  kowa  ya tsaya da cin abinci aka rinka binta da kallo saboda tsohuwar rigarta, ta tuna kallon wulaƙancin da Ameenatu ta jifeta da shi tana kiran kyaun ta da 'kyan ƙauye'.

Tadala ta juya ta gefe guda, ta sanya bayan hannunta tana share kwallan dake sintiri a idanunta. Wani irin daci ya tsaya  mata ciki, ta ayyana a ranta cikin tsananin kaɗaci: 'Wato talauci babban masifa ne! Idan baka da shi, ko a cikin danginka baka da mutunci. Mutuncinka duk yana gurin dukiyarka.' Cikin  tunani da kewar su Mansoor, baccin ɓawon kifi ya kwashe ta dab da asuba.


Tana idar da sallar asuba ta nufi banɗakin  ta watsa ruwa , ta fito tana goge jikinta , “Insha Allah ba za ku sake samun damar wulaƙanta ni ba.” Ta nufi akwatinta, ta buɗe ta shiga hargitsa kayan ciki har ta zaɓo kayanta  mafi kyau na alfarma wanda mansoor ya Dinka mata da sallah ,wani leshi mai launin  white da baƙi wanda aka mata ɗinkin riga da siket Ta zauna ta shafe jikinta da ragowar mayukan fuskarta masu kyau, ta sawa idanunta kwalli sannan ta naɗe kanta da baƙin mayafi mai santsi. Ta fito fes kamar wata sarauniyar hamada. Daurin da tayi ya ba dogon gashin ta damar fitowa har bayanta 

Duk da kyan da ta yi, Tadala ta gano cewa a gidan nan kowace kaza tana kwan mazauninta ne. Don haka ta koma kan gado ta zauna, ta ƙeƙeshe a ɗaki ba ta fito ba saboda tsoron kada ta shiga inda ba ta da iko ta janyo wa kanta wani abun.

Ta kusa share sa'o'i biyu a zaune, sai ga Bintalo ta turo ƙofar ɗakin, ta dube ta da mamakin canjin kyan da Tadala ta yi a safiyar nan. Bintalo ta yi murmushi tace, "mami tace ki fito ku zo ku karya, lokacin karin kumallo ya yi."

Tadala ta miƙe ta bi bayan Bintalo. Maimakon su nufi babban dining ɗin nan na jiya sai Bintalo ta wuce da ita ta wani dogon corridor dake ɓangaren Sadiya 

A gidan Alhaji Kamal, yadda tsarin yake da daddare kawai gaba ɗaya iyalin gidan ke haɗuwa a kan Main Dining Table na tsakiya don sadar zumunci. Amma da  safe ko rana, kowane ɓangare na kansa yake; s

Tadala ta shigo kicin mai hade da dining na ɓangaren Sadiya dake cike da ƙawatattun gilasai da zane-zane na alfarma (kasancewar Sadiya interior decorator ce). Ta sami Sadiya zaune tana sanye da wata doguwar rigar , fuskarta sumul saboda daddadan barcin da ta sha a daren jiya a gurin gidadon katsina . Safa da Marwa suna zaune kusa da ita kowace tana danna waya, yayin da Ahmad ya fara serving kansa 


Sadiya ta kurawa Tadala ido, ta kasa ɗauke idanunta daga kan kyakkyawar rigar leshin dake jikinta, wadda ta zauna daram ta fito da ainihin zubin jikinta mai siffar kwalba .  ta sauke ajiyar zuciya, ta gyara zama ta kalli Tadala sama da ƙasa, sannan ta saki wani murmushi ta ce 

"Yauwa Tadala! irin wannan shigar nake so ki dinga yin ta a gidan nan. Idan kika rinka fitowa fess haka, ai ko kishiyoyina ba za su taɓa samun damar  raina min ke ba, balle a jawo min gori." Ta juya ta kalli kujera ta ce, ", ki zauna ki karya."

