34
by @aishatouuu
Wajen ƙarfe biyar na yamma aka zo aka fita da Husna zuwa inda za'ayi mata tests ɗin da Dr ya rubuta, sun kwashe wajen awa ɗaya da rabi sannan suka dawo da ita ɗakin hannun ta sanye da kanula.
Ruwa suka sake daura mata suka yi mata allurori, likitan daya dubata ɗazu shiya sake yiwa Bahari bayanin sai zuwa gobe sauran sakamakon gwajin lafiyar Husna za su fito, so zai neme su zuwa goben.
Bahari da Aramma sukayi masa godiya ya fita daga ɗakin yana faɗin "akwai Nurse ɗin da ke kula da ita zata shigo ta duba in ruwan ya ƙare za su cire susa mata wani."
Bayan Sallar Magarba Aramma da Bahari suka yiwa Ramma sallama suka tafi gida bayan Bahari ya sake yiwa Ramma bayanin komai suke buƙata mai kawo abinci in yazo ta faɗa masa...!
Basu sha wahalar samun motar da zata maida su gida ba, sai wajen ƙarfe tara saura suka isa gida, suna sauka Bahari ya biya kuɗin Mota Aramma yayi ta binsa da addu'a dan ya rasa bakin ci gaba da yi masa godiya.
Saida Aramma yayi wanka ya ci tuwon dare sannan yasa a kira masa Lirwanu, Dije na zaune a gefan shi ya shigo ɗakin ya samu waje ya zauna yana gaida Aramma.
"Lirwanu abinda kayi ka kyauta ke nan uhm? Yanzu duk bama wannan ba Lirwanu ka kyauta ko baka kyauta ba nasan ka sani, inaso ka fara faɗa min tsakanin ka da Allah me Asma'ullahi tayi ma kayi mata duka bayan kasan bata da lafiya?"
"Aramma taya yasan bata da lafiya? Daya sani ai da bai dake taba ko?" Dije ta riga Lirwanu yin magana, dan bata son a faɗi asalin abinda yasa yayi mata dukan.
"Eh Aramma dan Allah a gafarceni wallahi bansan bata da lafiya ba raina ne a ɓace lokacin shi yasa ban gane ba." Lirwanu ya zayyano maganar kamar da gaske abinda ke ranshi ke nan, bayan a ƙasan zuciyar sa kuwa cin alwashi yake akan wallahi sai ya karɓi ɗan kunne da awarwaron nan kome za'a yi.
"Har yanzu baka bani amsar abinda tama ba, ko haka kawai ka rufe ta da duka?" Tambayar Aramma ta sake dukan kunnuwan Dije da Lirwanu, shiru ya ratsa gurin tsakanin Lirwanu da Dije kowa ya rasa abun faɗa ɗan sunsan ko giyar wake suke sha basu isa su furta dalilin dukan ba in suka faɗi gaskiyar magana kuwa to shakka babu sunyi biyu babu ko ɗaya dan Aramma ba zai taɓa bari su karɓa ba karshe ma ya haɗa musu da ɓacin rai suyi asara goma da ashirin.
"Shike nan Lirwanu tashi kaje kowa yayi nagari kai nasa, basai ka sake ganin ta zaka daka ba? In sha Allahu lokacin barin ta garin nan yayi, bazaka kashe ƴar ɗan uwanka ina kallo ba, tunda kai mutumin banza ne, ka ɗauka duk abinda kake wa yarinyar nan mutane basa gani kuma Abdullahi bai sani ba ko? Hmmm! Kayiwa kanka Lirwanu."
Kana ganin yadda Aramma yayi maganar kasan ranshi ya kai ƙololowar ɓaci, Dije kuwa saita taɓe baki a ranta tace "maganar barin gidan nan kuma ai an makaro tunda ga miji tayi anan. A fili kuma sai tace "Allah dai ya baka haƙuri kuskure dai Lirwanu ya yi shi."
Lirwanu harya tashi zai fita Aramma ya dube sa yace "yawwa karkaga Ramma bata nan ni nace ta zauna da Asma'ullahi a asibiti harta samu sauƙi, ina faɗa maka ne saboda hakkin kane ka sani."
"Babu komai Aramma Allah ya bata lafiya." Lirwanu yayi maganar yana ficewa daga ɗakin dan baya son ya kuma cewa wani abu.....!
