MUTUWAR AURE...! BOOK 1

36

by @aishatouuu

Ta kalle sa tayi masa Murmushi sai taga ya ɗan motsa hannun jallabiyarsa tana kallon sa yaɗan ja hannun rigar kaɗan saiga wani farin abun hannu akan tsintsiyar hannunsa Husna ta kalli hannunsa dake rufe da wani baƙin abu da bata san ko meye ba sai kuma ta maida hankalin ta kan wani farin abun hannu data gani a saman hannun sa da kallo ɗaya zaka yi masa kasan azurfa ce mai daraja, ta saman shi yana da ɗan faɗi kaɗan gefe da gefan shi kuma siriri ne, yadda zaka iya matse sa koka buɗe sa, irin warwaron azurfar nan ne da yawan ci zaka ganshi a hannun Mazan fulani, mutanen Niger ko Shuwa araf.

Tana kallon sa ya cire abun hannun ya miƙa mata da sauri ta karɓa dan yayi mata kyau, kallon saman warwaron tayi taga anyi wasu kananan rubutu da Arabic bata gane me aka rubuta ba, tace "Yaya nasa ka bani kyauta?" ta faɗa tana sakin murmushi, bata tsaya sake wata maganar ba tasa abun hannun a hannunta na dama sai taga ya yi mata yawa sosai har zatayi masa magana sai kuma ta fara matse shi a hankali sai taga yana haɗe wa saida taga yayi mata daidai a tsintsiyar hannun ta sannan tayi murmushin jin daɗi ta nuna masa hannun ta tace "Yaya kaga ni yamin kyau sosai Nagode sosai Yaya." ta faɗa bakin ta yaƙi rufuwa sai shafa abun hannun take tana murmushi.

             Shi kuwa saiya tsaida idanunsa akan ta tana murna yana binta da kallo, Husna nata masa surutu har lokacin da dare ya fara yi yayi ya miƙe tsaye tana ganin haka ita ma ta tashi tana kallon sa, ya sata a gaba suka biyo ta baya, saida ya rakata yaga ta shige gida sannan ya juya ya bar wajen.


                Washegari wajen karfe shida na safe sama-sama Husna dake bacci a ɗakin Ramma da yake Zahara ce tayi girki ita sai washegari zata karɓa, taji hayaniya da salatin mutane kamar a lungun su, harta koma ta sake kwanciya kuma sai taji ihun Dije da kamar maganar Aramma a cikin wajen.

"Aramma a lungun su Ramma abune da kowa yasan ba ƙaramin abu bane ace ya shigo wajen su.

Ɗankwali Husna taja ta ɗauka akan zane hudu da Ramma tayi mata anaya gobe zata kwanta jinya, Gilashin ta data ajiye akan Famekar Ramma ta ɗakko ta saka ta fito waje.

Taron mutane ta gani a lungun da yawa harda matan su Baba Adamu sai abokan Baba Lirwanu Mutum biyu tsaye anata hayaniya.

"Wayyo Allah na wayyo Allah na, bayana kafuna kaina jikina gaba ɗaya ciwo suke min wayyo Allah na." 

Husna taji Muryar Baba Lirwanu yana faɗa da ƙyar cikin azaba. Aramma daya gama ƙare masa kallo yace wa abokan shi dan Allah ku kaimin shi bakin rumbu bari nazo muga ko ƙafar karyewa tayi ko tsagewar kashi."
"Aramma.... Aramma wannan ba tsagewar Kashi bace wallahi sun karya ni, lah ilaha'illallahu Muhammadurrasulullahi." Lirwanu da bakin shi yaƙi yin shiru, mata anata yanyana zance kowa so yake yaji meya same shi."

              Yadda suka shigo dashi su biyu yanzu ma su biyun suka kamasa suka kaishi bakin rumbu inda Dije ta shimfida taburmar kaba suka ɗora sa akai amma sai ya kasa zama da kyau saida ya karkace.

