31
by @aishatouuu
_Aishatou_
***
_________________
Tun da Husna ta fita daga gidan bata dawo ba suna tare da Indo a gidan su har aka yi sallar isha'i suka ci tuwon dare suka tafi Dandali daga can kuma har zuwa lokacin bata gama yankewa kanta matsaya akan ta bawa indo ajiya ba ko a'a.
Suna zuwa Dandalin saurayin Indo ya zo ta tafi zance wannan yasa Husna taɗan tsaya cikin ƴan matan kafin daga baya ta bar tsakiyar Dandalin ta tafi inda suke zama.
A zaune ta samu yayan ta yana duban gaban shi, yana ganin ta ya janye ƙafafun sa dake sanye cikin baƙin takalmin soson da ta siya masa tun bayan yankewar da yayi, da taje cin kasuwa ta siyo masa saban takalmin sosai baƙi cikin ikon Allah kuma sai bata samu matsala da shiba sanda ta bashi takalmin dan tana basa ya karɓa sosai kuma hakan yayi mata daɗi, tun daga ranar duk inda zaka ganshi zaka ganshi sanye da takalmin.
A gaban shi Husna ta zauna kamar yadda ta saba tana sakin murmushi tace "Yaya yau ka riga ni zuwa?"
Kamar ko yaushe bata samu amsa ko nuna wata alamar fahimtar abinda tace daga gare shi ba.
Hannu tasa ta tallafe kumatun ta tana kallon shi tana juya shawarar da zuciyar ta ta bata tun ɗazu akan ta bashi ajiyar ɗan kunnen ta da awarwaron ta.
"To amma inna bashi ya yarmin fa? Tunda bashi da lafiya." ta ayyana hakan a ranta.
"Husna in baki bashi bama duk inda kika kai sai Dije da Lirwanu sun bi sun karɓo in kuma kika ɓoye da kanki dole zasu sa ki fito da shi." Wani sashe daga can ƙasan zuciyar ta ya tuna mata.
"Ki bashi kawai ya aje miki in Baban ki yazo saiki karɓo ki basa ya kaiwa Maman ki."
Tunani da hankalin ta ya sake tabbatar mata da tayi hakan kawai "Kuma gwanda ma ki bashi ajiyar kinga a wajen sa babu wanda zai yi tunanin kin bashi bare Baba Lirwanu ko Dije suje su karɓe miki."
Husna tayi nisa sosai a cikin tunanin, shi kuma tun yana kallon ta ta kasan idanun shi harya ɗago kai ya zuba mata ido kai tsaye yana ƙare mata kallo amma bata sani ba saboda nisan da tayi cikin tunani, gashi dai Idanun ta akan shi suke amma bashi ɗin take kallo ba.
Da Sandar shi ya ɗan bugi ƙafafun ta yadda baza taji ciwo ba. Firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data shiga sai kuma tace "Yaya dan Allah na baka ajiya zaka ɓoye min?"
Tayi masa tambayar tana tsare shi da manyan idanun ta akan fuskar shi dake cike da suma.
A fuzge ya kalle ta sai kuma ya dauke kanshi gefe ƙwaƙwalwar shi ke san gane abinda take nufi, sai kuma yaji ta sake cewa.
"Yaya dan Allah ka ajiye min a wajen ka kaga in na ɓoye da kaina Dije da Baba Lirwanu zasu ɗauke min, in kuma nace zan bawa Indo ta taya ni ɓoye wa a nan ma sai Dije ko Baba Lirwanu sunje sun karɓa, dama bazan bawa Ramma ajiya ba dan ita kona aje a ɗakin ta Baba Lirwanu yana tambayar ta zata bashi, hmmm ita mafa tsoron shi take ji."
Husna ta jero masa maganganun cikin rashin wayo da sakalcin da wahalar rayuwa ke sawa ta manta data iya yin ta, sai a irin wannan lokutan in suna tare da shi take jinta kamar a gaban Mamanta sannan take tunawa da wannan yanayin nata na kuruciya da bata sanin sanda take sauke masa su in suna zaune.
Yanzu kallon ta yake kai tsaye amma bai motsa daga yadda yake ba.
"Yaya zaka aje m.....?"
