Chapter 13
Tunda suka dau hanyar gidan shi babu abinda yake yi sai tunanin rayuwar shi wani abun idan ya tuna yayi dariya wani yaji babu dadi wani girgiza kai har suka qaraso gidan shi,driver yayi parking shi kuma ya wuce cikin gida bai tsaya ko ina ba ya wuce cikin bedroom din dake gefen na shi wayoyin shi kawai ya dire ya qarasa wurin drawer din dake dakin yasa hannu ya bude ya shiga ciki mamaki ne ya daskarar dani a wurin na kasa motsi ganin zai rufo qofar wardrobe din ya sa nayi saurin shiga kafin ya rufe,qarfen staircase ya riqe ya fara sauka qasa under ground building din ne sosai abun ya bani tsoro at the same time ya kuma birge ni,ginin wurin baki daya beyi kama da a Nigeria akayi sa ba yanayin ginin irin na turawa don baki daya gidan glass ne,tunda ya shigo parlour ya tsaya ya kasa daga qafarshi don rabon da ya shigo wurin nan kimanin shekaru shida kenan,a hankali ya daga qafarshi da tayi masa nauyi zuwa wurin wasu dakuna masu glass doors,babban dan yatsan shi ya saka a jikin glass door bayan yayi scanning hannun ya bude,dakin yayi qura alamun an dade ba'a shige shi ba,gado ne sai drawer kadai a dakin gaban drawer din yaje ya bude ya ciro wata trolley,gefen gadon ya dan bige inda ze zauna sannan ya bude zip din trolley din ya sa hannu ya ciro abun da ke ciki, wasu fararen cardboard papers ne da aka yi drawings a kai daya bayan daya yake ďaga su yana dubawa yana murmushin da yafi kuka ciwo, bayan ya gama duba su ya riqe wani drawing a hannun shi yana kallo hawaye ya cika idon shi yace ya Allah why did you take her away when i needed her the most,yana gama fadin haka yace astaghfirullah I'm in no position to question my creator indeed he knows better than me,ya Allah kai ka sa man qaunar ta a cikin zuciya ta ba tare da na shirya ma hakan ba ka kuma raba mu a lokacin da zuciyoyin mu suka mace da qaunar juna,Allah ka fi mu sanin dalilin faruwar hakan,Allah idan da alkhairi a cikin rayuwar da zamuyi tare ni da ita Allah ka bani qwarin gwiwar tunkarar ta a karo na biyu,bayan ya gama fadin haka ya goge hawayen da ke cikin idanun shi ya maida komai inda yake ya fito daga dakin ya nufi hanyar komawa dakin shi.......................................
Tuki take yi akan titi tana bin waqar p square forever,har ta qaraso gidan Hafsat bayan tayi parking motar ta a parking space din gidan ta yi knocking qofar parlour din bata dade ba aka bude gaishe da ita me aikin Hafsat tayi sannan tayi mata jagora har zuwa parlourn Hafsat sannan ta wuce don sanar ma da Hafsat tana da baquwa,bayan ta fada mata ta wuce kitchen ta dakko mata ruwa sannan tayi excusing kanta ta basu wuri,gaisawa suka yi sannan suka shiga hirar duniya,Layla ce tace qawata kin san Allah a da idan wani yace man Raj ze yi man abubuwan da yake yi a yanxu wallahi zan qaryata ko waye ya fadi hakan amma kinga yanxu ya zama se abinda nace masa dariya Hafsat ta saka tace ai dama kece kika tsaya wasa da tuni kin wuce wurin amma yanxu ma baki makara ba komai ze iya dawowa yanda kike so,ya zama se abinda kika ce shi za'a yi babu wanda ya isa ki aje kara a wuri ya tsallaka shi,amma duk ba wannan bama ni akwai maganar da nake so muyi da ke juyowa Layla tayi giving her all the concentration she needs,yawwa ni ina yarinyar nan da ta so aurar maki miji?nan da nan ta hade rai tace i don't have any business with her so please stop talking about her,dariya Hafsat tayi tace ke matsala ta dake banxa ce daga magana har ranki ya baci ni wani maganar ce zanyi maki daban,se a lokacin ta tsaya ta saurare ta yawwa abunda nake so dake shine be kamata ki taci banxa ba ai duk wadda tayi gigin kula mijin ki kamata yayi ace kin koya mata hankalin