MUTUWAR AURE...! BOOK 1

28

by @aishatouuu

_Aishtou_

***
_________________


Har bayan la'asar Husna na kwance, har lokacin kuma Ramma na tare da ita musamman da yake ba ita keda girki ba saita maida hankalin ta akan Husna, sai wajen ƙarfe biyar na yamma sannan zazzaɓin ya sauka gumi ya karyo mata, Ramma ta taimaka mata ta zauna dai-dai lokacin kuma Aramma ya shigo gidan Lirwanu na biye dashi a baya, randa ya buɗe zai sha ruwa yaga wayan Ramma najiyo shi a cikin gida yana faɗin "yau saina zane yarinyar ace har yanzu bata kawo ruwan nan ba." 
Yana rufe baki Aramma ya fito yana gyara nadin rawanin sa yace "kai me yasa baka da lissafi ne Lirwanu? Kasan me ya hanata zuba ruwan kake wannan furuci haka? kai kullum kana girma kana sake shiga jeji, to gata can kwance a lungun ka zazzaɓi ya rufe ta tun ɗazu saini na shigo da ita gida, saika ɗauki Saga ka karo ruwan tunda yau baiwar taka babu lafiya."

Aramma ya faɗa yana yin gaba kana ganin yadda yayi maganar kuma kasan ranshi a ɓace yake.

Dole uwar naki Lirwanu ya fita ya karo sahu biyu yana mita dan shi gani yake ciwon Husna iskanci ne kawai da lamɓo.

........Mahaukacin yayan ta kuwa tun rana yake zagaya inda suke zaman saida abincin rana amma sai yaga bata nan har aka yi sallar la'asar ya koma can bayan rumfar Bahari ya zauna yana kallon hanyar da take fitowa, yana jiran yaga ta zo ta wuce da Kunun yamma, nan ma shiru babu ita babu dalilin ta har rana ta fara faduwa babu Husna babu alamar ta.

Bahari ne yaga yanata zagaye tsakanin inda su Husna ke zama da hanyar da take biyo wa yazo makar zai wuce ta kusa dashi yace "Ma'u kake nema ko?" 
Bai tsaya ba kuma bai ce masa komai ba shima Bahari be yaji ya bashi amsa ba tunda sunsan baya magana amma duk da haka sai ya ɗaga murya yace "Nima tun ɗazu zaman jiran ta nake yau ko abincin rana batayi ba Kunun yammar ma shiru Allah dai yasa lafiya dan yau bata zuwa talla ƙyauyu ka." 
Bahari ke babatun maganar sa shi kaɗai dan shi tuni yayi nisa da inda yake.

Yana tafiya Bahari ya gano Indo tana taho wa zata wuce ya tsaida ita da tambayar.
"Ina Husna yau naga bata fito ba lafiya kuwa?" Indo ta tsaya tace "nima ban sani ba amma ɗazu tare muka ɗebi ruwa da ita a makaranta sai dai ta cemin kanta na ciwo inaga shi yasa basu yi kunu ba." Bahari ya jinjina kai yace "Eh inaga haka ne nagode to." 

Ya koma ya zauna akan bencin da yake zama ita kuma Indo ta wuce.

             Tunda aka yi sallar isha'i ya tafi can bayan bishiyar daya tsaya jiya ya zauna yana jiran ganin fitowar Husna Dandali, yana zaune a wajen har yan mata suka hura wuta suka fara waƙe baiga Husna ta wuce ba.

Can ya ɗago kanshi yaga Indo tana ƙwala wa Ummai kira, saida ya bari suka gama maganar su yaga tayi hanyar gidan su Husna, a hankali yake binta a baya ba tare data sani ba har ta shige gidan ya koma can cikin duhuwa ɗan nesa da gidan kaɗan ya tsaya yana jiran fitowar su.

Shiru shiru babu Indo babu Husna har tsawan wani lokaci sannan yaga Indo ta fito ita kaɗai ta sake komawa Dandali.

Ji yake kamar ya bita ya tambaye ta ina Husna take to amma ta yaya zai tambaye tan? Jikin shi yaji yana saki haka kawai shi kansa baisan me ya saba amma sai ya tsinci kansa cikin damuwa da rashin walwala, bashi da wani buri yanzu da yafi yaji kuma yasan halin da take ciki, ransa yaji ya ɓaci damuwa ta lulluɓe zuciyar sa, bai tafi ba haka yaci gaba da tsaiwa a wajen har zuwa wani lokaci mai tsayi sannan ya juya ya tafi yana jin babu daɗi.

                  Abu kamar wasa washegari ma haka ce ta faru gare shi dan babu Husna babu labarin ta, nan fa hankali sa yayi asalin tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye, daga tasha zuwa gidan su kuwa ba zai iya lissafa sau nawa yaje ya koma ba.

