Chapter fifteen
by @aysharano22
🤍SIRRIN ZUCIYA🤍
By Aysha Rano✨
🤍YOTA🤍
08
6 years back, Shri Mahatma Gandhi University, New Delhi, India.
Shekararsu daya kenan yanzu da zuwa India, gashi har sun gama 100 level sun shiga level 2.
Class dinsu daya da Lee likewise gidansu, sun hadu da juna tun farkon zuwansu school din wajen clearance kuma sai akayi sa'a gidan da aka kama musu ma daya ne kuma dakinsu daya. Wnn dalilin ya haifar da abokantaka da kuma shaquwa mai karfi a tsakaninsu dukda kasancewar shi Ayaan musulmi ne kuma ba'indiye yayinda shi kuma Lucas ya kasance Christian kuma bayerabe, snn ya girme mashi da two years don ko lokacinda suka hadu Ayaan was just 19 Lucas kuma 21.
Yanzu kuma Ayaan na 20 Lee yana 22. Friendship dinsu yayi karfin da komai tare sukeyi kuma basu boyema juna komai don su Umma da sisters din Ayaan duk sun san labarin Lucas a bakinshi, dukda tunda yazo bai taba komawa Nigeria ba kmr yanda shima Lucas din duk wanda suke tare dashi sunsan Ayaan, don maraya ne shi ba uwa ba uba sai 'yan uwa da dangi da ba kowa ma kebi ta kanshi ba tunda su suna can Ibadan ne shi kuma yawancin rayuwarshi yayita a Lagos har zuwa yanzu da shima scholarship ya kawoshi makarantar har suka hadu da Ayaan.
✨✨✨
Su biyun ne suke fitowa daga lecture hall dinsu, ko lectures basu gama ba Ayaan ya azalzalesu suka fito don ya samu yaje yaga halittar da soyayyarta ya zama tamkar wani jigo na rayuwarshi, yasan yanzu shine daidai lokacinda zata gama lectures dinta for today, kai tsaye kuma daga class cafeteria zatayi suci abinci da friend dinta kafin su koma gida.
Juwairiyya Salisu Jimeta kenan, kyakyawar bafulatana 'yar asalin Jimeta cikin Adamawa State. Mahaifinta babban politician ne a garinsu don yana daga cikin manyan 'yan siyasar da ake damawa dasu a wnn lokacin. Shekarunta 24 ne a duniya kuma she's a final year student of Biochemistry.
Tun kusan watanni hudu da suka wuce Ayaan ya ganta ranar da akayi wani Holi celebration a makarantar, tun daga nan kuma aka jarabceshi da matsananciyar qaunarta.
Sonta yakeyi sosai fiyeda zato, dukda ba komai ya sani dangane da ita ba ga kuma tazarar shekaru har hudu dake tsakaninsu, ita kuma batasan komai a kanshi ba infact batama san yana existing a duniya ba balle tasan yana sonta. Kaunar da yake mata ne ya sashi fara stalking dinta tun daga ranar daya fara ganinta har zuwa yanxu da yasan tarin abubuwa masu yawa gameda ita...yasan gidan da take zaune, yasan course da take karanta, yasan level nawa take, yasan sunanta yasan friend dinta yasan daga garinda take, yasan time da take fara lectures yasan time da take gamawa don tsaf ya haddace time table dinta, snn yasan duk wuraren da take zuwa apart from schoo sbd tsabar binta da yakeyi. Wani lokaci ko nashi lectures din bai gama ba in time din gama nata yayi haka zai bar nashin don kawai yaje yayita binta a baya yana kallonta, cikin lokaci karami duk ya wani susuce kmr wanda tayima juju inji Lucas...duk wnn abun kuma har yanzu bai ko taba attempting yi mata mgn ba balle yakai ga furta mata yana sonta shi tsoron tunkararta ma yakeji saidai stalking din kawai, musamman da abun ya hadu mishi da yarinta.
