MUTUWAR AURE...! BOOK 1

26

by @aishatouuu

_Aishatou_
        ***


Bahari bai aje taba yace "kai wa zai baki aikin wahala kawai muje yau kiyi mana kunun yamma dama kwana biyu bakiyi ba." 

Tana masifar Bahari ya sauke ta a bakin gari yaƙi saida ya kawo ta har ƙofar gidan su sannan yaja mashin ɗin shi yayi tasha.

Husna na shiga gida Ramma tace "kai har kinyi me? yanzu fa kika tafi kodai baki je ba?" Saida ta aje farantin tana zama saman turamin da suka gama surfe tace "naje harna siyar, da Bahari na haɗu ya rage min hanya."
Caraf Zahara tace "ai kuwa da munsan zaki dawo yanzu da munbar surfan nan kin mana muma mu huta." Husna ta kalle ta a ɗage tana miƙewa tsaye tace "ai har abada na daina muku surfe wanda nayi muku a baya ma Allah ya bani lada." Tayi gaba tabar Zahara da baki a buɗe.

            Wajen Baba kwade taje ta kai masa kuɗin shi ya bata ladan tallar ta yanata mata kirarin daya saba. 

Gida ta koma ta cewa Ramma tayi Kunun yamma sannan ta sake ficewa dan bazata zauna a gidan bama bare a sata wahala.

......zuwan ta tashar ke nan wani mutum daya sha zanzaro da belat akan baƙin Jens da farar riga yace ta bashi kunu, ko zama batayi ba ta zuba kunun ta tafi kai masa.

             Husna ta dawo daga kai masa Kunun ranta a ɓace tana tafe tana mitar fi'ilin mutumin data kaiwa kunun.

Ranta fal jin haushin mutumin tace "Ko daga ina ya fito oho masa mtchew." Taja tsaki tana zama, Indo tace "ke dawa kike mita?"
"Hmmm wancan ɗan renin wayon mana wai na kai masa kunu sai cemin yayi kin wanke robar ko? Dan bana son datti, jifa wulaƙanci ko waye Kazami? Ai wallahi daban zuba masa ba ya fadi haka da saidai ya siya a wajen wani." 
 
Indo tace "hmmm shine fa sabon headmaster ɗin da aka kawo, kinsan an canja wancan, ɗazu Ummai ke bani labarin sa wai ya sayi alalar ta jiya saida takai masa ya bata kuɗin yace ta tafi da ita baya so wai bata wanke cokali ba."
"Kut amma wannan bashi da mutumci, ai kuwa yawa kanshi wazai yiwa ƙaryar tsafta da wani tanƙwal ɗin shi har ƙyalli yake." 
Indo saida ta dara da maganar Husna sannan tace "haba Ma'u ance fa har mota gare shi mai kyau ƴar wulwula (ƙaramar mota) baki sani bama bai jima da korar kurman mahaukacin ki ba kika zo wai kyankyamin yake bashi kinga yadda yayi kanshi kuwa kamar zai dake sa saida akayi masa magana sannan ya kyale shi." 

Ran Husna yayi mugun ɓaci ta dubi Indo fuskar ta a cunkushe "shi ɗin ne ya yiwa Yaya haka? Ai kuwa wallahi zaiga wulaƙanci, kuma malama ba sunan shi kurman mahaukaci ba in bazaki kira shi da yayan Husna ba karki sake yin maganar shi, yanzu haka ma kishin ruwa ce ta kawo sa nan, aikin banza kawai mugu zai wani kore shi."
 Husna tayi maganar tana hararar Indo.

          Shi kuwa yana barin wajen da headmaster ya kore shi ya tafi can wajen rumfar Bahari ya zauna a ƙasan bishiya, bai jima da zama ba sai ga Dan Hajja ya zo ta bayan shi yana waya.

"Kai dan Allah? Ihu kace aikin Babba ne? to saina jika saika shigo ɗin." Dan Hajja ya sauke wayar bakin shi a buɗe, Gambo ne ya hango sa ya taho wajen yana faɗin.
"Ya mutumin ta samu ne? Naga tun daga nesa kana washe baki."

Dan Hajja ya bashi hannu suka kashe yana sakin dariya jin daɗi yace "kaidai bari yau zaka samu kuɗin ƙasar da kace za'a kawo maka, yanzu kuɗi suka sauka kayan Ogan sama sun wuce lafiya babu wata matsala." 

