30
by @aishatouuu
_Aishatou_
***
_________________
_Washegari_
Turawan nan suka dawo tare da ma'aikatan su, nan da nan suka fara aiki gadan gadan babu kama hannun Yaro.
Yayin da wannan abu daya faru a garin ya sake mai da Husna wata selebirity a garin, Dan Hajja kuma ya sake haukacewa akan ta ko ina ya zauna zancen ta yake yi kamar taɓaɓɓe.
Ta ɓangaren masu aikin ruwa kuwa cikin yan abinda baifi kwanaki ba aikin yayi nisa na ban mamaki dan aiki suke babu dare babu rana.
Ta ɓari ɗaya kuma Husna taci gaba da rayuwar ta kamar yadda ta saba.
Yau tana aje abincin siyarwar ta a tasha Headmaster yazo yace ta kawo masa, ƙuru-ƙuru tace masa "bana siyarwa bane."
Abun ya bashi mamaki dan yana gani ta rinƙa siyarwa wa mutane, Indo kuwa da tasan kwanan zance sai dariya take ganin headmaster ya tsaya yana kallon Husna cikin mamaki.
Chioma ce ta ce Husna ta kai mata farar doya, tana dawowa daga wajen ta taga headmaster yana korar Mahaukacin yayanta kamar zai dake sa harda zagi, abunda yayi masa ya matuƙar ƙonawa Husna rai har saida tace "Wai kai me yayi maka ne ka tsane shi? Naga dai baya shiga harkar kowa, amma duk kabi ka takura masa."
Headmaster ya tsaya yana kallon yadda Husna ta haɗe rai tana masa magana kamar wani sa'an ta.
"Ke baki da kunya ko? Ni kikewa magana haka?"
"Kai kuma baka fahimci me asalin kalmar humanity take nufi ba shi yasa kake korar mutum kamar dabba."
Husna ta faɗa da tsiwa, sai kuma ta juya inda ya koma ya raɓe yana kallon yadda take zuba masifa tace
"Yaya muje ka koma can ka zauna karka sake zuwa kusa da shi kaji? wannan bashi da tausayi."
Headmaster ya dube ta sai kuma ya kalli mutanen wajen da suke masa dariyar abinda Husna tayi masa, yace "is he her brother?"
Ganin kowa yayi masa banza sai ya dafe kai yace "Oh ashe fa baku gane me nace ba. Nace shi ɗin yayan tane da gaske?"
Garba ya zubawa ƙeyar Headmaster harara dan dama haushin sa suke ji tunda aka kawo shi garin ya fiya iyayi da kallon mutane a banza.
"A'a Baban tane." Garba ya faɗa yana barin wajen, aka bar Headmaster da budaddan baki.
Saida Husna taga yayi wajen Masallaci sannan ta koma kan abincin ta, tana Sallamar mutanen dake kanta ta siyo ruwa ta zuba abincin shi a leda ta tafi takai masa.
A bayan rumfar Bahari ta ganshi zaune yana kallon kamar sa da jini ke zuba.
Husna nayin ido biyu da kamar ta ƙaraso wajen da sauri ta aje kayan hannun ta a kasa a rude ta fara tambayar sa meya samu kafar shi.
"Yaya maika taka?" Ta sake tambayar sa Idanun ta harya tara hawaye, ta kai hannu zata taɓa kafar ya janye da sauri, jinin dake zuba ne ma yafi bawa Husna tsoro ganin ya hanata taɓa kafar saita miƙe da sauri ta tafi wajen Bahari.
"Bahari dan Allah zoka gani Yaya ne ya taka wani abu jini nata zuba a ƙafar sa." Hawayen daya cika mata ido ya ƙarasa zubowa.
Da sauri Bahari ya biyo bayan ta har zuwa inda yake zaune har yanzu a yadda ta barshi a haka yake.
"Subhanallahi meya taka haka? kai." Bahari ya faɗa yana duban kafar Husna tace "Dan Allah Bahari me za'a saka jinin ya daina zuba?"
Husna ta yi wa Bahari tambayar yadda kasan tana tambayar likita, Bahari yayi shiru yana tunanin sai kuma ya dube ta yace "Yawwa ki kira matar Sunday ta duba masa kafar mana ba kince likita bace?"
Da sauri ta ɗaga masa kai, yace "to jeki kirata saita duba masa wajen."
Husna ta amasa da "to."
Tana juyawa da sauri zata bar wajen sai kuma ta tsaya tace "Bahari dan Allah ka tsaya a wajen shi babu abinda zai yima yanzu zan kirata na dawo." Bahari yace "Naji jeki kina sake ɓata lokaci." Ta tafi harda gudun ta.