Tadala ta taka a hankali ta zauna a kan kujerar dining ɗin da har yanzu take jin alfarmarta ta yi mata yawa. Suka fara cin abincin ,Tadala ta ɗago cikin sanyin murya ta kalli Sadiya ta ce, "Anty Sadiya, ina kwana?"

Mami ta kaɗa kai kawai ba tare da ta amsa da baki ba, hankalinta ya koma kan kofin shayin dake gabanta. Safa da Marwa ma suka tabe baki suka kalli gefe kamar ba su ji ba, kowace ta ci gaba da latsa wayarta  cikin nuna halin ko-in-kula.

Ganin hakan, Ahmad ya ajiye cokalin hannunsa, ya kalli Tadala , ya saki murmushi  ya ce: "Anty Tadala, good morning ? Fatan dai kin tashi lafiya ?"

Wani sanyi ya ratsa zuciyar Tadala jin kalaman Ahmad, ta ji dacin dake ranta ya ɗan ragu. Ta kalli Ahmad  ta amsa masa da murmushi  "Lafiya lau Ahmad, nagode sosai."

Daga nan ta daure, ta juyo da kanta gurin su Safa da Marwa ta ce, "Sannunku dai, ina kwana?"

Safa da Marwa suka yi banza da ita, kowace ta ƙara basarwa kamar ba da su take maganar ba. 

Ganin hakan ya sa ran Sadiya ya ɓaci, ba don tana ƙaunar Tadala ba, a'a, don kawai bata son su nuna  rashin  tarbiyya a gaban Tadala a sami na kaiwa rahoto nijar . Sadiya ta ajiye kofin shayin hannunta da ƙarfi a kan table ɗin, ta daka wa su Safa da Marwa tsawa cikin fushi tace 

"Wai ku wasu  irin banzayen yara ne?  raini da fitsara a gabana! Tadala sa'ar ku ce?  A gaban nawa zaku rinka yi mata wannan wulaƙancin? Gaba  ɗaya kun cika gidan nan da rashin kunya, kuma nasha  gaya muku bana son rashin tarbiyya !"yanzu idan dad dinku Yau be fita da wuri ba haka zaku nuna ma cousin Dina rashin tarbiyar ku a gaban sa,to wallahi ku fito a idona 

Safa da Marwa suka haɗiye yawu da sauri, suka ajiye wayoyinsu cikin tsoron fushin mahaifiyarsu...


. Cikin muryar tsiwa ta dole suka ce, "Ina kwana," ba tare da sun kalle ta ba. Sadiya ta harare su sannan ta ci gaba da karyawa tana danna wayarta.

Ganin kowa ya kauda kai ya ba Ahmad damar sake gyara zama, ya dawo da hankalinsa gaba ɗaya ga Tadala cikin kulawa. Shi sam halinsa bai zo ɗaya da na mahaifiyarsa ko yayyensa ba; yana da sauƙin kai da son zumunci.

Ahmad ya matso da kujerarsa kusa da ita yace, "Anty Tadala, don Allah kici  abincin sosai ,dawo ki zauna kusa da ni kiyi karin kumallo da kyau."

Tadala ta saki jikinta ganin yadda Ahmad ya ba ta wannan damar , ta dawo ta zauna ta fara gutsurar bread a hankali. Don ta nuna masa godiyarta, ta dube shi cikin murmushi ta shiga ba shi labarin rayuwar hamada da kuma ƙanenta Aghali dake can Agadez.

"Aghali yana da hazaka sosai Ahmad," Tadala ta faɗa, idanunta na haskawa yayin da take tuno ƙanenta. "Kullum yana taya Baba fita kasuwa, amma yana son makaranta sosai."

Ahmad dake sauraronta da daukacin hankalinsa, ya gyara zama cike da shauƙi. Kasancewar Ahmad tunda aka haife shi  bai taɓa zuwa jamhuriyar Nijar ba ko sau ɗaya. Labaran hamada, raƙuma, da acts na mutanen Buzu dake fitowa daga bakin Tadala sun ba shi sha'awa sosai.