Duk abinda yake faruwa dashi kuma Bahari na ankare ya zuba masa ido ne kawai yana kallon ikon Allah, mamakin Mahaukacin ya kashe Bahari har saida ya tambayi kansa a sarari yace "wai dama ana haka?"

Duk da shi kansa Baharin rashin ganin Husna kwana ɗaya da wuni biyu ya sashi cikin tunanin san sanin halin da take ciki tunda yake a garin bai taɓa kwana ko wuni guda cur ba tare da yaga giftawar Husna ba, magana ta gaskiya shi kansa rashin ganin ta ya dame shi amma sai mamakin ganin zagayen da mahaukacin yayan ta ke yi tsakanin tasha da gidan su ya kashe sa a zaune, gaba ɗaya saiya rasa wani tunani ya kamata yayi.

         Indo na fitowa saida ƙosan yamma da sauri Bahari ya fara ƙwala mata kira tana zuwa inda yake ya tsare ta da tambaya.

"wai Indo ina ƙawar ki Ma'u? kwana biyu shiru bana ganin ta kodai tayi tafiya ne?" Bahari yayi wa Indo tambayar yana duban ta cikin zaƙuwar sanjin abinda zata ce.

"Lah Ma'u, wallahi bata da lafiya jiya da naje dubata tana ta amai bakaga yadda tayi ba, masassara (zazzaɓi) ce tayi mata mugun bugu."

Cikin jimamin halin rashin lafiyar da Husna ke ciki Bahari yace "Subhanallahi kai Allah ya bata lafiya."

Kamar yayi shiru ya danne tunanin dake ranshi sai kuma wata zuciyar ta hana sa tare da karfafa masa gwiwa, ya sake dubam Indo yace "dan Allah anjima ko zaki raka ni gidan su na duba ta." 

Indo ta ɗaga masa kai, ya koma wajen saida fetir ɗin sa ya zauna yana kada kafa wani tunani ya faɗo masa rai, tunanin yasa yadan buɗe ido da sauri sai kuma yayi wani cikakken murmushi haɗe da dariya ya ɗaga kai sama ya kalli sararin samaniya kamar me lissafa adadin gajimare yana kunshe dariyar sa, da wani irin nishadi ya sauke kansa yana shafa gemun sa a fili yace "da yace baya ji." 

Ya faɗa da nishadi kamar wani sakarai a karo na biyu ya saki murmushi yana dukan ɗaya tafin hannun sa ya koma ya zauna da kyau yana duban mutanen cikin tashar ɗaya bayan ɗaya har yanzu murmushi bai gushe daga saman fuskar shiba yadda kasan wanda aka yiwa albashir da farar haihuwa.



          _masu karatu nace ba, wai me kuke tunanin yasa Bahari irin wannan sambatu da farin ciki haka?🤔👇🏻_

_Mu haɗu a comment section_


Bayan Sallar Magarba Indo ta raka Bahari duba Husna, sanda suka je Aramma na masallaci dan baya dawowa gida sai bayan sallar isha'i saiya shigo gidan gaba ɗaya, Dije najin anzo duba Ma'u tace koma waye ya shigo jikin ta na rawa dan ta ɗauka Dan Hajja ne ya zo dubiya saida Bahari ya shigo taga bashi bane.

Ramma har kewayen su ta raka Bahari Indo na biye dasu, Husna na zaune akan taburmar da Ramma ta shimfiɗa musu ta jingina bayan ta da garu kanta babu ɗankwali ta juya kai gefe tana kallon waje guda kamar me tunani Bahari yayi Sallama Zahara na daga ƙofar ɗakin ta ta amsa tana sake kunna fitila dan daga waye da kyau.

Husna na ganin Bahari taja kallabinta ta rufa a saman kitson kanta daya fara tsufa.

"Sannu Husnah, ashe baki da lafiya shi yasa muka ji shiru? Wallahi sai ɗazu Indo take faɗa min, kai sannu Allah ya baki lafiya." Bahari ya faɗa yana duban ta duk tayi wani fayau da ita ta faɗa lokaci ɗaya, wuyan ta da jelar kitson ta ya sakko kai ya sake tsayi wasu ƙasusuwa suka ɗan bayyana alamun tayi rama.

Kai ta ɗagawa Bahari tana murmushi, Ramma ta amsa da "Amin an gode."

Bai wani jima ba ya tashi zai tafi ya aje mata dubu biyu akan taburmar da take zaune yace "kya siyi wani abu Allah ya ƙara lafiya."

"A'a kuma harda wahala? angode Allah ya bada lada." Ramma ta faɗa, Husna ta motsa bakin ta a hankali tace "nagde Bahari." 

