MUTUWAR AURE...! BOOK 1

29

by @aishatouuu

_Aishatou_

***
_________________


Yauma haka ya gama zagayen shi a Dandali babu Husna babu dalilin ta, har kowa ya watse yana tsaye yana kallo.

               Washegari da safe wajen ƙarfe goma saiga Indo da matar Sunday a gidan, da gwarin Hausar ta suka gaisa da matan gidan sannan Indo ta cewa Ramma.

"Naje siyan magi Sunday ke tambaya ta Ma'u kwana biyu nace bata da lafiya shi ne yace Matar shi tazo ta duba ta." 

Duka matan inuwar sai suka ƙara bin Matar da kallo dan basu taɓa ganin taba suna dai ji a bakin yara suna cewa Sunday ya kawo matar sa amma basu taɓa ganin taba sai yau.

Ramma tace "Allah Sarki muje to tana ciki yanzu na baro ta zata shiga wanka." Tayi maganar tana miƙewa Indo da matar Sunday suka bita a baya.

Suna tafiya matan inuwar suka kafa gulmar ta daga masu cewa farin ta yayi yawa sai masu cewa tayi ja da yawa.

            A bakin gado suka samu Husna harta fito daga wankan tasa kaya tana shafa mai.

"Ga bakuwa nan Ma'u tazo duba ki." 

Ramma ta faɗa tana nuna mata matar Sunday dake bin ta da kallo, duk sai taga ta rame idanun ta sun sake fitowa waje bakin ta ya bushe sosai kamar mai jin ƙishirwa.

Husna na murmushi suka gaisa da matar Sunday cikin harshen Ingilishi dan bata wani iya Hausa ba, sai suka zama abun kallo a wajen Ramma da Indo.

            "My friend kinajin jiki fa amma inkin yarda zan iya duba lafiyar ki, dan ni Likita ce a garin mu." Husna tace "da gaske?"

Chioma ta ɗaga mata kai tana murmushi, Husna ta dubi Ramma tayi mata bayanin abinda suke faɗa.

"To in kina ganin babu matsala ta duba kin mana, Allah yasa dai kuɗin wajen mu ya isa." 

Husna tayi shiru tana tunani, ita kanta tana so a duba ta saboda ciwon kan dake damun ta ga zazzaɓin da yana sauka saiya sake dawowa.

"to amma in kuɗin wajen su bai kai bafa?"
Wata zuciyar tace "saita fara faɗa muku kuɗin kanta baki magani." Da wannan shawarar ta zuciyar ta ta yarda ta dubi Matar Sunday tace  "ki dubani sai muji nawa ne kuɗin." 

Murmushi Chioma tayi wa Husna har saida fararen haƙoran ta suka bayyana sannan tace "bari muga menene matsalar ki sannan sai muyi maganar kuɗi daga baya."

Take ta fara duba ta kamar wanda ta zo da shirin ta ta zura hannu a aljihu ta fito da wani farin abu mai nombobi ajiki, a jikin rigar Husna tasa abun ta saitin ƙirjin ta saida yayi wasu mintina sanna ta cire ta duba jikin abun, ta kama hannun Husna ta duba ta buɗe idanun tama ta duba sosai.

"Zan je na dakko magani saina dawo." Ta faɗa tana tashi tsaye, Husna ta gyaɗa mata kai suka fice ita da Indo. Husna Tayiwa Ramma bayanin abinda tace.

"To bari naje mu ƙarasa kwashe surfan can kanta dawo." Ramma ta fita daga ɗakin.

Sha biyu saura matar Sunday ta dawo, wannan karon ita kaɗai ta dawo hannun ta riƙe da farar leda me ɗan girma.

Abinka da yare yanzu ma saida ta sake gaida matan inuwar sannan Ramma ta raka ta ɗakin ta wajen Husna.

Zazzabi harya sake rufe ta, tana rawar sanyi suka shigo ɗakin.

