Zumar Hamada 🍯 🏜️

Unexpected Encounters

by @zahrabmrs02


Ameenatu ta haihu, har ta cika kwanaki arba'in (40 days) na riga-kafin jego, ta shirya kayanta ta koma gidanta na aure. Wannan tafiya ta Ameenatu ya zama babban abinda ya yaye wa Tadala wani babban nauyi da baƙin ciki ; a take ta ji daukacin ranta ya yi mata fari sarai saboda samun sassauci.

Wata rana da daddare, bayan kowa ya yi barci, Tadala ta tashi daga kan gadonta  saboda tsananin ƙishirwar da ta tashe ta. Ta fito babban falon ƙasa cikin sanyin jiki, tana tafiya a hankali cikin duhun daren. Kwatsam, tana daf da ƙarasawa gun firiji, sai ta yi karo da wata doguwar siffar mutum a tsaye.

Cikin tsananin tsoro da fargaba, jikinta ya ɗauki rawa, ta ce cikin muryar kuka, "Waye...?"

"Shiiii..." Ta ji an yi mata alamar lallashi cikin muryar ƙasa-ƙasa dake cike da iko. "Calm down, nine."

Wata ajiyar zuciya Tadala ta sauke a lokacin da ta gane ashe Daddy ne (Alhaji Kamal). Yau da yake kwanan Falmata ne kuma tana can Maiduguri, shi yasa Daddy ya kwana shi kaɗai a sashensa, ya sauko ƙasa domin dakin karatunsa (study room) yana daf da dakin Tadala.

"Ina yini ... Good evening Daddy, ban sani ba ashe kai ne," ta faɗa cikin sanyin murya tana gaishe shi.

Kafin ma ya amsa mata, ta nufi firijin falon da sauri, ta ɗauki  ruwa mai sanyi. Ta juya da niyyar ta wuce ta koma ɗakinta, sai ta ji muryarsa ta manyan maza ta daki kunnenta.

"Ya makaranta ?"

Ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba, "Alhamdulillah, Daddy."

"Babu wata matsala?" ya sake tambaya cikin kulawa.

A lokacin, wani ɓangare na zuciyar Tadala yana hanzarin gaya mata cewa ta faɗa masa gaskiyar abin da yake faruwa; ta shaida masa yadda kuɗin motar haya (taxi) da Sadiya take ba ta da kyar yake isarta, har takan tsaya ciniki da masu mota a titi, ga shi ko sisi Sadiya ba ta taɓa ƙara mata ba, wanda shi ne ma ya sa yanzu take haɗawa da ruwanta da abincinta daga gida idan za ta tafi Base University.

Amma saboda fargaba da tsantsar kunya, sai ta dake ta ce, "Babu kowace matsala Daddy, nagode."

Ta gilgiza da sauri ta shige ɗakinta cikin hanzari. Sai a lokacin da ta shiga ciki ne ta tuna ashe da ƙaramar riga ta barci dake jikinta ta fito falon; take kunya ta kama ta, zuciyarta ta ci gaba da dukan sauri.

Wayewar garin gaba, Tadala ta shirya ta fito babban falon cin abinci (dining table) na ɓangaren Mami (Sadiya). Ta iske Alhaji Kamal zaune sanye da riga da wando na cotton masu laushi yana  (breakfast) duk sanda falmata tayi tafiya  a part din sadiya yake breakfast 

"Ina kwana Anty... Ina kwana Daddy," Tadala ta gaishe su cikin ladabi.

Sadiya ta amsa mata sama-sama, shi kuwa Daddy ya kaɗa mata kai yana amsa gaisuwar cikin natsuwa.

Abin mamaki, sai ga su tagwayen Mami (twins) har da haɗa baki wajen cewa, "Ina kwana Anty Tadala!"

Tadala ta ɗan yi mamaki, amma ta fahimci cewa sun yi hakan ne kawai saboda ganin idon Daddy da ke zaune a teburin. yaranda  ko hira ba sa taɓa yi da ita ta rasa me ta masu haka .

