A Voice From Home
by @zahrabmrs02
Alhaji Kamal ya danna hancin G-Wagon ɗinsa ta cikin get ɗin makarantar. Hasken motar mai ƙarfi yana haska kusan duk wani lungu da sako na harabar Base University. Ya riga ya zagaye kusan rabin makarantar, zuciyarsa cike da tunani kala-kala.
Ya Allah, idan yarinyar nan ta fita waje fa? Idan wani ya ɗauke ta? Yar amana ce aka bani daga wata ƙasa…
Hannunsa ya ƙara matse sitiyari.
Yana shirin juya motar zuwa yankin babban ɗakin taro, sai idanunsa suka hango wata siffa takure a kan wani benci ƙarƙashin inuwar bishiyoyi.Da sauri ya taka birki.
Ya kashe hasken motar, ya buɗe ƙofa ya fito.takunsa masu nauyi suka dinga karasowa a hankali.
A can, Tadala ta ji motsi. Da kyar ta ɗaga kanta. Jin takun takalmi yana ƙara matsowa ya sanya gabanta faɗuwa.Ta miƙe da ƙyar.Ta fara ja da baya. idonta cike suke da firgici.
Ba ta iya ganin ko waye saboda duhun.ganin yadda take rawa kamar wata ƙaramar tsuntsuwa da aka jefa cikin ruwa, Alhaji Kamal ya tsaya cak.Ya sassauta muryarsa.
“Tadala…”
Ta ci gaba da ja da baya.
“Kar ki ji tsoro…” ya sake faɗa cikin nutsuwa. “Nine… Alhaji Kamal.”
muryarsa ta shiga kunnenta, sai taji kamar an zare wani dutse daga ƙirjinta.Take ta fashe da wani irin kuka.Envelope ɗin dake hannunta ya zame ya faɗi ƙasa.
“Alhaji…!” ta kira cikin muryar kuka.duk tsoron da ta danne tun rana ya fashe gaba ɗaya.
Tana kuka kamar ƙaramar yarinya,Alhaji Kamal ya tsaya kawai yana kallonta.
Wani irin tausayinta ya cika masa zuciya Yarinya ce ƙarama Ba ta san gari ba Ba ta san kowa ba tadala ta yi ƙoƙarin takawa zuwa gare shi.
Sai dai tana yin taku biyu, jiri mai ƙarfi ya kwashe ta.Jikinta ya yi laushi
Da sauri Alhaji Kamal ya ƙarasa ya tare ta.Ya kama ta da kyau.
Jikinta na wani irin rawa saboda sanyi ya dafe bayanta cikin kulawa.
“Sannu… sannu…”
Bata ma iya amsawa ba.Ya tallabe ta a hankali.Taku bayan taku Har suka isa gaban motar Ya buɗe mata ƙofar gaba Ta shiga tana rawar sanyi shima ma ya zagaya ya shiga.
ya tada motar, ya lura yadda take ta ƙanƙame jikinta.Ba tare da ɓata lokaci ba, ya rage ƙarfin AC ɗin motar gaba ɗaya ya maida shi dumi Tadala ta sauke numfashi.
Amma har yanzu ƙwalla na zuba a fuskarta ,Alhaji Kamal ya kalleta.
Ya Allah…Yau karon farko ya ga yarinyar nan ta ba shi tausayi sosai.
Bai yi magana ba..Bayan sun fito daga makarantar, ya tsaya a wani babban shagon cin abinci da ke kusa Mintuna kaɗan.
Ya dawo riƙe da wata leda Ya shiga motar Maimakon ya ci gaba da tafiya gida, ya faka a gefe Ya miƙa mata ledar “Gashi… ki ci. Ta kalli ledar.kafin mu isa gida, ki ci ki ji ɗumi a jikinki.”
Ba tare da ɓata lokaci ba, Tadala ta karɓa Ta buɗe ledar Shinkafar tana fitar da hayaki saboda zafi Sam ta manta da kunya Ta shiga cin abincin da sauri Loma bayan loma.
Alhaji Kamal kuwa ya gyara zaman gilashinsa Ya juya gaba ɗaya yana kallonta Yana kallon yadda take cin abincin cikin tsantsar yunwa Ba wani iya bariki.
Tadala tana cikin cin abincin ne ta ɗago taga yana kallonta Take ta daburce Ta yi saurin sauke idanunta Kunya ta kamata Har ta kusa ƙwarewa.
Ganin haka, Alhaji Kamal ya buɗe robar ruwan Swan Ya miƙa mata.
“Sannu… sannu.”
Ta karɓa tasha tare da sauke wata ajiyar zuciya.
“Ya kike jin jikin naki yanzu?”
Ta ɗago.“Naji sauƙi… nagode.”
Sai kuma muryarta ta canza“Amma Alhaji… ni dai zan koma Nijar wajen su Uma.”Alhaji Kamal ya ɗaga gira.
“Me yasa?Ta haɗiye yawu.“Gidan nan akwai wahala…l
Alhaji Kamal ya gyara zamansa Ya girgiza kai.
“Ai kuwa ba inda zaki je.Ta ɗago ta kalle shi.“Sai kin gama karatun da kika zo yi ,ya ɗan yi shiru ke raguwa ce haka? kowane mutum a duniya yana fuskantar jarabawa kafin ya kai inda yake so. Wannan ƙaddara ce ta kawo ki nan. Dole ki jure. tadala ta kasa jure kwarjininsaTa sunkuyar da kai.
Ta fara wasa da yatsunta ,Alhaji Kamal ya tada motar kada ki sake mini maganar komawa Nijar.”
“toh … Daddy.Ya ci gaba da tuƙi.