"Heeee sorry my friend?" Matar Sunday ta faɗa tana fiffito da kayan ledar tarkacen Allurai ne magunguna da ledar ruwa guda biyu.

Ramma ta zauna a bakin gado tana kallon yadda matar ke neman jijiyar da zata ɗaura wa Husna ruwa.

Cikin kankanin lokaci tasa mata ruwan da Allurai tayi mata wasu a jiki, tana saka mata ruwan tana mata sannu, cikin mintunan da basu wuce biyar ba bacci mai nauyi ya ɗauke Husna saboda alluran data saka mata a ruwan harda na bacci.

Magungunan data kawo ta bawa Ramma da gwarin Hausar ta tace "zan zauna in ruwan shi ya ƙare zana saka mishi wani." 

Ramma ta karɓi maganin tana mata godiya tace bari taje waje tana zuwa.

Ramma na dawowa inuwar ta tadda Dije dawowar ta ke nan daga fitar da tayi tace "me kuke kullawa ne a ciki? Yanzu nake jin labarin Matar Sunday na cikin ɗakin ki."

Ramma ta dubi su Zahara a ranta ta jinjina wa munafuncin su sai kuma yace "Eh tazo duba jikin Ma'u ne sai kuma tasa mata ƙarin ruwa."

Ramma ta faɗa tana zama danta ƙarasa busar hatsin da take, Dije tace "ban gane ruwa ba? Saka ruwa kamar a asibiti." Sai kuma tayi hanyar ɗakin Ramma dan ganewa idan ta dahir.

Chioma na zaune tana jire Husna Dije ta bankada labulan ɗakin, ta kalli farar matar zaune tana danna waya Husna kuma na bacci ɗaure da ƙarin ruwa.

"Sannu Mama." Chioma ta gaishe da Dije.
"Sannu ƴar nan, dama likita ce ke?" Chioma ta bita da Ido dan bata gane abinda take faɗa ba.

"Hausa babu Mama." Chioma ta faɗa wa Dije haka a gwarance.
"Ikon Allah ke kuma Hausar ma bakya ji ke nan?" Dije ta faɗa tana sakin labunlan ta juya.

                Saboda tsabar sheda da sunan dubiya saida kowa ya zo dakin Ramma a cikin matan inuwar ya leƙa ɗakin Ramma yaga abunda ake yi.

Chioma tana zaune ruwan ya ƙare ta sake sa mata ɗayan, sai wajen ƙarfe biyu Chioma ta baro gidan bayan ta cire wa Husna ƙarin ruwan, da kwatance ta nuna wa Ramma in Husna ta tashi daga bacci tazo. 
Ramma nason tayi mata maganar kuɗi amma Chioma babu Hausa ita kuma ba turanci, kawai saita bari in Husna ta tashi taje taji nawa ne kuɗin ta. Ramma ta gane abinda take nufi saita ɗaga mata kai tayi mata godiya.

Husna bata tashi daga baccin ba sai bayan sallar la'asar, lokacin da ta tashi taji jikin ta yayi mata daɗi babu wani ciwo da take ji yanzu sai rashin kwarin jiki, dan fayau take jinta kamar iska.

Saida tayi wanka tasa kaya sannan Ramma ta faɗa mata yadda suka yi da Chioma.

A hankali Husna ta fito daga gidan su ta kama hanyar tasha dan zuwa shagon Sunday taji nawa ne kuɗin maganin da Chioma tayi mata, tana tafe tana addu'ar Allah yasa kuɗin wajen su ya isa su biya kuɗin maganin nata.

Chioma kaɗai Husna ta samu a cikin shago suka gaisa Chioma nata mata murmushi da jero mata sannu, Husna ta mayar mata da martanin murmushin ta sannan tace "thank you Mrs Sunday, nawa ne kuɗin ki? Baki dafa mana ba ɗazu." 

Chioma tayi murmushi tana kallon Husna sai kuma ta dafa kafaɗun ta tace "kin manta randa muka fara haɗuwa nace miki mu ƙawaye ne?" 