Gambo yayi ihun murna jin za'a biya masa kuɗin ƙasar da zai yi yabe, yace "kai amma naji daɗi kace yau bajau damu?" 
"Kaidai bari yau jina nake a cike an jima zaka rakani na gaida Kakar mutuniya ta (Husna ) nadan bata wani abu da Tawan ma da tana kula ni ai yau dana ɓata ta a garin nan, na kashe mata kuɗi, yawwa kasan meye abun daɗin?" Gambo ya girgiza kai.
"Yanzu mukayi waya da wanda Oga ya haɗa mu ka gane shi ai?" 
Gambo ya daga akai da sauri yana faɗin "Eh wanda ya zo kwanaki ko?"
"Shifa yanzu yake faɗa min a sabuwar Shekarar nan Oga zai shigo da wasu manyan kayan dabai taɓa shigo da irin suba Kuma kafin lokacin duk zai zo ya ganmu dan yafi so yana gari za'a wuce da kayan, kasan baya zama abunka da masu garin (masu kuɗi) kullum zakaji yana Saudiyya ko ƙasar turawa yana hutawa, ina faɗa maka kaya ne na manyan kuɗi masu nauyi za su wuce wannan karon Oga yayi mana albashir ɗin kuɗi masu kauri, duk wanda ta ɓangaren shi ba'a samu matsala ba zai ja wata million fa." 
"Kai mutumin maliyan fa kake kira?" 
Gambo ya faɗa yana zare Ido, Dan Hajja yayi dariyar nishadi yace "haba nawa million nawa take a wajen Ogan sama kasan kuɗin mutumin nan kuwa, bafa iya harkar madarar nan yake ba har shinkafa yana shigowa da ita wallahi harna matsu na ganshi."

Gambo ya gyaɗa kai kamar kadangare yace "lokacin ai ya kusa sabuwar shekarar Bature baifi kwana Arba'in ba nan gaba, Allah dai ya kaimu lokacin nasan zamu wataya mutumi na."
Dan Hajja ya daki kafaɗun shi yace "sosai ma zamuje tsangaya wajen Malam shima a ɗan bashi wani abu dan ya sake batar mana da sahu.
"Eh ya kamata gaskiya ai yana maka aiki babu wasa ya cancanci a jiƙa shi shima yau gidan shi aci fara (shinkafa)." 

Suka kwashe da dariya suna tafawa Dan Hajja ya juyo yaga inuwar mutum a bayan bishiya yana zagayawa yaga kurman mahaukaci zaune yana gangaɗi ya rungume Sandar shi a kirji yadda yayi dole ya baka tausayi.

"wa kake dubawa ne?" Gambo ya faɗa yana matsowa wajen.
"Oh ashe ma wannan kurman mahaukacin ne." Maganar Gambo ta tashe shi daga baccin daya fara ɗaukar shi.
Dan Hajja ya zaro sabuwar ɗari biyar daga aljihun sa yace "kaima gashi ka ɗan ɗana arziki." Ya jefa masa kuɗin su kayi gaba.

Kuɗin yabi da kallo sai kuma ya juya ya kalle su suna tafe suna hira da dariya.
               Basu jima da barin wajen ba Husna ta zo hannun ta riƙe da ledar kunun shi tace "Yaya ashe kana nan? Inata neman ka sai Indo ce ta ce min kana nan." Ta faɗa tana kallon yadda ya zauna a kasa ya mike ƙafafun shi kanshi jingine da jikin bishiyar yana duban gaban shi.
Kunun ta sake miƙa masa yaƙi karɓa ta tsaya tana kallon shi dan tasan yana san kunun tsamiyar sosai ta gane haka ne ta yadda taga inta bashi baya rage wa duka yake shanye wa, sannan baya sha da sugar dan ta taɓa zuba masa suga yana ɗanawa taga ya cire ledar a bakin sa sai kuma ya yamutsa fuska ya jefar, shike nan bata sake saka masa suga ba.

"To meya hanashi karɓa?" Ta tambayi kanta. 
Kiran ta aka fara yi a tsallaken titi ta kawo kunu sai ta sake kallon shi tace "Yaya ka karɓa kaga ana kirana a tsallake nakai kunu, karɓi sai naje naga waye me kiran." Ta faɗa tana sake miƙa masa ledar, hannu yasa ya karɓa amma sai taga ya miƙe tsaye riƙe da ledar Kunun.
"Yaya sai an jima." 
Ta faɗa tana juyawa ta duba titi saida taga babu mota sannan ta tafi zata tsallaka tayi taku ɗaya kan tayi na biyu taji "Woooof......!" An jawo hannu ta baya da wani mugun zafin nama ana jawota bayan kuma wata ƙaramar mota tazo ta wuce da mugun gudu Husna ta tsorata sosai dan wallahi saura kaɗan motar ta buge ta, ƙirjin ta ta dafe sai kuma ta juya taga wanda ya janyo ta.

Abinda Husna bata taɓa zato da kawowa ranta bane ya faru sanda ta juyo suka yi Ido biyu da mahaukacin yayan ta tsaye a kanta, yau ƙwayar Idanun shi ta fito fili ras Husna ke ganin cikin idanun sa masu ɗauke da wasu manyan blue eyes, cikin su ya turu sosai Blue ɗin yayi duhu bau cikin idanun kuma yayi wani batsi batsin zaiba, idanu ya zuba mata kamar zai maketa da sauri Husna ta ɗauke kanta tabar kallon sa gaban ta na wani irin mugun faduwa dan tunda take bata taɓa ganin mutum da blue eyes ba.

