Queen Of Baze
by @zahrabmrs02
A haka Tadala ta ƙarasa sauran kwanakin ƙarshen mako cikin jinya da hutu. Sadiya dai ba laifi, ta ɗan kula da ita saboda abin da ya faru ya firgita ta ƙwarai. Shi kuwa Ahmad, kusan kullum yana shiga ya duba lafiyarta, ya tabbatar ta ci abinci ko ta sha magani.
Dr. Mariya kuma, duk lokacin da ta samu sarari, sai ta shigo ta duba jikin Tadala cikin kulawa irin ta likita da uwa. Wannan abin ya sanya Tadala ta kasa gane dalilin da ya sa Mami ba ta taɓa ganin alherin Dr. Mariya ba.
Daren Lahadi, Tadala ta fito da kayan da za ta sa gobe zuwa Base University.
Doguwar riga ce ta al’adar Buzaye, an ɗinka ta cikin baƙi da fari, mai sauƙin gani amma cike da armashi da mutunci.
Ta shafa kayan da hannu, sannan ta murmusa a ranta.
“Ni kam ba zan taɓa jin kunyar mutanena ko inda na fito ba. Ko mutane za su yi dariya, su yi. Zan ci gaba da saka kayan al’adarmu cikin alfahari.”
Tana cikin tunanin ne aka turo ƙofa.
Ahmad ne A hannunsa wata ƙaramar leda ce.
“Anty Tadala!” ya kira yana murmushi. “Ga sabon SIM card na siyo miki, har na yi miki registration..
“Da gaske?”
“Eh mana.Ta karɓi ledar da hannaye biyu.
“Merci beaucoup, Ahmad… Nagode sosai. Can kuma ya zura hannu cikin aljihu, ya fito da wata wayar Samsung mai kyau“Ga wannan ma.”Tadala ta ɗaga kai cikin mamaki Wayar wa ce?
Tsohuwar wayata ce. Yanzu bana amfani da ita. Gabanta ya ɗan faɗi. Ka faɗawa Anty Sadiya za ka ba ni?
Ahmad ya ɗaga kafaɗa. A’a… amma ai ba za ta yi faɗa ba.
Kafin ta sake magana, ya zauna kusa da ita, ya sa mata layin, ya yi mata settings, ya buɗe mata WhatsApp, ya kuma saka mata wasu muhimman apps.
Tadala tana kallonsa cikin mamaki“yaron nan mai kirki ne sosai…”
Wayewar garin Litinin.
Tadala ta shirya cikin kayan Buzayen nata. Allah ne Shaida, ta yi kyau.
Baƙin kayan da farin zane-zanen da ke jikinsu sun fito da hasken fuskarta. Gashinta mai laushi yana kwance bisa kafaɗarta.Ta fito zuwa sashen Mami domin yin breakfast.Sadiya tana zaune tana shan shayi.Ta ɗago kai, ta kalli Tadala daga sama har ƙasa.
Girgiza kai ta yi.
“Ke yanzu, a haka za ki tafi jami’a?”
Eh Anty Sadiya.
“To shikenan. Idan kika zama abin dariya a can, ke kika sani.
Tadala ta sunkuyar da kai kawai.Ta tuna wayar da Ahmad ya ba ta.Ta ɗora ta kan tebur. Ahmad ne ya kawo min waya da layi jiya.
Sadiya ta ɗago kai.
“Ahmad?”
Daidai lokacin yaron ya shigo falon. rokanka ta yi ka saya mata waya? A’a Mami. Na ga tana buƙatar wayar ne saboda karatu. Sadiya ta ja numfashi.
Ahmad, kada ka sake yanke hukunci a gidan nan ba tare da sanina ba.“To Mami.
Sannan ta juya wajen Tadala.
Malam Awaisu zai kai ki makaranta. Ga adireshin gidan nan. Idan kun gama kuma, ga kuɗin taxi.
Ta miƙa mata kuɗi tadala ta amsa.
“Nagode.”
Ta juya za ta fita.“Ki ɗauki wayar mana”
Da sauri ta dawo ta ɗauka, sannan ta fice.
Malam Awaisu ya kai ta har gaban Department ɗinsu.Bayan ta yi masa godiya, ta sauka.A hankali ta isa ƙofar ajinsu.Ta yi sallama.Assalamu alaikum.”
Nan take hayaniyar ajin ta tsaya kowa ya juya yana kallonta Tufafin al’adarta sun sa ta fito daban da sauran ɗalibai.
