27
by @aishatouuu
_Aishatou_
***
Babu wanda yasan Husna ta shigo gidan harta shiga ɗaki ta kwanta, dan su Ramma na wajen su, Dije ma tana lungun ta.
Akan gadon karar da Ramma ta siya mata take kwanciya ta zauna tana tunanin mai yasa yau bai zo Dandalin ba. Wata zuciyar tace "koya kwanta bacci da wuri."
Ta ɗanyi jim tana tuna abinda ya faru ɗazu sai kuma can a kasan zuciyar ta tace
"To a ina ma yake kwana?"
"A makaranta mana." Wani bari na zuciyar ta ya bata amsa.
"Allah Sarki ko shi a ina Maman shi take?" ta faɗa a fili.
"Shima bashi da Mama kamar ke."
Husna ta sake faɗa a raunane, sai kuma tayi murmushi a fili tace "wata rana zaka warke Yayan Husna."
Tun tana zance da tunane tunane harta kwanta, duhun ɗakin ya sake taimakawa wajen zurfafar tunanin ta har bata san lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba.
.......shi kuwa tun daga fitowar ta daga gida har lokacin da ta koma komai akan idon shi ya faru, baibar inda ya ɓoye ba saida yaga shigar ta gida yaɗan jima a tsaye yana kallon mutane suna wucewa jifa jifa saidai babu wanda ya kula dashi har yabar wajen ya kama hanyar makaranta.
*****Washegari da safe Husna taje gaida Aramma ta samu Lirwanu zaune a gaban shi Dije na kusa da Aramma, da alama magana suke mai muhimmanci, Husna na gama gaida Aramma ta gaida Dije da Lirwanu ta miƙe zata fita Aramma ya ce "Asma'ullahi zo nan zauna maganar tamu ai taki ce zo kiji abinda Baban ki Lirwanu ya zo dashi."
Husna ta dawo da baya ta zauna tana fuskantar Aramma yace "Asma'ullahi Baban ki Lirwanu ne ya zo da maganar yana son zai fara siyan Barkono yana kaiwa kasuwa kina siyar masa, kamar dai yadda kuke zuwa yin talla duk ranar kasuwa, to banki ta tashi ba dan zaman banzan da yake ba abune mai kyau ba, sam bana jin daɗi daya ɗauki shawarar mu a baya ma da tuni an dade da wuce nan amma yanzun ma bai makara ba, saidai kamar yadda na faɗa masa bakya nan yanzu ma zan maimaita masa a gaban ki zaki bishi kasuwa kiyi masa talla ne kawai inya yarda duk adadin cinikin da kika yi masa za'ayi lissafi ya cire hakkin ki na ladan talla ya baki kamar yadda kike wa sauran mutane, in ya yarda shike nan sai nace Allah ya bada sa'a in kuma bai yarda ba to ya nemi yaran gari suyi masa talla ya biya su ke kuma kici gaba da yiwa wasu suna biyan ki."
"Amma Aramma ban tari numfashin kaba tsakani da Allah yanzu dan Ma'u ta yiwa Lirwanu talla sai ace saiya biya ta ladan talla? In Mai Kano tayiwa talla za ace ya biya ta ne?" Dije ta faɗa cikin jin haushin maganar da Aramma yayi.
"Kwarai kuwa Hadiza, yau ko Abdullahi Asma'ullahi tayiwa talla saiya biya ta hakkin ta in baya ɗauke nauyin matsalolin ta, kinga saita biyawa kanta buƙata dashi, in kuwa yana yi mata abinda ya dace matsayin shi na uba ita ma saita yi mata kyauta dan neman Albarkarsa." Aramma ya bawa Dije amsa da duka gaskiyar shi.
Lirwanu kuwa ya shaƙi baƙin ciki da furucin Aramma amma sai ya danne ya nuna babu komai a gaban shi dan yasan muddin ya nuna ba zai rinƙa bawa Husna ladan talla ba to tsaf zai hana ta zuwa kuma ta hanu babu yadda zai yi.
Dije zata sake magana Lirwanu ya riga ta da cewa "babu komai Aramma saina rinƙa bata ladan tallar."