Husna ta ɗaga idanun ta da suka sake girma saboda faɗawar da suka yi ta dubi Chioma cikin san ƙarin bayani akan abinda tace.

Chioma ta gane abinda take nufi sai ta sake sakar mata murmushi tace "Inason cewa komai kikaga nayi miki nayi miki shi ne kyauta saboda ƙawancen mu."
Husna ta buɗe baki da mamaki tana duban Chioma dan kowa a garin nan yasan Sunday mayan kuɗi ne baya kyauta bare sakada amma shi ne yanzu matar shi zatayi mata magani kyauta.

"Karki damu da gaske nake yi kyauta nayi miki, ina miki fatan sake samun lafiya." Chioma ta sake faɗa.

Husna ta gyaɗa kai tana murmushi zuciyar ta cike da mamakin ta a sanyaye tace "nagde sosai Mrs Sunday, Allah ya biyaki."
"Karki damu." Chioma ta faɗa, saida Chioma ta yiwa mata bayanin yadda zata sha maganin ta sannan ta baro shagon cikin juyayi da dunbin mamakin abinda Chioma tayi mata.

A hanyar Husna ta komawa gida tayi ta wai waye a cikin tashar ko zata ga yayan ta, amma harta wuce rumfar Bahari da taga wajen a rufe ta wuce ta ɗan Hajja bata ganshi ba, tana tafe tana tunanin ko ina yake kwana biyu nan tayi kewar sa, sai kuma tayi murmushi tana sake duban yanayin garin da yamma tayi sosai, tana jin dokin dare yayi taje dandalin.
A ranta tace "Allah yasa yau kazo Yaya."

Sanda Husna ta faɗawa Ramma yadda suka yi da Chioma sai Ramma ta cika da mamaki tayi ta jera mata godiya dan sosai taji daɗin abinda tayi musu dan dama ba wani kuɗin kirki bane a hannun su.

         Ana yin sallar isha'i Husna cikin sauri da doki ta cewa Ramma ta tafi dandali, Ramma ta dube ta sanda take saka Hijabin ta tace "amma Ma'u dakin bari kin sake warware wa, daga jin sauƙin ki yau kuma saiki tafi dandali." Husna tayi murmushi tace "Ramma nafa samu sauƙi, zan iya zuwa." Tayi maganar tana fita daga ɗakin da sauri dan Allah Allah take ta isa Dandalin.

Indo na tsakiyar ƴan mata ana shirin fara yekuwar saka Asure ta hango Husna na tahowa, fitowa tayi daga tsakiyar ƴan matan tayi wajen ta tana ƙwala mata kira.

"Aha Ma'u jiki yayi kyau, dama fa yanzu nake jira mu gama saka ranar Asure sai naje na dubaki ashe ma kinji sauƙi." 

Husna ta dubi Indo fuskar ta a sake tace "naji sauƙi."
Indo ta kama hannun ta tana janta tace "zo muje kinga har za'a fara yekuwar, kinsan yau zamu saka ranar bikin Asure." 

Husna taɗan yamutsa fuska tana cire hannun ta daga na Indo tace "wai har lokacin saka Asuren yayi? Lallai bana da wuri za'a yishi." 
"Eh yayi kinsan hatsi ya riga ya zo gida tuni shi yasa, zo  muje karsu fara babu mu, kinga sai ki hau dokin ki dama Ummai ce ta hau naki tunda bakya nan kuma dole saida mu za'a saka tunda mune ƴan Auran baɗi."

Indo tayi maganar tana jan Husna dan su isa wajen, Husna kuwa saita coge tana faɗin.
"Jeki kawai ni bazan jeba inkun saka naji."
Indo ta juya ta kalli Husna kamar zata yi magana sai kuma tayi cikin Dankalin da gudu soboda jin har sun fara shewar saka Asuren bata nan."

Husna kuwa saita juya ta tafi inda suke zama zuciyar ta cike da fatan Yayan ta yazo, abinda bata sani ba shine daga fitowar ta daga gida har zuwa tsayawar ta da Indo duka akan idanun shi ya faru.