Washegari Aramma da Bahari na tsaye a bakin titi suna jiran mota, Aramma ya dubi Bahari yace "kaga mutumin Asma'ullahi can tsaye, bawan Allah tausayi yake bani yanzu haka yan uwan sa sun yi neman sun gaji, inka bibiya matsalar tashi bata wuce ta sheɗanu ba, kwana biyu shima yace ina mai bani abinci take." Aramma yayi maganar cikin jimami da nuna tausaya wa.
Bahari kuwa sai yayi Murmushi yace "ai nima na ganshi tun da na fito da safe naga yana yawo a tashar nan."
"Allah ya basa lafiya." Bahari ya amsa da ."Amin."
Yauma suna sauka a Mota Bahari ya biya kuɗin, Aramma kawai sai ya bisa da ido dan ya rasa me kuma zai faɗa wa yaron.
Sun sami Husna jiki yayi sauki, suka gaisa da Ramma tare da tambayar ta me jiki tace da sauƙi.
"Babu wani abu da kuke bukata ko?" Bahari ya tambaya yana matsawa jikin fridge ɗin ya dudduba ruwa da moltinar da yaga an kawo.
"Wallahi babu komai, wani abun ma har yayi yawa ake bamu, Allah ya saka da Alkhairi." Aramma yayi murmushi yace "to Alhamdulillah."
Husna dai sai binsu take da Ido tunda suka gaisa bata sake cewa komai ba.
Bahari take so ta tambaya ko yaga yayanta amma ta rasa ta yadda zata tambaye sa, tasan yanzu yana can yana neman ta.
Wata zuciyar tace mata "keda yake fushi dake."
A hankali tasa yatsun hannunta ta shafa inda ya mare ta jiya, duk sanda ta tuna ya mare ta sai ƙwaƙwalwar ta ta toshe ta kasa gane komai, har yanzu hankalinta ya kasa yarda shiya mare ta, wallahi gani take kamar bashi bane yayi marin.
"Aramma muje wanjen Likita muji yadda ake ciki." Bahari ya faɗa, Aramma yace "to sai muje ɗin." Suka fita daga ɗakin.
Zaune suke a gaban likita bayan yasa an kawo masa duka sakamakon gwajin da suka yiwa Husna, saida ya gyara zaman eyesglass ɗin idan shi da kyau sannan ya fuskanci Bahari da Aramma ya fara musu bayani cikin ƙwarewa da sanin abinda yake magana akai.
"Kamar yadda binciken mu ya tabbatar mana Asma'u Abdullahi Mai Kano tana ɗauke da cutar matsalar rashin ganin abunda ke nesa da ita saida taimkon gilashi, wannan cuta a kimiyyance ana kiran ta da Myopia ko Nearsightdness (matsalar ganin nesa saida taimakon Gilashi)
Myopia (Matsalar ganin nesa) wata matsalar gani ce da ke sa idan mutum yana iya ganin abubuwan dake kusa da shi sosai, amma abubuwan da ke nesa dashi suna fita daga hankalin sa wato (blurred)
Misali
Mutum yana iya karanta littafi ko duba wayarsa lafiya amma idan aka nemi ya duba wani abu kamar rubutu ko mutum daga nesa ba zai iya ganinsa da kyau ba sai ya saka gilashin ido (eyeglass).
Akwai kuma hanyoyi da dama wanda ake kamuwa da cutar ko haddasa faruwar Myopia makar:
In tsawon ido ya wuce kima eyeball ya yi tsawo fiye da yadda ya kamata,
Cornea ko lens sun fi lanƙwashewa sosai (too curved) Wannan na sa haske da ke shiga ido ya taru gaban retina maimakon ya taru a kan (retina) ita ce sashen ido da ke karɓar haske domin kwakwalwa ta gane abin da ake kallo.
Akwai alamomin dake nuna mutum yana dauke da cutar Myopia (matsalar rashin ganin abinda ke nesa)
Rashin ganin rubutu ko abu daga nesa (misali allo a makaranta).
Yin ƙoƙarin matsar ido (squinting) don a ga abu.
Jin ciwon kai bayan duba abubuwan dake nesa na dogon lokaci.
Jin gajiya ko zafi a ido bayan karatu ko kallon talabijin (tv)
Misali saika matsa kusa da talabijin ko allo (yaron dake yin haka akwai Possiblity ɗin yana da Cutar myopia sai a ziyarci likitan ido da gaggawa).