Gefe guda ta zauna a raƙube, nesa da kowa, ta ɗauki sandwich ɗinta ta fara ci a natse cikin kwantar da hankali. Yau Ahmad bai tashi da wuri ba, shi yasa duk ta ji teburin cin abincin bai yi mata daɗi ba, domin a duk cikin gidan, shi ne wanda yake nuna mata ainihin ƙauna da kula.

Tana tsaka da cin abincin, ta ɗago kanta ke nan, suka haɗa ido daram da Alhaji Kamal. Wani irin kallo yake jifanta da shi ta gefen gilashinsa—kallo mai nauyi, cike da  shauƙi 

Ay kuwa a take Tadala ta daburce, numfashinta ya sarƙe, ta soma tari ta ƙware  saboda kaifin kallon da yake mata.

Sadiya da ke zaune ta yi saurin kallonta, ta taɓe baki ta ce, "Har yanzu dai kin ƙasa sabawa da cimar Abuja, Tadala. Yanzu menene na ƙwarewa a nan?"

Tadala ta shiga rige-rigen neman ruwa tana tari,  ta lura babu wanda ya tura mata kofin ruwa a cikin yaran ko Sadiya. Ganin haka, ta sanya hannu da kanta ta ɗauko ruwan ta sha, sannan ta dawo daidai. Shi kuwa Daddy, a take ya canza salon fuskarsa kamar ma baya cikin mutanen da ke zaune a teburin, ya ci gaba da juya jaridarsa cikin natsuwa...


Bayan sun tashi daga teburin abincin, Tadala ta fito da sauri ta shiga motar Malam Awaisu domin ya kaita makaranta. Tafiyar duka cikin shiru suka kalmisa ta har suka isa harabar jami'ar Base University. Malam Awaisu ya kashe motar, sannan ya juyo ya miƙa mata wani farin ambulof (envelope) mai kauri.

"Gashi, inji Alhaji," ya faɗa a taƙaice.

Gaban Tadala ya fadi daram, zuciyarta ta shiga fargaba. Ta kalli ambulof ɗin, ta kalli Malam Awaisu ta ce, "Wani Alhajin kuma?"

"Wanda kika sani mana. Alhaji Kamal. Ya ce na baki maza maza ki ɓoye," Malam Awaisu ya ba ta amsa yana murmushi.

Cikin sanyin jiki da fargaba Tadala ta ɗan ɓulla bakin ambulof ɗin ta leƙa. Gabanta ya ƙara tsananta wajen faduwa a lokacin da ta gani damin kuɗi ne sababbi, gaba ɗayansu 'yan dubu-dubu ne makil. Ganin yadda lafazin fuskarta ya canza kuma ta firgita, Malam Awaisu ya dafa sitiyarin motar ya ce, "Kada ki damu Tadala, kar ki ji tsoro. Haka fa Alhaji yake, yana da kyautar ban mamaki. Mu kanmu ma’aikatansa yana bamu maƙudan kuɗi a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba. Ina ga kuɗin kashewa ne na makaranta ya ba ki."

Jin haka ya sa hankalin Tadala ya ɗan kwanta, ta sauke ajiyar zuciya tare da ayyana cewa tunda yana kyautar asiri ga kowa, ashe ba ita kaɗai ba ce. Cikin karamci ta zura hannu ta ciro takarda guda biyar (₦5,000) ta miƙa wa Malam Awaisu ta ce, "Merci beaucoup... Ga wannan ka sayi ruwa." Sosai Malam Awaisu ya yi murna ya nuna godiyarsa, sannan ta fito ta nufi cikin makarantar.

