MUTUWAR AURE...! BOOK 1

35

by @aishatouuu

***
_________________


Da wuri suka iso gida, Aramma yana ta yi wa Bahari godiya suka rabu, shi ya tafi gida dan gaf ake da kiran sallar Magarba, Bahari kuma ya wuce wajen saida fetir ɗin shi.

Ya samu Garba a zaune yana shan fura, yace "sannu da ƙoƙari Garba kwana biyu na haɗa ka da wahala, kai wannan furar raina ya fiya kaɗan rage min mana nasan yanzu mai siyarwa ta tashi." Garba yayi dariya yana sake antaya furar shi ciki yace "karka damu na siya na aje maka dan nasan daga kunun Ma'u sai furar nan kake sha, ya jikin nata?" 
"Kai amma Garba yau ka biya ni wallahi, jikin Ma'u da sauƙi sunce gobe zasu sallame mu." Bahari ya faɗa yana zama akan bencin kusa da Garba.

Bayan Sallar Magarba Bahari ya hange shi can gefe ɗaya zaune yana kallon titi, har yaje kansa ya tsaya kuma bai nuna yaji alamun zuwan Mutum inda yake ba. 

Bahari yayi masa magana yayi banza ya rabu dashi ko kallon inda yake bai yiba, dama kuma shima Baharin bai sa ran yayi masa magana ba, dan haka ya tsaya da kyau yana duban sa yace "Kai yayan Ma'u tace kana jin mutane nidai ban yarda ba dan banga alama ba, amma dai ga amana nan saƙo ne ta bani tace na baka, ta kuma ce na faɗa maka kayi haƙuri ba zata sake ba." Har Bahari yayi maganar shi ya dire bai motsa daga yadda yake ba bare yasa ran zai ɗago ya kalle sa.

"Ahab banda ma kuruciya irin ta Ma'u wa yake aike wajen mara kan gado, wallahi badan nayi mata alkawari ba da babu abinda zai kaini magana da mahaukaci nima ana min kallon mara lissafi." Wannan karon saida ya juyo da kanshi daga inda yake tsaye Sandar shi ya jawo Bahari yayi baya kaɗan yana faɗin.

"Kai yasin in kamin hauka, wallahi duka zansa ama babu ruwa na itama kuma na faɗa mata kana min shirme zaka daku." Ya faɗa yana jefa masa ledar hannunsa yace "gashi nan kaci ko ka zubar matsalar ka."

Zai juya ya bar wajen yaji Dan Hajja daya taho wajen yana faɗin.
"Haba Bahari yada jifa kuma, hala wani abun yama? Kaga ni duk ba wannan bama, ta gidana ce bana gani kwana biyu mutuniyar ka, sai kuma ɗazu naji wani zance yana ɗan yawo wai bata da lafiya kaida Garba ne ma kuka kaita asibiti, ya meye gaskiyar magana?"  
"E to lafiya dai da gaske bata da ita, jikin ta kuma Alhamdulillahi, zancen mu muka kaita asibiti kuma wannan Magana ce kawai, mu muka raka Aramma dai ya kaita asibitin." Bahari ya faɗa a ransa yana tsinewa bakin Garba da baya shiru.
"Okay, kace gobe dole na fita dubiya, amma sai zuwa yamma saboda inada baƙin da zasu zo siyan riɗi gobe da safe." 
"Okay to yayi sai goben angon Ma'u ko basa so." Bahari ya faɗa yana bashi hannu suka tafa, shi kuma yayi dariyar jin daɗi.
"Shi yasa fa nake yin ka mai gaskiya." Dan Hajja ya faɗa, Bahari ya juya yana dariya shima ya koma shagon sa dama kuma shiya hango ya taso.

         Suna barin wajen ya dauki ledar da Bahari ya jefa masa, bai duba meye a ciki ba ya dukunkune ta ya saka a cikin burgujejen aljihun jallabiyar shi yaci gaba da zama a wajen yana tona rami kamar yadda ya saba.

Washegari da kyar Bahari ya roƙi Aramma ya yarda ya zauna shi ya tafi Dutse shi kaɗai tunda sunce yau zasu sallame su.

Ƙarfe goma na safe a cikin asibitin tayi masa, ya samu Ramma da Husna har sunyi wanka, Ramma tasa doguwar riga yarkanti da aka kawo musu jiya da daddare harda hijabi babba, Husna itama doguwar rigar tasa baka mai adon baƙin dutse mai ƙyalli a jiki sai ɗan ƙaramin farin hijabi mai bakin lace a ƙasa duka suna cikin kayan da aka shigo jiya aka basu, Ramma kuma data fita taji ana maganar rabon kayan sawar da aka yi a section ɗin.

