BABI NA GOMA SHA BIYAR
MUTUNCI MADARA...
©Fareeda Abdallah
Paid book ne. Kuɗin karanta labarin 1k kacal. Ki tura kuɗinki ta wannan account ɗin 7039080978, Opay, Farida Abdullahi, sai a tura min shaidar biya ta wannan numbern *** domin samun damar kasancewa a group ɗin da zan dinga posting ɗin littafin akan lokaci in sha Allahu.
Ina kuke Ƙasaitattun mata ƴan gayu waɗanda basa ƙyashin cire kuɗi su gyara kicin ɗin su da jikinsu? Me kike buqatar siya a gurinmu Hajjaju? To ki dakata a nan, domin kayanki ya tsinke a bakin kaba💃🏽 Idan ma kuɗin ne kike ƙyashin cirewa a lokaci ɗaya muna adashen gata don sauƙaƙa ma abokan hulɗar mu🥰 Duk abinda kike son siya za mu baki dama ki tara kuɗinsa sannu a hankali bayan kin gama biya ki karɓa bisa gaskiya da amana 🤝 Idan kayan kicin kike so ga link ɗin group kiyi joining.
👇👇👇👇
***
Bayan kayan kicin muna sayar da ƙayatattun Laces, Shadda, Atamfa, Veil's, Shoes, bags. Abin burgewar kuma shi ne muna bada kayanmu akan farashi mai sauƙin gaske👌🏽👌🏽🥰 ku yi joining group ɗinmu ku kwashi garaɓasa Sisters💃🏽💃🏽
👇👇👇👇
***
Sannan kuma muna da Group da muke siyar da Lagos shoes, muna bada sari daga 6pcs akan farashi mai kama da kyauta🥰👌🏽Wannan dama ce ga masu son fara sana'a, da kuma waɗanda suke sana'ar💃🏽💃🏽
👇👇👇👇
***
15)
Ƙarshen Free Pages
Tsawon wasu daƙiƙu Kamal yana tsaye a tsakiyar falon kamar wanda yake neman wani abu. A hankali ya sake kai dubansa kan kujerar da Sakina ta saba zama. Kamar yadda ya gani a farkon shigowarsa, har yanzu babu ita.
Ya ɗan ɓata fuska, ya ce a fili ranshi a ɓace.
"Me ma zai sa in neme ta? Aikin banza da wofi kawai."
Ya ja tsaki, sannan ya nufi dining. Sai ya ga ta shirya masa abinci cikin kuloli sababbi masu kyau.
Duk da ba ya tare da yunwa, yadda kulolin suka ɗauki hankalinshi yasa shi ya ja kujera ya zauna. Murfin warmers ɗin ya buɗe. Ƙamshin lafiyayyen abincin ya daki hancinsa. Farar shinkafa ce da aka dafa ta da su grean beans, karrot, da miyar kaji.
Ya ɗauki plate ya zuba ƴar kaɗan, ya ɗiba a cokali ya kai baki. Daɗin abincin yasa shi lumshe idanu ya cigaba da tauna sannu a hankali.
A wannan lumshe idanun da ya yi, ba zato ba tsammani kwatsam sai zuciyarsa ta fara tuna mishi ranar farko da Sakina ta fara dafa mashi abinci, a lokacin suna tsaka da jin daɗi da garɗin soyayya.
'A wancan ranar azumi yake yi. Ko da ya sanar da ita yana azumi kamar wasa ta ce mishi za ta shirya mishi kayan shan ruwa. Ya ce ta bari ta ce ita dai a'a! Ya ja, ta ja, Sai kawai ya ce to ya yarda. Ana gaf da shan ruwa ya isa gidansu, bayan ta ishe shi da kiran waya da cewa tana jiranshi fa. Bazai manta ba... Haka ta shirya mishi garar arzikin da ko Mama da ta haifeshi baza ta taɓa shirya mishi haka kawai don yana azumi ba.
Shi kuwa ya buɗe ciki ya kwashi gara iya gara, ko kaɗan bai nuna wata baƙunta ba. A wancan ranar, haka ta yi ta zagaye falon cikin rawar jiki da firirita tana jiran ya yaba ɗanɗanon girkinta. Shi kuwa duk da ya gane abinda take buƙata sai ya fuske, ya ci yai hani'an, yana haramar tashi bai ce komai akan ɗanɗanon abincin ba kawai ta durƙusa ta saka mishi kuka.