Duk ya koma gida kuma haka zai yita tunawa da abubuwan da tayi yana murmushi saidai Lee yata bala'i yana cewa dududu shekararshi 20 amma yana neman ya daurama kanshi bala'in soyayyan da yafi karfinshi. Ayaan bai taba damuwa ba dukda shi kanshi watarana yana mamaki sosai na yanda yake jinta cikin zuciyarshi kmr don ita aka halicceshi amma dukda haka yasan yayi karami da fara soyayya, soyayyan ma na wacce ta bashi good shekara hudu. Koda bashi ya daurama kanshi ba Allah ne ya daura mashi yana kuma da yaqinin bazai daura mashi abinda bazai iya ba...da irin wnn tunanin yake samu yana kwantar da hankalinshi duk ya fara jin kmr kawai yana kokarin daukama kanshi dala ba gammo ne bai zama lallai ta soshi ba, ga wani shahararren kishi da Allah ya zuba mashi baisan ko don bai taba son wata mace bane sai a kanta ko kuma don kananun shekarun da yake dasu ne yasa nashi kmr yafi na kowa, amma duk ya ganta da wani namiji sai yaji kmr ya mutu don baqin ciki, gashi ita kuma ya lura ba wani isashen kamun kai ne da ita ba don yanda take mu'amala da namiji kmr yar uwarta mace ta daukeshi...to yawancin rayuwarta tayishi ne abroad batasan da yawa daga cikin cultures na hausa ko fulani ba...shi kanshi ilmin addini ba wani wadatarta yayi ba boko kawai akasa a gaba kmr bazaa mutu ba..kmr dai yanda yawanci yaran da sukayi rayuwar abroad suke ba wani cikakken kamun kai sun dauki rayuwar turawa sun aza ma kansu to Juwairiyya ma haka take koma ince ta zarce haka.
Shi kuma zafi yakeji sosai duk ya tuna haka har sai yayi kmr ya daina stalking dinta sai kuma daga baya yaji bazai iya ba don ko yini yayi bai ganta ba sai yaji kmr zaiyi rashin lfy sbd tsabar yanda ya kwallafa rai a kanta.
At this point ko karatun nashi ma ba wani maida hankali yakeyi kanshi ba kmr yanda ya maida kanta, donma yanada kwakwalwa ne yasa bai faduwa exams dinshi amma da zai maida hankali a karatun kmr yanda ya maida kanta da ba karamin genius zaayi ba don yanada kokari sosai kawai bashida maida kai ne.
Kai tsaye daga lecture hall din hanyar class din su Juwairiyya suka nufa Lee sai shan kunu yake yana bata rai don ba karamin qular dashi Ayaan keyi akan wnn yarinyar ba.
Dan nesa da class din suka tsaya lokacin students nata fitowa don gama lectures dinsu kenan, Ayaan ya maida dukkanin wani hankali da nutsuwarshi kan kofar yana jiran yaga fitowarta sai kuwa gata nan sun fito tareda Friend dinta da kullum yake ganinsu tare mai suna Nusaiba da kuma wani namiji wanda da ganinshi kasan indian ne yana rikeda jakarta sai kallonta yake yana basu lbr suna dariya…wani irin abu da yaji ya taso mashi tun daga cikin cikinshi saida yaji kmr zuciyarshi ce zata baro kirjinshi...ya kura musu ido yana sake kallon yanda guy din har hannunta yake rikewa sunata dariya abunsu, nan take yaji legs dinshi kmr bazasu iya daukanshi ba kawai sai yayi kasa ya zauna a hankali gefen kujerar da Lee ke zaune akai...dagowa Lee din yayi ya kalleshi yaga yanda lokaci daya idanuwanshi suka sauya face dinshi yayi jajawur tsabar bacin rai sai ya maida kallon garesu nan kuma ya fahimci dalilin wnn kuncin...tsaki ya saki yana dan tabe baki yace "i told you ai indai bazaka daina stalking yarinyar nan ba watarana saita hadaka da hawan jini"...sauke ido Ayaan yayi daga kallonsu bai iya cewa komai ba amma can cikin zuciyarshi yasan wnn mgnr na Lucas is not far from the truth, matukar zai cigaba da stalking dinta to ko bata hadashi da hawan jini ba zata hadashi da matsananciyar damuwa. Dafa shoulder dinshi yaji Lee yayi yana dan sassauta tone din voice dinshi yace "kabi shawarana Ayaan kabar wahalar da kanka haka nan ka cireta daga cikin zuciyarka, idan kuma bazaka iyaba then go to her...confront her and tell her that kana sonta"...girgiza kai kawai Ayaan keyi don baiji zai iya aikata ko daya daga ciki ba, daidai nan kuma yaga giftawarsu ta gefensu sun nufi hanyar cafeteria...da sauri ya mike yana binsu da kallo yacema Lee "let's go"...ba musu Lucas ya mike saidai maimakon ya bishin su tafi juyawa yayi ya kama hanyar inda gidansu yake yana cewa "bazan je ba", bai jira cewarshi ba ya wuce abinshi.