A can gidan Maitama kuwa, motar ta tsaya Alhaji Kamal ya kashe injin Ya fito Ya zagaya,Ya taimaka wa Tadala ta fitoHar yanzu jikinta babu ƙarfi suka nufi cikin gidan.
Gaba ɗaya mutanen gidan suka miƙe Sadiya ta yi saurin tashi.
“Hubbi
Ya dubeta da wani irin kallo mai nauyi ,sannan ya ce“Biyo ni ɗaki.”
Gabanta ya faɗi Ta bi bayansa zuwa sama.
A ƙasa kuwa…
Ahmad ya yi saurin zuwa gaban Tadala.“Anty Tadala
Amal ma ta riƙe hannunta. Gaba ɗaya hankalinmu ya tashi.”
Iklas ma ta matso Tadala ta kasa magana kawai ta dinga jinjina kai.
Idanuwanta cike da ƙwalla Dr. Mariya ta matso.Ta taɓa wuyanta.
Take ta ji zafin zazzabi Ta juya.
“Ahmad, matsa. Ta sake kallon Tadala.
“Tana buƙatar drip. Jikinta ya bushe.”Nan take ta taya Tadala zuwa ɗakinta.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta ɗaura mata drip cikin gwaninta.Ta gyara mata kwanciya.
Ta rufe ta da bargo mai kauri.
A wannan lokacin ne Alhaji Kamal da Sadiya suka shigo idanun Sadiya sun yi jawur saboda kuka.
Ta kalli yadda Dr. Mariya ke kula da Tadala ta sauke numfashi.
“Dr… nagode sosai.”
Dr. Mariya ta gyara mayafinta.
“Ba damuwa.”
Ta ɗan yi shiru.
“Sai dai ka ƙara wa Sadiya faɗa, Alhajina. Idan ta san ba za ta iya kula da yarinyar nan ba, gara ta maida ta ƙasarta.”
Sadiya ta yi ƙasa da kai.
Alhaji Kamal ya kalli Dr. Mariya inshaAllah Dr zaa kiyaye an gode Allah ya miki albarka
“Dama bakya abu dan Allah Mariya. Sai kin saka magana a ciki wato har da cewa a mun fada sadiya ta ayyana a ranta
Amma ba irin Hajiya Falmata ba ce.
Falmata sam ba ta cika shiga sabgar cikin gida ba.Tun da aka kawo Tadala ma, ba ta taɓa yin magana a kanta ba.tun wata rana Sadiya ta rage kishinta gare ta.
Wata rana tana zaune cikin motarta a parking lot motar tinted ce.
Tana shirin fitowa sai ta ji muryar Falmata a waya.haba ke kuwa Yagana! Wallahi ni ba ni da lokacin kishiyoyina.Sadiya ta yi luff.
“Kina ganin sanda ya auri Buzuwar nan, kin ga na tada hankali?”
Ta yi dariya.“Nifa mijina ne a gabana. Neman Aljanna nazo yi, ba zaman kishi ba.”
Ta ci gaba.
“Ba zan taɓa zama ƙawance da su ba, kin san bana iya pretending. Kowacce ta yi harkar gabanta.” kuma kar ki kara min maganar boka ko malam ko wani bana so i cant tread my iman akan wani namiji
Tun daga ranar…
Sadiya ta gane tana wahalar da kanta ne.Domin ko sau ɗaya ba ta taɓa kama Falmata da wata makirci ba.
Focus ɗinta kawai yana kan mijinta da rayuwarta.Bayan ɗan lokaci…
Magungunan suka fara aiki.
Zafin jikin Tadala ya ragu A hankali ta yi barci.
AsubaTadala ta tashi Ta yi sallah Ta lura an cire mata drip
Umma ce ta shigo cikin dare ,kenan ?ta sake komawa ta kwanta bacci ya sake ɗaukarta
tana buɗe idanunta ta ga wata siffa zaune kan kujerar L-shaped Ta guntse gashinta Ahmad ne Yana kallonta
“Anty Tadala! Sannu! Ya kike jin jikin naki?”“Alhamdulillah… na ji sauƙi.”Ya sauke numfashi.
“Gaskiya hankalinmu ya tashi jiya.
“Da asuba Mami da su Twins sun zo dubaki. Amma kina barci wani dumi ya ratsa zuciyar Tadala.“Nagode sosai Ahmad.”Ya ɗauki wayarsa.
“To bari na kira Bintalo ta kawo miki breakfast.”Take idanunta suka haska.Ta tuna su Uma.
Ta kalli Ahmad.“Don Allah… za ka ara min wayarka? Ina son jin muryar su Uma.”“Haba! Babu komai.”
Ya buɗe wayar.Ya miƙa mata.Tadala ta karɓa da sauri.Ta danna lambar da ke ƙwaƙwalwarta.
Bugu ɗaya.
Biyu.
muryar Uma ta ratsa kunnenta.
uma !”
Take hawaye suka cika mata ido.
“tadala …”
Suka gaisa .suna tambayar lafiyar juna daga nan ta gaisa da Papa.
Sai Aghali.
“Yaya! Ina kewarki!”
Tadala ta yi murmushi cikin kuka.
“Nima ina kewarka.”
Ta share hawayenta.
“Uma… Papa… ku kwantar da hankalinku. Ina lafiya. Wannan wayar Ahmad ce na aro. Idan an siya min layin Najeriya zan kira ku da sabuwar lambata.”
Suka yi mata addu’o’i.
Ta amsa tana murmushi.
Bayan sun gama sallama…Ta miƙa wa Ahmad wayar.
A karon farko tun zuwanta Abuja…
Ta ji wani irin sanyi da kwanciyar hankali a zuciyarta.
Yanzu ta sake samun ƙarfin guiwar fuskantar duk wata ƙaddarar da ke jiranta a birnin Abuja.