Kanta ƙarasa maganar taga ya miƙa mata hannun shi a buɗe alamar ta bashi koma meye, ganin ya miƙo mata hannu saita saki Murmushin jin daɗi.
Ga mamakin sa sai yaga ta fara ƙoƙarin cire ɗan kunnen ta amma sai yaƙi fita ta daɗin rai saboda matse shi da Mama tayi sosai, tanayi tana yarfe hannun ta daya ƙage harta samu ta cire ƴan kunnayen ta ɗora masa akan tafin hannunsa dake buɗe, zaman ɗan kwalinta ta gyara sannan ta ciro awarwaron hannun ta guda biyu masu kauri ta sake zubawa a tafin hannun shi tana sakin murmushi tace "Yaya ka ɓoye min su kaji, Mamana ce ta samin ɗan kunnen tace karna bari kowa ya cire min, su kuma awarwaron nawa ne ta ɓoye min tace saina sake girma sai ta bani, da Baba ya kawo ni nan randa Mariya ta ɗebe min kayana na gansu a cikin akwatina shi ne na ɓoye sai yanzu nake sawa, shi ne fa ɗazu wannan Maman Ɗan Hajjan tazo gidan mu take faɗa wa Dije wai in an siyar dasu za'a samu kuɗi har ɗan maraƙi ma za'a iya siya da kuɗin, shine Baba Lirwanu zai karɓe min ni kuma na gudu gidan su Indo tun da yamma, ai dai zaka ɓoye min ko?" Husna ta faɗa fuskar ta na canjawa.
Tsam yayi yana ƙare mata kallo irin kallon da tun randa ta siya masa takalmi bai sake yi mata irin shiba, duban ta yake da duka ƙwayar Idanun sa.
Maganar tace ta katse masa tunanin da ƙwaƙwalwar shi tayi nisa cikin yin sa.
"Yaya zaka ɓoye min ko?" Shi kanshi bai san sanda ya rufe tafin hannunsa data zuba ɗan kunnen da awarwaron aciki ba, tana kallon shi ya zuba su acikin aljihun jallabiyar jikin shi. Hakan yasa Husna sakin dariya mara sauti...
Suna haka sai ga Indo tazo wajen daga baya ta tsaya tana duban Husna tace "Ma'u zo kiji."
Husna ta kalli inda Indo ta tsaya ɗan nesa dasu kaɗan, ita ta rasa me yasa Indo take tsoron yayan ta bayan bai taɓa yiwa kowa komai ba, haka kullum cikin yi mata mitar ta daina kula shi take karyayi mata illa wata rana.
"Ma'u wallahi baki da wayo kiyi ta shigewa Mahaukaci har kina kiran shi da yayan ki." Ire-iren maganganun Indo ke nan a duk lokacin da tazo ta same su tare.
Husna ta miƙe tsaye tana kade jikin ta sai kuma ta dube shi tace "Yaya ina zuwa."
Tana zuwa Indo taja hannun ta suka yi wajen bishiyoyin dake gaban Dandali kaɗan Husna na tambayar ta ina zasu? bata ba ta amsa ba saida ta kaita har wajen mai kiran tana.
Husna ta kalli mutumin da dake kiranta tsaye a jikin mashin ɗayan kuma da bata gane waye ba yana tsaye a gefan shi.
"Dama na cema yanzu zan nemo maka ita." Indo ta faɗa tana dariya, mutumin da yaɗan manyan ta kaɗan yayi dariya yana mata jinjina yace "gaskiya ne kin cika alkawarin ki saura nawa." Ya faɗa yana zura hannu a cikin aljihun sa ya ciro ɗari biyar sabuwa ya miƙawa Indo, ita kuwa tasa hannu ta karɓa tana godiya.
"Haba ai kin fi haka yau tunda kika kawo min ƙawar ki." Ya faɗa yana duban Husna data ɗauke kai gefe yace "Gimbiya ta Ma'u sannu da zuwa, kawai sai kika ganmu a garin ku ko? Ai Indo yau ta biya ni data faɗa min garin ku, tun ɗazu muka shigo munata neman ki bamu ganki ba saida nagan ta ta nemo min ke."
Mutumin ya jero zancen ko haɗiyar yawu babu yana magana yana bin ta da kallo kamar maye bakin shi yaƙi rufuwa.