Ayaan bai wani damu ba cox sun saba irin haka dama most of the times ma bai cika rakashi ba cewa yake shi bazai iya aikin wahala ba saidai shi kadai yaje don haka yanxun ma shi kadanshi yabi bayansu har zuwa cafeteria...ciki ya shiga ya zauna table dake dan nesa da wanda suke yanata kallon yanda wnn shegen sai shishige mata yake yana babbaka dariya kmr mara hankali...ganin bazai iya cigaba da jure abunda yake gani ba salin alin yayiwa kanshi fada ya tashi ya bar wurin don ya fuskanci indai yacigaba da zama yana iya kamuwa da hawan jinin da Lee ke kira mashi yau din nan ma ba sai watarana ba. Kai tsaye gida ya nufa tunda sun gama lectures dinsu na yau, koda yaje ya samu Lee har ya musu girki yana zaune yana cin nashi.
Bathroom ya wuce kai tsaye yayi wanka snn ya fito daure da towel, lokacin Lee har ya gama cin abincinshi ya haye gado yana chatting da new catch dinshi don shi sam bai yadda da wani soyayya ko aure ba a cewarshi bazai iya rayuwa da mace daya ba so yafi gane kawai ayi flexing ayi chilling da duk wacce ta shigo hannu inyaso daga baya sai a saketa a samo wata...yana chatting din yanata kallonshi har ya gama abinda yake ya maida towel bathroom snn ya hau kan sofa ya kwanta tareda lumshe ido dukda yasan ba bacci zaiyi ba...ajiye wayar Lee yayi ya sauko daga gadon ya zauna gefe yana fuskantarshi yace "how come you are back early?"...bude ido Ayaan yayi ya kalleshi kmr bazaiyi mgn ba sai can dai ya mike zaune shima yana fuskantar nashi duk ranshi har snn a bace yana tura baki yace "bazan iya cigaba da binta ba, seeing her with another man hurts"...murmushi Lee ya saki yana dan girgiza kai yace "shiyasa nace ka rabu da ita don da ganin yarinyar nan kasan ba wani kamun kai ne da ita ba, dan banzan rawar kai ne da ita unlike sauran muslims dana sani"...kai Ayaan ke gyadawa murya a matukar raunane yace "i know that, amma bazan iya rabuwa da itaba Lucas, bakasan irin sonda nake mata bane". Yana rufe baki Lee yace "then tell her...idan ma bazaka iya zuwa kai kadai ba i'll escort you snn zan tayaka fada mata how much you love her, i'll tell her everything"...kallonshi Ayaan keyi kmr bai yadda da abinda yake fada ba yace "kana ganin she'll love me?"...tun bai rufe baki ba Lee yace"of course mana, me ta fika da har kake ganin bazata amsa love dinka ba?"...saida ya saki dan murmushi kafin yace "well she's rich and am poor"...katseshi Lee yayi da cewa"oh stop it yaar you are not poor...you are a very smart and intelligent young man who has a bright future ahead of him...snn kuma ga wnn mahaukacin son da kake mata meyasa kake ganin bazata soka ba?"...numfashi Ayaan ya sauke kafin yace"am just feeling nervous and scared at the same time"... Lee yace "scared of what exactly?"...yace "scared of rejection. Kawai bansan yanda zanyi ba idan tace bata sona"...Lee yace "then saika sama ranka cewa zata soka"...girgiza kai Ayaan keyi yace "baka ganeba Lucas this girl is older than me, she's four years older than me so what if tace baza tayi soyayya da yaro ba"...yanda ya karasa mgnr kmr baby sbd yanda yayi da face dinshi saida Lee yayi murmushi kafin ya taso daga inda yake ya dawo kusa dashi ya zauna yana cigaba da murmushin yace "kaima kasan yaro ne kai kenan"...harara Ayaan ya watsa mashi baidai ce komai ba, saida Lee ya gama dariyarshi snn yace "you just have to be positive Ayaan...ka sama ranka cewa zata soka"...shiru kawai yayi bai sake cewa komai ba as baisan meyasa har yanzu yakejin kmr koya fada mata bazata soshi ba.