Aramma ya iso wajen riƙe da wani mai kamar man shanu yace "Tsalaha ku riƙe min shi na fara duba kafar kan tayi tsami." Aramma ya faɗa yana zama a gaban Lirwanu.

Lirwanu yana ihu yana komai su Tsalaha suka rike shi Aramma ya fara gyara masa kafafun da kashin wajen ya goce ɗayar kuma kashin sane ya tsage, ihu Lirwanu yake zundumawa yana zufa da magiyar a sake shi, amma basu saurare saba saida Aramma ya ce ya gama su barshi sannan suka sake sa suna maida numfashi.

           "Wallahi duk tsinannan daya yima wannan abun sai ya dandana kuɗan shi, har ni za'a yiwa iya shege a garin nan." Dije ta faɗa bakin ta na kumfar jaraba.

"Ina.....Iya wallahi ba mutane bane, wannan Aljanu ne Aramma kumin maganin Aljanu inba haka ba zasu kashe ni wallahi kashe ni za suyi." Lirwanu ya faɗi yana sharbe majina.

Aramma ya dube sa da kyau yace "yanzu dai zakayi mana bayanin meya same ka ko kuwa sokiburitson zakaci gaba dayi na kama gaba na."

"Zanma bayani Aramma dan a samo min maganin Aljanu ma zan faɗa maka."
"To yayi meya same ka, ba tare mukayi Sallar asuba ba?" Aramma ya faɗi yana duban Lirwanu.

        "Aramma muna fitowa daga masallaci titi na miƙe na tafi bahaya can bayan makaranta, saida na gama bayan gari na baro wajen ko taku biyar masu kyau banyi ba naji an ɗaure min ƙafafu da wani abu na kasa gaba na kasa baya, zan juya bayana da naji takun mutane sai aka saka min wani abu me ƙarfi aka manne bakina, da ido na, ina neman yadda zan cire abun ido da baki na aka zare min riga da karfin tsiya aka ɗaure hannayena ta baya wallahi na dauke yan mafiya ne kawai sai naji saukar duka tako ina su ke duka na babu bakin ihu da neman ceto saida suka yimin lilis sannan sama-sama naji ana faɗin ya daku ku barshi haka amma ku buge ƙafafun sa, wallahi da aka buga min wani abu a kafata wannan ta dama saida wajen yayi ƙara, da kansu suka mayar min da kaya na sannan suka kunce min ƙafafu da hannu, a wajen na zube ban sake gane abinda yake faruwa ba saida aka shigo dani gidan nan."

"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!" Mutane wajen suka ɗibi ambaton Allah da masu Salati Husna dai tana tsaye a kusa da Ramma tana ganin ikon Allah, dan wallahi babu ƙarya ya daku duka ba kaɗan ba kuwa, saida Aramma yasa aka cire masa riga sanan akaga yadda jikin sa yayi wani irin burdin burnin bulala ga fuskar sa tasha maruka hakorin sa nagaba ya fita.

Tsalaha abokin Lirwanu yace "Wallahi Aramma muna tafiya zamu bayan gari muka ganshi yashe a ƙasa baya numfashi har munji tsoro da farko dan bamu gane waye ba saida muka kawo shi makaranta muka zuba masa ruwa muka daye abinda aka rufe masa baki da ido da ƙyar sannan muka gane Lirwanu ne."

Tsalaha ya faɗi yadda suka samu Lirwanu a jeji yashe, Dije ta fara zazzaga tsinuwa tana faɗin sai ta ɗauki mata ki.

Aramma kuwa rasa tunanin daya kamata yayi ma yayi, gaba ɗaya kanshi ya kulle dan haka yace kowa ya tafi yabar wajen, ya dubi Lirwanu yace "kodai kayi rigima da wasu ne?" 

"Wallahi babu wanda muka yi rigima Aljanu ne kawai wannan dukan bana mutane bane." Lirwanu ya faɗa yana zufar wahala.

Aramma yace shike nan kayi haƙuri za'a sama maka magani.