            Tana isa inda suke zaman ta cika da farin ciki da wani irin jin daɗin ganin shi a zaune akan ican da suke zama riƙe da sandar shi da baya rabo da ita yana bubbaga ta a ƙasa kanshi na sunkuye, daɗi ya cika zuciyar Husna ta washe masa baki tana kallon sa tace "Lah Yaya yau kazo." Ta faɗa da murna, ya ɗago kanshi kamar mai jiran isowar ta wajen ya kalle ta ta cikin rufaffun Idanun sa, Husna kuwa saita cire takalman ta ta saka a gaban shi ta zauna akai tallafe da kumatun ta tana ƙarewa fuskar shi data cika da gashi kallo cikin jin daɗin ganin sa tace "Yayaaaaa." Ta kira shi a sakalce.

           Idanun sa ya buɗe gaba ɗaya ya zuba su akan Husna ta cikin hasken farin watan daya ratso ta inda suke zaune yake ƙare mata kallo, duk sai yaga ta rame masa fuskar ta tayi kuyat, hakan saiya ƙarawa Idanun ta girma da haske.

Maganar Husna ta dawo da shi daga tunanin daya shiga, tana masa murmushi take faɗin.
"Yaya ranar nan bakazo dandali ba nayi ta jiranka." Kamar yadda tasan ba zata samu amsar maganar ta daga gare shi ba hakan kuma baisa ta tsaya da maganar ba taci gaba da cewa.

"Yaya rashin lafiya fa nayi, kwana nan uku bani da lafiya, Aramma da Ramma sunata siyamin magani amma cuwon yaƙi warkewa saida matar Sunday tazo ta bani magani."

Sai kuma ta ɗanyi shiru tana jin ciwon Abinda Baba Lirwanu yayi mata yana taso mata, a hankali tace "Kuma bata karɓi kuɗi ba wai ni ƙawar tace, Yaya ai dai tana da kirki ko?"

Husna tayi maganar tana kallon sa, sai taga shima idanun sa har yanzu suna kanta, ganin idanunshi sun fito sosai fiya da randa mota ta kusa kade ta, sai ta ɓata fuska ta kumbura masa baki tace "Ni Yaya ka daina kallo na da idan ka tsoro yake bani."

Bai motsa daga yadda yake ba amma sai taga yaja Idanun sa luuuuu ya rufe su ruf, Husna ta saki Murmushi tsce "yaya Bahari ma yana da kirki saida ya zo ya duba ni kuma har kuɗi ya bani, amma Baba Lirwanu ya kwace kuɗin Ramma tana ta roƙon shi ya bari ta raka ni asibiti dashi amma ya hana ta." 
Husna ta faɗa tana tuno abinda yayi mata ranar sai Idanun ta suka cika da hawaye kukan baƙin cikin da take ta dannewa tun randa abun ya faru taji ya taso mata lokaci ɗaya, tayi ƙoƙarin danne kukan amma saita kasa dan tsawan kwanakin nan tayi sune cikin kuncin zuciya da rashin daɗin rai muryar ta na rawa tace "Mamana tace min zalunci babu kyau duk wanda ya zalunci wani Allah saiya saka masa, Yayana yace cin kayan daba naka ba haramun ne ka ɗauka Allah baya son haka, amma shi Baba Lirwanu ya zalince ni kuma banyi masa komai ba." Husna tayi maganar kuka na kwace mata.

Ba zai iya fadin hali ko yanayin da zuciyar sa ke ciki ba amma tabbas ta tashi hankalin sa a gaba ɗaya gangar jiki da zuciyar sa yake jin wani irin mugun tashin hankali da kukan da take yi a gaban sa, ya zai yi ya hanata kukan ne kuma bai sani ba.