Kayan kala biyu biyu ne hijabi ma biyu, rigar tayiwa Husna kyau sosai kamar saida aka gwada ta aka ɗakko kayan, fuskarta tayi fayau a cikin farin hijabin, Idanun ta sunyi fari babu jan ko kaɗan dan eye drop ɗin da take sawa sosai take jin daɗin shi.

Bahari yau daya shigo ya ganta harda tsokanar ta saida yayi, ita kuma bata kula shiba sai harara data sakar masa.

"Ah kyayi yarinya tunda kin farfaɗo, oh su Ma'u da yanzu yau mukayi sadakar ukun ki fa ko?" Ya faɗa da sigar tsokana, Ramma tayi dariya tace "ashe kaima haka kake da zolaya Bahari."

Suna zaune Ramma da Bahari suna hira jefi jefi, likita ya shigo ɗakin Nurse na biye dashi a baya riƙe da File ɗin Husna.

"Sannu da zuwa likita."

Ramma ta faɗa tana matsawa ta bashi waje, hannu yaba Bahari suka gaisa Husna kuma ta gaisheshi, ya amsa yana tambayar ta saukin jikin ta.
"Babu ciwo yanzu." Ta faɗa a hankali.
"To Masha Allah, Allah ya ƙara lafiya." Ya juya ya karbi wani kwali a hannun Nurse ɗin, covers ɗin eyesglass guda biyu ya ciro ya aje ɗayan a gefen gadon ya buɗe ɗayan ya ciro shi.

Frame ɗin eyesglass ɗin mai ɗan faɗi jikin shi golden zagayayye mai kyau, Dr. Da kanshi ya matso kusa da Hausa yasa mata saida ya daidaita zaman shi a kan idanun ta sannan yaɗan ja da baya yana kallon fuskarta yace "kai Masha Allah, ciwo babu daɗi amma na daɗe banga wanda eyesglass ya yiwa kyau kamar kiba, Allah ya sawaƙe miki gaba ɗaya, ga spire guda ɗaya nan, ki rinƙa kula kinji?"

Husna ta ɗaga sama ka tana jin fuskar ta wani iri alamar rashin sabo da glass ɗin.

Can karshen kofa Dr. ya koma yace ta faɗa masa yadda ya tsaya da abunda ya riƙe a hannun sa. 

Tirayan tiryan ta faɗa masa komai dan fes take iya ganin shi.
"Good, ga takardar sallama nan Allah ya baki afiya."

Ya faɗa yana miƙawa Bahari paper, yasa hannu ya karɓa yana sake masa godiya, yace "haba karka damu aiki na ne fa, nima yanzu zan wuce Kano dama ku kuka tsaida ni." Ya faɗa yana musu sallama ya fita Nurse na biye dashi a baya, Ramma da Bahari suka raka sa da addu'ar sauka lafiya.

"Inye su Ma'u an zama ƴan gayu masu saka gilashi."

Ta cikin gilashin ta zabga masa harara tace "in baka tsokane ni bama Bahari ai sai Allah ya tambaye ka."

Ai kuwa ya kwashe da dariya dan sosai yaji daɗin martanin ta, dan burin shi ta sake kan su isa gida.

Ramma kuwa kai ta girgiza ta fara haɗa kayan su waje ɗaya.

           Ƙaramar Mota Bahari ya samo musu drop ya ɗauka ya zauna a gaba su suka zauna a baya.

Cikin kankanin lokaci suka iso gida dan babu tsaye tsaye ga motar babu lefi tana tafiya, tunda suka baro asibitin Husna ke kallon hanya tana tunanin abinda zata sake komawa, ɗaya barin zuciyar ta kuma cike yake da ɗoki da murnar san zuwa ta ga yayanta.

Saida Motar ta kaisu har ƙofar gida Bahari yayi musu ala huta gajiya sannan suka dawo tasha ya sallami mai Motar.

Da sallama suka shiga gidan Ramma ce a gaba riƙe da ledar kayan su Husna na biye da ita a baya.

Su Naja suka zuba musu ido sanda suke takowa cikin gidan babu tabbacin akwai wanda ya amsa Sallamar su ma tsabar shaida, yau inuwar gidan nasu a cike take ga turame nan masu casa nayi masu surfe ma nayi.

Husna kuwa duk sun zuba mata ido kamar zasu cinye ta, su da ya kamata a yi wa sannu da zuwa, amma sai Ramma ce tayi musu sannu da aiki, Husna kuwa duba ɗaya tayi musu ta wuce ɗakin da take kwana, Dije ta bita da harara.

