SIRRIN ZUCIYA

Chapter sixteen

by @aysharano22

Bayan kusan 30 mins sai gata ta fito yau yayi sa'a ba tareda namiji suke ba ita kadai ce ko Friend din nata ma babu...wani murmushi ne ya subuce mashi sa'adda ya kura mata ido yana kallonta sai yaji kmr yaje yayi hugging nata don ya dade bai ganta da shigar hausawa ba...tayi mishi kyau sosai cikin budaddiyar doguwar rigar atampa mai zubin maternity gown...ta daura dankwalin atampar a kanta ta jashi baya yanda gashin goshinta data sama gel ya kwanta bisa goshin sai dan siririn veil daya shiga da atampar ta makala a kafadarta don dai ba yafashi tayi ba...shagala yayi sasai yana kallonta har ya zamana bai jin komai bai ganin komai a wnn lokacin dai sai ita kadai...duk yanda yakai da jarumta da iya boye abu a cikin zuciya yau dai kasawa yayi...yana ganin tana tahowa zuwa direction dinshi amma ya kasa koda janye idanuwanshi daga kanta balle har yasan matakin da zai dauka...ya shagala sosai wurin kallonta har bai fahimci lokacinda ta iso kusa dashi ba kawai sai ji yayi tana neman saka mashi two fingers dinta a ido...da sauri yayi blinking idanun yana sake budesu a kanta nan take kuma ya fahimci abinda ke faruwa, yayi zumbur ya mike tsaye yana waige waige kmr wanda ke naman wani abun...sam baisan wajenshi ta nufo ba ai da tuni yasan inda dare yayi masa. 

Sunkuyar da idon nashi yayi bayan ya kammala waiwayen da yake,  haka nan yaji bazai iya kallon idanunta ba sbd wani yanayi mai girman gaske daya cika mashi kwakwalwa da zuciya har kwarjini yaga tayi mashi...kama qugu tayi tana sake matsawa kusa dashi kmr zata fada jikinshi shi kuma yayi saurin ja da baya don yanda zuciya da gangar jikinshi suka fara azabtuwa da wnn kusancin nasu...sake matsawa tayi shima ya sake ja baya haka har saida ya fada kan kujerar daya tashi akai ita kuma ta gyara tsayuwa tana sake riqe waist dinta da hannayenta ta shiga gyada mashi girarta duka biyun tana cewa "malam yadai?...are you stalking me?"...girgiza kai yayi da sauri ba tareda ya dago kanshi ba, kafin ma yakai ga yin mgn ta sake cewa "no, actually this is not the question cox i know you are stalking me infact you've been stalking me for the past few months now, so tell me, why are you stalking me?"...dagowa Ayaan yayi da sauri yana kallonta sbd yanayin da yaji tana mgn duk sai ya daburce ya rasa amsar bata to abunka da yaro, inba quruciya ba ina mace zata dinga ma namiji kwarjini har haka...idanuwansu na haduwa ya janye nashi da sauri ita kuma ta sake repeating mashi question, wnn karon dai da kyar ya iya tattaro kalaman da zasufi sauqin fitowa a bakinshi yace"am not...stalking you"...kura mashi ido tayi jin yanda yake stammering sai kuma ta saki murmushi tareda zaunawa nan kusa dashi cikin zuciyarta tace "he's just a baby"..tana masa dariya...Ayaan dai gum kakeji kmr mara baki nan kuwa shi kadai yasan abinda yakeji a jikinshi don kujerar da suke zaune ba wata babba bace har jikinta na gogar nashi, hakan yasa ya rasa inda zai sanya kanshi ya samu sukuni.

Ita kuwa Juwairiyya dariya sosai ta shiga mashi mara sauti don da gaske dariya yake bata kuma mugun kallon baby take mashi...saida tayi me isarta snn ta sake gyara zama tana fuskantarshi dukda bai yadda sam ya dago kanshi ba yanata jira yaji ta sake maimaita tambayar dazu amma to his very biggest suprise sai cewa tayi "ok you don't have to answer that but i know for a fact that you are stalking me"...kallonta yayi da mamaki saidai bai iya cewa wani abu ba, itama bata damu yace din ba tace "don't be surprised am not a fool, i know when someone is following me"...a hankali yace "sorry", tace "no it's fine, it's ok"...sake dagowa yayi wnn karon da wani katoton murmushi kan fuskarshi yace mata "thank you"...murmushin itama takeyi mashi tace "so what’s your name?"...da sauri yace mata "Ayaan...Ayaan Agnihotri", kai ta shiga gyadawa tana cigaba da kallonshi tace "Indian?"...kmr zai ce mata he's not indian sai kuma yaga dogon bayani zai janyoma kanshi don haka kawai ya amsa mata da "yeah. Indian".

