Soyayya ko Zalunci

Babi na days

by @102565813543784586917

Bismillahir rahmanir rahim


 “Kar ki zo daga baya kina cewa da-na-sani. Shawara muke baki. Duk namijin da zai zo yana kushe matar gidansa a gaban budurwarsa, to wallahi wannan ba mijin aure ba ne.”


Muryar Siyama ce ta fito daga cikin wayar cikin nuna damuwa da takaici. Fatima na zaune a gefen gadonta, ta jingina bayanta da bango yayin da take sauraron conference call ɗin da yayyenta biyu, Siyama da Qawwama, suka kira ta.


“Fatima, mai son ki shi ne yake gaya miki gaskiya,” Siyama ta ci gaba da magana cikin natsuwa. “Kin yi babban kuskure da kika yarda aka sa ranar aurenki da wannan mutumin.”


Fatima ta ja numfashi a hankali. Tun kafin Siyama ta gama magana, ranta ya riga ya ɓaci matuƙa. A ganinta, babu wanda yake fahimtar Muktar kamar ita. Duk lokacin da yayyenta suka fara magana a kansa, sai ta ji kamar suna zaluntarsa ne ba tare da sun san hakikanin halayensa ba.


“In shaa Allahu, alkhairi ne,” ta faɗa cikin ɗan ɓacin rai. “Ba wani da-na-sani da zan yi. Muktar yana sona, ni ma ina sonsa. Yana girmama ni, yana girmama Abbi, har da ku ma. Maganar matarsa kuwa, ita ce ta kasa sauke nauyin da Allah Ya ɗora mata. Ta barshi babu kulawa da tarba irin ta mace.”


Siyama ta girgiza kai a hankali, duk da cewa Fatima ba ta ganinta. A zuciyarta tana jin kamar an lullube ƙanwarta da wani irin mayafi na soyayya wanda ya hana ta ganin gaskiyar da ke gabanta.


“Fatima,” ta ce cikin murya mai cike da takaici, “kar ki taɓa yarda da kowace magana daga bakin namiji ba tare da kin bincika ba. Never trust a single word from a man.”


Qawwama, wadda ita ce babbar su, ta yi gyaran murya kafin ta yi magana cikin nutsuwa.


“Fatima, tun kafin a kai ga wannan matakin kin nuna mana cewa ba za ki saurare mu ba. Allah Ya jiƙan Ammi, da tana raye da wannan ba zai faru ba. Mun baki shawara, mun gaya miki abubuwan da muka hango, amma kin zaɓi kin yi kunnen uwar shegu. To shi ke nan, idan kin zaɓi tafiyar da za ta kai ki inda ba ki sani ba, ki tabbata za ki ɗauki alhakin zaɓinki. Kada daga baya ki zo kina kawo mana kuka.”


Fatima ta yi dariyar takaici.


“Kar ku manta,” ta ce cikin ɗan zafi da ɓacin rai, “da ba ku yi aure ba da sai na yi tunanin ko hassada kuke min ko wani abu makamancin haka.”


Maganar ta faɗi musu kamar walkiya.


“Fatima!” suka kira sunanta kusan a tare cikin mamaki.


Siyama kuwa ta fusata.


“Mu za mu yi miki hassada?” ta faɗa cikin mamaki. “Daga Aliyu har Yaya Irfan sun fi wannan yaron ninki ba ninki ba. Kyau, hankali, ilimi da kudi. Wane bakin ciki za mu yi? Da wa? Da wannan mutumin da ko kamanni masu ɗaukar ido ba su tare da shi?”


“Siyama, ya isa haka!” Qawwama ta katse ta cikin tsawa mai cike da gargaɗi.


Sai ta juya ga Fatima da murya mai sanyi.


“Tun da har abin ya kai ga kina zarginmu da yi miki bakin ciki, babu abin da zan ce sai Allah Ya ba ki sa’a. Allah Ya nuna mana alkhairinsa.”


Fatima ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce:


“Yau ne aka sanar da aurena. A matsayinku na yayye, ya kamata ku taya ni farin ciki. Amma tun daga lokacin da kuka ji labarin, abin da kawai kuke yi shi ne kushe mutumin da zan aura. Lokacin aurenku ni ce mafi farin ciki a cikinku, amma yanzu da nawa ya zo babu abin da nake ji daga gare ku sai suka da zargi.”


Siyama ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.


“Allah Ya sauwake kawai,” ta ce.


Qawwama kuma ta ce:


“Allah Ya sanya alkhairi, Ya kai mu lokacin lafiya.”


Ba tare da ta jira amsar Fatima ba, ta katse kiran. Nan take ya rage Fatima da Siyama kaɗai.


Siyama ta yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ta sake cewa:


“Ni kam ba zan ce Allah Ya sanya alkhairi ba. Abin da zan roƙa shi ne Allah Ya canza wani. Ba wannan mutumin ba.”


Kafin ta ƙara cewa komai, Fatima ta katse wayar.


Ta jefa wayar kan gadon da ƙarfi, zuciyarta na tafarfasa da ɓacin rai. Ta zauna tana kallon bango cikin tunani mai nauyi.


Ashe lokaci zai zo da yayyenta za su juya mata baya haka?


Tun da farko ba ta taɓa kawo irin wannan tunanin a ranta ba.


Me Muktar ya yi musu ne?


Me ya sa ba sa ganin abin da ita take gani?


Mutumin da take ƙauna. Mutumin da take ganin rayuwarta ta rataya a kansa.