"Wow! Anty Tadala, gaskiya ina matƙar son zuwa Nijar wata rana nima na ga garin ku!" Ahmad ya faɗa fuskar sa cike da zumuɗi.

Tana tsaka da ba shi labarin, sai Mami ta ɗago kai daga wayarta, ta dubi Ahmad da fuskar sam babu wasa tace:

"Ahmad! Yi sauri ka kammala abin da kake yi ka tashi a wajen nan. Ka san last day ɗinka  ne na weac ko ? 

Ahmad ya ɗan shafa kansa, ya juyo ya kalli mahaifiyarsa yana murmushi  domin ya kwantar mata da hankali yace, "Mami baki da matsala, zan kammala komai yanzu."

Ya sake juyowa da sauri gurin Tadala, ya rage muryarsa yana murmushi yace, "Anty Tadala,  anjima idan na dawo daga makaranta... Don Allah za ki ƙara ba ni sauran labarin garin ku baki ɗaya ko? Kuma don Allah ki gaya mini, shi Aghali aji nawa yake a makarantar tasa ta can Agadez?"

Tadala ta yi Murmushin  da ya fito da kyan fuskarta ta ji daɗin yadda Ahmad yake nuna mata ƙauna  a gidan da kowa ke harararta.


Safa da Marwa suka haɗiye yawu cikin takaici, suka dubi Mami, sannan kowace ta ɗauki handbags dinsu   suka yi sallama suka fice daga sashen baki dan tafia nile university idan suke zuwa tare da amal da zarah 

Bayan fitarsu ne Bintalo ta shigo kicin ɗin tana kwashe kofunan shayi. Mami ta gyara zaman ɗankwalinta , ta kalli Tadala da kyau, 

"Yauwa... Maza Bintalo, ajiye abin da kike yi, ki ɗauki Tadala ki kai ta ɓangaren Umma (Dr. Mariya) su gaisa 

Ta juyo ta kalli Tadala, ta rage murya tana fadin. So nake ki je ta ganki yadda kika yi wannan shigar ta alfarma a safiyar nan. Kin san kishiyata Dr. Mariya mace ce mai ji da kai, don haka dole ne na ƙanƙaro ma dangina girma da tasiri a idon kowa na gidan nan. Karki sake ki nuna mata wani rauni."

Tadala ta jinjina kai a sanyaye, ko da yake a ranta ba ta ji daɗin yadda Sadiya take son yin amfani da ita azaman makamin yaƙi na gasar kishinta ba. Ta miƙe ta bi bayan Bintalo suka nufi ɓangaren uwar gida.

Sashen Dr. Mariya yana ɗauke da kwarjini na daddadan al'ada, manyan kujeru na alfarma masu nauyi, (sofas )da kuma natsuwa irin na gidan manyan likitoci.ba wani hayaniya very simple 

Tadala ta shigo falon da sallama Ta sami Dr. Mariya zaune a kan kujera mai zaman mutum ɗaya, tana sanye da fararen kaya na likitoci, tana duba wasu takardun bincike na asibitinta a kan tebur. Ameenatu na zaune a gefenta tana shan custard , cikinta na wata takwas ya fito ras 

Suna ɗagowa baki ɗaya su kalli Tadala, idanun Ameenatu suka kafe a kan Kayan tadala baƙin lace din  na fitar da hasken fatarta. Ameenatu ta kusan haɗiye cokalin bakinta saboda takaicin ganin yadda Tadala ta fito fess, babu alamar kauyencin  jiya.

Dr. Mariya ta ajiye takardun hannunta, ta fito da dukkan dabarunta na manyan mata masu ilimi. Ta saki wani ƙayataccen murmushi—amma na Baki ne, bai kai can cikin zuciyarta ba (fake smile)—ta kalli Tadala 

"Masha Allah! Sannu da fitowa Tadala. Lallai kuwa yau an tashi fess kamar tauraruwa. Wannan shigar ta yi kyau sosai, ta dace da ke."