da duk wani da namiji se ya dena birgeta talk less of your husband,a'a kinga ni tunda ta rabu da miji na babu ruwana da ita taje can tayi duk abinda zata yi ni dama matsala ta mijina ne yanxu kuma ita da shi se dai hange,ai dama nasan se kin yiman gardama ke ba'a taba yi maki abin arziqi,toh wallahi zan fita a harkarki kiyi duk abinda kike ganin ya dace,kin san ita me take taqama dashi idan taje tayi abinda yafi qarfin namu fah yaya zakiyi?and wallahi duk abinda ya biyo baya ki kuka da kanki na cire hannu na daga cikin lamarin ki,sosai hankalin ta ya tashi tace kinga bama haka dake ni na yadda da duk abinda kika ce,a'a kar ma ki yadda kanki ake ji ni na gama nawa idan kin shirya se kiyi man magana, ni ko yanxu kika ce man ai na dena yi maki musu duk abinda kike ganin dai dai ne se ki fada man,Hafsat tace yanxu kika yi magana i think we should just leave it till after our exams since we are starting exams next week,yeah it's a good idea let's just leave it till then daga haka suka koma hirar su ta qawaye..................................................
Toh ummi keda Munarh ina ganin ya kamata ayi discharging dinku tunda jiki yayi kyau sosai,shi kuma ina tunanin se zuwa nan da three days idan ya qara samun sauqi,tohm shikenan Jay ina ganin ita Maimunatu taje gida ta huta ni se na zauna a asibitin idan safiya tayi se ta karbe ni naje na huta dan murmushi Jay tayi tace ai masu jinya basa zama a asibitin nan muna da masu kula mana da marasa lafiyan mu,toh masha Allah se mu tafi mu duka goben se mu dawo,yanxu dai a fara bamu bill din mu muyi clearing first kafin mu tafi dariya Jay tayi tace haba ummi ai anyi clearing bill dinku tuntuni a dai cigaba da yi mana addu'a,toh Allah yayi albarka ya qara budi ameen Ummin mu,hade rai munarh tayi tace ummi kin ganta ko wai ummin mu ita da wa dariya ummi tayi tace toh Allah ya hada ni da tom and jerry sai suma duk suka sa dariya,dama na tashi a aiki se mu tafi gida ko?muje se ki aje mu a gida tunda mu babu mota a hannun mu tabbbb ummi ai gidan mu zamu tafi ya za'a yi na bari ku tafi ai yau kwana zamuyi muna hira tunda kun sami lafiya ta fada tana dariya suma dariyar suka yi Jay tace muje ku qara duba jikin shi se mu wuce gida.......................................................
Safiyyah ce zaune a kan gadonta bayan ta dawo daga gidan shema'u tana ta saqe saqe ganin tunanin babu inda ze kaita yasa ta dau wayarta tayi dialling number Momma bayan ta dauka tace ina kwana Momma daga dayan bangaren ta amsa da lafiya qlau safiyyah amma kina lafiya kuwa?naji muryar ki yayi qasa sosai dan murmushin yaqe tayi tace babu komai momma kawai ina son nazo gida idan kina nan dan jimmm tayi sannan tace toh shikenan bana nan amma yanxu nake kan hanyar komawa in sha Allah but are you sure you are okay safiyyah?i am momma don't mind me kai na ne kawai yake dan yiman ciwo,toh shikenan sai kin zo ta kashe wayar.........................
Knocking aka yi a bakin qofa Nafeesah dake zaune a parlour ita da Aunty ta miqe don bude qofar wa zata gani tsaye wani tsalle ta buga tace Sa'adarh wai dama dagaske kike zaki zo?a'a da qarya ta fada tana harararta ke ni matsa na shigo kin tare man hanya sai a lokacin ta matsa suka shigo tare gefen kujerar da aunty take kai a zaune ta tsugunna ta gaishe da ita, ta amsa mata da fara'a tana tambayar ta mutanen gida tace mata duk lafiyan su qlau zata zauna aunty tace a'a tashi zaki yi Nafeesah ta raka ki kije ki gaida yaya don nasan idan kika zauna har ki bar gidan nan baza ki jeba,sunkuyar da kanta qasa tayi tace toh aunty ta kama hannun Nafeesah suka tafi part din mama.......................................................