"To madallah ke Asma'ullahi kinji ko? In Allah ya kaimu Litinin saiki bishi Beguwar, Allah ya sawa newa albarka."
Lirwanu ya amsa da Amin yana kunshe tsari da shirin shi a ƙasan zuciyar sa, yayin da Husna taji saukar maganar bin Baba Lirwanu Kasuwa kamar bugun guduma a tsakiyar kanta.
"Wai yaushe zata huta ne daga masifa da kuntatawar Baba Lirwanu?" Ta tambayi kanta tanajin rauni rashin gata da rashin madafa na lulluɓe duka illahirin jikin ta, wani ciwon kai mai zafi ta bari ɗaya ya saukar mata take, idanun ta suka canja.
Kasa tashi tayi daga tsakar ɗakin saida Aramma ya yayi mata magana sannan ta miƙe tsaye da ƙyar tana hado duka dauriyar ta waje ɗaya.
"Asma'ullahi koda wani abu ne?" Aramma ya jefa mata tambayar da da zata iya ce masa zatayi "bazan yi wa Baba Lirwanu talla ba saboda cutata zai yi."
Amma maimakon ta bashi wannan amsar data dace da tambayar shi sai ta girgiza masa kai ta fita daga ɗakin da sauri tana jin Idanun ta na mata zafi.
Tana fitowa daga lungun Dije taji ana sanar da lalacewar Famfon cikin gari.
Duk halin ciwon kan da take ciki sai da ta ɗanyi turus dan tasan yau ɗiban ruwa zai yi wahala tunda Famfon cikin gari ya samu matsala saidai su tafi na makaranta indai suna son samun ruwa da wuri.
Ramma nayi mata magana ta wuce ta ta shige ɗaki ta kwanta a ƙasan leda tana mai da numfashi, baƙin ciki ke cinta ga wani kuka daya maƙale mata a wuya wanda bata son yinshi saboda ciwon da idanunta ke mata duk lokacin da tayi kuka saita kwana biyu cikin idan ta na mata ciwo kan ya daina.
"Ma'u wani abun ne ya faru?" Ramma data biyo ta ɗakin ta tamabaya tana zama a bakin gado.
"Babu komai kaina ke ciwo."
Husna ta bata amsa muryar ta a ƙasa.
"Ayya sannu bari na samu yaro ya siyo miki paracetamol a shagon Sunday saiki sha."
Ramma tayi maganar tana miƙe wa Husna ta tashi zaune tana dafe gefan kanta tace "barshi kawai ɗiban ruwa zamu, nasan yanzu an fara tafiya makaranta tunda an sanar da ɓacin Famfo, gwanda naje da wuri kada layi yayi yawa." tayi maganar tana fita daga ɗakin, Ramma ta raka ta da Ido, a zuciyar ta tana jin babu daɗi dan tasan dole akwai abinda ya faru kawai ba zata faɗa bane tunda tasan tana da zurfin ciki zai yi wahala kaji Husna tayi ƙorafi, tunda ta rasa gata ta koyi dauriya da kafiya kamar Namiji.
Har akayi sallar azahar Husna sahu biyu na ruwa ta kawo gidan, wannan karon data koma tana sa layin jarkokin ta ta koma gefe ta zauna ta kife kai tana mai da numfashi dan sosai yanzu kanta ke mata ciwo inta shiga rana kuwa ji take kamar ana zuba mata ruwan sanyi.
Har wajen ƙarfe uku bata sake kawo ruwa ba, Lirwanu ya shigo Zahara uwar ƴan ƙorafi da mita tace "yau dai fa gidan nan namu babu ruwa, bana jin kona saka sanwar dare zamu samu."
Lirwanu ya dube ta sai kuma yace "Ma'u bata kawo ruwan bane?"
Kan Zahara tayi magana Ramma tace "ta kawo sahu biyu, kasan yau Famfo zai yi layi tunda babu na cikin gari."
"Wanne zancen banza ne kuma wannan, rashin Famfon cikin gari sai ya hana a samu ruwa? Da da yake lalacewar a samu ruwam fa? Iskanci ne kawai irin nata da in bata gadamar yin abuba saita ɓatawa mutane rai."