Tadala ta ƙaraso da sauri, ta tsuguna a kan kafet ɗin falon cikin ladabi tace, "Umma, ina kwana? Kun tashi lafiya?"

Dr. Mariya ta ci gaba da wannan murmushin na kissa da nuna karamci a fili tace, "Lafiya lau Tadala, an tashi lafiya. Ya ɗakin naki na ƙasa? Fatan dai baki yi jinyar sanyin AC ba 

"Na kwana lafiya Umma, nagode," Tadala ta amsa tana sunkuyar da kai.

Ameenatu ta saki tsaki a hankali ta ajiye kofin hannunta, ta kalli mahaifiyarta sannan ta kalli Tadala ta ce "Hmm... Umma ai dole ta kwana lafiya. Tunda ta baro ƙurar hamada ta zo daular Abuja ta sami gado mai laushi  da AC, wa zai yi kukan sanyi? Gaskiya Mami tana ƙoƙari, har leshi ta Baki daga zuwa ?

Ba nata bane nawa ne tadala ta amsa ameenatu a sanyaye 


Rann Dr. Mariya ya ɓaci da kalaman Ameenatu. Ta juyo mata  wani  kallo na bacin rai,  

"Ke Ameenatu! Wace irin rashin tarbiyya ce haka? Kamata ya yi ki san matsayinki na babbar ƴa a gidan nan kuma mai aure dake jiran haihuwa! Me yasa zaki rinka jifan baƙuwa da irin waɗannan kalaman ? Idan ba zaki fadi   alkairi ba, ki yi shiru da bakinki!"

Ameenatu ta haɗiye yawu ta haɗe fuska, ta tura kofin gabanta gefe 

Dr. Mariya ta sake juyowa gurin Tadala, ta canza fuskarta zuwa murmushi "Karki damu Tadala, ki saki jikinki a gidan nan kiyi karatunki lafiya, kin ji ko? Maza tafi ɗaki ki huta kafin lokacin makarantar yayi."

Tadala ta miƙe tana godiya, zuciyarta cike da farin ciki da girmama Umma saboda yadda ta kare ta ta yi wa ƴarta faɗa a gabanta. 

Bayan fitar Tadala , Dr. Mariya ta cire gilashin idonta, ta ajiye shi a kan tebur, sannan ta juyo gaba ɗaya gurin Ameenatu wadda take ta faman turo baki.

"Wato Ameenatu ba zaki taɓa amfani da hankali ba ko?" Dr. Mariya ta faɗa cikin murya ta ƙasa-ƙasa dake cike da tsegumi da takatsantsan. "Baki ga dabarar da na yi ba kike son lalata min tsari da fitsararki?"

Ameenatu ta gyara zama  tace, "Haba Umma, gani na yi kina ta faman washe mata baki kina mata murmushi . Duba kiga fa irin leshin da ta sanya, duk don su kankaro ma kansu girma ne fa ita da Mami."

"Kyale ta Ameenatu! Shi yasa nake gaya miki lallai kina da sauran koyon dabarun zama da mutane. Shi murmushin da kike gani ina mata, na nuna mata karamci ne don kar Sadiya ta sami kafar cewa na tsani danginta ko na fara nuna kishi a gidan nan tunda aka kawo yarinyar. Yarinyar nan ai ƴar ƙauye ce, ba ta wayewa  . Idan na nuna mata tsantsar karamci da ƙauna, ta saki jiki da ni, ai shikenan na gama sanya ta a hannu."

Umma ta ɗan yi gyaran murya ta ci gaba da cewa Yarinyar tana zaune ne a can ɓangaren Sadiya. Idan ta amince da ni ta sani a matsayin mutuniyar kirki, baki gani ba da kanta za ta rinka kawo min  labaran cikin gidan Sadiya da abin da suke shiryawa? Ta wannan hanyar zan rinka samun duka sirrin Sadiya ba tare da na sha wahala ba. Ke dai kawai ki riƙe bakinki, kar kiyi mata tsiya idan ta zo, muna buƙatar ta kusa da mu."