Duk wannan maganar da suke yi yana zaune yana jinsu amma ko motsawa daga inda yake baiyi ba har Husna ta dawo tare da Chioma, sai kuma fur yaƙi bari Chioma ta taɓa masa kafar saida Husna ta tsugunna a gaban shi tana kuka tace "Yaya nasan kana jina dan Allah Yaya ka bari ta dubama ciwon kaji?"
Ya ɗauke kanshi gefe yana jawo sandar sa zai tashi ta riƙe masa hannu abinda bai taɓa zato ko tsammani ba ke nan, Bahari ya ware ido yana kallon gefe da gefan su dan kar wani ya gani. Husna kuwa ko a jikin ta ita harga Allah da zuciya ɗaya take masa magana.
"Dan Allah fa nace Yaya?" ta faɗa tana sake sakin kuka kawai saiya koma ya zauna yana sunkuyar da kanshi ƙasa, Bahari daya mutu a tsaye da mamakin Husna sai ya jinjina kai, Chioma ta matso kusa da kafar ta fara dubawa.
Husna na tsaye tana kallo Chioma tasa wani ƙaramin almakashi ta fara ƙoƙarin yanke jikin baƙin abunda ya rufe masa ƙafa saida ta yanke gefan abun inda jinin yafi zuba sannan ta saka auduga ta fara rage jinin kanta fara wanke masa wajen, Husna ta rintse ido da sauri sanda taga Chioma ta zuba masa haidirojin akan ciwon.
A hankali Chioma take wanke masa wajen ciwon har sai da ciwon ya daina jini, a tare Husna da Bahari suka kalli inda ciwon yake yanka ne mai ɗan girma ata gefan tafin kafar shi yankan ya danyi zurfi, Husna tabi gefan kafar shi da kallo ta wajen da Chioma ta yanke baƙin abun duk da iya wajen ciwon ne babu baƙin abun da Husna ta kira sa da safa amma tana iya ganin wata farar fata sosai kwance a wajen da bakaken gashi a saman ta sai dai ba sosai kake iya gani ba saika saka wa wajen ciwon ido sosai.
"Gaskiya sai an ɗin ke wajen nan, sannan dole ayi masa Allurar Totonos dan kamar da ƙarfe ya yanke." Chioma ta faɗa ba tare kuma data jira cewar Husna da Bahari ba ta juya da sauri tana faɗin "ina zuwa."
"Sannu Yaya."
Husna ta faɗa tana zaman dirshan a kusa da shi ita ko tsoro ma bata ji.
Bahari ya kalli Husna ya girgiza kai a ƙasan zuciyar shi kuwa saiya saki Murmushi, Chioma bata jima ba sai gata ta dawo da sauri riƙe da wata yar jaka baƙa, a kusa dashi ta tsuguna ta fito da wata allura a cikin jakar yadda kasan wacce ta shirya wa samuwar ciwon ko zuwan wannan ranar haka take haɗa komai daki daki, saida ta gama haɗa ruwan Allurar Husna da Bahari na kallon ta.
"Please someone should help me to do this." Chioma ta faɗi maganar tana duban su, sai Husna ta kalli Bahari fuskar ta gwanin ban tausayi tace "Bahari dan Allah ka taimaka mata tayi masa Allurar." Ido ya zare yana kallon ta ita kuma saita karyar dakai gefe guda tana duban Bahari cikin roko tace "Please babu abinda zaima." Sai kuma ta juya wajen shi tace "Yaya Bahari zai taimaka wa Chioma tama allura kaji?" Bata jira amsawar shiba dan tasan ba amsar zaiyi ba.
Bahari da kana ganin shi kaga wanda yake a tsorace sai ya matso kusa dashi ya riƙe masa hannu Chioma ta daidaita inda zata yi masa Allurar ta tsira masa Allurar ta saman kayan shi.
Har tasa allurar ta cire bai motsa daga yadda yake zaune ba sai Idanun sa daya sake rufewa, Bahari ya fara jinjiga masa hannun a hankali dan kar allurar ta kume masa, Husna kuwa sai sannu take jera masa.
Bahari ne dai ya sake riƙe kafar shi ya ɗora ta akan cinyarsa Chioma ta fara ɗinke masa yankan, Husna na ganin an fara ɗinkin ta rufe idanun ta da sauri saboda tsoratan da tayi bata san sanda ta riƙe ɗaya hannun sa ba.
Kukan tausayin shi take mara sauti sai hawaye kawai ke bin fuskar ta, cikin kankanin lokaci Chioma ta gama ɗinki ta maida komai cikin jakar ta zuge zip ɗin.