Husna kuwa mai makon bayan masallaci da take zuwa tayi kuka da suturun ta yau saita sashi a gaba tana kuka tana faɗin.
"Yaya banyi masa komai ba, haka kawai ya tsane ni kuma haka ya cewa Aramma yanzu shi zan rinƙa yiwa talla a kasuwa, Aramma yace sai dai ya rinƙa biyana ladan talla inba haka ba bazan masa talla ba, shi ne yace ya yarda zaina biyana hakkina amma wallahi yaya nasan ba zai rinƙa bani komai ba, nasan yanzu shike nan  haka zanyi ta masa talla baya bani ladana."

 Ta ɗanyi shiru tana share hawayen Idanun ta da suke ta zubowa sai kuma taci ga da magana.

"Ranar mafa Famfon cikin gari ne ya lalace gashi bani da lafiya inata ciwon kai da zazzaɓi shi yasa na kasa ɗebo ruwa da wuri amma shi ne Baba Lirwanu yayi ta zagina da marina yace wai ni munafuka ce dan karna ɗebo ruwan nace bani da lafiya." Husna na faɗin haka ta sake fashe masa da kuka fiye dana farko, dan abinda Baba Lirwanu tayi mata ranar dama yana danƙare a zuciyar ta inta tuno maganar binsa kasuwa talla sai taji kamar tayi ta kuka.

Yana zaune yana jinta da kallon ta sai kuma yaga tasa hannu tana share hawayen ta tace "babu komai nasan da Mamana da Yayana suna nan da bazan zo nan ba." Sai kuma kukan data tsaida ya dawo sabo.

Ta kife kai s saman cinyar ta tana kuka, yasa Sandar hannun sa ya ɗan daki ƙafar ta kaɗan yadda ba za taji ciwo ba, Husna ta ɗago tana duban sa sai taga idanun sa sunyi wani irin Blue kamar ba na mutane ba, bataji tsoron ganin idanunsa ba, shi kuma saiya cusa hannun sa a cikin tulin sumar kansa yana girgiza mata kai, lamarin daya bawa Husna mugun mamaki ke nan, ta tsaya tana kallon sa, ganin ya zuba mata ido yana juya kai saita saka bakin hijabinta ta share hawayen fuskarta.

Tana kallon sa har yanzu ya ɗan yi baya kaɗan sai kuma ya saka hannu a cikin burgujejen aljihun jallabiyar jikin shi ya ciro wata farar leda mai kyau ya miƙa mata, Husna ta kalle sa ta kalli ledar, sake bata yayi tana kallon fuskar shi ta karbi ledar sai taji da ɗan nauyi.

Tana buɗe wa taga wani Shortbread mai ɗan girba sai wata chaculate babba guda ɗaya da wasu sweet guda biyu Husna ta ɗago tana kallon sa sai kuma a hankali tace "yaya waya baka wannan?" 

Kansa ya ɗauke ya maida gefe, Husna ta cika da mamaki ta kalli cikin ledar ta kalle sa.
"Yaya a ina ka samu wannan?" Wannan karon tana rufe baki taga ya juyo da sauri ya miƙa mata hannun sa alamar ta bashi abun sa, Husna ta kalle sa ta kalli hannun sa me zako-zakon farata daya miƙo mata saita maƙe masa kafaɗa a sakalce tana yin gefe ɗaya da ledar, yadda tayi abun kamar wata yar shekara biyu saiya koma jikin bishiyar ya jingina bayan sa tare da maida hannun sa.

Husna kuwa man kanta da lissafin ta bai faɗa mata komai ba tace  "Yaya bani ka bawa ba?" 
Kallon ta kawai yake amma babu amsa, itama kuma bata tsaya jiran amsar tasa da tasan ba zata samu ba ta buɗe biskit ɗin a gaban shi ta fara ci, shi kuwa saiya ci gaba da ƙare mata kallo har saida taci rabin biskit ɗin sannan yaga ta miƙo masa sauran tana masa murmushi tace "uhm! Yaya yana da daɗi ban taɓa cin irin saba, kaima kaci kaji."

