GIDAN YAWA

Episode 14

by @zahraroyal

GIDAN YAWA

By

Zahra Royal Star

TALLAH TALLAH TALLAH

RC: 8578922

RABEJI

TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.

Connecting worlds, Building futures.

IATA Accredited Agent

NANTA

QATAR AIRWAYS القطرية

aero taking you safely

AIR PEACE ...your peace, our goal

MaxAir

SAUDIA السعودية

TURKISH AIRLINES

Kenya Airways The Pride of Africa

EGYPTAIR

AWA AFRICA WORLD AIRLINES

TRAVEL & TOURS

- Visa Facilitation

- Ticketing/Reservation

- Hajj/Umrah Packages

- Packaged Tours/Cruise

- Hotel Booking

- Chartered Flight

- Honeymoon Planning

- Car Hired Services Home and Abroad

- International Universities Admission & Facilitation

- Consultancy Services

OTHER SERVICES

- Furniture Making

- General Farming

- Properties and Real Estate

- Import and Export

- General Registration

- General Contracts

- Clearing and Forwarding

- Food and beverages

Office Address:

Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano

Email:

***

Phone:

***

***

Episode 14

BAHIJJA POV

“Ke Bahijja dan ubanki wato abunda kika zab’a kenan wai aure kina y’ar haka dake?, dube ki fa?, ina miki kallon mai hankali ashe baki dashi?”

Turo baki tayi tana k’unk’uni k’asa-k’asa

“Kaima dai ka gani Safiyanu gata nan dai wai ita nan a hakan harta san aure duka yaushe aka haufe ta ma?”

Umma ta fad’a da mamaki.

Safiyanu ya zauna akan kujerar parlo ya ce.

“To ai ita tayi ma kanta yanzu dai gashi nan har an samarma Zahra makaranta naje kankia na gama mata komai ga takardun makarantar nan kina dai gani, Lokacin da zata fara kwasar albashi zakiyi mamaki ne, ko ni da kike gani na nan bana son wahala dole tasa na dage ina karatun nan gashi harna kusa had’a degree d’ina kuma ina aikin k’arfi duk dan ina son rayuwar jin dad’i ai dole Sai an had’a da karatun. Ni shi yasa ma Umma da kike fad’an wai halinmu d’aya da wannan mahaukaciyar nake jin ba dad’i”

“Ni dai ba haukaciya ba ce wallahi”

Bahijja ta fad’a can ciki tana murgud’a baki.

“Mi kika cewa ne naji kamar kinyi magana marar kunyar banza?, ni ba Zahra ba ce da zan tsaya kina gayan magana banci ubanki ba wallahi”

“Ya isa haka Safiyanu dan Allah. Yanzu dai ba Zahra takardunta ta adana please ka tashi kaje”

“Umma bata da kunya ne wallahi, wai haka za’ai mata aure?, ai ko dole bakin rashin kunyar nan ki saita shi domin ba’aima wani namijin hakan idan ba haka ba ya sallamoki gida”

“Ohh’ni Safiyanu wai baza kai shirun ba dana ce shin?”

“Ke Zahra ga takardunki ranar Monday zaki fara zuwa school sana kayan makarantar naki na kaisu d’inki wata k’ila gobe naje na amso na kawo miki”

“Tom Yaya na gode”

Bai sake magana ya fice Umma ta bisa da kallo tana girgiza kai zam halinsa halin mai sunansa wato Kawunsa Safiyanu.

Tashi Bahijja tayi ta shige uwar d’aka tana tab’e baki ko a jikinta tana jin Zahra na d’okin fara zuwa school amma ita ko a jikinta.

Baba ne ya shigo gidan kai tsaye parlon ya shigo. Zahra na gaida shi ya amsa da sakin fuska Umma ta mik’e tana kawo masa ruwa da abincinsa ta aje tana cewa.

“Harka dawo yau da wuri haka?”

Yana shan ruwa bayan ya sauke ya ce.

“Yau da wuri na tashi wajan aikin na biya wajan Mama Oto munyi magana da ita akan auren Bahijja da Nura”

Gyara zama Umma tayi Zahra dama tuni tabar parlon ta shiga uwar d’aka ta basu waje.

“To Mlm ya ake ciki?”

“Eh gaskiya munyi magana da ita sosai kuma taje gidan Bawan yaji dad’i sosai kuma ya amince dan har cewa yayi koda Nura d’in nada wacce yake so dole ya had’a da ita Bahijjar”

Ya d’an lumfasa yana kallon Umma sosai yadda take jinjina kai ya sake cewa.