Ai kuwa nan da nan hankalinshi ya tashi, a ruɗe ya dinga rarrashinta yana tambayarta abinda yake damunta, domin shi duk tunaninshi ko wani ciwon ne ya kama ta farat ɗaya. Sai da ya daɗe yana rarrashinta sannan da ƙyar ta ce mishi bai ce abincinta ya yi daɗi ba.
A lokacin duk yadda ya so hana kanshi yin dariya ya kasa, sai da ya ƙyaƙyata sosai sannan ya daure ya tsagaita dariyar ganin kukanta na ƙara ƙarfi. Ya yaba mata da zaƙaƙan kalamai kamar yadda ta so, sannan ya bata tukwuici mai tsoka...'
A bazata murmushi ya suɓuce mishi bayan ya gama tunanin da yake yi. Sai kuma ya girgiza kai, ya cigaba da cin abincinsa.
Amma fa duk yadda yake ta ƙoƙarin mayar da hankalinsa kan cin abincin, zuciyarsa tana ta komawa kan tunanin Sakina. Duk da ba yau ne ya fara dawowa bai ganta a falo ba, ya rasa dalilin da yasa rashin ganinta na yau ya tsaya mishi a zuciya.
'Ko me ya hana ta fitowa falo tayi kallo kamar yadda ta saba mafiyawancin lokuta?'
Ya sake jan tsaki a fili. Ya ajiye cokalin hannunsa ya miƙe tsaye.
Ko tunaninsa ne ya harba wani guri Oho! Kawai sai ganin ƙafafunsa yayi sun fara tafiya zuwa hanyar ɗakin Sakina. Bai ankara ba sai da ya kai bakin ƙofar, sai ya tsaya cak!
Wani irin ɓacin rai ya lulluɓe shi. Nan take shaiɗan ya fara dawo mishi da laifukan Sakina a zuciyarsa. Sai kuma ya juya da sauri ya nufi ɗakinsa. Bayan ya shiga ciki ne tunanin alkhairan Sakina suka cigaba da bijiro mishi.
Ya cire agogon hannunsa ya jefa kan gado. Ya cire hula itama yai hurgi da ita.
Ya zauna yaraf! A kan kujera, sai kuma ya miƙe ya nufi bayi. Har ya kama handle ɗin ƙofar sai kuma ya saki, ya koma kan kujera ya zauna kamar wanda aka ɗaure da igiyar tunani.
Yana cikin wannan halin kiran Mama ya shigo cikin wayarsa, sai a lokacin ma ya tuna ɗazu yana hanya ta kira shi, bai ɗaga ba ya ce idan ya isa gida zai kira ta sai kuma ya manta. Jikinsa a sanyaye ya ɗaga wayar da sallama a bakinsa.
"Assalamu alaikum! Mama barka da dare."
Ta amsa da murya mai ɗan nauyi. Bayan sun gaisa ne ta ce
"Kamal na kira ka ɗazu baka ɗaga ba, kuma baka kira ni ba daga baya. Me yake faruwa?"
"Kiyi haƙuri Mama. Kin kira ni ina hanya, da na shigo gida kuma sai wani abu ya ɗauke min hankali."
"To Madallah! Dama na kira ka ne in tuna maka maganar zuwa gidansu Sakina yi ma iyayenta godiya. Yaushe ne ka saka ranar zuwa?"
Ya yi ɗan shiru, ƙasa-ƙasa ya ce
"Mama dole ne zuwan?"
"Ƙwarai kuwa dole ne."
Ta amsa mishi da salon jaddadawa a muryarta.
"Haba Mama! Ba fa addini bane..."
"...Al'ada ce mai kyau da ake yi tun iyaye da kakanninka. Don haka kaima dole sai ka je."
"Maamaaa..."
Da faɗa-faɗa a muryarta ta katse shi da cewa
"Wallahi Kamal sai ka je. Umarni ne ba shawara ba, lallai ka samu su Ma'aruf gobe idan Allah ya kaimu da La'asar ku je ku gaida Iyayen Sakina kuyi musu godiya. Ka ji abinda na ce?"
"Na ji Mama."
Ya amsa ba don ranshi yana so ba.
Mama ta sassauta muryarta ta cigaba da magana.
"Kamal?"
"Na'am Mama."
Ya amsa yana ƙara bata hankalinsa.