Husna ta kalli mutumin ta watsar kamar bata sanshi ba sai kuma ta dubi Indo da suke magana da ɗaya mutumin suna dariya.
A ranta take faɗin za su haɗu da Indo sai tayi mata rashin mutunci, dama wannan mayan mutumin ne ya zo shi ne jikin ta ke rawa saboda kwaɗayi.
Ɗan Union kamar yadda Husna tasa masa sunan ya daɗe yana cewa yana sonta amma bata taɓa sauraren shi ba, mutumin ɗan Union ne a Kasuwar Litinin beguwa a ƙasan Mainar da suke zuwa cin abincin rana yake, wajen akwai masu saida abinci kala kala..... tunda suka fara zuwa wajen yake bin Husna taƙi kula shi dan ya fiya kallon jaraba gashi da suturu, duk sanda suka je sai dai su karaci maganar su shida Indo ya siya mata abinci ya bata kuɗi, Husna kuwa koya siya mata bata ci haka bata karɓar kuɗin sa, ɗazu a kasuwa tana kallon shi da Indo suna zance ashe garin su ta kwanta ta masa.
"Haba gimbiya ta baza a yimin magana ba?" Ya faɗa, Husna ta kalli Indo da suka bar wajen ita da ɗayan mutumin ta juya zata tafi yasha gaban ta yana faɗin.
"Haba Asma'u ai kya tsaya mu gaisa mana uhm? Kinsan fa ina sonki, kinga tsaya muyi magana duk abinda kike so shi za ayi haba mana ke sai kace ba wayayyiya ba." Yayi maganar yana wani kallon ta ƙasa ƙasa.
Husna kuwa ganin ya hana ta wucewa saita koma jikin bishiyar ta tsaya ta ɗauke kanta gefe.
"Yawwa ko ke fa, yanzu dai ya gida?" Ya faɗa yana matsowa kusa da ita.
"Nifa bana zance ka matsamin na tafi gida." ta faɗa muryar ta na ɗan rawar rashin sabo.
Kallon ta yayi da kyau yaga rashin wayo ƙarara a tare da ita sai yayi murmushi a ranshi yake faɗin "af ashe ma bata da wayo baza tayi wahalar jan hankali ba."
A fili kuma sai yayi murmushi yace "Ayya ashe baki taɓa zance ba, ai kuwa zance babu wata matsala ki saki jikin ki yanzu saina koya miki yadda ake yi ko?"
"A'a nidai bana so ban taɓa yiba gida zan tafi."
"A'a ai ba'ayi haka ba Ma'u, nima yanzu zan sallame ki ki tafi gidan amma sai munyi zancen kaɗan sai ki tafi ko?" Ya faɗa yana sake matsawa kusa da ita.
Husna na son ja da baya dan sun yi kusa da yawa sai kuma bishiya ta tokare ta.
"Caraf taji ya riƙo hannun ta yana murza wa yana wani mici mici da ido kamar munafuki yace "kinga wani abu zan nuna miki ki taɓa min shi da hannun ki saina sallame ki ki tafi kinga har kuɗi zan baki da yawa jaka goma zan baki in kika yimin da kyau kinji Ma'u mai kyau."
Husna gaba ɗaya saita tsorata da yanayin shi kamar wata shashasha kuma saita ɗaga masa kai dan ita burin ta kawai ya bata hanya ta tafi.
Shi kuma gaulan ganin tayi haka sai yayi murmushin samun nasara a ranshi yana faɗin "kai ashe ma sakara ce mara wayo na tsaya ina bin kanki, ai da nasan haka kike ba wayo da tun a kasuwa na shafe ki." Ya zayyano zancen a ranshi a fili kuma sai yaci gaba da hillatar Husna har ya fito da jikin shi bata sani ba.
"Kinsan wannan abun."
Ya faɗa yana turo mata shi gaban ta Husna ta girgiza kai tana kallon abun cikin rashin wayo da tsoro tace "wallahi ni ka matsamin na tafi gida.
"To kin gan shi yana motsi ko? To har Ruwan sama yake yi kuma taɓa ma kiji."
.......Tun bayan jan Husna da Indo tayi yake zaune a wajen yana jiran dawowar ta amma sai yaji shiru wajen bishiyoyin da yaga sunyi yabi da kallo wajen ya ɗanyi duhu da yawa duk da akwai farin wata amma ba lallai ka iya ganin wanda ke zaune a kasan bishiyoyin daga nesa ba sai in kazo kusa dasu.
