Episode 13
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star
TALLAH TALLAH TALLAH
RC: 8578922
RABEJI
TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.
Connecting worlds, Building futures.
IATA Accredited Agent
NANTA
QATAR AIRWAYS القطرية
aero taking you safely
AIR PEACE ...your peace, our goal
MaxAir
SAUDIA السعودية
TURKISH AIRLINES
Kenya Airways The Pride of Africa
EGYPTAIR
AWA AFRICA WORLD AIRLINES
TRAVEL & TOURS
- Visa Facilitation
- Ticketing/Reservation
- Hajj/Umrah Packages
- Packaged Tours/Cruise
- Hotel Booking
- Chartered Flight
- Honeymoon Planning
- Car Hired Services Home and Abroad
- International Universities Admission & Facilitation
- Consultancy Services
OTHER SERVICES
- Furniture Making
- General Farming
- Properties and Real Estate
- Import and Export
- General Registration
- General Contracts
- Clearing and Forwarding
- Food and beverages
Office Address:
Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano
Email:
***
Phone:
***
***
Episode 13
“Babawo mi yasa kake biye masu ne?, da kaga suna janka ai saika kyalesu kayi shigowarka gida, amma kai ba haka ba sai rashin hak’uri cike da ciki, to yanzu gashi nan rashin hak’urin naka yaja maka duka haka kawai”
Mama ta k’are maganar tana tab’a fuskarsa inda shatin hannun Inna Habi ya fito b’aro-b’aro.
“Uhmm Binta kenan, nifa banga abinda Babawo yayi ba da zata d’auke shi da Mari haka, idan gaskiya zata bi ai Sule ne ya kamata tayi ma wannan marin ba Babawo ba, amma da yake gidan nan kowa nasa ya sani ai”
“Hmm Abban Babawo kenan duk da hakan ya kamata kana masa fad’an hakuri da lamarin gidan nan, gashi dai ya fara girma tunda Secondary fa zasu gama”
“Ni wallahi ina wani tunani ne ma so nake yaron nan nasa shi makarantar aikin Soja ina son yayi aikin kaki kowanne iri ne”
“Walllahi Abba ina so dama yin Soja”
Babawo ya fad’a da fara’a kamar ba shine ke kuka yanzu ba.
Murmushi Abba ya saki ya ce.
“Karka damu insha Allah zakayi Soja”
Ganin yadda Mama tayi shiru tana kallon bakin k’ofar d’akin tunda aka d’akko maganar aikin Soja yaga yanayinta ya sauya a hankali ya ce.
“Babawo d’auki abincinka kaje waje ka ci”
Da to ya amsa yana d’auka ya fita, yana fita Abba ya matso kusa da Mama ya ce.
“Binta mi kike tunani haka?”
Sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa.
“Kai kana ganin Babawo zai iya aikin Soja nifa ina tsoron irin wannan aikin na zuwa yak’i lokaci d’aya ace ka rasa d’anka”
Ta k’are maganar cike da d’an tsoro akan fuskarta.
“Idan banda abunki Binta ai shi aikin Soja d’in nan ai taimakon k’asa ne kuma insha Allah ba abunda zai sami Babawo kuma abinda yasa na yanke hukuncin nan shine Babawo yana da taurin zuciya ga k’arfi tun yanzu baya d’aukar raini ina ji a jikina ba k’aramar gudunmuwa sai bayar ba a ciki”
“Hmm hakane Abban Babawo amma kai ta ina zaka fara nemar masa makarantar sojojin da kake magana?”
“Ai munyi maganar ma da abokina Hamisu d’ansa Sadiq ne zai tafi makarantar horan Sojojin shi ne na ce masa nima da zai taimaka min da an samar ma Babawo shine ya ce insha Allah karna damu zaiyi magana kuma tare zasu tafi dashi Sadiqun yaron wajansa”
“To ashe ma harkun gama magana kenan?”
“Mun gama gaskiya shi dai nake jira muji daga gare sa”
“To amma ba sai sun gama wannan makarantar ba?”
“Sai sun gama ai aji d’aya suke dashi Sadiq d’in kuma naga gaf suke da zana jarabawa ta kammala secondary school shi yasa ma ya fara nemar masu kuma yana da hanya ne”
“Hakane amma ni Babawon ne nake ganin kamar ma yayi k’arami da gama secondary d’in nan fa”
“Injiwa ya gaya miki Babawon da yanzu zai shiga shekara ta 18 inaga?”
“Kai Abban Babawo ai na d’auka bai wuce 15 fa?”
“A’a kin dai manta dai ki duba takardar haihuwarsa amma ai ko a jikinsa ansan ya wuce hakan”
“Ai kasan jiki bashi bane shekaru sai kaga mutum babba amma ba wasu shekaru garesa ba”
Zaiyi magana suka ji magana a k’ofar d’akin.
“Wai Kawu Rabiu kaje inji Kawu Bature yana turakarsa yana jiranka a can”
Cewar Kabiru yana fad’a ya k’ara gaba abunsa.
“Neman mi ake maka haka tsakiyar ranar nan?”
“Nima ban sani ba, bari naje naji miye”
Ya fad’a had’e da mik’ewa tsaye ya fita.
Saita bisa da kallo tana tunanin Allah yasa dai ba Inna Habi ce taje ta had’a wani abun ba dan yadda taga ta fashe da kukan nan dama tasan sai abun yaje kunnan Kawu Baturen. Ita ta rasa abunda ta tsare ma mutanen gidan nan wadda har ya shafi d’an uwansu haka?………
Book d’in nan na kud’i ne akan 1k kacal domin na kusa gama free pages hanzarta ka biya domin tafiyar da kai
Account number 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank
Shaidar biya👉 ***