"Na san kana jin babu daɗi akan katsalandan ɗin da nake maka a lamarin Sakina. Amma ka sani, wannan abinda nake maka ba takura bane. Ba kuma son zuciya bane. Wannan shi ne asalin soyayya ta gaskiya da zan gwada maka a matsayina na wacce ta haife ka."
Ya lumshe idanunsa, da sanyin murya ya ce
"Haka ne Mama. Na gode."
Nasiha ta cigaba da yi mishi, tana haɗawa da buga mishi misalai na yadda idan ya yi haƙuri ya rungumi Sakina da gaskiya da riƙon amana zai ci riba a rayuwarshi, sai da ta tabbatar ya yi laushi sosai sannan Mama tayi mishi sallama ta katse wayar.
Bayan sun gama waya da Mama, ya daɗe zaune yana kallon ƙasa, a zuciyarsa yake ta ƙara jujjuya nasihohin Mama, duk da ya san gaskiya ta faɗa mishi, amma shi ya rasa yadda zai yi da zuciyarsa har ya iya tanƙwarata ta yafe ma Sakina ta sake karɓar da hannu bibiyu a karo na biyu.
****
A can ɗakin Sakina kuwa a daidai wannan lokacin tana zaune ne kan sallaya bayan ta idar da nafilar Shafa'i da wuturi. Alƙur'ani ne ajiye a gabanta, sai dai ba karatu take yi ba, ta yi shiru ne kawai idanunta na kan Alƙur'anin, zuciyarta ta lula can duniyar tunani.
Hawayen da take ta ƙoƙarin hana su fitowa daga cikin idanunta suka zubo. A nutse ta ɗaga hannuwanta sama ta ce
"Ya Allah ka zaɓa min abinda ya fi zama mafi alkhairi tsakanin wannan murɗaɗɗen zaman da tafiya."
Sai kuma ta share hawayenta. Ta buɗe Alƙur'anin ta fara karantawa cikin nutsuwa. Tun tana karatun a hankali har zaƙin karatun ya ɗebe ta ta ƙara ɗaga murya da zazzaƙar sautinta.
****
A ɗakin Kamal yana kwance akan gadonsa ne kawai, idanunsa a buɗe suke. Tun ɗazu yake ta ƙoƙarin barci ya ɗauke shi amma inaaa. Sai juye-juye kawai yake yi.
Idan ya gaji da juyin kuma sai ya sake jan lallausan bargo ya lulluɓe jikinsa. A ƙarshe da yaga barcin ya ƙi zuwa sai ya miƙe zaune, kamar wanda yayi gudu yana ta sauke ajiyar zuciya a kai-a kai.
Can kuma sai ya ji kamar yana jin ƙishin ruwa, ya taka a hankali zuwa ƙofar ɗakinsa ya buɗe ya fita. Har zai nufi kicin, sai kuma ya nufi ɗakin Sakina, bayan ya yi tunanin ya kamata ya faɗa mata gobe za su je gaida su Daddy kamar yadda Mama ta umarce shi.
Yana murɗa hannun ƙofarta wata sassanyar murya mai zaƙi tana karatun Alƙur'ani ta bugi kunnuwansa. Ya tsaya cak! A hankali ya ɗaga kansa yana hangen can cikin ɗakin, sai ya hango ta zaune akan Sallaya tana karatu. Tana sanye da Hijabi fari kar a jikinta.
Ba ta san yana kallonta ba, ba ta san ma akwai wani bayan ita a cikin ɗakin ba, karatunta ta cigaba da yi cike da shauƙin Alƙur'ani a muryarta. Shi kuma ya cigaba da kallonta cikin nutsuwa.
A karon farko tun bayan aurensu ba ya kallonta da idanu masu cike da ƙiyayya. Ba ya kallonta da idanu masu cike da fushi. Kawai kallonta yake yi kamar wanda yake ganin wani sabon abu a tare da ita.
Wata nutsuwa ta mamaye fuskarta da yake hange. Wata annuri da bai taɓa kula da ita ba yanzu yake gani a fuskar Sakina. Sai ya ji wani abu da bai san ko menene ba ya ɗan motsa zuciya. Sai kuma ya kawar da kansa da sauri daga kallonta.
A daidai lokacin kuma Sakina ta tsaya a ƙarshen Surah! Ta ɗaga hannuwanta biyu sama tayi addu'ar da ba ya jin me take cewa, can kuma sai ta shafa addu'ar, ta rufe Alƙur'anin.
