Forgotten In The Cold
by @zahrabmrs02
Malam Awaisu ya danna hancin motar cikin get ɗin jami’ar Base University dake tsakiyar birnin Abuja. Yana yin parking, ya juyo cikin ladabi ya kalli Tadala.
“hajiya Tadala, gashi mun iso.
Tadala ta jinjina kai. Ta shafa addu’ar da ta saba yi duk lokacin da za ta shiga sabon wuri, sannan ta buɗe ƙofar motar ta fito riƙe da envelope ɗin takardunta.
“Allah Ya ba ki sa’a,” Malam Awaisu ya faɗa da murmushi.
“Amin. Nagode.”
Da haka ya tada motar ya fice daga makarantar baki ɗaya, kamar yadda Sadiya ta umarce shi.
Tadala ta tsaya a tsakar harabar jami’ar tana kallon wurin.
Makarantar ta haɗu ƙwarai. Manyan gine-ginen zamani masu sheƙi sun yi layi, bishiyoyi da korayen ciyayi suna ƙawata ko’ina. Dalibai suna kai-komo cikin walwala.
Amma duk da wannan kyawun, sai wani sanyin gwiwa ya ratsa ta.
Ta rasa ta ina za ta fara.
Gashi kyawunta na asali da siffarta ta matan Buzu sun sanya ta zama kamar wata tauraruwa a wurin. Duk wanda ya wuce sai ya juyo ya sake kallonta.
Wasu samarin ma har sun tsaya suna kallonta.
“Who is she?”
“Maybe she’s mixed…”
“Kai! She’s beautiful!”
Tadala ta ji kamar idanu sun yi mata yawa. Kunya ta mamaye ta.
Da sauri ta nufi wani benci dake ƙarƙashin wata bishiya ta zauna. Ta rungume envelope ɗinta a ƙirji, tana tunanin me za ta yi.
Tana cikin wannan hali ne sai ga wata kyakkyawar yarinya ta taho da sauri.
Sanye take da jeans da T-shirt mai tsada, a kafaɗarta akwai jaka, fuskarta kuma shake da murmushi.Ta zauna kusa da Tadala.“Hi! Sannu da zama.Ta miƙa mata hannu.sunana Fareeda Abubakar Ta yi murmushi ,Na ganki zaune a nan tun ɗazu kina ta kalle-kalle. Lafiya dai?Tadala ta ɗan sauke ajiyar zuciya.sannu … Sunana Tadala. Wallahi lafiya lau. Sabuwar zuwa ce kawai. Ban san kowa ba, ban ma san ta ina zan fara ba.Fareeda ta tafa hannuwanta,masha Allah! Ashe ke ma fresher ce?Lallai Allah Ya haɗa mu. Ni ma yau ce rana ta farko. Na zo ƙarasa registration ɗina ta Direct Entry.Ta ɗan matsa kusa“Wanne Department kike?”
Tadala ta nuna mata takardunta.Mami ta ce Accounting zan karanta. Direct Entry ne, zan fara daga 300-Level.Fareeda ta zaro ido.“Whaaat? Ta miƙe tsaye.
Accounting? DE?
Ta kama hannun Tadala“Lallai kam mu ne asalin classmates! Ni ma Accounting zan karanta, kuma DE ce ,muje kawai. Na zo da mota. sai mu karasa process din tare.Kuma daga yau… mun zama ƙawayen juna, farin ciki ya mamaye zuciyar Tadala.Nan take ta tuna addu’ar da ta yi jiya cikin kuka.ya Allah, Ka haɗa ni da alherin Najeriya. Ta kalli Fareeda.
wataƙila wannan ce farkon alherin.Ta miƙe tana murmushi ta bi bayan Fareeda.
Fareeda na tuƙi cikin ƙwarewa. Motarta ƙirar Vibe tana ratsawa cikin kyawawan titunan makarantar.Ta ɗan juyo.“Wai kin san me?“Tun ɗazu nake juya sunanki a raina. Gaskiya ban taɓa jin sunan Tadala ba. Daga ina kike ne?tadala ta yi murmushi.ni ƴar jamhuriyar Nijar ce. Na fito ne daga Agadez. Mu mutanen Buzu ne.
“Wow…
Fareeda ta kalleta.lalle kam! Shi ya sa nake ganin kin banbanta. Ga gashi mai tsawo, ga wannan fuskar…gskia kun gaji kyau. tadala ta yi ƙasa da kai cikin kunya.
A haka suka shiga block din .Fareeda ta taimaka mata wajen cike takardu da duk wani abu da ya shafi Turanci.
Cikin ikon Allah, kafin Azahar suka gama komai.“Gashi yau Friday ne Fareeda ta ce tana miƙa mata wayarta.Monday za mu fara lectures in sha Allah. Rubuta min number ɗinki tadala ta yi shiru na ɗan lokaci.Sai dai ki rubuta taki a takarda.”