“To da dai naso na katse Mama Oton da cewar gaskiya idan har yana da wacce yake so d’in a kyale maganar kawai, to kuma sai ta ce a nan aka kira Nuran Mahaifinsa ya tabbayesa cike da kunya Nura ya ce shi gaskiya yanzu bashi da wacce yake so, sosai Mahaifin nasa yaji dad’i domin Allah ya sani tunda Mama Oto tazo masa da maganar yaji had’in ya shiga ransa kuma yana son auren had’in. Shine Mahaifin nasa ke masa bayanin yaje yaga y’ar gidan nawa ita Bahijja su dai-daita kansu. To dai Yanzu maganar da nake miki yana nan zuwa gobe ko jibi”

Sauke lumfashi mai d’umi Umma tayi kamin ta ce.

“Tom Masha Allah, Allah ya kawosa lafiya, yasa a dai-daita kuma”

Da amin Baba ya amsa yana ci gaba da cin abincinsa.

Tashi Umma tayi tana shigewa d’akin inda suke.

Zahra na k’asa zaune Hamshakiyar taku na saman gado tana latsa wayar Umma a hannunta.

“Mi kike min a cikin waya?”

“Umma kallo fa nake”

Zama Umma tayi Akan wata kujera ta madubi ta ce.

“Aje wayar nan ina son magana dake”

Ajewa tayi tana mik’ewa zaune tana kallon Umma d’in.

“Gobe ko jibi zakiyi bak’o kuma shine muka zab’a miki a matsayin miji, saura idan yazo don Allah kayi masa shirme da rashin kunyar nan taki. Sana Bahijja ki shiga hankalinki aure zakiyi duk wata rashin kunyarki da shiririta tun a nan ki ajesu, domin auren ba abun wasa bane, sana kuma auren naku idan har kun dai-daita kanku ba wani jansa za’ai ba”

Jinjina kai tayi kamar wata mai hankalin a lokacin.

“Ke kuma Zahra zan k’ara jaddada miki cewar kiyi tsaya kiyi karatu shine ya kaiki ba shashanci ba, duk da nasan ke mai hankali ce ba irin y’ar uwarki ba, domin nasan kin fita natsuwa da hankali da fahimta,to dan Allah karki watsar da tarbiyyar da muka baki, sana kin san da sanin kema kina fara karatun idan har miji yazo tofa dole kiyi aure idan yaso kina gidan Mijinki kin k’arasa karatun naki”

“Insha Allah Umma zaku same ni mai rik’e maku amana fiye da yadda bakuyi zato ko tsammani ba insha Allah”

“To yayi Allah yayi maku albarka”

Da Amin suka amsa ta tashi ta fice, tana fita Bahijja ta mik’e tana murmushi kamar gonar auduga tana cewa.

“Yaya Zahra wai kin san waye su Umma ke son had’ani dashi?”

“A’a ya zan sani Bahijja tunda bata gaya mana ba?”

“Ni dai naji ance kamar Nura idan wadda na sani ne d’an uwanmu d’in nan to tabbas ina sonshi wallahi”

“Au nan har kinji waye ma kenan?”

“Eh naji mana, nasan kema ai kinji daga can parlon ai ana jin komai daga nan”

“Hankalina ni baya wajan Bahijja, amma dai wanne Nuran kike nufi ke?”

“Dan gidan Muhammad Bawa mana”

Jinjina kai kawai Zahra tayi tana sakin murmushi ta ce.

“Ai ko idan har Ya Nura ne tabbas na tayaki murna domin kowacce mace zatai murna da samun kamar Ya Nura”

Ta k’are maganar da farin cikin taya y’ar uwarta murna.

Sai taga kuma Bahijjar ta sha kunu tana tab’e baki.

Girgiza kai kawai tayi tana kallon Bahijjar dake magana k’asa-k’asa tana jinta tana cewa.

“Haba yabon ya isa haka, Nura ne dai nawa ne ya kuma haramta gare ki a’ato”

Tana k’unk’unin nata ta koma ta kwanta tana juya ma Zahra baya. Zahra na mamakin hali irin na Bahijja kamar abun arzik’i sun fara fira Amma ji yadda ta sauya fuska lokaci d’aya?. Yo ita Allah na tuba bata jin ko mutuwa Bahijjar tayi Yanzu zata amince ta auri wani Nura.

Girgiza kai ta k’ara yi tana ci gaba da abunda take yi kawai, dan tasan idan har Bahijjar data sani ce zatayi abunda yafi haka………

Book d’in nan na kud’i ne akan 1k kacal domin na kusa gama free pages hanzarta ka biya domin tafiyar da kai

Account number 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank

Shaidar biya👉 ***