A zaune suke suna launch su uku Faruq Billy da Meeamrh,Billy ce ta budi baki tace Meemarh please i want to go and meet my new friend harararta tayi tace you are not going anywhere kwabe fuska tayi kaman zata yi kuka tace but I don't have friends before Meemarh and now that i have one why won't you allow me to visit her, you are going nowhere and that's final Meemarh ta fada babu alaman wasa,kuka ta sa ta tashi ta tafi dakin ta,girgiza kai Faruq yayi yace auta akwai rigima Allah dai ya shirya mana ita Ameen Meemarh tace tana cigaba da cin abincin ta,bayan Faruq ya gama cin abincin sa ya goge bakin shi yace Meemarh i'm going to kano tomorrow morning in shaa Allah dandanan fuskan ta ya fadada da murmushi tace toh Allah ya kaimu ya kaika lafiya yace ameen sannan yayi mata sallama ya fita................................................
Qofar shiga part din mama abude yake don haka suna zuwa suka shiga,mama bata parlour sai zulaikha da Hannatu dake zaune a parlour suna kallo,suna ganin Sa'adarh suka miqe zulaikha tace sis kece yau a gidan namu lallai za'a yi ruwa da qanqara Nafeesah ce tace wallahi kuwa aunty zulaikha nima nayi mamaki da na ganta,Hannatu ce tace aunty sa'adarh sannu da zuwa sun barki a tsaye qaraso ki zauna,zama tayi tace mama ko bata nan?sai a sannan zulaikha tace Hannah je ki kira mama,tashi tayi ta nufi dakin mama bayan dan lokaci kadan sai gasu sun dawo tare,qasa Sa'adarh ta sakko ta zauna suka gaisa da mama, tana ta sunkuyar da kai don Allah ya sani tana matuqar jin kunyar mama bata dade ba ta yima mama sallama ta tashi suka koma part din aunty ita da yan matan gidan...........................................
Lokacin da safiyyah ta qarasa gidan su momma ta dawo gida,kallo daya tayi mata tasan da abun da yake damunta kuma ta kasa fada,bata takura mata sai taji abunda yake damunta ba,tace ita da auta su shiga kitchen su sama masu abincin da zasu ci,lokacin da suke girki auta tace aunty safiyyah what's wrong with you please you look down, you don't look your normal self, you are not as lively as you used to be,is something bothering you and you are keeping it away from us?ta jero mata tambayoyin nan lokaci daya, murmushi kawai tayi tace auta kenan anya baxa kiyi change of course ba kuwa daga nursing ki dawo mass communication,ganin tayi diverting questions din da ta tambaye ta yasa bata qara cewa komai ba saboda ta santa da zurfin ciki duk yadda zata yi baza ta fada mata meke damunta ba shiyasa ta sa a ranta zata qara saka ta a cikin addu'oin ta, a haka har suka gama girki suka serving momma ta sakko suka ci,bayan sun gama cin abincin momma ta kalli auta tace Maryam bamu wuri zanyi magana da aunty ki babu musu tace toh momma ta miqe ta barsu a zaune a akan dining,safiyyah Dume damata ma,(meke damunki)? Momma Allah wala ko damata am (momma Allah babu komai) To a yaccai min dada ma moi on a yaccata?safiyyah (kina da wanda zaki fada ma banda ni mahaifiyarki)? Allah wala ko damata am, Wannam du'a tan (kawai ki taya ni da addu'a),bazan ta kura maki ba idan kina ganin bai kamata na sani ba amma ina so ki sani ni kadai gare ki a yanxu sai yan uwanki mahaifinki baya duniyar don haka duk lokacin da kike da matsala kar kiyi jinkirin sanar dani,hawaye ne ya cika idanun ta, a zuciyarta ta riqa cewa kaico ni momma kiyi man afuwa na watsar da duk wata tarbiyar da kika dora ni akanta kaico na babu komai a rayuwa sai da na sani,a hankali tace in shaa Allah momma duk lokacin da na shiga matsala nayi maki alqawarin kece mutum na farko da zata sani,murmushi tayi tace toh Allah yayi maku albarka ya tsare ku gaba dayan ku da yan uwanki.......................................