Sake duban shi tayi a karo na biyu sai taga ya mai da idanun ya rufe ya koma baya ya ɗauki Sandar shi daya barta a ƙasan bishiyar bai sake duban inda take tsaye ba ya miƙe titi ya barta anan tsaye tana binshi da kallon mamaki haɗe da tsoron idanun shi.
"Dama akwai Ido irin haka?"
Husna ta tambayi kanta, wata zuciyar tace "shi haka Allah ya halicce sa ko kuma ciwo ne tunda bashi da lafiya." 

Husna ta girgiza kai a fili tana yarda da shawarar zuciyar ta na ciwo ne yasa idanunsa yineBlue.

Kamar daga sama taji ance "Tunda ya taimake ki yau kema saiki gode masa oh! Su Ma'u da yanzu an ziyarci barzahu." Maganar Bahari ta katse wa Husna tunani, sai lokacin kuma tunanin wani bai gansu ba yazo mata.
"Dama kana ganin abinda ya faru?" ta jefa wa Bahari tambayar dake cinta, sai taga yayi murmushi yace "ina gani har fa zan yi ihu na ɗauka wani abun zai miki sai naga ashe taimakon ki yayi Allah sarki Bawan Allah ashe mahaukaci ma yasan mai masa rana, kai Allah ya ba shi lafiya."

Husna saita zama lost ta rasa me zata ce tayi gaba Bahari ya bita a baya yana faɗin "ki rinƙa kula in zaki tsallaka titi kinsan motoci gudu suke sosai musamman ma ƙananun nan..." Zuciyar Husna a karye tace "wallahi Bahari na duba ni banga Motar ba shi yasa na tafi zan tsallaka." 
Bahari ya maimaita "kin duba baki ganta ba kuma?" 

Husna ta ɗaga masa kai, kamar ya sake mata magana sai kuma yayi shiru yace "muje naga sauran kunun na nawa ne ya rage na siye nayi sadaka." 

Husna bata dake masa magana ba har suka ƙarasa kan botikin kunun ya duba yace "ai ya kusa ƙare wa." 
"Eh." 
Ta faɗa a sanyaye dan har yanzu tsoron motar data kusa kade ta bai barta ba.

         Kuɗin Kunun ta faɗa wa Bahari ya siye ya bawa masu so, ta karɓi kuɗin ta ya riƙo mata botikin tayiwa Indo sallama suka tafi gida Bahari na biye da ita a baya yana mata zance kamar yadda ya saba ita kuma yau babu baka sai kunne.


......Tunda tazo Dandalin take duban hanya amma ko alamun shi bata gani ba gaba ɗaya sai taji ta damu zaman wajen ya daina yi mata daɗi, Indo tana mata zance da bata Labarin bikin Asure da za'a saka gobe a Dandalin amma Husna gaba ɗaya hankalin ta baya wajen.

"Wai inata miki magana kina juye juye me kike nema ne?" Indo ta tambaye ta.
Husna saita tsinci kanta da cewa Indo "babu komai." 
Kafin Indo ta sake mata magana ta miƙe tace "nifa gida ma zan tafi." Indo tayi mata kallon mamaki.
"Baki da lafiya ne Ma'u? naga duk jikin ki yayi sanyi."
"Babu komai kawai bacci nake ji saida safe." ta faɗa tana juyawa tabar Indo da rakata da Ido.

Husna na tafiya a hanya ta haɗu da Dan Hajja da Gambo dan korar sa.
"A'a Budurwar mu ina zuwa kuma? Wajen kifa zamu." 

Husna ta ɗaga kai ta dube su a sheƙe sai kuma tayi gaba ta barsu a tsaye.

Gambo da yayi maganar ya dubi Ɗan Hajja yace "wallahi Ma'u yar wulaƙanci ce ji yadda ta ɗebe mu ta zubar kamar ba mutane ba." 

Ɗan Hajja ya bugi kafadar Gambo yana raka bayan Husna da Murmushi yace "karka damu saura kaɗan ta shigo hannu, kaji abin da Malam yace mana ɗazu a kanta dole sai mun bita a hankali."

Gambo da takaicin wulaƙancin da Husna tayi musu ya ƙume yace "ai wallahi naso ayi mata kiranye dandai kawai Malam yace ba zai yiwu bane."
"Dama kaika matsa min Gambo shi yasa nawa Malam maganar ta amma banda haka nawa Ma'u take a wajena da har saina haɗa ta da Malam, Hmmm ina sata a gidana fa zance ya wuce duk wannan dage kan zata dena min."
Gambo yayi ƙwafa "kasan Allah inaga Aramma ba haka yabar yarinyar nan ba, banda haka yaushe za'a ce wai komai nata a rufe yake ba'a iya ganin komai a kanta."

"Matsala ta dakai kana da gaggawa Gambo dan Allah muje." Dan Hajja ya faɗa yana yin gaba Gambo ya rufa masa baya....