Episode 11
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star
TALLAH TALLAH TALLAH
RC: 8578922
RABEJI
TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.
Connecting worlds, Building futures.
IATA Accredited Agent
NANTA
QATAR AIRWAYS القطرية
aero taking you safely
AIR PEACE ...your peace, our goal
MaxAir
SAUDIA السعودية
TURKISH AIRLINES
Kenya Airways The Pride of Africa
EGYPTAIR
AWA AFRICA WORLD AIRLINES
TRAVEL & TOURS
- Visa Facilitation
- Ticketing/Reservation
- Hajj/Umrah Packages
- Packaged Tours/Cruise
- Hotel Booking
- Chartered Flight
- Honeymoon Planning
- Car Hired Services Home and Abroad
- International Universities Admission & Facilitation
- Consultancy Services
OTHER SERVICES
- Furniture Making
- General Farming
- Properties and Real Estate
- Import and Export
- General Registration
- General Contracts
- Clearing and Forwarding
- Food and beverages
Office Address:
Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano
Email:
***
Phone:
***
***
Episode 11
Kallonsa tayi har ya zauna, zata mik’e domin d’akko masa abinci ya ce.
“Yi zamanki na d’akko ai kinyi nauyi ne Binta”
Murmushi ta saki tana komawa ta zauna ya d’akko abincin ya bud’e ya fara ci da bismillah yana ci ya d’ago yana cewa.
“Na shigo naga matan gidan nan sunata wasu surutai Allah dai yasa bada Binta tata suke ba?”
Murmushi tayi kawai tana cewa.
“Kai dai ko dai santi kake yi ne Abban Babawo?”
Murmushi ya saki shima yana girgiza kansa ya ce.
“Ai dole ne ma nayi santin kin san idan kikai girki kamar na k’arya chokalin fa haka nake ji dan dad’insa”
Dariya ta saki kad’an tana basar da zan can daya d’akko na tabbayar mike faru ya tadda matan gidan suna gutsiri tsoma kamar yadda suka saba idan suna so ayi tashin hankali?. Sai ta rink’a jansa da fira harya gama.
Yana cikin shan ruwa suka ji hayaniya kamar kukan Babawo a tsakar gidan, tare da muryar Inna Habi a sama-sama.
Da sauri Mama ta mik’e duk da nauyin cikin nata amma bata san lokacin data mik’e ba.
“A’a kamar muryar Babawo ko?”
“Shine naji kamar shida Inna Habi ne a waje”
“Ba makaranta ya tafi ba?”
Tana tafiya zuwa waje kusan a tare zasu nufi wajan ta ce.
“Ai kasan yanzu lokacin tashinsu yayi k’arfe kusan biyu da rabi, kuma jarabawa ya ce zasu fara ne shi yasa ba’a masu komai Yanzu”
Idasa fitowa sukai suna kallon yadda Inna Habi ta wanke Babawo da wani mari a dai-dai Lokacin da suka fito d’in, sai Sule a gefenta yana faman kuka.
“Ah ah Habiba mi yake faruwa ne?”
“Mifa zai faru? Marar kunyar d’an nan naka zai kama Sule da duka haka kawai k’arfinsu d’aya zaije ya nakasta min yaro?”
Da sauri Mama ta janye Babawo daga jikin Inna Habi dake mangare masa k’eya.
Wata uwar harara Inna Habi ta wurgama Mama tana fad’in.
“To sannu mai d’a na ce”
“Haba Habiba ai ya kamata ki tsaya kiji abunda ya had’asu ko?”
“Mi kake nufi ne Rabe ban San abunda nake yi bane ko mi?”
“Babawo miya had’aka da d’an uwanka?”
“Abba bashi bane na dawo daga makaranta kawai zan shigo gida na gansu shida abokansa shine ya fara jana da mai fitsarin kwance, shine abokan nasa suka d’auka suna ce min k’ato da fitsarin kwance ina tafiya suna bina suna ce min hakan, shine ni kuma na d’auki dutse na jefa masu shine ya fad’a akan Sule, daga nan yazo ya kamani da kokowa ni kuma na biye masa”
Wata irin ajiyar zuciya kawai Mama ta saki tana jin Inna Habi na sake fad’in.
“Aikin bazan aikin wofi, dan kawai sunce maka haka nan sai ka d’auki dutse ka jafa masu dan bak’ar zuciya irin taka?”
“Duk dai haka ai Habiba sune suka fara jansa. Dan haka sai kiyi ma shi Sulen fad’a gaskiya”
“Au Rabe ko rashin kunya zaka min akan na daki d’anka d’an gwal?”
“Bafa maganar rashin kunya a nan Habiba, yaga gaskiya a fili kuma sai a danneta?”
Wani kukan munafurci Inna Habi ta saki tana cewa.
“Ni kake gaya ma magana haka ina matsayin Matar wanka?, ahhh lallai Rabiu wallahi Binta ta gama da kai akanta da Yaron nan babu wadda bazaka iya yima rashin kunya ba”
Zaiyi magana Mama ta jawo hannunsa tare da Babawo dake jikinta har lokacin yana kuka Saboda yadda ta maresa cike da mugunta har inda ta mare san sawun hannunta saida ya fito rad’au gasu nan.
Baki sake Inna Dije data fito ta bisu da kallo tana fata hannu had’e da cewa.
“Ohh’ni y’asu yau ga lusarin namiji, ke duba fa yadda ta wani jashi ya kuma bita kamar wani rak’umi da akala?. Ba shakka Binta kinfa mori Malami wallahi”
“Ta kuwa mora, ki duba ki gani yanzu sai abunda ta ce, ta jashi ya bita zugi-zugi kamar wani sakarai”
“Yo kema Habi ai zama sakaran a wajanta”
Duk wata magana da sukeyi akan kunnansu Mama ita ke tausar Abban akan Mata ne su karya biye masu, sana akwai k’aracin ilimi Kama dana bokon harna iddini a tare dasu, saboda gaba d’aya matan gidan nasu y’an k’auye ne gaba da baya gashi ba ilimi shi yasa abun yayi masu yawa, Bintar ce kad’ai y’ar birni domin a Katsina ya auro ta ya kawota garin a lokacin yana da rufin asirinsa kamin komai yazo ya k’are suka koma haka…………
Book d’in nan na kud’i ne akan 1k kacal domin na kusa gama free pages hanzarta ka biya domin tafiyar da kai
Account number 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank
Shaidar biya👉 ***