Ga fuskar nan kamar an zana ta.Ga dogon gashin Ga nutsuwa da kunya.Tadala ta ji kamar idanun mutane sun mata yawa.
Ta sunkuyar da kai ta wuce can bayan aji ta zauna.Ta fito da wayarta.
Tana ƙoƙarin nemo lambar Mansoor kafaɗarta aka dafa Ta juyo.“Laaa! Farida!”kinzo ?Farida ta turo baki.
“Eh na zo. Amma gaskiya na yi fushi da ke.”“Me na yi?”
“Na ba ki lambata tun Friday. Ban ga kira ba.”
Tadala ta marairace fuska.
“Kiyi haƙuri. Rashin lafiya na yi wallahi. Zazzabi mai zafi. Sai jiya aka ba ni layin Najeriya.”kuma naga dare yayi shiyasa ban kira ba
Farida ta ɗaga gira.“Waye ya gaya miki ina yin barcin dare da wuri?”
Dukansu suka yi dariya.Kafin su ƙara magana Lecturer ya shigo.
Nan take kowa ya gyara zamansa.
Ya gabatar da kansa sannan ya ce kowa ya tashi ya yi introducing kansa tunda sabon lecturar ne be koyar dasu a level 100 da 200 ba Har aka zo kan Farida.
Ta miƙe.“I am Farida Abubakar, from Yobe State, but I reside in Abuja.”
Ta zauna turn din tadala yazo .gabanta ya buga.
Ta miƙe.Je m’appelle Tadala…Da sauri ta rufe bakinta fuskarta ta yi ja..Ta gyara.
“I… I am sorry. My name is Tadala Attaher. I am from Niger Republic. Wasu suka yi murmushi.wasu kuma suka kaɗa mata tafi.Tadala ta sake jin kunya.Amma wani sanyi ya shiga ranta Babu wanda ya yi mata ba’a.
Bayan an gama lecture ɗin waasu ’yan mata biyu suka zo gabanta.
“Hi beautiful!”
Suka yi mata maraba suka gaya mata cewa su sun daɗe a ajin tun daga Level One kuma dukansu family ɗaya ne.Tadala ta yi musu murmushi cikin kunya Ba ta saba sabo da mutane da wuri ba Daga baya aka fara batun Assistant Class Captain.
Najaatu Sani, tsohuwar Assistant, ta koma Cyprus da karatu.Kowa ya fara cewa,
“A ba Tadala.“Ai ita ya kamata.Tadala ta kaɗa hannu A’a! Non! Ba zan iya ba.”
Dariya ta barke.“Me yasa?
Ni ma ba jin Turanci sosai nake yi ba.
Suka ƙara dariya wani ya ce,Ai saboda haka ma muke son ki. Ke baƙuwarmu ce daga ƙarshe…
An rubuta sunanta Ta zama Assistant Class Captain.
Lokaci ya wuce.
Tadala ta fara sabawa da rayuwar jami’a.Farida ta zama babbar ƙawarta.
Har ta kai tana jin kamar sun daɗe suna tare tun suna yara. kwana ya juya mako.Mako ya juya makonni.Har makonni uku suka cika.
A gida kuwa…Babu wani canji.
Dangantakarta da mutanen gidan ta tsaya ne a gaisuwa.akwai ranar da Tadala ta dawo daga jami’a, ta shiga kitchen domin ɗauko ruwan sha. Sai ta tarar da Ameenatu da Kuna zaune a kan stools suna cin snacks suna hira.
Ameenatu na hango ta, sai ta ɗaga gira ta kalli Kuna. Kin lura kuwa, Kuna? gidan ya samu sabuwar sarauniya.
Kuna ta ɗan yi dariya. “Wallahi kuwa. Kullum sai ado kamar za ta je bikin sarauta.
Tadala ta yi kamar ba ta ji abin da suka ce ba. Ta buɗe fridge ta ɗauko robar ruwa.
Ameenatu ta sake cewa cikin sigar habaici, “Kuma wai an ce har a makaranta ana kiranta The Queen of Base. Kai! Wasu mutanen ma suna son ɗaukar kansu da muhimmanci.” queen of kauye taje tana fafa da da sunan daddy a base
Kuna ta ɗaga kafaɗa. “Ni dai ban ga abin burgewa ba. Kyau kawai ba shi ke sa mutum ya fi kowa ba.”
A hankali Tadala ta juya ta kalle su. Duk da kalaman sun ɗan soki zuciyarta, ta daure ta ce cikin ladabi:
“Ni ban taɓa cewa na fi kowa ba. Kuma ba ni na sa wa kaina wannan sunan ba.