 
                ******
Da misalin sha biyu na rana ɗan aiken Mai gari yazo kiran Aramma ya same sa a kofar masallaci suka tafi wajen Mai gari tare, Aramma yana tunanin ko lafiya.

A ƙofar Mai gari yaga wata mota ƙirar Honda Accord Baƙa da wani matashin saurayi da ba zai wuce shekara ashirin da uku zuwa da biyar ba tsaye a jikin motar, Aramma bai kawo komai a ransa ba ya shiga rumfar mai Gari da sallama.

"Wa alaikumussalam maraba da Aramman gari, bismillah." Mai gari ya faɗa yana nunawa Aramma wajan zama.

Saida suka gaisa cikin mutuntawa Sannan Mai gari yace a kira masa baƙuwar da tazo a cikin gida.

Suna zaune ta shigo da gwarin Hausar ta da kana ji kasan a sama ta koya suka sake gaisawa da Mai gari, Mai gari ya dubi Aramman yace "wannan baƙuwar kace, ɗazu tazo aka rako ta nan tace min ita da ɗanta ne suka zo zaka ganshi nan waje da mota, wajen ka tazo amma bazata je gidan kaba saboda abinda ya kawo ta magana ce daya kamata ayi ta a gabana to shi ne yasa na aika a kiraka."

Aramman ya dubi matar yace "baiwar Allah sannu da zuwa daga ina haka dan ban gane kiba." 

Saida ta rusuna ta gaishe da Aramma ciki girmamawa kamar yadda yare suke yi sannan ta gyara zama ta fuskanci Aramman tace "Ni sunana Mansura Abdulkadir Mai Shinkafa, daga Kano nake ni yayar Safiya ce tsohuwar matar Abdullahi" 
"Allahu Akbar kabiran, wallahi ban gane kiba saida kika faɗi haka sannan naga kuna yanayi da safiya, sannu da zuwa Mansura ya kika baro manyan? Ina Alhaji ƙarami (kanini Husna)" Aramma ya faɗa yana duban Aunty Mansura.

"Kowa yana nan lafiya Alhamdulillahi."
"To Masha Allahu." Aramma yayi shiru yana sauraren ta, Aunty Mansura ta sake tara hankalin ta waje ɗaya tace "Aramma nazo ne domin ka bani Husna na tafi da ita, saboda mu inganta rayuwar ta, munyi ta zuwa duba lafiyar ta a gidan Baban ta amma saiya sanar damu tana nan, tun muna saka ran zai dawo da ita Kano sai kuma muka ji shirun yana sake yawa wannan dalilin yasa ni na wanke Kafa nazo wajen ka ka bani ita da adalcin ka na tafi da ita, in ma bakwason zaman ta damu kamar yadda Maman Abdullahi ta kafa sharaɗi a wancan lokacin da tasa Abdullahi ya saki Safiya to mun yarda zan maida ita gidan Baban ta taci gaba da zama acan, amma shi zaman nan ɗin ne ga yarinyar da bata taso anan ba kamar Husna sai nake ganin gaskiya akwai shiga hakki." Aunty Mansura ta jero maganganun cikin salama da kwantar da kai.

Mai gari ya gyaɗa kai ya ce "tabbas tabbas akwai shiga hakki kam, yarinya mai basira irin wannan."

Aramma yayi shiru yana juya zancen Aunty Mansura filla filla yake musu bashin baƙi, wato dai Dije ce tasa Abdullahi ya saki Safiya ta ƙarfin tsiya kamar yadda yayi tunani a wancan lokacin, sannan ita ce ta hana su riƙe Asma'ullahi. Lallai rashin adalcin nata ya kai, tabbas duk maganganun ta haka suke kuma tazo akan gaba, tabbas daya faɗa wa Abdullahi halin da Asma'ullahi take ciki da babu shakka zai ce shiya aiko ta, amma danya sake tabbatar wa sai yace mata.

