GIDAN YAWA

Episode 12

by @zahraroyal

GIDAN YAWA

By

Zahra Royal Star

TALLAH TALLAH TALLAH

RC: 8578922

RABEJI

TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.

Connecting worlds, Building futures.

IATA Accredited Agent

NANTA

QATAR AIRWAYS القطرية

aero taking you safely

AIR PEACE ...your peace, our goal

MaxAir

SAUDIA السعودية

TURKISH AIRLINES

Kenya Airways The Pride of Africa

EGYPTAIR

AWA AFRICA WORLD AIRLINES

TRAVEL & TOURS

- Visa Facilitation

- Ticketing/Reservation

- Hajj/Umrah Packages

- Packaged Tours/Cruise

- Hotel Booking

- Chartered Flight

- Honeymoon Planning

- Car Hired Services Home and Abroad

- International Universities Admission & Facilitation

- Consultancy Services

OTHER SERVICES

- Furniture Making

- General Farming

- Properties and Real Estate

- Import and Export

- General Registration

- General Contracts

- Clearing and Forwarding

- Food and beverages

Office Address:

Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano

Email:

***

Phone:

***

***

Episode 12

A hankali Abba ya zauna kusa da Mama Oto yana murmushi had’e da gaida ita, bayan sun gama gaisawa ta nisa ta ce.

“Abunda yasa kaji ina nemanka haka, wata magana ce nazo da ita mai mahimmanci”

K’ara natsuwa Baba yayi sosai yana sauraran Mama Oto data k’ara gyara zama ta sake cewa.

“Akan yaran nan ne na wajanka Zahra da Bahijja, ina so su aje maganar karatun nan daga gefe azo ayi maganar aurensu, dan ina ganin shine kawai yafi, domin dama ai sun isa auren kuma dama mutumcin y’a mace ai gidan Mijinta, ku kanku sai hankulanku sunfi kwanciya”

Nisawa Baba yayi yana jinjina kai ya ce.

“Mama nima kusan maganar dana zo miki da ita kenan ai. Domin dai na tarasu su duka na tabbayi ra’ayinsu akan karatun, ita Bahijja ta nuna bata ra’ayinsa sai Zahra ta nuna tana son karatun sosai”

Jinjina kai Mama Oto tayi tana cewa.

“Ita Zahra d’in? Ai na d’auka ma su duka auren zasu d’auka dan Zahra kanta ya fara rawa gaskiya nifa hankalina sai yafi kwanciya a had’asu duka ayi bikin nasu rana d’aya gaskiya”

“Bank’i ta taki ba Mama, amma dai a duba ra’ayin kowa kuma Zahra ban tab’a ganin mai nutsuwa a cikin y’ay’ana ba irinta, Bahijjar ce dai mai rawar kai”

“Hmmm haka dai kuke gani amma ni da zaka ji ta tawa daka yi abunda na ce kawai”

“Mama adaiyi hakuri ko yaya ne ta fara karatun idan yaso ko tana cikin yin karatun sai azo ayi maganar auren nata idan Mijin yazo”

“To ai Shikenan tunda haka ka ce. Wacce magana ce zamuyi daka ce?”

K’ara gyara zama yayi ganin yau basuyi doguwar magana ba, batayi fad’a ba akan abunda ta kawo daya kawo mata maganar ra’ayin kowa dan da a birkicenta yazo ya sameta yasan ba wadda ya isa yasa Zahra ta wuce karatun nan, dan Mama Oton irin tsayayyun mutanan nan ne wadda idan suka yanke abu tofa sai anyi sai dai idan wani abu daga Allah kawai.

“Dama akan ita Bahijja ne. Mahaifiyarta ta ce gara na zab’a mata Miji da kaina basai mun bata damar zab’a da kanta ba, saboda har yanzu Bahijja bata da hankalin zab’arma kanta abunda ya dace da ita, kuma ba wasu samari ne dasu ba”

Mama Oto tayi jim sosai kamin ta sauke lumfashi ta ce.

“Kasan yaran zamanin nan ba’ai masu irin haka fa, amma dai maganarku gaskiya ce. To kai waye kake ganin zaka had’ata dashi?”