        Ga mamakin ta sai taga ya miƙa mata hannu, ta kalli hannun nashi da yayi wani baƙi baƙin da ya hana a gane asalin kalar fatar jikin shi, sai kuma ta ɗago ta kalle shi, Shortbread ɗin ya nuna mata da hannu tace "Za kaci?" 
Shiru yayi mata yana duban ta, saita miƙa masa amma sai yaƙi karɓa saida tasa a ledar sannan ya karɓa ya fara ci tana kallon shi tana murmushi, duka ya cinye ya mai da mata sweetie ɗin da chaculate ɗin. Abin saiya yi mata daɗi, batayi tunanin komai ba ta ci gaba dayi masa hira zancen nata duk labarin Yayanta da Maman tane sai ƙanin ta da bata sani ba, har lokaci yaja ya miƙe tsaye ta tashi yauma tana gaba yana binta a baya saida yaga shigar ta gida sannan ya juya yabar wajen gaba-daya.

Kwanan Husna huɗu tana jinya ta warke gaba ɗaya ta fara fita kasuwa.

Yau jumma'a Garki za su tun safe Lirwanu ya tafi tare da faɗa mata inda zata same shi a kasuwar Husna duk ranta babu daɗi ta amsa masa.

              Suna cikin motar Naira saiga Bahari ya zo wajen yana tsokanar ta.
"Lallai su Ma'u jiki ya warke har za'a koma filin daga?" Husna ta ɗan harare shi.
"Ɗan sa ido ne fa kai Bahari." Ta faɗa.

Yana tsaye a wajen Motar suna hira har motar ta cika suka tafi.

Ta samu Lirwanu a rumfar daya faɗa mata, harya sari buhun barkono biyu Husna ta aje farantin ta yana daura wa tana jerawa a farantin saida farantin ya cika ta ɗauka ta shiga cikin kasuwa.

Kafin kace meye wannan harta siyar ta sake zuwa ɗiban wani, haka ta rinƙa zuwa tana ɗauka yana ƙare wa har lokacin da suke siyan abincin rana suci yayi, ta faɗa wa Lirwanu ya bata kuɗin abinci sai ya dube ta fuska a haɗe yace "bakinci tuwo ba kan ki taho zaki wani ce na baki kuɗin abinci dan gulma." 

Kawai saita tsaya tana kallon shi dan abun nasa wani lokacin kamar wanda baya tunani da ƙwaƙwalwa.

Naira ashirin ya ɗakko ya bata yana mita.
"Gashi nan saiki siya abincin."
Husna ta kalli kuɗin ta kalle shi, kawai saita dauki Barkonon tayi gaba tana share hawayen daya cika mata ido. 

Yunwa take ji tun ɗazu dan lokacin da zuke zuwa cin abinci har ya wuce, ganin bai ce mata ga kuɗin abincin rana ba yasa ta tambaye shi ashe ma tambayar tata bata da amfani.

Haka ta wuni a kasuwar tana masa talla babu abinda taci, ta riga duka sauran abokan tafiyar ta gama saida barkonon ta. 

Lokacin da ta dawo daga sahun ƙarshe Lirwanu ya nade buhhunan shi ya daure Husna na tsaye tana kallon shi saida ya gama haɗa ya nashi ya nashi sannan ya ciro ɗari biyu ya miƙa mata.
Gashi ki tafi gida ni sai anjima zan taho."

Husna tabi hannun shi da ɗari biyun da kallo.
"Bazaki karɓa bane na maida kuɗi na?" Ya faɗa a tsawace, ta karɓi kuɗin kuka na taho mata ta juya ta bar wajen tana share hawayen baƙin ciki.

"Dama nasan Baba Lirwanu bazai bani kuɗin talla ta ba." Ta fada a sarari tana goge fuskar ta.