Ameenatu ta saki baki cikin mamaki, take fuskarta ta washe da dariyar dabarar mahaifiyarta, ta ce "Lallai Umma! Yanzu na gane lissafinki. Wato dabarar ’kura ce sanye da fatar tumaki’ kika yi mata? Gaskiya banyi wannan tunanin ba. To shikenan zan dake na zuba ido na ga yadda zata rinka feso mana asirin Mami!"

Su biyun suka kunshe da dariya a falon, suna taya juna murnar dabarar da suka shirya wa Tadala ba tare da yarinyar tana da masaniya ba.


Bayan Tadala ta fito daga ɓangaren Umma (Dr. Mariya) cike da farin cikin yadda uwar gidan ta nuna mata ƙauna tare da yi wa Ameenatu faɗa, ta ɗauki hanyar da zata mayar da ita sashen Mami (Sadiya). Sai dai saboda tsananin girman gidan da sarkakiyar corridors ɗin dake haɗa sassan gidan, Tadala ta ɓace. Da kyar  ta tsinci kanta a daidai ƙaramin dining ɗin nan na kicin ɗin Sadiya inda suka karya da safe.

Ta zauna a kan ɗayan kujerun dining ɗin tana tunanin anan ne ya kamata ta tsaya. Shuru... shuru, kusan awa ɗaya cur Tadala tana zaune a gurin ita kaɗai, ba ta san inda ainihin falon Sadiya yake ba, kuma tana tsoron yin yawo a cikin gidan kada ta shiga gurin da bai kamata ba.

Tana cikin wannan zaman ne, sai ga Bintalo ta fito daga cikin babban kicin ɗin riƙe da tiren kofuna. Tadala ta sauke numfashi ta miƙe da sauri ta kira ta, "Bintalo... don Allah kiyi haƙuri. Wai ina ne ainihin falon Anty Sadiya yake? Tun dazu na dawo na rasa inda zan nufa."

Bintalo ta tsaya cak, ta saki baki ta zuba wa Tadala ido cikin tsananin mamaki kafin ta fashe da dariya tace, "Haba bakuwa! Tun ɗazu kina zaune a nan? Ai ainihin falon Mami yana can bayan wannan babban labulen . Biyo ni na nuna miki."

Tadala ta bi bayan Bintalo tana ɗan turo baki saboda kunya. .

Falon Sadiya ya kasance babban guri na musamman da ba kowane mutum zai iya fassara shi ba, kasancewar Sadiya babban kwararriya ce a fannin gyara da ƙawata gidaje (Interior Decorator). Falon ba na wasa ba ne; kowace kusurwa an tsara ta ne da tsantsar daula da fasaha.

Kujerun falon gaba ɗaya na alfarma ne masu launin madubin fari da ratsin zinare (white and gold royal velvet sofas), waɗanda aka shimmfiɗa musu matasai masu taushi na alfarma. Bangon falon baki ɗaya an lulluɓe shi da wani rikitaccen wallpaper mai zanen gwal dake sheƙi duk lokacin da hasken fitulun chandelier dake lulawa a silin ya dake su. A tsakar falon akwai wani ƙatafaren tebur na gilashi (italian marble center table) dake ɗauke da wasu kwalabe na gwal da furanni masu banƙanshi dake tashi a hankali. Kowane fanni na falon yana nuna tsantsar ƙasaita da zane-zane na ƙasar waje dake nuna cewa wadda ta mallaki gurin tana da kuɗi da kuma gata.

Tadala ta taka a hankali ta zauna a gefen ɗaya daga cikin kujerun tana bin falon da kallo, tana mamakin yadda mutum guda zai mallaki dukiya da fasaha haka.

Tana nan zaune tana kallon kyan falon, sai ga Sadiya (Mami) ta fito daga bedroom tana sanye da wani leshi green , tana tafe tana danna wayarta ta iPhone. Ta ɗago kai ta ga Tadala zaune, sai ta canza fuska ta ɗure gira 

"Tadala! kin dade baki dawo ba. Me kika tsaya yi ne a can ɓangaren na tsawon wannan lokacin? Kar dai kice min part din falmata kk je ?