Ta miƙe tsaye, tana juyawa karaf! Idanunsu suka haɗu. Tsawon wasu daƙiƙu babu wanda ya yi magana, ita tana kallonshi da ɗan mamaki a fuskarta, shi kuma yana kallonta da yanayi mai wuyar fassara.
Ita ta fara kawar da idanunta, fuskarta a sake, amma ba murmushi take yi ba. Kuma bayan mamakin da ta nuna na ganinsa bata nuna wani yanayi da zai ga ta yi farin cikin ganinsa ba.
Ta duƙa ta ɗauki Alƙur'anin za ta wuce ta mayar inda take ajiyewa Kamal ya kasa haƙuri da sanyin murya ya ce
"Sakina?"
Sai ta tsaya cak! Kiran sunanta a bakinsa kuma cikin mutunci da darajawa bayan kwanaki masu yawa da bai yi ba ya sa zuciyarta motsawa.
Sai dai ba ta bari hakan ya nuna a fuskarta ba. Ta kalle shi a nutse ta ce
"Na'am."
Sai kuma ya ɗan daburce ya rasa abin cewa. Shaf ya ma manta abinda ya kaishi ɗakinta a wannan lokacin. Shiru ya ratsa tsakaninsu. Daga ƙarshe ya ɓuge da cewa
"Kin ci abinci kuwa?"
Tambayar ta ba Sakina mamaki ba kaɗan ba. Amma sai bata nuna ba, a nutse kuma a gajarce ta sake amsa mishi da cewa
"Eh."
Kamal ya gyaɗa kai. Sai kuma ya ce
"To."
A ruɗe ya sake cewa
"Shi ke nan!."
Sakina dai na tsaye tana jira ko zai sake cewa wani abu mai muhimmanci, da ta ji kame-kame yake yi sai ta juya ta nufi gurin ajiye Alƙur'anin hannunta, lokaci ɗaya tana ce ma Kamal
"Sai da safe."
Ba ta ji ya amsa ba har ta ajiye Alƙur'ani da Hijabin jikinta ta shige bayi.
A dole Kamal ya fice daga ɗakin zuciyarsa cike da jin haushin kansa, musamman yadda ya kasa riƙe kansa a gaban Sakina. Ya ja tsaki bayan ya tuna ainahin abinda ma yasa shi shiga cikin ɗakinta a wannan lokacin, amma ya rasa dalilin da yasa suna haɗa idanu tayi mishi wani mugun kwarjini, ya dinga kame-kame kamar bawan da yayi ƙarya a gaban Sarki.
******
Tana goga mishi tsayayyun manya-manyan na shanunta farare tas masu barazanar rinjayarta ta kira shi a tausashe da sunan da ita kaɗai take kiransa da shi.
"Nurul hayat?"
"Na'am Honey"
Ya amsa da ƙyar, saboda tsananin shauƙin daɗin da yake ciki saboda abinda take mishi.
"Akwai wani giɓi ko ɗan kaɗan da na rage na sha'awar wata ƴa mace a zuciyarka da ban cike shi taf ba?"
"Babu Honey!"
Ya amsa da sauri.
"Wallahi kin cike ko ina taf! kin gama min komai, ke ɗaya kin ishe ni rayuwa... Banda ke da Mama duk matan duniya kallon maza nake yi musu a idanuna..."
Ta ƙyalƙyace da wata sakaltacciyar dariya mai bayyana matsanancin jin daɗin maganganunsa. A hankali ta janye ƙirjinta daga na shi, ta kama hannunsa suka isa bakin gado ta zaunar da shi, ta tsuguna a gabansa ta fara yi masa wani irin birkitaccen salon karuwanci da ya sa shi fara gurnani yana wani irin sambatu yana zambarma kamar zai yi hauka saboda ƙololuwar jin daɗin da yake ciki. Sai da ta tabbatar ta kai shi wani ƙololuwar mataki da duk abinda ta ce bazai iya mata musu ba sannan ta ce
"Idan da gaske kake faɗin wannan maganar ina so a yanzun nan ka saki Sakina..."
Tun kafin ta rufe baki ya ce
"Ni Kamal, na Saki..."
Firgigit! Kamal ya farka daga nannauyan barcin da ya ɗauke shi daƙyar bayan dawowarsa daga ɗakin Sakina. Ya haɗa zufa ya yi kashirɓin kamar wanda aka sheƙa mishi ruwa a cikin barcin.