Suna tafe a motar Naira ana shewa kamar yadda aka saba amma wannan karon banda Husna dan har suka iso gida ta tafasa bata ce ba, Indo ma gajiya tayi dayi mata magana ta kyale ta
.
Suna sauka a motar tayi gida a wahalce ta shigo gidan ga gajiya ga yunwa, Ramma ta rinƙa jera mata sannu cikin tausaya wa.

Sauran kwaɗon ranbon da Ramma tayi da rana ta bata taci tasha ruwa ta kwanta a tsakar ɗaki tana maida numfashi.

Ganin Husna rai a ɓace ga ta shigo da yunwa yasa Ramma bata tambaye ta komai ba dan dama tasan talla tsakanin Lirwanu da Ma'u baza a wanye lafiya ba.

Yauma a dandali Indo na tafiya zance ya zo wajen ya zauna Husna tayi ta masa hira kamar yadda ta saba.

Washegari Asabar suka tashi da baƙin Turawa a garin ƙofar mai gari ta ɗinke da mutane, dama tun da motar su ta shigo garin mutane suke kus kus ɗin baƙin waye.

Kowa da abinda zai faɗa akan baƙin wasu suce daga gidan governoty suke wasu suce a'a ba haka bane.

Husna na gida Indo tazo tana haki tace "Ma'u Ma'u zo muje kinsan me yake faruwa?"
"A'a wani abun ne?" Husna ta faɗa tana duban Indo.
"Ai yau baƙin Turawa ne a gari suna ƙofar mai gari zo muje ki gansu farare tas gashin su wani iri." 
Indo tayi maganar tana jan hannun Husna da farko kin zuwa tayi dan bata son zuwa abubuwa irin wannan, a garin zai yi wahala ka ganta a wajen kallon abu Irin wannan, saida Ramma tasa baki sannan tabi Indo suka tafi kofar mai gari.

          Ƙofar Mai gari ta cika jama'a suna jiran suji me yake tafe da baƙin Turawa saidai kaf garin an rasa wanda zai shiga tsakani suyi magana da Mai gari, dan su basa jin Hausa shi kuma Mai gari babu turanci, Sunday aka tafi kira yayi musu bayanin abinda turawan ke faɗa sai aka yi rashin sa'a baya nan ya tafi Kano siyan kaya, matar shi kuma babu Hausa, acikin manyan wajen wani yace a kira headmaster.
"Ai yau Asabar baya zuwa." Mutane suka faɗa, anata tunanin yadda za'ayi Bahari ya matsa kusa da Mai gari yace "ranka ya daɗe ko za'a kira Ma'u tunda ita tana jin turanci saita fassara mana abinda suke faɗa." 
"A'a Ma'u dai Jikar Aramma Abdussalamu?" Mai gari ya faɗa da mamaki, Bahari ya ɗaga masa kai.

Indo da Husna na daga can gefe suna kallon mutane su basu san wainar da ake toyawa ba saida Aramma ya zo shiga wajen da ɗan aiken Mai Gari sannan ya gansu.

              "To Aramma kaji dalilin da yasa muka aika kiran ka." Aramma yayi shiru yana tunani bayan ya gama jin bayanin Mai Gari, sai kuma ya numfasa yace "to ranka ya daɗe Allah yasa ita ta gane me suke faɗa ɗin tunda ance basa gane irin turancin da Samarin mu ke musu suma basa gane nasu."
"Aramma ai su nasu a Lagos suka koyo sa ba lallai su gane ba tunda broken ne." 
Bahari ya faɗa yana tsaye kusa da Aramma.
"To shi turancin har kala kala ne ke nan, Allah mai iko, to Allah yasa ta gane ɗin, bari a kira ta na gansu nan baya kaɗan ita da Indo." Aramma ya faɗa zai miƙe Bahari ya juya yana faɗin.
"Bari na kirata."

Su Husna na tsaye Bahari ya zo yace taje inji Aramma yana cikin rumfar Mai Gari.
"Lafiya ko?"  ta tambaye shi, saida Bahari yayi murmushi sannan yace "ƙarar ki nakaiwa Mai gari zo muje suna jiran ki." 