"Gashi kuma shi Abdullahin bai faɗa mana zakizo ɗaukan taba."
"Eh kamar yadda na faɗa maka da farko Aramma Abdullahi baisan nazo ba, wannan zuwan kaina ne." Aunty Mansura ta sake faɗa tana karantar yanayin Aramma.

"To babu lefi kin kyauta Mansura Allah ya baki ladan zumunci yaji kan mahaifin ku mutumin kirki sannan kin zo akan gaɓa, dan cikin satin nan nake zuba idon Abdullahi ya zo ya ɗauke ta ko nakai masa ita da kaina, amma tunda Allah ya kawo ki shike nan faɗuwa tazo daidai da zama, yanzu bari nasa a kirata."

Aramma ya faɗa zai tashi mai gari yace "a'a Aramma ai ba sai kaje da kanka ba duk ga yara nan bari nasa su kirata." Mai gari ya faɗa yana miƙewa ya shiga cikin gidan shi saida ya tura a kirawo Husna a gidan su sannan ya dawo rumfar sa ya zauna.

Husna tana zaune tana taya Ramma tsintar wake yaro ya shigo yace taje inji Aramma yana wajen mai gari.

Tsaram Husna ta zare hannunta ta shiga ɗaki ta dakko gyalan doguwar rigar dake jikin ta ta fito, ƴar uwar rigar da aka basu ce a asibiti a jikin ta, rigar ruwan goro ce mai dubu ta saukar mata har ƙasa gata da faɗi mayafinta bashi da wani girma sosai Husna ta yafa gyalan a kanta fuskar ta sanye da eyesglass ɗin ta ta tafi gidam mai gari, inda akace Aramma na kiran ta.

A kofar gidan ta wuce Abdulyassar dan Aunty Mansura sam bata gane shi ba kamar yadda shima bai gane taba.

A bakin rumfar Mai gari tayi sallama daga ciki mai gari yace "shigo Ma'u."

Aunty Mansura najin an ambaci sunan ta ta zuba wa ƙofar shigowar ido.

Husna ta shigo cikin sanyin hali da nitsuwar ta ta halitta, Aunty Mansura ta bita da kallo daga sama har ƙasa.

"Husnan Safiya ce ta girma haka? Allahu wahid, tayi tsayi saidai ta rame sosai fuskarta tayi fiyau, kayan jikin ta ta kalla da mamaki tabbas tasan rigar da kuɗin ta dan design ɗin na cikin irin kayan da suka kawo na karshen nan. Abdullahi nada zuciyar yiwa iyali ba wani abu bane dan ya siyawa Husna wannan rigar ba." Aunty Mansura ta ayyana a zuciyar ta.

Saida Aramma ya nuna wa Husna Aunty Mansura dake zaune sannan ta kula da ita, da sauri ta ɗaga kai tana kallon ta tace "Mami....Mami yaushe kika zo nan? Mami tare zamu tafi ko?" 
Husna ta faɗa tana yin kan Aunty Mansura da sauri ta faɗa jikin ta ta ƙanƙame ta kamar ance mata zata gudu ta barta sai kuma ta fashe da kuka.

"Mami dan Allah ki tafi dani kinji? Mami ki kaini wajen Yaya ni bana son zaman nan Mami dan Allah karki tafi ki barni."

Husna ta jero maganganun tana rusa kuka, sosai hankalin Aramma ya tashi zuciyar shi tayi masa babu daɗi.

"Allah sarki Husna ashe danne ta akayi shi yasa take zaune anan dan bata da yadda zata yi amma dubi daga ganin wacce zata iya tafiya da ita yadda take kuka tana haɗa ta da Allah karta tafi ta barta."

Aramma yayi zancen a rasa a fili kuwa sai yace 
"In sha Allahu tare zaku tafi Asma'ullahi yau kin gama zaman nan sai dai kizo mana da ziyara." 

Husna ta saki Aunty Mansura dake share hawayen tausayin ƴar ƙanwar tata tace "Aramma da kaske."
Ya daga mata kai yana Murmushi alamun tabbatar wa.