"In kinwa mutane ma magana kinci guzumar uwarki shegiya muguwa mai baƙin hali."
Ramma ta girgiza kai a ranta tace "ko yaushe Dije zata canja hali? Mutun ya dawo daga asibiti zaman jinya babu tambayar ya jiki ba komai sai marabar zagi dacin mutumci."
Ita ma bata zauna a wajen ba ta shige lungun su, tana barin wajen kuwa aka dasa gulmar ta.

"Wai baku kula da kayan jikin su ba, dubi ma'u harda wani gilashi sai kace wanda suka je bulaguro maraya, ni sai naga duk sun yi wani fayau dasu." Zahara ta faɗa tana kama baki.
"Yo Gilashin banza Cutar makanta cefa ta kamata, ai da farko har zansa a kira min Mai Kano na ɗauka shi ne ya biya kuɗin asibitin, sai jiya Aramma yake faɗan min wai taimakon governoty ne."
"Nifa ince wannan Yaron Bahari dake rawar kai ina yaga uban kuɗin yin duka wannan wahalar, dan ni tun farko ma shina ɗauka ya biya musu kuɗin komai." Zahara ta tari numfashin Dije, Naja da sauran matan suka yi dariya suka ce "yo kuɗi ai sirri ne?"
"Ko uban sirri ne kuɗi wannan kina ganin shi da fiki fikin ido da zungureran gemu kamar bunsuru kinsan bashi da ko sisi, kai ko yana da shi ma Ma'u ta Ɗan Hajja ce yawwa magana ma ta faɗa sai zaman jiran lokaci." Dije tayi maganar tana wani cika irin wacce ta isan nan.

Husna kuwa kwanciya tayi a ɗakin saida Aramma ya shigo sannan ta fito, yana ganin ta yayi murmushi yana faɗin.
"Alhamdulillah Asma'ullahi jiki yayi sauki, ai yanzu muka dawo daga Salifawa munje gaisuwa naga Baharin a bakin titi yace min har kun dawo, Sannu Asma'ullahi Allah ya ƙaro lafiya." Aramma ya faɗa yana dafa kan ta cikin nuna kulawa.
"Amin nagode Aramma." Ta faɗa, yayi murmushi, bata sake cewa komai ba, daga ƙarshe ta tashi ta fita daga lungun.

               Da da daddare Husna sanye da rigar da tasa a asibiti da gilashin ta da Indo keta santin sa tunda tazo gidan suka tafi dandali da wuri dan Allah Allah Husna take dare yayi taje Dandalin ko zata ga yayan ta saboda ta fita tasha neman shi ɗazu bata ganshi ba, dan haka yanzu ta cewa Indo su tafi da wuri.

Suna zaune a inda suke zama aka fara taruwa a Dandali aka hura wutar kara, ba'a daɗe da fara gaɗa ba aka yi kiran Indo ya rage wajen sai Husna ita kaɗai, har tashi tayi ta leƙa wai ko zata ga tahowar sa amma har Indo ta daɗe da tafiya bai zoba.

Gajiya tayi da leken hanya ta koma ta zauna tana jin zuciyar ta babu daɗi.

Fuskarta harta canja hawaye ya cika kata ido ta cire Gilashinta ta goge hawayen da bayan hannun ta sannan ta mai da shi tana haɗiyar zuciya dan Dr. Yace ta daina yawan kuka inba haka ba bazata warke ba.

Abin da Husna bata sani ba shine duk abin da take yana can gaban su bayan wata bishiyar maina yana kallon ta duk leken da take yana ganin ta, dan shima da wuri yazo dandalin dan yana son haɗuwa da ita.

         Ta yunƙura zata tafi gida kamar yadda ta yanke shawarar yin hakan a zuciyar ta sai kuma taga yana tahowa da sauri kamar wanda aba biyo.

Tsabar munar ganin sa da tayi saida ta saki dariya haƙoranta suka fito waje fetal.

Yau shiya zauna a ƙasa ita kuma ta zauna akan ican tana ta kallon sa tana murmushi.

"Yaya inata jiranka baka zoba harna haƙura zan tafi gida nace Yayan Husna ba zai zoba yau." tayi masa maganar a sakalce." 

Kamar yadda ta sani bai yi magana ba sai kanshi daya ɗago ya kalleta blue eyes ɗin sa fes a waje, Husna ta ɗauke Idanun ta a kansa da sauri dan wallahi tsoro ƙwayar idan shi ke bata, ita bata taɓa ganin mai irin idan sa ba sai a kanshi.

"Yaya idan ka tsoro yake bani nika daina kallona dasu." Luuuu taga ya maida idanunsa ciki ya rufe su ruf, ta ƙasan ido yake ƙare mata kallo tayi masa kyau cikin riga da farin hijabin haka gilashin yayi mata kyau.