A ranar, bayan ta shiga aji, ta shafe sa'o'i tana fuskantar karatu gami da yin hira da su Mufida da Aliyya, waɗanda suka zama abokan hira tun bayan da aka zaɓe ta a matsayin Assistant Class Captain. Sai dai gaba ɗaya jikin Tadala ba dadi saboda rashin ganin ƙawarta Farida tun sassafe.

Misalin ƙarfe ɗaya na rana (1:00 PM) aka kammala dukkan darussan ranar. Tadala ta fito ta ɗauki wayarta ta kira Farida domin ta ji dalilin rashin zuwanta.

Daga ɗayan ɓangaren, muryar Farida ta fito a mace, tana rawar sanyi, "Tadala, ba ni da lafiya ne wallahi, shi yasa ban sami damar zuwa makaranta ba."

Cikin damuwa Tadala ta ce, "Subhanallah! D'accord (shikenan), bari na taho yanzu na duba jikin naki mu gaisa."

"Farida, me na gani haka? Gaba ɗaya sai zufa kike yi kamar wadda ta yi tseren gudu, ga fuskarki ta canza!"

wallahi tadala zazzabin ne ya sauka shine nake ta zufa kamar na hadiye kwado "

Bayan sun zauna a falo  Tadala ta kara  mata sannu da jiki, sai ta kasa daurewa. Tambayar da take addabar zuciyarta tun makonni uku da suka gabata ta taso mata.

"Farida, don Allah ina son tambayarki wani abu na rasa wanda zan tambaya a gidanmu. Ranar nan kika ce mini ana kashe  kuɗi ayi  yi BBL, menene ma'anar abun nan ne wai?"

Farida ta bushe da dariya mai sauti,  ta ce, "BBL ma'anarsa Brazilian Butt Lift. Wata irin tiyata ce ta zamani (surgery) da likitoci ke ɗaukar kitse daga cikin mutum ko babbakensa su mayar da shi bayan sa da kwankwasonsa domin jikinsa ya fito da kyawun sura da ciko na musamman."

Tadala ta zaro idanu cikin firgici ta dafe baki, "Haba? Ikon Allah! To amma Farida, me yasa har mutum zai jure zafi yaje  a  masa  wannan abun?"

Farida ta runtse idanu tana murmushin alfahari, ta kalli Tadala ta ce, "Saboda masu irin  sana'ata 

"Sana'a kuma? Wace irin sana'a ce wannan da take buƙatar canza fasalin jiki?" Tadala ta tambaya cikin tsananin rashin fahimta.

Farida ta tsurawa Tadala ido, ta rage murya ta ce, "I am a stripper." (Ni mai rawar taya maza nishaɗi ce a gidan dare ba tare da kaya ba sai pant da bra .

Nan take Farida ta shiga fassara mata daki-dakin abin da kalmar take nufi da yadda take samun maƙudan kuɗi a gidan dare wajen rawa tsirara a gaban manyan maza masu kuɗi na Abuja. Tadala ta saki baki da hanci, idanunta sun kaɗa sun yi jawur, ta gaza cewa uffan saboda tsantsar mamaki da tsoron irin rayuwar da ƙawarta take yi a birnin.

A daidai wannan lokacin, a can tsakar rukunin ofisoshinsa na alfarma da ke cikin babban birnin Abuja, Alhaji Kamal yana zaune a kan kujerarsa ta alfarma. Yana sanye da fararen kaya na alfarma, gashin kansa ya sha gyara. A zaune a gabansa akwai aminin sa na jiki kuma babban abokin kasuwancinsa, Alhaji Mukhtar.

Alhaji Kamal ya ajiye biros dinsa, ya lula cikin duniyar tunani, can ya kalli aminin nasa ya ce cikin muryar manya, "Mukhtar, ina cikin tsananin soyayya. I am deeply in love."

Alhaji Mukhtar ya tsagaita da duba takardun da ke hannunsa, ya ɗago kai yana kallon Kamal cikin tsananin mamaki gami da fuskantar cewa abokin nasa da gaske yake.