Ai Husna saita dena kukan ta saki Murmushi ga wahaye ga dariyar jin daɗi, Aunty Mansura ta cire mata gilashin idan ta ta share mata fuskarta da hawaye ya jika tana kallon ta, sai kuma ta goge mata gilashin ta ɗaga shi sama tana ƙare masa kallo da sauri ta dubi Husna idanun ta a waje cikin tsoro tace "Husnah matsalar ido gare ki?" 

Husna ta ɗaga mata kai Aunty Mansura kawai saita koma da baya ta zauna daɓas a ƙasa tana sauke numfashi riƙe da gilashin tace "lahaula wala ƙuwwata illa billah, mun shiga ukku ni Mansura."

"Subhanallah! Kulla karki sake faɗin haka Mansura jarrabawar Husna ke nan in sha Allahu zata warke."

Aramma ya faɗa da yanayin nuna wa Aunty Mansura ba komai bane hakan.

Mai gari ma ya jajan ta mata Husna kuwa na zaune a kusa da ita ta maƙale mata, suka sake tattauna wa da Aramma sosai akan Husna ta kira Abdulyassar ya gaida Aramma ta nuna masa Husna yayi mamakin ganin ta.

Da yarabanci yake cewa Aunty Mansura "Amma ta girma." Sai yaga Husna tayi murmushi ta gaisheshi da Yarabanci, abun ya bawa Aunty Mansura mamaki har saida ta kasa haƙuri ta tambaye ta bata manta yare ba.

Husna tace "eh akwai wani mai shago ana Ibone amma yana jin Yerabanci shi yake min yare." sosai Aunty Mansura taji daɗi.

Aramma ya tashi yace wa Aunty Mansura bari ya yi wa uwar riƙon ta magana sai tazo tunda ita tace ba zata koma gidan suba.

Aunty Mansura tayi murmushin jin kunyar tsohon amma kuma tayi alkawarin bazata gidan su Abdullahi ba dan ko kaɗan bata son ganin Dije, kar taje ta faɗa mata wata maganar ta biye mata su kunta hali shi yasa ma ta zaɓi zuwa gidan Mai gari.

              Aramma ya tafi ya faɗawa Ramma zuwan Aunty Mansura.

Sanda Aramma ya fadi zuwan Aunty Mansura da tafiyar da zatayi da Husna balli saiya nemi tashi dan Dije ɗora hannu tayi aka tace bata yarda ba shi kuma Aramma yace babu wanda ya isa ya hana a tafi da Husna.

Lirwanu ma yana fama da kanshi amma saida yabi bayan Dije, Aramma yace wa Ramma.

"haɗa ya nata ya nata ki tafi gidan Mai gari, yau zanga wanda ya isa ya hana su tafiya a garin nan."

Ramma ta shige ɗaki haɗa kayan Ma'u har cikin ranta murna take taya Husna sai dai akace wai sabo shi ake wa kuka gaba ɗaya saita rude ta rasa abinda zatayi a ɗakin saida Aramma ya turo Zahara tayi mata magana sannan ta haɗo ɗan kayan Ma'u da basu fi kala shida ba daga sabin har tsofin ta zuba a kongwaramar akwatin ta ta tafi gidam Mai gari.

Nan fa zance ya tashi a gidan, da masu yiwa Husna murna da masu cewa hakan bai dace ba, da munafukai masu fuska biyu irin su Zahara.

Dije kuwa baƙin cikin rusa mata tsari da Aramma yayi ne ya ƙume ta ya sata kuka gaba ɗaya ya lalata mata komai. Taso ta maida Ma'u jari a wajen Hajja da Ɗan Hajja amma yanzu an lalata mata komai. Inta tuna abubuwan da zasu kuɓce mata dalilin tafiyar Husna bata sanin sanda take fasa sabon kuka, kaf dangin Safiya kuwa babu wanda bata tsinewa albarka ba sai wanda ta manta...