Kai ya jinjina ba tare daya sake duban inda take ba ya fice daga wajen yana fita Lirwanu na shigowa yaɗan tsaya suka gaisa ya tambaye shi mai jiki bai kuma jira amsawar saba ya wuce sa shi kuma Lirwanu ya shiga cikin lungun nasa yana kallon bayan Bahari.

          Ramma ta ɗauki kuɗin tace "Alhamdulillah Ma'u gobe saina rakaki Doko kiga likita akwai kuɗi a hannuna saimu hada da wannan zai isa, kinga zazzaɓin nan da ya sauka yake sake hawa maganin da Aramma ya siya miki kuma in kika sha na dare ya ƙare."

"Kema dai Ramma da fi'ilin tsiya kike banda haka duk zazzaɓin da yaran gidan nan ke yi naga dai magani suke sha har su warke, shi ne zakice wani zaki ɗauke ta kuje asibiti sai kace mai ciwon mutuwa." Zahara ta faɗa tana duban Lirwanu daya shigo, Husna kuwa ƙala bata ce ba ta koma ta kwanta.

Lirwanu ya tambayi zancen me ake Zahara da dama dan yayi magana tayi zancen tsaram ta fara maida masa yadda maganar take, shi kuwa babu kunya babu tsoron Allah ya miƙawa Ramma hannu.

"Bani kuɗin nan, dama akwai abin da zanyi da kuɗi neman su ma na shigo yanzu, tunda Allah ya kawo su cikin sauƙi kuma shi ke nan ta kwana gidan sauƙi bani su nan." Yayi maganar yana miƙawa Ramma hannu.

"Haba Lirwanu Ma'u fa da zazzaɓin nan take kwana take wuni, wallahi koya sauka saiya dawo, amma in muk......."

"Nace ki bani kuɗin ba tsari nace kimin ba ƴar Iya." 

Lirwanu ya katse Ramma a faɗace, zuciyar ta babu daɗi ta miƙa masa kuɗin yasa hannu ya karɓe ya jefa su aljihu ya fice daga gidan gaba ɗaya, Zahara kuwa zuciyar ta tayi fari fes dama burin ta ke nan ya karɓe kuɗin, kuma ya amshe.

Bahari da Indo kuwa suna fitowa daga gidan su Husna suka ga Mahaukacin yayan ta tsaye a jikin bishiyar Kofar gidan yana kallon ƙofar fitowa kamar me jiran sallahu.
"Turus." 
Bahari ya ɗan ja da baya ya tsaya saboda mamakin ganin sa a wajen sai kuma ya ɗan basar ya dubi Indo yana gyaɗa kai yace "taɓ Allah mai iko Indo dubi mahaukacin Ma'u a tsaye, wallahi da alama ita yake nema yo Mahaukaci mafa ke nan yasan me basa bare mai hankali?"

Bahari ya dire zancen da sigar mamaki, Indo tace "kasan jiya ina zuwa duba Ma'u tana rawar sanyi amma saida ta tambaye ni shi, ita ko tsoron sa ma bata ji."

Bahari ya ɗan matsa inda yake tsaye yace "to Ma'u dai bata da lafiya saika juya kabar nan wajen, kazo ka tsaya musu a ƙofar gida." 

"Bahari wai kaima maganar kake masa irin na Ma'u sai kace wani me hankali?" Maganar Indo ta katse Bahari, ya juyo yaga ta riƙe baki cikin mamaki saida Bahari yayi Murmushi sannan yace "yo tunda yasan ya nemi me bashi abinci ai kuwa yaci ya gane zance na."

            Shi dai har suka yi maganar su suka wuce sa bai ɗago ya dubi kowa a cikin suba, Saida suka jima da tafiya sannan ya juya yabar wajen.

Bai daɗe da tafiya ba kuma Dan Hajja da Gambo suka shiga gidan riƙe da ƙatuwar leda cike da lemo da ayaba.

Dije najin Sallamar Dan Hajja ta fito dan dama tasan tunda ta aika a faɗa masa Ma'u babu lafiya dole zai zo ya dubiya shi yasa ma ɗazu da taji anzo dubiyarta ta ɗauka shi ne.

"Maraba da jikan arziki lalle marhaban ku ƙaraso nan tana wajen su bari a kirata." Dije ta faɗa tana basu hanya suka shige lungun ta.

"Ina wuni Dije?" Su Dan Hajja suka fara gaida ita, ta amsa musu bakin ta buɗe, sai kuma ta miƙe tana gyara ɗaurin zani tace "Bari a kira maka ita saiku gaisa."
 
Ta fice kiran Husna su kuma suka Zauna zaman jiran dawowa ta.

"Muguwa bazaki tashi muje ba ƴar baƙin ciki, yaron kirki mai rufun asiri yana sonki kinawa kanki da mutane bakin ciki, duk garin nan daga manya har Samari irin sa faɗa min mai rufun asirin shi, ko wacce yarinya so take ya taya ta amma ke yace yana sonki shi ne zakiyi wa mutane iya shege, kin tashi ko saina hau kanki da daren nan." 