"Ban gane ba, Kamal? Kana da mata har guda uku a gidanka—Sadiya, Dr. Mariya, da Falmata—kuma yanzu kake maganar kana cikin soyayya kuma?" Mukhtar ya tambaya yana girgiza kai.

Alhaji Kamal ya kaɗa kai, idanunsa suka yi haske da irin tunanin kyakkyawar fuskar  da take  ta ruda masa tunani, ya kalli aminin nasa ya ce, "Yeah, you heard me right... Na kusa hauka a kan yarinyar nan, kuma ko muddin hakan zai janyo kowace irin dambarwa ko tashin hankali (against all odds), sai ta zama tawa!"


Tadala ta saki baki ta zuba wa Farida idanu cike da tsantsar mamaki da kaɗuwa bayan ta ji ainihin sana’ar da ƙwawayar tata ke yi ta stripping.

Ganin yadda Tadala ta firgita, Farida ta ɗan taɓe baki tare da gyara zamanta, "Me nene na mamaki a nan Tadala? Ni na zaɓar wa kaina hakan, don a gani na, shi ne mafi mafita a gare ni. Amma kada ki damu, muna gama school ɗin nan, Sugar Daddy na ya yi mini alƙawarin samar mini da aiki a bankin CBN. Zan daina da zarar na samu, kin ga na sami mafita kenan ko?"

Tadala ta yi jimm cike da tunani a ranta. Tsaf Farida ta lura da yanayin shurun nata, sai a lokacin kuma idanunta suka sauka a kan babban ambulof ɗin dake riƙe a hannun Tadala.

"Ƙawata, menene a cikin wannan ambulof ɗin?" Farida ta tambaya tana nuna hannunta.

Tadala ta kalli ambulof ɗin sannan ta kalli Farida, "Kuɗi ne... Mijin cousin ɗina da nake zama a gidansu ne ya ba (driver) ya kawo mini."

Farida ta zaro idanu cike da zumuɗi, "Ah! Lallai kuɗi ne masu yawa a ciki, buɗe mu gani!"

Haka kuwa aka yi. Nan take Farida ta karɓi ambulof ɗin ta fito da tulin kuɗin ta soma ƙirgawa. Tana gamawa ta zaro idanu waje cike da mamaki, "Dubu ɗari biyar ne cif (\bm{500k})! Me yace kiyi da waɗannan maƙudan kuɗi?"

Tadala ta ɗan turo baki, "Wai na sayen abubuwan buƙata na makaranta ne."

Farida ta sheƙe da dariya, "Lallai kam! Na ga alama har yanzu ba ki saba da yanayin kuɗinmu na Najeriya ba. Dubu ɗari biyar na makaranta? Ya kamata ki buɗe asusun banki (bank account) yanzu ki riƙa saka kuɗinki a ciki."

Tadala ta girgiza kai, "A'a, zan fara nuna wa Anty Sadiya tukunna."

Farida ta haɗe gira, "Wace kuma Anty Sadiya?"

"Cousin ɗina ce, wacce mijinta ya ba driver ya kawo mini kuɗin."

"Haba dai Tadala! Wace irin magana kike yi haka?" Farida ta katse ta da sauri. "Da yana so ta sani, ai ba zai ba driver a ɓoye ya kawo miki ba! Don haka kiyi shiru da bakinki, kar ki kuskura ki faɗa mata."

Tadala ta jinjina kai, "To shikenan. Yanzu zan iya tura wani sashi na kuɗin can ƙasarmu ta Nijar?"

Farida ta yi murmushi, "Of course! Za ki iya tura masa mana."

Tadala ta kalli kuɗin sannan tace, "To shikenan, raba kuɗin gida uku. Ki ɗauki kashi ɗaya ya zama naki, kashi ɗaya na riƙe, sai kashi na ukun mu tura shi Nijar."

