33
by @aishatouuu
Ɗaya daga cikin nurses ɗin ta ɗago tana duban Bahari tace "Kai ne Bahari?"
"Eh nine." ya faɗa da sauri.
"Okay gashi ka tafi musu da wannan, sister dan Allah rakashi VIP room 08." Ta faɗa tana miƙa wa Bahari wata leda, wacce zata raka shin kuma ta taso tace "muje"
Bahari saiya zama lost dan ya kasa gane inda zancen nasu ya dosa. Maganar Nurse ɗin ce ta katse masa tunani.
"Muje mana." Ta sake faɗa tana yin gaba, Bahari bashi da option saina yabi bayan ta koma menene ya tambaye su yaji, Aramma ya yiwa magana sukabi Nurse ɗin ta raka su har jerin ɗakunan da aka kira da VIP section.
Wajen yayi kyau kamar ba asibiti ba, babu warin asibiti babu ƙarni haka babu hayanir mutane, ɗakunan ajere suke tsaf dasu ko wanne ɗaki mutum ɗaya ne a ciki sannan a ko wanne ɗaki akwai toilet da ɗan ƙaramin fridge, komai na kayan wutar ɗakin suna aiki kama daga kan AC fan da sauran su.
Har gaban ɗakin nurse ta raka su sannan ta juya, Bahari ya kwankwasa ƙofar daga ciki Ramma tace "a shigo."
Da sallama suka shiga ɗakin Bahari ya nuna wa Aramma wata kujera daga gefan gadon ya zauna shi kuma ya tsaya daga gefe Ramma ta tashi ta koma kan gadon wajen ƙafafun Husna ta zauna tana nuna masa inda ta tashi tace "Ka zauna mana Bahari."
Ya zauna Aramma ya dubi Husna dake kwance ya sake mata sannu tare da tambayar jikin nata kamar bata son yin magana tace "da sauƙi."
"Allah ya ƙara miki lafiya."
Ramma ta amsa da "Amin."
Bahari da tunda suka shigo yake bin ɗakin da kallo sai ya dubi Ramma zai yi mata magana ta riga shi da miƙa masa wata farar paper a naɗe.
"Gashi ance na baka." Bai tsaya tambayar ta wa yace ta bashi ba ya karɓa ya fara buɗe ta saida ya warware linkin da aka yiwa paper sannan ya ɗora idan shi kan rubutun da aka yi a tsakiyar takardar.
_"F*** you."_
Bahari ya cukwikwuye girarsa bayan ya gama karanta rubutun, a ransa yace "How?"
Sai kuma ya fara duba abin da ke cikin ledar da aka bashi a wajen biyan kuɗi abinci ne takeaway guda uku sai chaculate da robar Popcorn.
Kawai saiya girgiza kai ya miƙe da sauri ya bawa Ramma ledar yana faɗin "ga abinci nan Aramma kuci dan Allah bari na duba abu a waje yanzu zan dawo." Bai jira cewar suba ya fita daga ɗakin da ɗan gudu yayi waje yana dube dube.
A farfajiyar asibitin ya hangi wani mutum sanye da ƙananan kaya kanshi rufe da p-cap yasa bakin eyesglass daya ɓoye kamanin sa yana takawa cikin sassarfa, Bahari na gano shi ya fara sauri yana son cim masa, amma ina kanya iso wajen sa har ya shiga cikin wata karamar baƙar mota yana rufe kofar kuma ko second ɗaya ba'a ƙara ba aka ja Motar da gudu aka bar cikin asibitin.
Bahari ya bi bayan motar da kallo "mtchew." Yaja tsaki ya koma ciki yana zuba mita a ransa.
A yadda ya barsu haka ya shigo ya same su.
"A'a bakuci abincin ba, Aramma dan Allah kuci abincin sai muje muyi Sallah, da zaka yarda ma da saika koma gida ka huta in yaso gobe ka dawo nima suna gama yi mata tests ɗin dole gida zan dawo sai Maman mu ta kwana da ita."
Aramma yayi murmushin su na manya sannan yace "kaima kasan tafiya baza ta yiwu a wajena ba yanzu, muje muyi Sallar tukunna in mun dawo mayi magana." Bahari ya karanci mai Aramma yake nufi da wannan maganar dan haka sai ya riga shi da cewa.
"Eh nima dama ina son faɗa maka, daga wajen biyan kuɗi nake abin farin ciki kuma sai suke sanar dani ai governoty ta ɗauki nauyin komai na rashin lafiyar duk majinyacin da bai wuce shekara goma sha takwas ba, dan haka yanzu babu abinda zamu biya daga kan abinci har kuɗin magani." Aramma ya ce "to...to...to Masha Allahu kai amma ya kyauta wannan bawan Allah, Allah ya biya sa, ashe na cikin binni suna samun taimakon governoty mune dai na ƙyauye irin wannan baya zuwar mana saida dalili, to ya kyauta dama maganar kuɗin jinyar tata nake so naji yaya ake ciki dan gaskiya ba zai yiwu a ɗora maka wahala ba, wannan kaiwa da komowar ma daka tsaya kai da ƙafafun ka kanayi Allah ya biya ka ya baka mata ta gari da yaran da zasu ji ƙanka."
"Amin Aramma Husna ai ƙanwa tace, iyalin ma akwai su sai dai yaran." Bahari ya faɗa yana shafa kai.
Aramma yace "Ah Masha Allahu, ashe babban mutum ne, to Allah ya baku masu albarka, muje sallar sai mun dawo."Suka fita daga ɗakin.
_Masu karatu muɗan koma baya kaɗan......!_
Bayan tafiyar Bahari kiran Aramma, bai jima da fita ba wani likita ya zo ya karɓi takardar hannun Ramma bata hana shi takardar ba dan ta ganshi da kayan likitoci, wajen biyan kuɗin yaje saida ya biya komai yayi wa Nurses ɗin wajen bayani tare da nuna musu su Husna sannan ya juya yabar wajen da sauri.
_wannan ke nan....!_
Ramma ta taimaka wa Husna taje banɗaki ta wanke jikinta, saida ta taimaka mata ta zauna sannan ta ɗakko mata abincin ta bata, da ƙyar taci cokali uku ta ajiye shi gefe, Ramma ta bata ruwan robar da ta gani a saman fridge tasha ruwan sosai zata sake kwanciya tace "a'a Ma'u ɗaure kidan zauna mana wannan yawan kwanciya ai sai jikin ki ya sake nunewa." Fasa kwanciyar tayi Ramma ta miƙa mata robar Popcorn ɗin data gani a ledar tace "To ga mutumin ki sai kici tunda kinki cin abinci." Husna ta karɓa ta fara ci a hankali, sai gashi ta kusa cinye wa dan sosai yayiwa bakin ta daɗi.....