“Munyi shawara da mahaifiyarta akan mi zai hana a had’ata da Nura?”

Mama Oto ta kallesa sosai kamin ta ce.

“Wai Nura kake nufi d’an gidan Bawa?”

“Shi fa Mama nake nufi”

“Gaskiya yaron kirki ne kuma har Yanzu shima baiyi aure ba, amma dai irin wannan had’in sai naje gidan nasu naji shin baida wadda yake nema? tukunna idan babun sai yaje su gana da ita Bahijjar idan tayi masa itama yayi mata sun fahimci juna ai Shikenan dama haka akeso”

“Hakane Mama, to da kanki zakije gidan Kawu Bawan?”

“Insha Allah ni zanje da kaina shi kanshi Bawan zaiyi murna da hakan domin sake k’ulla zumunci ne ai”

“Shikenan Mama Allah yasa hakan ya zama alkhairi”

Da amin ta amsa kamin ta sake cewa.

“Amma ka sake zama da Zahra kaja mata kunne kar taga an bari zatai karatun bokayen turawan nan kuma ta ce ta samu saken da zata zubar mana da mutumci a cikin zuru’armu, sana data fara karatun itama ayi saurin aurar da ita ta idasa karatun a d’akin Mijinta, dan hakan sai yafi gaskiyar magana kenan”

“Insha Allah Mama yadda kika ce hakan za’ayi”

“To yayi Allah yayi maku albarka kaida zuru’arka baki d’aya”

Cikin jin dadi ya amsa yana mik’ewa ya ce.

“To ni Inna zan koma Allah ya bamu alkhairi”

“Har zaka wuce, bazaka tsaya kaci abincin rana ba gashi mai aikin tawa harta gama?”

“A’a Mama wani zuwan naci. Ashe Lantana tana nan?”

“Ai ko dai Lantana na nan ta rik’e aikin da kyau ai”

“Hakan yayi ai Mama. Toni na wuce”

Da addu’ar Allah ya tsare ta bisa. Mahaifinsu Bahijja shine d’anta na fari sai Jamila dake aure a Jigawa sai kuma Safiyanu dake aikinsa a Kano yana da k’arfi mai hali ne shi yana da mata d’aya da yara uku duk maza yanzu haka shi yasa aka d’akko mata y’ar aiki yake biyanta duk wata, duk da shima Mahaifinsu Zahra yana aikinsa na gwamnati yana kuma sayo kayan abinci duk wata ya dire mata ita kanta Jamila dake can Jigawa tana aiko ma da Mama Oto da wani abu duk wata saboda tana sana’o’i kala da kala kuma sana’ar ta amsheta tana samu sosai. Suna mugun shiri da Zahra domin har hutu tasha so zuwar mata can Jigawa, banda Bahijja basa shiri ko kad’an Aunty Jamilar ubanta take ci akan halin nan nata shi yasa basu cika shiri ba, ko gidanta bata zuwa tayi kwanaki mai tsawo sosai kamar yadda Zahra keyi. Safiyanu kuwa irin mutum ne shi wadda baya son mutane ko kad’an a rayuwarsa, daga matarsa sai Mahaifiyarsa su yafi sakar magana fuska ko suna idan matarshi ta haihu baya taran suna gidansa kuwa su Zahra bama sa zuwa amma Matarsa tana da kirki sosai Sai dai shine baya son mutane, Mama Oto tayi-tayi akan halinsa akan ya rink’a kula da y’an uwansan nan su biyu amma ina dan Jamila kam basa ko waya saboda bata son halinsa haushinsa take ji, Mahaifinsu Zahra ne kawai suke matuk’ar shiri da Jamila dan ta maida shi kamar Mahaifinsu tunda Mahaifinsu ya rasu shita taso ta gani kuma yana jawota a jiki, sab’anin Safiyanu da ba’a nan ma ya tashi ba a Kano yayi rayuwarsa harya gina iyalinsa sunaa can…………

Book d’in nan na kud’i ne akan 1k kacal domin na kusa gama free pages hanzarta ka biya domin tafiyar da kai

Account number 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank

Shaidar biya👉 ***