Dan kwata kwata bama shiga harkar juna .

Tadala ta ɗan tsorata da yanayin Sadiya, ta gyara tsayuwarta da sauri tace, "A'a Anty Sadiya... wallahi tun ɗazu bayan na fito na dawo nan na zauna a kicin ɗinku na dining. Ban san inda ainihin part ɗin falon ki yake ba, shine nake ta jiran Bintalo ta fito ta nuna mini."

Sadiya ta sauke numfashi ta yi gyaran murya, tana mai jin daɗin yadda yarinyar ta nuna tsoro da baƙunta. Ta taka zuwa kan kujerar dake fuskantar Tadala ta zauna, ta ajiye wayarta, sannan ta dubi Tadala da idanuwanta dake shake da kishi da son jin tsegumi, ta matso kusa 

"To shikenan... gaya mini, me Umma (Dr. Mariya) tace da ta ganki a safiyar nan cikin wannan shigar?"


Tadala ta gyara zaman mayafinta, fuskarta cike da farin ciki na rashin sani tace, "Wallahi Anty Sadiya, Umma tana da kirki sosai. Da  gaske ta ji daɗin gani na, har cewa ta yi nayi kyau Masha Allah. Kuma ma lokacin da Ameenatu ta fara min tsiya, Umma daka mata tsawa ta yi, ta yi mata faɗa sosai a gaba na tace ta riƙe girmanta."

Mami ta saki wani ƙayataccen murmushi na gefen baki, amma can cikin zuciyarta, wani irin daci da kishi ne ya cika ta. ‘Dr. Mariya kenan! Makira ce matar nan, wallahi nasan halinta sarai,’ Gara falmata  daga ni har Mariyan bata damu fada sabgar muba ,dan ban taba ganin kishina a  Idonta ba ,Sadiya ta ayyana a ranta Tana son ta lallashi yarinyar nan ne don ta juyo da ita ɓangarenta, ta nuna ita ce mutuniyar kirki.’

Ta kauda tunanin ta hanyar gyara zaman leshinta, ta miƙe ta ɗauko wani babban envelope na takardu a kan drowa, ta dawo gaban Tadala 

"Yauwal Gashi nan, Malam  awaisu direba yana jiran ki a waje, zai kai ki makarantar yanzu don ku kammala komai. Sashenku (Department) shi ne Accounting (Kula da Akant), tunda accounting din kikayi diploma 

Sadiya ta taɓe baki ta ci gaba da cewa, "Kinga idan kika maida hankali kika gama, fatana ma shi ne ki sami aikin banki a nan Abuja. Daga nan kuma, sai ki haɗu da wani babban banker mai kuɗi ki aura, ki fita daga  talauci  ."

Jin kalaman Sadiya ya sanya Tadala lulawa cikin duniyar tunani. A take ta shiga ayyana kanta sanye da suit na matan banki, tana tsaye a cikin  banki  a tsakar birnin Abuja, tana sarrafa kuɗi. Wannan hoton ya sanya ta murmushi, ta ji daukacin dokin karatun ya ninka a ranta.

Sadiya ta katse mata tunani ta hanyar miƙa mata envelope ɗin hannunta, 

"Amma fa ki saurara kiji Tadala... Iya yau ne kaɗai Malam awaisu  zai kai ki makarantar , don kawai ku gama hidimar rajista tunda bakisan gari ba. Amma daga ranar da zaki fara halartar lectures , babu maganar motar gida. Sai ki dinga ɗaukar Bolt ko tasi (taxi) kina tafiya da kanki."

Ga takardunki nan, na riga na biya miki duka kuɗaɗen makarantar (school fees) na gama komai, sai ki ƙarasa sauran process ɗin da kanki a can."

Tadala ta amshi takardun cikin murna da godiya, ta miƙe ta nufi waje don haɗuwa da Malam awaisu , yayin da zuciyarta ke dokawa da fargaba da dokin shiga Base University.