Fareeda ta ɗago kai.Ba ki da waya?”
“Ina da ita… amma jiya na zo Najeriya. Ban da layin Najeriya.Ta yi murmushi cikin kunya.idan siya mini zan kira ki.”
Fareeda ta ɗan taɓe baki.
Awww…
Ta rubuta lambarta.To ga nawa. Ki kira ni da zarar an siya miki suka fito filin ajiye motoci.fareeda ta buɗe motarta.muje na kai ki gida,tadala ta girgiza kai.
“Gaskiya nagode sosai.“Amma… wallahi ban ma san sunan unguwar da muke zaune ba.Fareeda ta zaro ido.
“Ba ki sani ba?
anty Sadiya kawai ta ce za a turo direba ya ɗauke ni..“To shikenan ƙawata. Sai mun yi waya.Ta yi mata bankwana ta tafi.
Bayan tafiyarta, Tadala ta dawo kan bencin.Ta zauna.Tana jira time yana tafiya.
Ɗaya…
Biyu…
Uku…
An yi Azahar.
Babu Malam Awaisu.
An yi La’asar.
Har yanzu babu shi.
Cikinta ya fara murɗawa saboda yunwa.
Tun safe rabonta da abinci tun ɗan bread din datace .cikin ta ya ƙara murɗawa.
Ta zura hannu cikin jakarta.Babu ko sisi.
Hawaye suka cika mata ido.Da sauri ta ciro tsohuwar wayarta domin ta kira Sadiya ta kunna…wayar ta mutu.Worst part ma, layin Nijar ne.Ba zai yi aiki a Najeriya ba.A hankali ta koma ta zauna.Ta rasa me za ta yi.Ba ta san lambar kowa ba.Ba ta san sunan unguwar ba.Ba ta san ta ina za ta kama hanya ba.
Ta zauna tana kuka a hankali.Har yamma.
Ɗalibai suka fara watsewa.Harabar makarantar ta fara yin tsit..
A can Maitama kuwa…
Rayuwa ta ci gaba kamar babu wata halitta da aka bari a waje.
Sadiya tana sashenta, tana waya da ƙawarta Hajiya Sumayya.
Dariya take yi tana ba ta labarin nasarar da ta samu a daren jiya a wajen mijinta.
Ƙarfe takwas na dare.
Dukkan iyalan gidan sun hallara a babban dining.
Suna cin abinci cikin natsuwa.
Dr. Mariya ta ajiye cokali.
Ta ɗago.“Mami… wai ina Tadala ne?
Shiru.“Ban ga ta ba tun ɗazu.”
A take jinin Sadiya ya daskare.Gabanta ya faɗi.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Ta dafe ƙirji.“Tana can Base University!
TYa Allah… gaba ɗaya na manta da ita!”
Falon ya yi tsit.Alhaji Kamal ya ajiye cokali da ƙarfi.
Ya juyo sadiya Kin manta da ita?
Sadiya ta fara rawar jiki.
“Wallahi Daddy… na manta. Abubuwa sun carkame ni.”
“How comes?!” Dr. Mariya ta furta.
“Yarinya baƙuwa . Ba ta san gari ba. Ba ta da kowa. Yaya za ki manta da ita?”
Ahmad ya ajiye kofinsa.
“Mami… nima na zaci tana ɗaki maybe gajiyar school ne yasa bata fito ba shiyasa ban nemi ta ba.”
Hawaye suka cika idanun Sadiya.
“Allah Ka rufa mini asiri!
Ta fara kuka.“Idan wani abu ya sami yarinyar nan me zan ce wa su Uma a Nijar?”Alhaji Kamal bai ce komai ba.
Ya miƙe tsaye.Ya ɗauki makullin motarsa ta Mercedes-Benz G-Wagon.Ya fice.
Sadiya ta durƙushe tana kuka“Ya Allah… ka tsare mini ita.Falmata ta kalli Sadiya.
Ta taɓe baki.“Allah ya kyauta gaba.
A can Base University…
Duhu ya fara mamaye harabar makarantar.An yi kiran sallar Isha’i.
Sanyi mai karfi daga iskar Abuja yana kaɗawa.Tadala na zaune a kan benci.
Jikinta yana rawa.
Yunwa.
Sanyi.
Kaɗaici.
Ta takure guri guda.Ta rungume ƙafafunta.Hawaye suna zuba a fuskarta.Ta tuna papa.Ta tuna Uma., Mansoor,Fiza.
“Dama na sani…”
Ta fara shessheƙar kuka“banzo Najeriya ba…hawayenta suka ƙara zuba.
“Mami ta yaudare ni…”
Ta girgiza kai“Ta bar ni a nan… don na mutu.”A wannan lokacin…
Wani kare ya yi haushi daga wani sashe na makarantar. tadala ta firgita.Ta ƙara rungume jikinta.Fararen fitilun wata ƙasaitacciyar mota suka haske inda take zaune.