Yana dogara Sandar shi ya biyo ta wajen yana ɗan waiwayen ta inda suke, wani mashin ya gani a kafe a gaban ƙatuwar bishiyar maina harya wuce baiga kowa ba sai kuma yaji kamar magana ƙasa ƙasa, da baya ya dawo yana buɗe idon shi da kyau, can jikin bishiyar ya hango hefan hijabin Husna wani mutum mai kiba mara tsari yana tsaye a gaban ta baya iya ganin fuskar mutumin saboda ya bashi baya, amma yana iya jiyo maganar Husna tana cewa "ka barni ni gida zan tafi Babana ya hanani kula kowa."
Husna kuwa tana fama mutumin ya rabu da ita yaƙi saboda jaraba da rashin tsoron Allah sai kuma tayi shiru tana kallon ɗan Union da abunda yake ta roƙon ta taɓa masa zai bata kuɗi da yawa har wani rufe ido yake yana numfashin jaraba, tsautsayi ne ko ganganci ko kuruciya da rashin wayo yasa Husna ta yanke wa kanta shawarar kawai bari ta taɓa masa abun danya barta ta tafi gida tana miƙa hannun ta zata taɓa dai-dai lokacin kuma ya zagayo ta ɗaya gefan akan idanun shi ta miƙa hannun ta zata taɓa taji an jayowo ta baya da wani mugun ƙarfi.
Kanta tantance waye ya jawota da abunda ke faruwa taji an sauke mata wasu masifaffun marika guda biyu a ciki ƴan sakonnin da basu gaza biyu ba sai kuma ya turata bayan shi ya shaƙi wuyan Dan Union daya tsorata da ganin mahaukaci a gaban su.
Kan ɗan Union ya gama tantance waye har ya buga kanshi da jikin bishiyar a jejjere yake kifa masa marika ta hagu da dama Ɗan Union tsabar azabar marikan da rudewa sai ya kasa ihu, ga wajen babu mutane sosai, ga ihun waƙe da gadar ƴan mata ba lallai aji sautin marikan ba.
Husna kuwa saida ta faɗi a kasa kanta ya juya taga wasu taurarin azaba sun gifta ta gaban Idanun ta, takai wajen minti biyu kanta gama dawowa dai-dai.
"Innalillahi Yaya."
Ta faɗa tana miƙewa tsaye tayi wajen shi ganin ya shaƙe wuyan Ɗan Union a jikin bishiyar idanun sa sun yi wani iri kamar za su juye zaboda azabar shaƙa wandon shi ya zazzago ƙasa ga tsaraicin shi nan a fili.
"Yaya dan Allah ka sake shi karya mutu."
Wannan furucin na Husna shi yasa ya sake sa ya faɗo ƙasa tim bai sake sakon ɗaya a wajen ba yaja hannun Husna da mugun ƙarfi suka bar ɗan Union a wajen riƙe da maƙogwaro yana maida numfashi da ƙyar.
Da wani irin sauri yake jan ta tana masa magana bai tsaya ba, saida ya kawo ta har ƙofar shiga cikin gida sannan ya jefa ta ya juya zai bar wajen ta sake biyo shi tana masa magana ya juyo a wani irin fusacen da bata taɓa gani ba ya ɗaga Sandar hannun sa yayi kamar zai dake ta, ta koma baya da sauri ta shige cikin gida.
Har ya bar wajen babu wanda ya ganshi saboda ta baya ya biyo da ita, da wani irin sauri yake barin cikin garin gaba ɗaya.
Husna kuwa a mugun tsorace ta shige gida tana mai da numfashi, Ramma na mata magana bata tsaya ba tayi ɗakin da take kwana ta shige ta kwanta ta dukun kune jikinta, take kuma ciwon kan daya fara zame mata jiki ya rufe ta, sosai take jin ciwon kan har cikin Idanunta ta.
Dan Union kuwa yana samu ya dawo dai-dai ya ja wandon shi ya ɗaure bai tsaya neman abokin tafiyar saba ya buga mashin ɗin sa da mugun gudu yabar garin a mugun tsorace dan shi kaɗai yasan abunda ya gani....!