A gajiye ta shigo cikin gidan tana shigowa ta tarar da mom da Ayaanah a parlour suna kallon cartoon,Ayaanah najin sallamarta ta miqe da gudu tana mummy oyoyo daga ta sama tayi tace my baby i miss you,sai a lokacin mom ta lura da mutanen dake bayan Jay,da sauri ta miqe tace o ni Bilkisu Jay sai yaushe zakiyi hankali?ji yadda kika bar mutane a tsaye just because kinga yar ki, sai a lokacin ta tuna tare da su ummi suke hannu tasa ta rufe fuskarta tace oops my bad ummi kuyi haquri come inside please ta fada tana nuna masu hanya Munarh sai kallon Ayaanah take with admiration can dai ta kasa yin shiru tace come here cutie I'm also your mom because all her thought was yarinyar Jay ce,Ayaanah yarinya ce me wayo and bata da baqunta tana da saurin sabo da mutane without a second thought ta je wurin Munarh,riqe hannunta tayi suka qarasa shigowa cikin parlour din,bayan sun zauna sai ga hajiya mama ta fito daga dakinta zata je kitchen sai taga mutane zaune a parlour ta qaraso tayi masu barka da zuwa sai kuma tace Bilkisu ko sune wanda kika je kika duba dazu a asibiti? Mom tace eh sune hajiya an sallame sune toh toh masha Allah ai haka ake so ga alamu nan ma ai jikin da sauqi Ummi ta dan duqa ta gaida hajiya mama sannan Munarh ma ta gaishe da ita,amsa masu tayi da sakin fuska tana qara jajanta masu da addu'ar Allah ya tsare gaba suka ce Ameen, miqewa tayi ta nufi hanyar kitchen tana cewa oh ni jikar mallam Hamza Naja ban san me kuma kike yi ba tun dazu daga nace kiyi man kwadon zogale shikenan kika kama zama a kitchen kamar na aiki bawa garinsu,daga cikin kitchen aunty Naja tace hajiya na kusa gamawa yanxu zan kawo maki in shaa Allah,A'a ba dani za'a yi haka ba bari na zo na tsaya ki gama ki bani kayana don na gaji da jira........................................................
Hello,how far man kana ina?there is an important issue i want to discuss it with you if you are free daga daya bangaren Zannur yace I'm at home any problem?nazo gidan kane ko zaka zo gidana? don't worry bro I'm not at home so let me just drove to your house,daga haka yayi ending call din ya dauki hanyar da zata kaishi gidan Zannur, yana zuwa me gadi ya bude mashi gate ya shiga cikin gidan da motar shi yayi parking,bayan ya kashe motar shi ya dauki wayar shi ya shiga kiran Zannur bayan ya dauka yace ina waje ka fito,daga daya bangaren Zannur yace kaga in baka shigowa ka bari gidan baqon kane kitttt ya kashe waya,babu yanda ya iya ya qarasa jikin qofar parlour yayi knocking,kaman dama Zannur yana bakin qofa yana yin knocking ya bude mashi side hug ya bashi sannan ya bashi hanya ya shigo ciki a parlour suka zauna can sai ga Lateefah na tahowa daga hanyar kitchen da tray a hannun ta dauke da snacks da lemu,bayan ta aje tray din da murmushi a fuskarta ta yau da alamun za'a yi ruwa da qanqara kenan,uncle yau kaine a gidan namu? Murmushi kawai yayi bece komai ba,gaishe shi tayi ya amsa yana tambayan ta ina Areef tace mashi yana school,bayan sun gama gaisawa ta basu wurin don suyi magana, bayan ta tafi Zannur ya kalli HAYDAR yace man wai meya faru dazu naji ka wani iri? Girgiza kanshi yayi yace nima na rasa meke damuna abu daya na sani shine tabbas inaji na kaman wani sabon mutum,hannun Zannur ya riqe sannan yace don Allah dan uwa na ka qara saka ni a cikin addu'oin ka,ina matuqar buqatar addu'a kallon tausayi Zannur yake bin shi da shi,hannun HAYDAR dake cikin nashi ya qara riqewa yace nasan kana cikin damuwa dan uwana amma in shaa Allah komai ya kusa zuwa qarshe,gyada kan shi yayi yace i hope so,Zannur ne ya qara yin magana yace abu daya nake son qara tuna maka shine,ka qara riqe ibada duk da nasan kana yi amma ka qara babu wani abu dake saurin yayema dan adam damuwa kaman qara kusanta kanshi da mahaliccinsa gyada kai kawai yayi baice komai ba,kuma ina son ka sani nisan ta kanka da ita baya nuna komai sai cewa ka haqura da ita and a kowane lokaci zaka iya jin wani yana nemi aurenta wata qila ma har a saka ranar aurenta,tun kafin Zannur ya gama magana yaji wani abu me daci ya tokare masa qirji,Zannur ganin ya samu abinda yake so yasa be qara ce masa komai ba ya tsaya yana kallon reaction dinsa can kuma suka canja maganar zuwa ta wani contract da zasu karba na ginin wani company....................................................