Ana iya samun Myopia ta hanyar Gado (genetic factors) Idan iyaye suna da Myopia, yaro na iya gado.
Karatu da yawa ko amfani da wayar hannu na dogon lokaci (close work).
Sannan akwai rashin zama a waje sosai, haske rana yana taimakawa wajen hana ci gaban Myopia ga yara.
Ɗaukar tsawon lokaci a gaban kwamfuta, TV, ko waya.
Yin amfani da
Gilashin ido (Eyeglasses) ita ce hanya mafi sauki na magance cutar.
Likitan ido zai auna girman matsalar (da “eye test”) sannan ya rubuta maka gilashin da ya dace da halittar idanun ka.
Sannan ana amfani da lenses masu nisan gani wato concave lenses (-).
Lens na ido (Contact Lenses)
Maimaikon amfani da gilashi, wasu suna amfani da contact lenses.
Suna taimaka wa wajen gani da kyau amma suna bukatar tsafta da kulawa sosai.
Ana iyayin tiyata (Laser Surgery)
Misali LASIK ko PRK.
Ana gyara siffar cornea ta hanyar laser domin a dawo da daidaiton idanu.
Amma ana yi ne ga manya da idonsu ya daina canzawa.
Barin yara su fita waje, su sami hasken rana yana taimakawa wajen kare su daga cutar Myopia.
Sanna a rage musu lokutan da suke amfani da waya ko kwamfuta sosai ( ba wayewa bace ko gata ki bawa yaro waya yayi ta kallo da sunan wasa dan ɗauke masa hankali)
Sannan a dinga duba lafiyar ido a kai a kai.
In ana jin wahala ganin abin da ke nesa ko fama da yawan ciwon kai bayan karatu ko matsawa kusa da talabijin ko screen din waya dan ganin abu da kyau to a ziyarci likitan Ido.
Likitocin ido na duniya wanda ake kiran su da (Ophthalmologists da Optometrists) sunyi bayanin gwajin da ya kamata mai Myopia yayi kamar
Binciken tarihin lafiya (Medical & Vision History)
Likitanka zai fara da tambayar
Shin kana ganin abu daga nesa yana fita (blurry)?
Yaushe ka fara lura da haka?
Shin iyayenka suna da irin wannan matsalar?
Kana yin ciwon kai ko gajiya idan kana karatu?
Kana yawan amfani da waya/kwamfuta kamar sau nawa a rana?
Wannan yana taimaka wa sosai wajen gano dalilin kamuwa da ciwon.
Myopia tana da alaƙa da gado ko sabon abu ne da ya taso saboda halin rayuwa (lifestyle) misalin yadda ya faru da Husna.
Binciken hangen nesa (Visual Acuity Test)
Ana yin sa da akwatin gwaji (Snellen chart) wanda ke da haruffa masu girma da ƙarami.
Mutum zai tsaya a nesa (mita 6 / ƙafa 20) sannan a duba ya yake iya karanta rubutun a nesa?
Idan yana rike da gilashi, shin gani sa yafi ko a'a?
Refraction Test (Gwajin daidaita hangen nesa)
Wannan shi ne mafi muhimmanci don auna karfin Myopia.
Ana amfani da na’ura mai suna Phoropter ko Auto-refractor dan dubawa.
Mutum zai zauna yana kallo ta cikin na’ura, gwaji yana taimakawa wajen sanin nau’in gilashi da za a rubuta wa mutum.
Retinoscopy (Gwaji da haske a ido)
Ana yin wannan domin tabbatar da sakamakon refraction.
Wannan yana nuna yadda haske ke taruwa a cikin ido, wato ko yana gaban retina (Myopia) ko bayan retina (Hyperopia).
Sannan akwai binciken sashin ido (Slit-Lamp Examination)
Ana amfani da na’ura mai haske da guga domin duba cornea, lens, da retina.
Dan a tabbatar babu wata cuta (kumburi, tabo, ko infection).
Likita na yin wannan gwajin musamman kafin a yi LASIK ko PRK surgery.
Ana binciken nisan hangen ido (Pupil & Eye Alignment Tests) ana duba:
Shin idanu suna aiki a tare? Ko akwai matsalar “strabismus” (idan daya na karkata gefe)? Da “accommodation” (ciwon ido wajen mayar da hankali)?
Wannan yana taimakawa wajen kada a rubuta gilashi mara dacewa.