Lirwanu yayi maganar a zafafe, dai-dai lokacin kuma Husna ke shigowa da Ruwan a bakin randar Dije ta ajiye Sagar ruwan data debo maimakon ta juye saita zauna a ƙasa tana maida numfashi dan wallahi da ƙyar ta iya kawo ruwan gida dan ma Indo ta tayata buga ruwan da ba zata iya debowa ba.
Shiru shiru bata tashi ta juye ruwan ba, ran Lirwanu ya ɓaci da ganin ta zauna a bakin randar bata juye ruwan ba.
A zafafe yazo kanta yana mata magana, saita ɗago da jajayen idanun ta da ƙyar ta kalle sa, babu tausayi ko kula da yanayin da take ciki ya kwashe ta da marin da saida ta kifa saboda zafin shi, sai kuma ya balbale ta da masifa yana cewa.
"Ke saboda kin raina mutane ana miki magana kikayi banza, tun safe ana jira ki kawo ruwan sai yanzu kike shigowa da shi kuma sai ki zo ki sake zauna wa, to uban waye zai zuba miki sauran ruwan? ko kuma salon dare yayi kija ana zagina a gari."
Husna ta yunƙura ta taso da ƙyar tana jin cikin idanun ta kamar zasu faɗo ƙasa saboda ciwo tace
"Baba Lirwanu kaina ciwo yake bazan iya ɗebo ruwan ba." ta faɗa tana layi kamar zata faɗi ƙasa Allah ya taimake ta ta dafe jikin ican rumfar Dije.
A tsiyace ya kalle ta daga sama har ƙasa yace "Ni zaki renawa wayo? A'a mutuwa kike ba ciwon kai ba, kin wuce kin kawo min ruwa gidan nan ko saina ɓalli tsimagiya na nuna miki jikin ki yanzun nan."
Yayi maganar da hargowa, zuciyar Husna na wani irin ciwo mai raɗaɗi ta saka hannu ta ɗauki sandar sagan ruwan tasa ajikin jarkokin ta saɓa a kafadar ta ta juya tana tangaɗi ta kama hanyar fita daga gidan.
Data fito maimakon ta tafi saita samu waje a ƙofar gida ta zauna ta sunkuyar da kanta da take jinshi kamar ba'a jikin taba.
Bata san adadin tsayawan lokacin da ta ɗauka a wajen a zaune ba sai da taji maganar Aramma yana kiran sunan ta.
"Asma'ullahi....ke....Asma'ullahi lafiyar ki kuwa? Me kike yi nan a zaune?" Aramma ya jero mata tambayoyin yana isa inda take.
"Subhanallah! Baki da lafiya kike zaune a nan?" Aramma ya faɗa yana zare hannun shi daga wuyan ta da yaji yayi mugun zafi kamar garwashin wuta.
Da taimakon Aramma suka shiga cikin gidan yasa yara suka shigo da jarakunan ciki, shi kuma ya kamata saboda jikin ta rawa yake kamar ana kada mata gangi zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ta, Ramma na gano shigowar su ta taso tana tambayar.
"lafiya?"
Dan dama tun fitar ta daga gidan hankalin ta yaƙi kwanciya.
Kamata ku shiga ciki Zazzaɓi ne ya buge ta can na ganta zaune a ƙofar gida, ina Iro yake? Yazo ya siyo mata maganin zazzaɓi tasha, Allah ya sawake." Aramma ya faɗa yana ƙwala wa Iro daya hango acikin kewaye kira, Naja da sauran matan su Baba Adamu sai sannu suke jerawa Husna, Yaron Zahara Ramma tasa ya shimfida mata taburma a kewayen su ta kwantar da Husna dake ta rawar sanyi, ɗakin ta ta shiga ta dakko zanin gado ta rufa mata.
Tana zaune a kusa da ita Iro ya kawo maganin da Aramma yasa ya siyo, saida ta ɗebo ruwa sannan ta tashi Husna ta bata maganin, da ƙyar ta iya karɓa tasha tana rawar sanyi, ta koma ta kwanta Ramma ta sake rufe ta da zanin gado....