Bayan sunyi sallar la'asar Sa'adarh ta dauki handbag dinta ta leqa dakin aunty tayi mata sallama akan zata wuce gida,turare ta dakko ta bata sannan tace ki gaida gida kice ma yaya ina gaishe da ita,karba tayi tace toh in shaa Allah aunty sai da safe,suna tsaye suna jiranta bayan ta fito Hannah tace tace wai don Allah aunty Sa'adarh dagaske yanxu zaki tafi kaman wadda ake kora?dan murmushi tayi tace Hannah bana son nayi dare ne kuma ma akwai abinda zanyi idan na koma,babu yadda suka iya haka suka fito rakata don yi ma mama sallama,a hanya zulaikha gaskiya sis wannan ba ziyara kika zo ba kawai dai kin leqo ne murmushi tayi tace amma dai ni ai na fiku tunda ku yaushe rabon da naga qafan wani a cikin ku? Dariya zulaikha tayi tace soon muma zamu zo in shaa Allah,Nafeesah ce ta hangi motar Sadeeq dake parking lots tace laaaa ashe yaya ya dawo,gaba dayan su suka juya suka kalli direction din da take kalla suka ga motar shi a wurin,Hannah ce tace maybe yaje masallaci be dawo ba,bayan sun shiga part din mama suka jira ta fito daga daki Sa'adarh tayi mata sallama, ita ma da mamaki tace Sa'adatu ba dai har kin fito ba? Qara sunkuyar da kanta tayi tace mama bana son nayi dare a hanya ne shiyasa,eh to kuma kema kina da gaskiya Hannah ta kalla tace auta jeki saman gado na akwai wata leda na aje ki dakko ma Sa'adatu kinji,miqewa tayi tace toh mama tayi hanyar daki,suna zaune suna jiran auta saiga Sadeeq ya shigo gaishe da mama,Zulaikha ce ta fara cewa ashe yaya ka dawo?toh sannu da dawowa,ya amsa da yawwa Sa'adarh ma daga gefe tace ya Sadeeq ina yini, dagowa yayi ya kalleta don be lura bayan zulaikha akwai wani mutum ba,lafiya qalau yace sannan ya juya ya gaishe da mama yace mata xe fita,yana cewa haka tace masha Allah kaga saika taimaka man ka sauke Sa'adatu a gida dama yanxu nake shirin nasa driver ya maida ta amma tunda gaka ma zaka fita ai shikenan,ji yayi kaman yace wayyyo Allah,don kawai baze iya yima mama musu ba amma da yace ta saka driver ya maida ta shi ba hanyar zai bi ba,babu yadda ya iya yace toh ta fito ina jiranta,yana fita Hannah ta dawo da leda a hannunta ta bama mama Sa'adarh ta miqama tace toh ki gaida yan gidan kinji karba tayi ta mata godiya sannan tace toh ku kuma ku tashi ku rakata ko bakin mota ne mana kuka zauna,tashi suka yi gaba dayansu suka tafi rakata........................................