Farida ta ji daɗin kalaman ƙawar tata, ta yi murmushi mai  ta ce, "Haka kike da kyauta Tadala?To nagode sosai, amma gaskiya ba na buƙatar waɗannan kuɗin don ina da su a hannuna sosai, Alhamdulillah. Tashi muje kawai na raka ki ki buɗe asusun bankin."


. Suka dunguma zuwa babban banki dake cikin tsakiyar birnin Abuja. Cikin ƙanƙanin lokaci, da taimakon wayewar Farida, aka gama tsara wa Tadala asusun banki. Ba tare da ɓata lokaci ba, Tadala ta tura wa yayanta Moussa dake can Agadez tulin kuɗi har 400k domin su magance matsalolinsu na gida, sauran 100k ɗin kuma ta adana su a cikin sabon account ɗinta.

Lokacin da suka fito daga bankin, har yamma ta yi nisa, gajimare ya turnuƙe sararin samaniya cike da alamun ruwan sama. Suka yi sallama a gaggace, Farida ta so ta rage mata hanya amma Tadala ta ƙiya saboda tsantsar rashin son takura.

Farida na tafiya, Tadala ta tsaya a gefen titi tana jiran tasi (taxi). Shiru-shiru ba mota! Kowace tasi ta zo ta wuce, sai ta ganta maƙare da mutane a ciki. A daidai wannan lokacin ne aka fara yayafi ƙasa-ƙasa, iska mai sanyi tana dukan fuskarta. A nan ne Tadala ta fara da-na-sanin ƙakin bin Farida da ta yi tayin ajiye ta a gida.


Cikin fargaba da sanyin dake shirin ratsa ƙasusuwanta, ta zaro wayarta ta danna wa Anty Sadiya kira ko ta sami mafaka ko wata dabarar komawa gida. Wayar na shiga, Sadiya ta ɗauka.

"Hello Anty Sadiya... Don Allah an fara yayayefi ga shi yamma ta yi sosai na rasa tasi baki ɗaya. Ko Malam Awaisu yana nan gida ne ya zo ya ɗauke ni?" Tadala ta yi maganar muryarta na ɗan rawa.

Daga ɗayan ɓangaren, Sadiya ta yi magana cikin  halin ko-in-kula, "Baya nan... Dazu na ga Doctor ta aike shi, kuma har yanzu ban ga shigowarsa ba."

Tadala ta matse labba cike da damuwa, "Yanzu ya zan yi to?"

Sadiya ta saki wani ɗan gajeren tsaki na takaiçi, "Tadala yanzu ke ba bakuwa bace a garin nan da zaki tsaya kina tambayana abin da zaki yi. Ki ƙyale ni haka nan Yau fa Hubbi a ɗakina yake!"

Kit! Ta kashe wayar gaba ɗaya.

Tashin Hankali a Kan Titi

Tadala ta bita da kallo da mamakin yadda Anty Sadiya ta yanke wayar ba tare da ta damu da halin da take ciki ba. Tana nan tsaye,  ruwa mai ƙarfin gaske ya barke a take! Ba shiri ta soma gudu-gudu a kan titin tana neman inda za ta labe, duk da cewa tuni jikinta ya soma jikewa da ruwan saman.

Tana tsaka da gudun ne ta ji ƙarar hon ɗin wata haɗaɗɗiyar mota a bayanta ba kakkautawa. Jiiiiii! Motar ta zo da gudu ta silale ta gabanta sannan ta tsaya cak.

Zuciyar Tadala ta soma bugawa da sauri-sauri. A hankali ta ga gilashin motar (tinted glass) yana sauka ƙasa.

"Shigo Tadala!"

Muryar Daddy (Alhaji Kamal) ta dake kunnenta da ƙarfi dake ɗauke da wani irin ikon da ba za a iya musu ba. Cikin tsananin sanyi, fargaba, da mamakin yadda suka hadu , Tadala ba ta tsaya wani tunani ba...  ta buɗe motar ta shige ciki da gaggawa!