Ta ɗauki ruwan da ke hannunta ta juya za ta fita.
Ameenatu ta taɓe baki. “Mtsww! ”
Tadala ta fita daga kitchen ɗin cikin sanyin jiki. Ta ji maganganunsu sun ɗan taɓa zuciyarta, amma sai ta tuna maganar Hajjo“Mutunci ba ya cikin abin da mutane suke faɗi a kanki, yana cikin yadda kika zaɓi amsawa.
A hankali ta share ƙwallar da ta taru a idanunta ta nufi ɗakinta ba tare da ta sake cewa komai ba.Abin da ya fi ba ta mamaki shi ne rashin ganin Mama Adiza.
Wata rana ta tambayi Mami.Anty Sadiya… Yaushe za mu je wajen Mama Adiza?”
Mami ta kalle ta.
“Ai Mama ba jiha ɗaya muke ba. Ita tana Zaria.“Oh…”
Nan maganar ta ƙare.
Wata rana.
Tun bayan lecture na ƙarfe takwas na safe…Ba su sake samun lecturer ba. sai sai ƙarfe huɗu.
Farida ta yi ajiyar zuciya.
Tadala… mu tafi gida mana.
“Gida?
“Eh. .
Tadala ta kalli lokaci ƙarfe goma.
Suka shiga motar Farida abin mamaki…
Gidansu bai da nisa da makarantar Suka shiga wani haɗaɗɗen estate Motar ta tsaya gaban wani kyakkyawan gida.
Farida ta buɗe Suka shiga. idon Tadala suka buɗe. kujeru masu tsada Turare mai ƙamshi komai cikin tsari.
Ta juya.
“Farida… yan gidanku ba sa nan ne?”
Farida ta yi dariya.
“Waye ya ce miki tare da su nake zama?”
Ta nuna kanta.
“Ni kaɗai nake zama a nan.”
Idanun Tadala suka zaro.
“Ke kaɗai?!
“Eh.
Ta girgiza kai.
kar ki damu da tambayoyi yanzu. Ga remote ki kunna TV.
Tadala ta zauna cikin mamaki.Rayuwar ’yan birni ta ba ta mamaki Bayan ɗan lokaci…Farida ta fito da babban tire.Noodles ne da aka shaƙe da sardines,Ga yogurt ,Ga Civita,Ga inibi mai sanyi Suka fara ci suna hira.
Can Farida ta kalli jikin Tadala.Ta yi ajiyar zuciya You are blessed.
Tadala ta ɗaga kai.
Dubi yadda Allah ya ba ki kyau da surar jiki. wasu sai sun kashe kuɗi kafin su samu irin wannan shape din ta hanyar yin BBL tadala ta haɗe gira.
menene kuma BBL?
Farida ta bushe da dariya.
No worries, my friend. Za ki sani nan gaba. Bayan sallar La’asar suka koma makaranta already Malamin ya riga ya fara lecture sai da suka yi tsaye a bakin ƙofa suna ba da haƙuri da yake private university ce ba wata takura sosai ya barsu suka shiga.
Bayan ya gama lecture, ya ce,class Captain da Assistant dinsa su tsaya.
Garba da Tadala suka miƙe.
Malamin ya kalli Tadala.Ya gane ita ce ta shigo a makare Ya ɗure fuska.You? Wannan late-comer ɗin ce Assistant ɗinku?
Ajin ya yi tsit.
“You people need to do better. Ya juya ya fita.Tadala ta tsaya jikinta ya yi sanyi.Farida ta taɓa hannunta“Kada ki damu. Ta jinjina kai.Amma maganar ta tsaya mata a rai.
Lokaci ya yi gudu.An kawo ƙarshen zangon farko.An gama exams.Hutu ya kama tadala ta dawo zaman gida.
Sam zaman bai mata daɗi ba.Amma…
A Base University kuwa…Sunanta ya riga ya bazu kusan kowane sashe ya san ta samari kala-kala suna neman saninta Wasu saboda kyantaWasu saboda nutsuwarta Wasu saboda asalinta na Nijar.
Har aka fara kiranta da suna guda
“The Queen of Base.”
Sai dai…duk da yawan masoyan da suka kewaye ta…Fafur Tadala ta ƙi ba kowa dama Domin zuciyarta tana can Agadez…Tana riƙe da sunan mutum guda.Mansoor.
Kuma wannan kamun kai nata ne ya ƙara ɗaga darajarta a idon kowa.A hankali…
Ba tare da ta sani ba…
Sarauniyar Base University ta fara zama tauraruwa a rayuwar mutane da dama.