"Malama Ma'u Saiki sakar masa hannu an gama ɗinki mai ɗan uwa." Bahari ya faɗa yana miƙewa tsaye yana karkade jikin sa, kamar ya san me Husna take shirin yi kuma sai ya cewa Chioma.
"Nawa ne kuɗin aikin ki?"
Chioma ta gane me yake nufi dan haka sai tace "Three thousand Naira."
Bahari yasa hannu a aljihu ya fito da kuɗi ya irga ya bata ta kudin ta, Chioma ta karɓa tana masa godiya ta tafi.
"Nagode Bahari in sha Allahu zan kawo ma kuɗin ka kaji."
Husna ta faɗa tana duban shi, sai yayi murmushi sannan yace mata
"Ma'u ai bake kaɗai kike neman ladan ba nima sadaka nayi masa karki damu." Ta buɗe baki tana kallon shi ya sake tabbatar mata da kyauta ya biya masa.
"Mun gode sosai Bahari."
Husna tayi ta jera masa godiya kamar zata ari baki, Bahari wajen ya bari yana mata murmushi.
Sai ta juyo zata yi masa magana taga ya tashi tsaye "sannu Yaya." Ta sake faɗa, shi kuwa bai kalli inda take ba ya fara dogara Sandar shi yana barin wajen.
A hankali yake tafiya da gefan kafar sa Husna na tsaye tana kallon shi yana bin gefan titi yana tafiya har saida ta dena ganin shi da kyau sannan ta koma wajen kayan ta.
Taje ta samu Indo harta siyar mata da sauran doyar tayi mata godiya ta ɗauki kwanunkan ta jikin ta a sanyaye ta tafi gida.
Wunin ranar a haka ta ƙarasa shi tana tunanin koya yake yanzu, har dare jikin ta a sanyaye, rashin zuwan shi Dandali kuma saiya sake saka jikin Husna yin sanyi.
Da safe Husna ta fita duba shi a tasha bata ganshi ba har yamma babu shi banu dalilin sa, nan fa hankalin ta ya fara tashi yanayin damuwa ya shige ta, komai yinsa kawai take babu kwarin jiki har dare yayi ta tafi dandali da wuri tana addu'ar Allah yasa yau yazo, amma sai addu'ar ta bata karɓu ba dan yauma dai irin jiya ne wato bai zo Dandalin ba, nan fa ta rasa inda zata saka ranta.
Kwanan shi biyu Husna bata ganshi ba sai ana ukun da daddare tana zaune a Dandali ta haɗa kai da gwiwa tare da zabga abun tagumi ta faɗa duniya tunanin inda yayanta ya shiga tsawan kwanakin nan, abun duniya duk ya ishe ta, tana cikin tunanin kamar daga sama taji an zunguri kafar ta, a ɗan tsorace ta motsa sai kuma ta ganshi tsaye a kanta yana duban ta sosai yau ma idanun sa a waje, da sauri ta mike tsaye tana faɗin "Yaya inaka shiga? Ya ciwon kafar ka? Ya warke? cikin murnar ganin sa take maganar tana ƙare masa kallo, "Har yanzu wajen yana ma zafi?" ta jero masa tambayoyin dake cinta.
Yau shiya Zauna a gaban ta yana fuskantar ta saidai kamar yadda ta sani baice mata komai ba sai binta daya rinƙa yi da kallo.
"Yaya kafan ya dena maka ciwo?"
Ta sake jefa masa tambayar kamar zata saka masa kuka. Bai ce mata komai ba sai taga ya miƙe Kafafun shi daya nade, wacce yaji ciwon ya miƙe Husna ta kalli wajen sai taga ciwon ya warke sai ɗan abida baza'a rasa ba, tana sakar masa murmushi tace
"Yaya naji daɗi ciwon ka ya kusa wake wa."
Idanunsa ya ja ya rufe ya mai da duban shi ƙasa, ita kuma ta fara zuba masa surutu da bashi labarin neman shi data rinƙa yi tsawon kwanakin nan. Tana masa surutun yana jinta wani abun kuma inta faɗa saiya ɗago kai ya kalle ta.
_Bayan sati uku_
Rayuwa tayi wa Husna babu yabo babu fallasa musamman yanzun da bata zuwa ɗiban ruwa dan an daɗe da gama aikin ruwan garin ga famfuna nan tako ina a layi kan gari lungu da saƙo, ruwa ya wadaci ko ina, ga ruwan mai kyau da daɗi.