Washegari ma same thing happens, dukda week end ne ba lectures suke ba amma haka Ayaan ya hana kanshi bacci ya fito da nufin zuwa gidanta don gida guda mahaifinta ya kama mata tun farkon zuwanta garin shine suke zaune da Friend dinta Nusaiba wacce ita kuma tazo daga Taraba State, sai kuma ya tuna ashefa tayi joining Hindi Class two weeks back tana zuwa Saturdays da Sundays don haka kai tsaye ya tafi school din don ya rigada ya san school din sbd shima yayita...lokacin farkon zuwanshi India bai iya komai ba a yaren Hindi wanda yakeda tabbacin shine yaren iyayenshi haka nan sai yaji yanaso yayi learning language din koda watarana Allah zai hadashi da iyayenshi yasan ba da hausa zasuyi mgn ba snn ko don yanda yayi kama da indiyawa yanada kyau ace ya iya Hindi din, kar watarana a tabashi aji bai iya komai a ciki ba. Wnn dalilin yasa yayi joining Hindi class tun farkon zuwansu yana zuwa week end, week days kuma yaje makaranta...kuma da yake yaren a jininshi yake baiyi taking nashi wani long lokaci ba kafin ya iya, nan da nan ya zama expert a yaren kai kace dama can ya tashi dashi a baki har yana koyama Lee da always suke tare.
Murmushi ya saki daya tuna lokacin da yake zuwa makarantar hatta malamai kowa saida yayi mamakin jin bai iya yaren Hindi ba, gashi dai indian sak amma ko zo in kasheka bai saniba da Hindi a wancan lokacin amma yanzu gashi kmr ba'ayi ba har ya koya ya wuce wurin, dama kuma shi mutum ne mai saurin koyon abu shiyasa yakeda kokari sosai a makaranta sbd akwai sharp brain...murmushi ya kara saki daya tuna duk kwakwarshi har yanzu ya kasa gane dalilinda zaisa tayi joining Hindi Class tunda ba dashi ake musu karatu ba meyasa takeso ta iya?...gara shi yasan a jininshi yake so ba abun mamaki bane don yana sonshi amma ita fa?, why?...wnn shine tambayarda har ganzun ya kasa samawa kanshi amsarta, haka dai har ya isa makarantar yanata tunane tunanenshi...inda ya saba zama ya nufa kai tsaye bayan ya shiga ciki ya zauna yana jiran fitowarsu...zuciyarshi sai harbawa take tana sa mishi jin cewa yau daya dai ya sameta suyi mgn ko iya gaisuwa ne amma wani bangare na zuciyar nace mishi sam kar ya soma indai ba so yake ya barar da soyayyarshi tunma kafin a fara ba.
Saida yayi zaman kusan 1 hour basu fito ba amma hakan sam bai dameshi ba da alama ya rigada ya saba da hakan ne...yanata zaune a wurin idanuwanshi kirr akan kofar class din yana jiran fitowarta gashi
wnn karon shi kadai yazo don Lee cewa yayi indai bazai fada mata yana sonta ba to shi bazai iya wahalar da kanshi ba shidai da yaga zai iya sai yayita yi amma ba da dan mutanen Ibadan ba, shiyasa ya kyaleshi ya taho shi kadai.
Rano✨