Ba yayyenta kaɗai ba, har sauran mutanen da suke kewaye da ita kamar ba su san shi ba ne.


A ganinta, Muktar mutum ne mai karamci, kulawa da mutuntawa. Yana sonta fiye da yadda ta taɓa zato. Yana girmama iyayenta da danginta. Yana nuna mata kulawa a kowane lokaci.


To idan namiji yana da waɗannan halaye duka, me kuma mace za ta nema daga mijin aurenta fiye da haka?


Tambayar ce ta ci gaba da yawo a cikin zuciyarta yayin da soyayyar Muktar ke ƙara rufe mata ido daga ganin abin da wasu ke ƙoƙarin nuna mata.


*****************************************************


A farfajiyar gidan Alhaji Asim Inuwa, Fatima da Muktar ne zaune a ƙarƙashin inuwa mai sanyaya zuciya. Iskar yamma tana kaɗa ganyayen bishiyoyin da ke kewaye da gidan, yayin da tsuntsaye ke ta shawagi suna komawa mazaunansu.


Sai dai duk da wannan yanayi mai daɗi, Fatima ba ta cikin walwala kamar yadda aka saba. Tun da suka zauna, ta yi shiru fiye da kima, tana wasa da yatsunta cikin damuwa.


Muktar ya lura da canjin da ke tattare da ita. Ya karkata kansa kaɗan yana kallonta cikin kulawa.


“Lafiya kuwa?” ya tambaya cikin murya mai cike da tausayawa. “Yau kin yi shiru sosai. Me yake damunki? Ko ba kya jin daɗi ne?”


Fatima ta sauke numfashi mai nauyi. Ta yi shiru na ɗan lokaci tana nazarin ko ta gaya masa abin da ke damunta ko kuma ta ɓoye. Amma daga ƙarshe ta yanke shawarar cewa tunda shi ne mutumin da take shirin aura, bai kamata ta ɓoye masa komai ba.


Kafin ta samu damar magana, Muktar ya sake cewa:


“Faɗa min mana. Ina saurarenki. Wallahi kin fara sa zuciyata ta yi nauyi. Allah Ya sa ba ni na ɓata miki rai ba?”


Fatima ta girgiza kai a hankali.


“A’a,” ta amsa cikin sanyin murya.


“To me ne yake damunki?” ya sake tambaya yana matsowa kaɗan kusa da ita.


Fatima ta ɗan sunkuyar da kanta kafin ta ce:


“Ban san me ya shiga tsakaninka da ’yan gidana ba… amma kamar ba sa sonka.”


Muktar ya zaro ido cikin mamaki, sannan ya maimaita:


“Ba sa sona?”


Ya yi ɗan shiru kamar wanda ke ƙoƙarin fahimtar abin da ya ji.


“Me na yi musu?” ya tambaya cikin murya mai nuna rashin fahimta. “Allah Ya sa ba wani laifi aka ɗora mini ba. Kin san ina da maƙiya da mahassada da yawa.”


Fatima ta girgiza kai.


“Ni ma ban sani ba,” ta ce. “Amma dai ba sa sonka. Musamman Yaya Siyama. Duk lokacin da aka ambaci sunanka, sai ta nuna rashin amincewa.”


Muktar ya yi murmushi mai laushi, sannan ya miƙa hannunsa ya dafa nata cikin sigar kwantar da hankali.


“Me ya sa hakan zai dame ki?” ya faɗa cikin salon lallashi. “Ai muddin sarauniyata tana sona, me kuma zan nema?”


Ya ɗan matsa kusa da ita yana murmushi.


“Ke ce zinariyar Muktar. Ke ce mai ɗauke da zuciyarsa. Ke ce farin cikin rayuwarsa.”


Kalaman suka sa zuciyar Fatima ta yi wani irin bugawa da sauri.


Muktar ya ci gaba da cewa:


“Ki kwantar da hankalinki. Lokaci ne kawai bai yi ba. Nan gaba kaɗan za su fahimce ni, su gane ni, kuma su fara sona kamar yadda kike sona.”


Ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da murmushi.


“Kuma tunda Abbi ya amince ya ba ni ke, ai magana ta kusa ƙarewa. Sauran kuma lokaci ne zai tabbatar musu da ni.”


Fatima ta ɗaga kai ta kalle shi. A wannan lokacin, kalamansa sun kasance kamar maganin da ya saukar mata da duk wata damuwa daga zuciyarta. Ta yi murmushi a karo na farko tun bayan zuwansa.


A ranta tana ƙara tabbatar wa kanta cewa duk wanda bai ga alherin Muktar ba, watakila bai san shi yadda ita ta san shi ba.




Shin kuna ganin Fatima tana bin zuciyarta ne… ko kuwa tana tafiya kai tsaye zuwa tarkon da har yanzu ba ta gani ba? ❤️📖


Dear readers ❤️


wannan shi ne kashi na farko na wannan labari.


A ganinku, Fatima tana bin soyayya ta gaskiya ne, ko kuwa tana yin watsi da red flags da za su iya sauya rayuwarta har abada?


Wannan littafin ci gaba ne na Halimatus Sa’adiya, amma tare da sabuwar tafiya mai cike da abubuwan mamaki da darussa.


Please support the story by:

🗳️ Voting

💬 Commenting

📢 Sharing


Your feedback motivates me to keep writing.


Ra’ayoyinku da goyon bayanku su ne abin da ke ƙarfafa ni wajen ci gaba da rubutu.


Nagode da kasancewa tare da ni. ❤️


— Meena Majeed