Gidan su Husna yana ɗaya daga cikin gidajen da akaja musu ruwa har cikin gida.
Rana nayi ruwan zai fara zuba ba zai ɗauke ba har Magarba. Wannan sauƙi ne babba a wajen Husna da ire-iren ta, randa ruwan ya fara zuwa kuwa murnar ta kin ɓoyuwa tayi, tana zuwa dandali ta saka Yayanta a gaba tana bashi Labarin ruwan da aka kai musu gida da irin daɗin da taji.
Yadda yake mata dai har yanzu haka ne babu wani canji komai tace masa babu amsa sai dai ya jita kawai.
Yau Litinin beguwa ke ci Husna dawowar ta ke nan ta shigo gidan hannunta riƙe da farantin tallar ta, yauma ranta a ɓace yake dan tunda ta fara yiwa Baba Lirwanu talla duk ranar kasuwa da ɓacin rai take dawowa gida.
Ramma tayi mata sannu ta amsa tana wucewa ciki, saida tayi wanka ta canja zanin jikin ta da doguwar riga baƙa, ta sallar bara ce da Baban ta ya kawo mata farin hijabin ta mara girma ta saka mai kawai ta shafa tasa kwalli ta fito.
A ƙasan inuwa ta sake samun matan gidan tana zama Iro ya fito daga lungun Dije yace "Ma'u kije inji Dije."
"To me kuma ya faru?" Husna ta faɗa a ranta dan tasan Dije bata kiran Alkhairi.
Da sallama ta shiga wajen ta samu Dije tare da wata bakuwa, bakuwar ta amsa mata sallamar tana binta da kallon ƙurulla daga sama har ƙasa kamar wacce aka bawa aikin tantance halittar da Allah yayi mata.
Husna ta dubi matar a fuzge a shekaru dai ba zata gaza 50 ba, irin Hajjojin nan ne na Saudiyya tasha doguwar riga ruwan makuba anyi mata ado da yellow zare, ta saka ƙaramin hijabi sai kuma ta rufa mayafin rigar akan hijabin, fuskarta duk zane bakin ta yayi baƙi baƙi, tun daga bakin lungun shigowa wajen Dije kuwa zakaji wani kamshin tulare mai ɗan karfi na tashi a jikin ta, saida matar ta gama ƙarewa Husna kallo sannan tace.
"A'a Hadiza kardai ki cemin wannan ce ma'un ɗan Hajja?" Matar ta faɗa tana sake ƙurawa Husna ido.
Saida Dije tayi dariyar jin daɗi sannan tace "ita ce fa Hajja, ya kika ganta?"
"Marra wannan tayi har fiya da zato na, la la la gaskiya za'a yi mace anan Masha Allah. Gaskiya dole ɗan Hajja yace min shifa sai Ma'u, ashe haka Asma'un tashi takai, ah lallai takai a jirata, gaskiya muna kamu wannan babu wasa kanna koma Makka kawai za'a gama magana Hadiza."
Dije bakin ta yaƙi rufuwa Hajja ta cewa Husna "zo nan mu gaisa mana suruka ta, kai Masha Allah."
Husna ta ɗan tsaya kamar ba zata jeba sai kuma taɗan matsa kusa da ita fuskar ta a cunkushe dan sai yanzu ta gane Maman Dan Hajja ce.
Hajja ta sake kallan kunnen Husna da warwaron hannun ta da tunda ta shigo idanun ta ke kansu kamar tayi shiru sai kuma tace "Ah ƴata wa ya baki wannan abu mai daraja haka? Lallai surukar tawa ƴar gata ce." Hajja ta faɗa tana taɓa ɗan kunnen dake kunnan Husna da warwaron hannun ta dan ta sake tabbatar da abinda Idanun ta suke gane maba ba kuskuren idanun ta bane sai tace
"Yata muga wannan ɗan kunnen naki?" Hajja ta sake fada tana kallon Husna.
"Mamana tace karna bari kowa ya cire min." Husna ta bata amsa tana matsa wa daga kusa da matar dan tularen ta harya fara hawa mata kai.
"Eh tana da gaskiya ai ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba data baki su kike yawo dasu a gari ba, irin wannan kadarar ai ɓoye su ake, lallai Maman ki na sonki.
Dije data kasa gane kan zancen Hajja saita dube ta cikin neman ƙarin bayani tace "shi ɗan kunnen har wani abu ne? kin ganta nan tunda uban ya kawo ta nan ya aje shi ne a kunnen ta sallah biki ko suna bata taɓa cire wa ba, haka wannan abun hannun nata na jaraba da bata bari a taɓa shekara uku ke nan yanzu."