Kan dai take gyadawa har snn kuma bata daina kallonshi ba tace "India is a nice country i must say", yana gyada kai yace "indeed"...tace "are you from Delhi?"...yace"no, Mumbai"...tace"wow Mumbai!...i've never been to Mumbai maybe you should take me someday"...wani gagarumin farin ciki yaji ya lullubeshi jin abinda ta fada, kenan tana nufin zasu cigaba da haduwa, da sauri ya shiga gyada kai yana dubanta duk murna ya gama nunawa a face dinshi kuma ya kasa cewa komai.

Gyara zama tayi duk sai sake matsarshi takeyi ta hana mashi sukuni amma ita ko a jikinta sai ma cewa da tayi "so, are you not going to ask me my name?"...murmushi taga ya saki tareda shafa kanshi and for the very first time yana kallon cikin idonta yace "Juwairiyya..Salisu..Jimeta"...wara idanuwa tayi cikeda mamaki tace "Oh my God how did you know?"...murmushin dai har snn yake jifanta dashi yace"not just your name, i know alot more"...kai take gyada da alama mamakin bai saketa ba tace "i see you've taken stalking to another level huh?...but why are you stalking me thou?...do you want us to be friends or something?"...diff yayi dajin kalmar friends, da farko sai yaji kmr yace mata no he want to be her boyfriend sai kuma yaga gaggawa ba nashi bane don haka yace mata "yeah, i want us to be friends"...wani duka takai mashi a kafada tana kyalkyalewa da dariya tace "you are such a silly boy..why didn't you speak up sooner?"...kai kawai ya girgiza mata alamar nothing, daidai nan kuma wayarta dake cikin jakarta ya fara ringing ta daukota da sauri ganin Nusaiba ke kira tayi picking tareda kaiwa kunnenta idanunta kan Ayaan da yayi kmr ba kallonta yakeyi ba tace "Nusaiba muyi mgn da hausa akwai wanda banaso ya gane abinda muke fada...kinsan me?"...daga can bangaren Nusaiban ta amsa mata da "meya faru?"...tace"hmmm, ina wnn yaron da ranar nace maki bibiyata yake kikace ba haka ba?"...Nusaiba tace "yes what about him?"...Juwairiyya ta saki tsaki tana cewa "nace karkimin turanci amma saida kikayi banziya"...da sauri Nusaiba tace "oh sorry na manta, tell me meya faru?"...Juwairiyya ta girgiza kai jin still dai turancin take mata ganin zata bata mata lokaci kawai tace "yau dai gani gashi a school...innnalillahi Nusaiba kinga wani irin kyau kuwa?"...banji me Nusaiban tace ba sai can ta sake cewa "eh mana, kyakyawa wlh kmr shi yayi kanshi, amma daga ganinshi yaro ne"...ta karasa mgn har snn idanunta kan Ayaan da shima yake dan kallonta time to time yana sakin murmushi jin wai nan mgn take da hausa don kar ya gane batasan kila ya fita ma jin hausa ba...dariya ce takeso ta kufce mashi amma ya rasa yanda zaiyi don yasan yana yinta saiya nemi dalilin bata tunda dai bazai kama dariya shi kadai kmr mara hankali ba.

(Wnn fa shine karin mgn da hausawa suke cewa abin ba dadi wai anyi da mutum yaji🤣ita nan duk a tunaninta sirri takeyi batasan bonono takeyi ba wai rufe kofa da barawo ba🤣🤣🤣).






500 ne kacal ta WhatsApp. 0013569116 Aisha Ahmad Tijjani Jaiz Bank,sai a tura receipt ta wnn number ***.





Rano✨