Akwai kuma dilated Eye Exam (Bude ido da magani)
Ana shafa eye drops da ke bude pupil (hankali na ido), sannan likita yana duba retina da optic nerve sosai da microscope.
Wannan yana tabbatar da cewa babu lalacewar sashin ciki na ido, musamman ga masu Myopia mai tsanani (high myopia).
Sai Keratometry / Corneal Topography
Wannan na musamman ne idan ana shirin yin LASIK surgery.
Ana auna Siffar cornea da kaurinta, a tabbatar da cewa tana da kyau kuma tana iya karɓar tiyata.
Idan cornea tana da rauni ko siriri sosai, likita ba zai yarda a yi LASIK ba sai dai PRK ko Ortho-K.
Bayan gama gwaje-gwajen nan, likita zai ba da ɗaya daga cikin waɗannan sakamako.
Myopia mai sauki (-0.25 zuwa -2.00) Gilashi za'ayi amfani dashi kawai.
Matsakaici (-2.25 zuwa -5.00) Gilashi ko contact lens.
Mai tsanani (-5.00 zuwa sama) Gilashi, Ortho-K, ko tiyata idan ya dace
Myopia mai ci gaba a yara Ƙarin kulawa da Atropine drops ko Ortho-K."
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un." Aramma ya faɗa a fili bayan sauraren bayanan likita.
Bahari kuwa shiru yayi yana sake juya bayanan likitan, saida ya numfasa sannan yace "Dr yanzu meye abin yi akan ciwon nata?"
Saida likita yayi musu murmushin kwantar da hankali sannan yace "Baba karku damu ba wata matsala bace mai zafi, kuma a binciken da mukayi akan dalilan kamuwar ta da Myopia (matsalar ganin nesa) munyi realizing ta kamu da Cutar ne saboda yawan kuka da matsanancin ciwon kai da take yi, wanda hakan ya kai har tsawon lokacin da ya fara taɓa jijiyoyin idanun ta ba tare da an kulaba, dama kuma kamar yadda na faɗa muku Myopia tana da alaƙa da gado (genetic factors) ko sabon abu daya taso saboda halin rayuwa (lifestyle).
A gwajin hangen nesa (visual Acuity test) da muka yi mata mun gano idanun ta suna da cikakkiyar lafiya da daidaito, tsawon idanun ta bai wuce kima ba haka eyeball din ta sun yi daidai, baiyi tsayi fiya da yadda ya kamata ba, cornea da lens basu lankwashe ba (too curved), sannan munyi mata gwajin daidaita hangen nesa (refraction test) wanda shi ne gwajin mafi muhimmanci dan auna ƙarfin Myopia, kuma munyi mata retinoscopy gwaji da hasken ido don mu tabbatar da sakamakon refraction dan mu gane yadda hasken ke taruwa a cikin idon ta ko yana gaban retina (Myopia) ko bayan retina (Hyperopia).
Sannan munyi (slit-lamp examination) dan tabbatar da babu wata cuta (kumburi, tabo ko infection) a cikin idanun ta. a takaice zamu iya kiran dalilin nata Myopian da yanayin rayuwa ne ya haddasa mata shi wato (lifestyle) ɗaya daga cikin dalilan dake iya kawo ta ke nan inka cire gado (genetic factors) da yawan amfanin da wayar hannu na dogon lokaci (close work) rashin zama a waje a samu hasken rana musamman ga yara, ko yawan kallon talabijin (tv) da dadewa a gaban kwamfuta.
Bayan duka gwaje gwajen da mukayi mata zamu bata eyesglass wanda zai taimaka wa ganin ta, sannan zamu bata eyes drop wanda zata rinƙa amfani da shi, idan har Idanunta suka samu kulawar data kamata akwai Possiblity ta iya warkewa daga cutar gaba ɗaya." Dr. Ya ƙara sa fito musu da bayanin yadda zasu gane dan yaga tashin hankali kwance a kan fuskokin su.
"Mun gode sosai Dr. In sha Allahu za'a kula, kuma zuwa yaushe ne za'a iya samun glass ɗin?" Bahari ne yayi tambayar yana kallon Likita.
"Yeah bana jin zai ɗauki lokaci tunda mun riga mun gano matsalar so zuwa gobe zamu iya sallamar ku zuwa lokacin eyesglass ɗin ta zai zama ready in sha Allah." Likitan ya faɗa, Aramma ya sake masa godiya sannan suka baro office ɗin.