Dije keta fama da Husna tana zuba mata masifar ta tashi suje wajen su Dan Hajja su duba ta amma fir taƙi tashi, Ramma tasa baki ma duk tayi banza ta rabu dasu.

Zahara ce ta dubi Dije tace "kema fa Iya kinsan taurin kan Ma'u in bata so yin abuba bata yinsa, to me zai hana kawai kice suzo nan ɗin saisu suba ta."
"Kaji ƴar Albarka ni ai banyi wannan tunanin ba, shegiya ƴar baƙin ciki zata yimin buƙulun abinda zan samu bari naje nazo dasu." Dije ta faɗa tana juyawa dingis dingis ta fita daga lungun.

             Bata jima da fita ba sai gasu sun dawo da su ɗan Hajja tana gaba suna binta a baya, a gefan taburmar da Husna ke kwance suka zauna, Gambo ne ya fara mata sannu tayi masa banza kamar wacce ke bacci, haushi ya sake ƙume Dije dan tasan ba bacci take ba.

"Sannu Ma'u, Allah ya baki lafiya." 

Ɗan Hajja ya faɗa yana kallon ta shi ɗin ma banza tayi masa sai Ramma ce ta amsa da "Amin an gode."

Dije kuwa cewa tayi "kunsan jikin nata ne babu daɗi inaga bacci tayi dan ɗazu ma da nazo kiran ta kasa tashi tayi, kai ai Ma'u najin jiki, wannan zazzaɓi ba ƙaramin kamu yayi mata ba."
 
Ramma ta saki baki tana kallon Dije na yanko ƙarya Zahara kuwa murmushi tayi dan tasan wannan abun da Dije ke yi da biyu aljihun ta take gyarawa, dan haka ita ma ta taya ta da cewa.
"Wallahi kuwa Iya Ma'u na jin jiki Allah dai ya tashi kafaɗun ta." Zahara ta faɗa da tata manufar kunshe a ƙasan rai.

Ɗan Hajja ya dubi Dije yana karkace wa ya ciro ƴan ɗari biyar biyar sababbi saida ya irga guda goma sannan ya ajiye wa Dije a gaban ta yana faɗin "gashi a kaita asibiti ai batayi ta zama da ciwo ba, mu zamu tafi sai goben in kun shirya zuwa asibitin Gambo sai ya zo ya kaiku taga likita." 
Dan Hajja ya faɗa yana miƙewa tsaye Gambo ya ajiye ledar hannun shi yana faɗin "Allah ya bata lafiya."

                "Kaga yaron arziki kuma harda kuɗi bayan wannan wahalar da ake tayi damu? An gode an doge Allah yaji kan Malma Mudi (Babansa), ai da yake Aramma ma ya siya mata magani kasan masassara ce da naci." Dije ta faɗa tana raka su, suna tafe tana zuba wa Dan Hajja addu'a, saida suka fice daga gidan sannan ta dawo wajen su Ramma.

Ma'u ke dai akwai muguwa ƴar baƙin ciki, da har zaki jamin asara na rasa wannan kuɗin badan shawarar Zahara ba." 

Dije ta faɗa tana zubawa Husna harara sai kuma ta dubi Zahara tace "Zahara dubi abun arziki yaushe raban na kama farare irin wannan ai tun Salisu na raye."
Sai kuma "fesssss..." Ta bace majina tana tsane hawaye tace "Allah yaji kanka Salisu." 
Da sauri Zahara ta amsa da "Amin Amin Iya."

Ɗari biyar Dije ta cire a cikin kuɗin da ɗan Hajja ya bata ta mika wa Zahara.

"Ungo wannan kema kisa albarka."

Zahara tayi caraf ta amshe tana zuba godiya da banbaɗancin kwaɗayi.

"Ke kuma da yar baƙin cikin naki sai kuci kanku sisi na baza ku gani ba wallahi, tunda ai iskancin da Ma'u ke yi mini wani ke kike zigata." Dije ta faɗa tana kallon Ramma data zuba musu Ido tana kallon ikon Allah, Husna kuwa ko inda Dije da kuɗin suke bata duba.

Ledar da Dan Hajja ya kawo Dije ta buɗe ta cire lemo da ayaba guda biyu biyu ta bawa Ramma Zahara kuma ta bata lemo ɗaya ayaba ɗaya, ta kulle sauran ta tafi dasu.

Tana fita daga lungun Zahara tace "kai gaskiya Iya badai san kaiba, yanzu duk yawan lemo da ayabar nan da aka kawo ta rasa nawa zata bamu sai ɗai ɗai."
Ramma da Husna suka yi banza da ita kamar basu ji abinda tace ba...