Husna da Indo suka biyo bayan shi, ta ɗaya bangaren da babu cukowar mutane Bahari yabi dasu ata nan kuma Husna taga Mahaukacin yayan ta zaune a kan ice yana kallon su zata je wajen shi Bahari yace "Aramma na jiranki fa." 
Saita fasa zuwa ta bishi suka shiga cikin rumfar shi kuma Bahari ya tsaya daga bayan su kaɗan ita kuma ta ƙarasa wajen Aramma.

Aramma yayi mata bayanin abinda zatayi, Husna ta ɗanyi shiru kamar baza tayi magana ba sai kuma ta ɗaga kai.

Mai gari jikin shi har rawa yake ya nuna mata Turawa guda biyu sunsha ƙananan kaya idanun su sanye da farin eyeglasses.

Cikin harshen Ingilishi a nutse ta fara gaishe su, suka amsa suna jin dadin an samu me musu magana.

Mutane suka zuba musu ido musamman Husna dake faɗin duk abinda suka faɗa da Hausa, tna faɗar abinda suka ce wani ɗan kanzagi daga bakin rumfar Mai Gari yana maimaita wa mutanen dake waje.

            "Munzo ne daga Cikin Kano mu ƙungiyace mai zaman kanta NGOs wacce take bi garuruwan Nigeria daban daban tana duba inda suke da matsalar ruwan sha sai mu samar musu da famfunan zamani wanda za su rinƙa amfani da hasken rana ba tare da sun biyamu ko sisi ba, wannan aikin namu muna yinshi ne sadaƙatul jariya, idan mutanen wannan gari sun amince zamu fara yi musu aikin samar musu da ruwa a cikin wannan gari gobe."

Baturan nan suka jero wa Husna bayanan su daki daki, tun daga ganin yadda fuskar ta ke murmushi jikin mutanen wurin ya fara rawa baya Mai Gari daya matsu su gama bayanin ta faɗa musu me suka ce.

"Sunce su wata kungiyace daga Kano......" 

Tirayan tiryan Husna tayi musu bayanin abida suka faɗa mai shela daga waje yana maimaita wa, Husna tana bayanin mutane suka kaure da iface ifacen murna da sowa, Bahari kuwa yana daga gefe yana Murmushi harda yiwa Husna jinjina, Dan Hajja kuma yana ta can waje cikin abokai yana fasa kai da sake maimata musu Ma'u tashi ce.

Saida Mai Gari ya tsawatar wa mutane sannan wajen yayi shiru Husna ta ƙarasa faɗa musu abinda suka faɗa.

            Nan da nan Mai Gari da sauran manyan Garin suka ce sun amince tare da godiya.
Husna ta faɗa wa Turawan abinda Mai Gari da mutanen sa suka ce. Su kayi murmushin jin daɗi.

Bata ƙara ko minti ɗaya a wajen ba ta fice Bahari na binta a baya, Aramma kuwa farin ciki ya cika masa zuciya, mutanen gari sai murna ake ana mai da yadda aka yi da faɗin duk garin Ma'u ce tayi magana da Turawa.

             Lokacin da suka fito daga rumfar Mai gari Husna ta duba inda tabar yayan ta zaune ɗazu sai taga baya wajen ya tashi.

Bahari ya ce "ai daga yau Ma'u na canja miki suna zuwa Baturiya, ashe haka kika iya Ingilishi?" Ya faɗa yana riƙe baki, Husna ta harare shi suka tafi gida dan turawan har sun fito sun tafi akan sai gobe kuma in sun zo fara aikin.

Mutane ma duk sun watse sai manyan gari a cikin rumfar Mai Gari suna sake maida zance.

              Aramma na dawowa gida yasa aka kira masa Husna tana zuwa ya bata wani rubutu da garin magani a ƙwarya yace "Maza shanye Asma'ullahi maganin baki ne, yau kin ɗakko magana a garin nan ko ina ka gifta sunanki kaiwa ake kira."