Hankalin Aramma yayi mugun tashi dajin wannan labarin dan saida Bahari ya rinƙa kwantar masa da hankali da tabbatar masa da Husna zata warke in sha Allah.
Bahari na sake kwantar mai da hankali ne kawai amma shi a ransa ji yake tabbas basu kyauta wa Husna ba.
"Amma komai ya zo ƙarshe bazan saka ido a lalata rayuwar kiba in sha Allahu, a wannan karon koda kaina ne nayi alƙawarin saina maida ke gidan ku Asma'ullahi." Aramma ke wannan zancen da zuciyar shi.
Jikin Husna nata warware wa dan yau bata wuni da zazzaɓi da ciwon kai ba, sosai ake kula dasu a asibitin, hatta abincin da ake kawo musu mai kyau ne wanda zai sake taimakawa mara lafiya ya samu kuzari, haka indai za'a kawo abincin sai an haɗa da Popcorn, biskit da manyan chaculate wanda Husna ma ba cinsu take ba iyakar ta taci Popcorn ɗin abincin ma kaɗan take ci sai yougot da take yawan sha.
Bayan Sallar la'asar su Aramma suka yi musu sallama zasu tafi, Aramma ne ya fara fita Bahari ya tsaya duba abinda basu dashi, Ramma ta shiga banɗaki ya rage daga shi sai Husna a ɗakin da yaga ta kwanta ya ɗauka ma bacci take saida yazo fita daga ɗakin yaji saukar muryar ta tana tambayar shi.
"Bahari ina Yaya?"
Cak ya tsaya yana sauraren ta, saida ya rufe idanunsa ya buɗe su a hankali sannan ya juyo yana mata murmushi yace "yana nan lafiya ko ɗazu da safe mun gan shi nida Aramma."
"Dan Allah kace ina gaisheshi kuma kace nace yayi hakuri bazan sake ba."
Sai kuma ta sa hannun ta share hawayen da suka zubo mata, tace "Bahari zan baka amanar abu ka kaiwa Yayana kace masa ina gaishesa kaji, babu abin da zai ma kaga baya faɗa kuma baya duka dan Allah kar kaji tsoron shi?"
Bahari ya ƙurawa Husna ido sosai yana kallon zallar kuruciya da rashin wayo a tare da ita, banda haka mahaukacin zai bawa sakon duka wannan maganganun nata.
"To mema tayi masa take cewa a basa hakuri harda bazata sake ba? to amma tana da zuciya mai kyau, sannan bata da wayon da zata fahimci rayuwa a yadda take, yasan dole tunanin ta ba zai zama ɗaya dana shi ba, sannan ɗan uwa da soyayyar data taso cikin ta take neman makwafin ta, har cikin rai da zuciyar sa yaji yana mata fatan alkhairi da samun cikar muradin ta, wani bangare na zuciyar sa kuma sai yaji tausayinta nayin irin wannan mugun sabo da wanda bata sani ba, bata san waye shiba, sai wanda ta gani a tashar garin su cikin ciwon hauka.
Bahari yayi nisa cikin tunanin Husna da halayen ta muryarta ce ta katse masa tunanin da yake.
"Bahari zaka bashi saƙon?" ta faɗa tana kafe shi da idanun ta da suka washe jan da sukayi suk dun baje sai ɗan abinda baza'a rasa ba.
"Zan basa in sha Allahu, amma fa inya dake ni ko yamin hauka sawa zanyi a zane min shi babu ruwana."
"Shiba mahaukaci bane karka sake kiran sa mahaukaci." Husna tayi maganar ranta a ɓace daidai lokacin kuma Ramma ta fito daga banɗakin.
"A'a Bahari baku wuce ba?"
"Eh Babarmu yanzu zamu tafi." Ya faɗa yana duban Husna yace "bani saƙon to Aramma yana jirana."
Ledar kusa da ita data saka Popcorn ɗin da akan kawo mata da rana bata ciba ta ɗakko tasa biskit da chaculate a cikin ledar sanan ta miƙa masa.
"Okay wanna ne sakon?" Bahari ya faɗa yana kallon ta, sai ta ɗaga masa kai tana murmushi.
Shima murmushin yayi mata ya juya ya fita riƙe da ledar yana sakin wata boyayyiyar dariyar da shi kaɗai yasan manufar ta....