"Yaya kwana uku kaga bana nan ko?" Bata tsaya da magana ba tunda tasan ba amsa zata samu daga wajen shi ba taci gaba da yin maganar ta hankali kwance.

           "Yaya bani da lafiya ne saida aka kaini asibiti nayi kwana uku sannan naji sauƙi, ɗazu muka dawo gida, Yaya kasan wanda ya kaini asibitin?" Yanzu ma bata jira amsa ba taci gaba da cewa "Bahari ne fa yana da kirki sosai Aramma yace zai faɗa wa Babana yayi masa godiya sannan yace min in sha Allah Babana in yazo zaisa ya tafi dani ko shi ya kaini da kansa."

Sai kuma ta ɗanyi shiru, har saida ya ɗago ya kalleta sai yaga ta cire Gilashin idanta tana goge idanun ta da hawaye ya zubo.

Kasa ɗauke kanshi yayi a kanta ya zuba mata Ido sosai yake ƙare mata kallo, muryar ta tayi ƙasa sosai tace "Yaya nafi son na koma wajen Babana duk da Nana tana min mugunta tana da faɗa gayin zagin da Mama tace haramun ne, tana ce min ƴar arniya baƙa, kumafa Mamana tana Sallah har karatun Alkur'ani take koya min dan Allah arne ai baya Sallah ko Yaya?" Ta faɗi maganar tana kallon shi kamar me jiran ya bata amsa.

"Hmmm Dije mafa haka take cemin dangin arna, wai ita tasa Babana ya saki Mamana ta kore su ita da Yayana, kasan me yasa nafi son can akan nan?" Sai kuma ta girgiza kai tana ɗan murmushin daya sake zubo da hawaye ta tace "acan Nana bata duka na, amma fa ta taɓa min duka sau ɗaya ta fasa min baya da yawa da cinya ta sukayi ta jini harda tabo yawwa kaga ma irin tabon dukan da tamin a hannun na." Ta janye hannun rigar jikin ta sama ta nuna masa tsintsiyar hannun ta inda shatin bulala ya kwanta sosai tabon dukan ya fito yayi duhu fiya da asalin kalar fatar jikin ta, hannun ya zuba wa Ido yana kallo duk masifar ka kuma bazaka gane yanayin da fuskar sa take ciki ba.

"Tom kaga har jikina ma akwai irin wannan, ita kaga tun daga lokacin bata sake duka na ba, zagina mafa batayi sai Baba baya nan, kuma kaga acan ina zuwa makaranta nasan da Baba bai kawo ni nan ba da yanzu na gama primary na shiga irin tasu Yaya ko?" Tayi masa maganar da sigar tambaya.

"Amma kaga anan Baba Lirwanu yana dukana sosai ka tuna randa nayi lefi ka mare ni?" Tayi maganar tana kallon shi, saiya sunkuyar da kansa ƙasa, Husna tayi murmushi kamar mai karantar yanayin sa tace "ai Mamana tace in Yaya ya daki ƙaninsa to dan yayi masa lefi ne in yana so ya dena saiya dakesa kaɗan, to kaima ai haka ne ko Yaya? Nasan Irin dukan da Yayana ke min ne a gida in naƙi yin homework ko na tsokane shi, shi kamin ko Yaya?" Shi dai har yanzu kansa na ƙasa Husna ta sake yin murmushi tace "shi yasa nace wa Bahari ya ce kayi hakuri bazan sake ba, ai ka haƙura ko?" 

Wannan karon kansa ya mai da gefe kamar mai kallon wani abu, tace 
"Kaga randa kamin marin nan ko? Hmmm shine fa na kwana da ciwon kai har da zazzaɓi da safe kuma Baba Lirwanu yamin dukan tsiya saboda na baka ɗan kunne da awarwarona ka ɓoye min, wai dole saina bashi ina yi musu baƙin ciki da mugunta."

Husna ta faɗa kukan da take tason dannewa ya kwace mata.

Yanzu kam kai tsaye yake kallon ta da hawayen dake bin kumatun ta, inka kalli hannun shi da kyau kuwa za kaga kamar suna kaɗawa, Sandar shi ya ɗauka ya babbuga a ƙasa har yanzu ƙwayar idanunsa da suka fito waje suna kan Husna dake ta share hawaye, tana kukan tace "Yaya bana son yin Kuka saboda likita yace na daina kuka in ba haka ba idona ba zai warke ba, amma to kukan ne yake zuwa ban sani ba." Tayi maganar a karye daga ƙarshe kuma a sakalce.

Saida ta goge hawayen duka sannan ta maida Gilashin saman idonta....