Wani zirrr! Ya ji a jikinsa, aikuwa kamar an ce mishi ya taɓa babbar hedkwatar shi na ƴan sanda. Yana taɓawa sai ya ji shi kaca-kaca ya ɓata jikinsa, lamarin da ɓai taɓa faruwa da shi ba duk iya tsawon shekaru biyun da suka kwashe suna soyayya da Sakina.
******
Kwanaki suka cigaba da tafiya a hankali. Wasu lokutan idan mutane suna cikin farin ciki sai suga kwanakin na gudu kamar wucewar iska. Amma ga mutane irin Sakina da Kamal kuwa, sai suke jin ko wace rana kamar tana ƙara tsawo fiye da wacce ta gabata.
Har yanzu a tsakanin zamantakewarsu yanayin da ya fi ƙarfi shi ne na shiru da kamewa. Ƙarara babu soyayya musamman ta ɓangaren Kamal, amma kuma an ɗan samu sauƙin zazzafar ƙiyayyar da yake nuna mata a baya. Kuma tun daga wancan ranar da ya kusanceta da mafi munin wulaƙanci har yau da suka kusa cika watanni biyu bai sake nemanta ba.
Sakina kuwa ta ƙara tattara shi ta ajiye a gefe ɗaya, duk da ba wai ta daina jin ciwon yadda abubuwa suka rikiɗe suna tafiya a tsakaninsu bane. Ta cigaba da rayuwarta cikin nutsuwa da taimakon Ubangiji da ta dogara da shi. Tana tsaftace gidanta ko wane lokaci. Tana kula da kanta ƙal-ƙal, kullum cikin kwalliya take duk da babu mai yabawa.
A ranar da suka cika watanni biyu da aure tun asubah Sakina ta farka da wani irin amai da tashin zuciya, tun tana ɗaukan al'amarin da wasa, har dai da ƙyar ta iya amfani da wayarta ta kira Aunty Amina don ta duba ta bayan ta fara kaiwa ƙarshen galabaita.
A lokacin da Amina ta je gidan, Kamal ya gama barcinsa ya fito falo yana zaune a kan kujera yana cin abinci. Bai san me yake faruwa ba, a taƙaice tayi masa bayani sannan ta wuce ɗakin Sakina da sauri, shi kuwa ya raka ta da idanu.
Yana da gurin zuwa fa, amma haka kawai sai ya kasa fita. Zuciyarsa sai ta kwaɗaitu da son sanin abinda yake damun Sakinan, don haka ya cigaba da zama a falo yana jiran fitowar Amina ya tambayeta.
Sai dai kuma Minti biyar, goma, sha biyar, ashirin, har arba'in bai ga Amina ta fito daga ɗakin Sakina ba, don haka shi sai ya miƙe da zaƙuwa ya nufi ɗakin Sakinan.
Yana zuwa jikin ƙofar, har ya ɗaga hannu zai kama hannun ƙofar ya murɗa sai ya ji muryar Amina na tashi da karaɗin farin ciki da dariya. Don haka sai ya fasa buɗe ƙofar, ya kara kunnensa sosai ta jikin ƙofar da ba'a gama rufewa gaba ɗaya ba sai ya ji Amina tana cewa
"Alhamdulillahi Sakina. Ki gode ma Allah kawai, kina gani dai a karo na uku ga shi nan na sake gwadawa layuka biyu sun fito ɓaro-ɓaro. Ko ki yarda ko kada ki yarda kina da ciki, amma saboda in share miki tantama barin je gida in ɗauko abu in ɗebi jininki a gwada a asibiti, na san idan kika gani ta gwajin jini dole za ki yarda..."
Lokaci ɗaya hankalin Kamal yai masifar tashi bayan wani tunani ya ɗarsu a zuciyarsa, kamar zai shiga ɗakin, sai kuma yayi saurin barin gun kamar walƙiya kafin Amina ta fito.
Yana maƙale a bayan labule yana kallo Amina ta fice a gidan, tana fita, ya fito a haukace kamar bijimin zaki ya nufi ɗakin Sakina. Kallo ɗaya za a yima Kamal a hango gagarumin mahaukacin ɓacin rai a tare da shi.
Ya banke ƙofar ɗakin Sakina ya afka ciki, a kan kujera ya ganta tana kwance, ai kuwa baiyi wata-wata ba ya fincikota ya hurga kan gado sannan ya bita ya shaƙo mata wuya.
Muryarsa na fita sama-sama saboda ɓacin rai da masifa ya fara tuhumarta yana cewa
"Uban waye yai miki ciki????"
Ƙarshen free pages