"Ai bazata bari a taɓa ba Hadiza ita kanta da tasan me take yawo dashi a hannu ai da tuni ta daɗe ta cire wa ta adana abunta saboda gudun asara."
Husna ta dubi Hajja sai kuma ta ɗauke kai.
"Kai Hajja ɗan kunne ne fa kawai da warwaro sai kace wani kayan gabas."
Saida Hajja tayi dariyar jin maganar Dije sannan tace "to wannan da kike gani a kunnen ta da hannun ta dukan su gold ne mai daraja ma kuwa, dan yanzu wannan kuɗin da za'a karɓa dasu ba ƙananan kuɗi bane, tsaf kuɗin su zai siya mata kayan ɗaki da ɗan maraƙi (Sa)."
Dije ta zare idanu tana matsowa kusa da Hajja tace "ke Tsahare karki zolaye ni."
Hajja tayi dariya a fili a ranata kuwa sai tace "haba nidai nasan baku san mene wannan ba, ai kuwa ta faɗi gasassa karɓa zanyi na baku wani abu na riƙe su, wannan inna kai Makka ai saina linka kuɗin shi."
A fili kuma sai tace "wallahi rantsuwar ɗan musulmi Hadiza in kuna son siyarwa ma ni akwai wanda zan haɗa ku dashi ku karɓi yan kudaden ku, yarinya kema a siya miki wani abu mai amfani da kuɗin har a samu canji."
Ai jikin Dije saiya fara rawa taji kuɗi faɗi take "kai Hajja zuwan ki yafi zuwan Sule Lamiɗo (Governor Jigawa) ai kuwa bari Lirwanu ya shigo muyi magana a nutse zaki jimu gobe duk yadda muka yi dashi."
Husna dai tana tsaye tana jinsu ana haka sai ga Sallamar Lirwanu dawowar shi ke nan daga kasuwa ya shigo lungun Dije.
Nan fa Hajja ta sake zuzuta musu abinda za'a samu in aka saida ɗan kunnen Husna da awarwaron ta.
Ai Lirwanu sai yafi Dije rudewa babu abinda yake hasasowa sai ruwan kuɗin da Hajja ta kira musu, a zabure ya dubi Husna yace "Ke zo nan a cire su tun yanzu kar a samu matsala kan goben, Hajja ki tambayi me saiyan kawai." Lirwanu yayi maganar yana kallon Husna data tashi zata bar wajen.
"Dan ubanki ba magana nake miki ba kike tafiya kamar baki jini ba." Ya faɗa a zafafe yana yowa kanta ta kwasa da gudu ta fice daga lungu Dije, ya yunƙura zai rufa mata baya Dije tace "kai dawo nan ka rabu da ita karka bita, ai a gidan zata kwana da daddare sai ka karɓo mana inta kwanta, shegiyar yarinya ƙarama sai mugunta."
Lirwanu ya fasa bin bayan Husna Hajja kuma taci gaba da zuga Dije cikin dabara da iya bariki.
Husna na barin lungun Dije kuwa ta fice daga gidan ta tafi gidan su Indo tana tafe tana tuna huɗubar da Mamanta tayi mata akan ɗan kunnen.
"Husnah karki bari wannan ma a cire miki kinji Mamana? Duk wanda yace kizo ya gani karki je, kuma koda wasa karki sake naga kin cire sa inba haka ba babu ruwana dake, haka zan bar miki kunnen ki yayi ta kuraje babu ɗan kunne tunda kinga duk wanda aka saka miki kunnen ki baya so, kina jina ko?" Maman ta ta faɗa mata tana sake maimaita mata kashe din.
Awarwaron hannun ta kuwa randa ta fara ganin sa a wajen Mamanta har kuka tayi akan saita bata tasa amma sai ta hanata tace "haba Husnan Babanta kiyi hakuri yanzu yayi miki yawa saikin sake girma saina baki kisa daman ai naki ne, kinji." Da haka tayi mata wayo ta ɓoye shi daga ranar kuma bata sake ganin saba sai randa Mariya ta buɗe zif ɗin ƙasan akwatin ta.
"Yanzu ya zan yi dasu kar Dije da Baba Lirwanu su kwace min?" Husna ta yiwa kanta tamabayar a fili.
Wata zuciyar tace "ki bawa Indo ta ɓoye miki a ɗakin Ladi."
Sai kuma ta girgiza kai tana jin hakan ma bai yi mata ba.
"To ya zatayi dasu?"
_nima A'isha ina daga gefe nace fans kuna ganin a ina Husna zata ɓoye su tsira?_