GIDAN YAWA

Episode 15

by @zahraroyal

GIDAN YAWA

By

Zahra Royal Star

TALLAH TALLAH TALLAH

RC: 8578922

RABEJI

TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.

Connecting worlds, Building futures.

IATA Accredited Agent

NANTA

QATAR AIRWAYS القطرية

aero taking you safely

AIR PEACE ...your peace, our goal

MaxAir

SAUDIA السعودية

TURKISH AIRLINES

Kenya Airways The Pride of Africa

EGYPTAIR

AWA AFRICA WORLD AIRLINES

TRAVEL & TOURS

- Visa Facilitation

- Ticketing/Reservation

- Hajj/Umrah Packages

- Packaged Tours/Cruise

- Hotel Booking

- Chartered Flight

- Honeymoon Planning

- Car Hired Services Home and Abroad

- International Universities Admission & Facilitation

- Consultancy Services

OTHER SERVICES

- Furniture Making

- General Farming

- Properties and Real Estate

- Import and Export

- General Registration

- General Contracts

- Clearing and Forwarding

- Food and beverages

Office Address:

Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano

Email:

***

Phone:

***

***

Episode 15

Sallama yayi bakin k’ofar, Yaya Bature yayi gyaran murya alamar ya shigo.

Zama yayi a k’asa yana cewa.

“Ance nazo kana son ganina?”

“Eh na ce kazo ne dan naji miye had’inka da iyalina da har zaka tsaya kana fad’a tana fad’a kamar wasu sana’annin juna?”

Da sauri ya d’ago yana duban Yaya Bature da yayi kamar ba shine ya jefo masa tabbayar ba. Da zallar mamaki yake Jinjina kai yama kasa magana.

“Dole zaka min shiru mana kana jinjina kai, tunda kasan rashin darajar daka tabka. Kai Yanzu Rabiu kamar ni matata zaka tsaya kana ma rashin kunya?”

Nisawa Abba yayi yana jin b’acin rai na taso masa. Ace su da an tab’asu kamar an tab’a gwal wato shine karkatacciyat kuka mai dad’in hawa wato a gidan?.

“Kamin shiru kana ji ina magana?”

“To amma Yaya Bature ita Habibar bata fad’a maka abunda ya faru bane?, ni ban mata rashin kunya ba, tunda ba halina bane kafi kowa sani kuma”

“Ah ah ni ya za’ai na sani Rabiu? Ko waccar matar taka da aketa fad’a ita ce ke zugaka kana ma na gaba da kai rashin kunya?”

“Ni Binta bata tab’a cewa naje nayi maku abinda ba dai-dai ba, bare har ta zugani, hasalima kullum k’ok’arinta shine taga na kyautata maku, amma ace kullum laifinta kuke gani”

“Ahh gaskiya ashe abunda aketa fad’a akan matarka gaskiya ne?, cewar ta mallake ka ashe gaskiya ne?, Ina fad’a kana fad’a hakan an fad’i laifin matarka y’ar gwal hala?”

Cike da b’acin rai Abba ke duban Yaya Bature dake abu kamar Mace wa’innan maganganun ai na mata ne ba wai ace kamar Yaya Baturen zai zauna yana yinsu ba.

“Yaya Bature irin wa’innan maganganun bai dace damu ba, wannan tsegumin ai na mata ne, kuma ni ba wani abu na ce ma Habiba cewa nayi kawai ta had’esu da Sule dashi Babawon tayi masu hukunci shine fa kawai”

“Sannu Sarkin iya zance na ce sannu ko wadda yasan dai-dai”

Abba dai bai sake magana ba yabar Yaya Bature sai mita yake wadda da ba halinsa bane amma zama da mata fiye da biyu sun koya masa halin da ba nashi ba.

Saida ya gama fad’ansa tukunna Abba yayi masa sallama ya fito baya jin ma ya amsa sallama tashi ya baro inda yake cike da mamakin wannan abu na gidan nasu.

************ “Amma tsakani da Allah Dije yanzu kuna ganin Akuyar nan ta nufi wajan da Binta ta baza Masarar nan data surfa bazaku kore ta ba?, dubi Yanzu yadda ta kusan cinye rabin Masarar domin Allah kuna zaune kuna gani kuma?”

Tab’e baki Inna Dije tayi tana cewa.

“To y’ar iya, y’ar son a sani mai mutumci da imani, ai gaki nan kin fito Yanzu ko sai ki korar mata Akuyar ai ko?, ko kuwa mune y’an aikinta data aje muyi mata tsaron Masara?, ai tasan dai gidan nan da Dabbobi bawai babu ba, kuma ai kiwansu muke yi”

“Ke rabu da ita dallah ni wallahi wai Sakina mi kike ji dashi ne a gidan nan shin da har kike shige ma Binta?”

Inna Sakina data matsa ta kori Akuyar tana cewa.

“Ba wani abu da nake ji dashi ba, illa gaskiya ce nake fad’a maku ba wani abu ba, kuma dama ance gaskiya ai d’aci ne da ita”

Mama ce ta fito da sauri hankalinta a tashe domin surfe aka kawo mata dama ta surfata shine ta bazata a k’ofar kusa da d’akinta ta shiga yin sallah kuma harga Allah ganinsu zaune wajan ta d’auka bazasu bari wani abu ya tab’a masarar ba. Ai bata d’auka k’iyayyar da suke mata ta kai haka ba, wato mutanan gidan nasu kullum k’ara shayar da ita mamaki suke, ita kam wai mita tare masu wai shin?……….

To a masu karatu a nan zan tsaya free pages sun k’are maza hanzarta ka biya domin tafiyar da kai, domin Yanzu aka fara tafiyar. Kunsan AL’KALAMI NA baya rubutun banza……✍️

Book d’in nan na kud’i ne akan 1k kacal domin na kusa gama free pages hanzarta ka biya domin tafiyar da kai

Account number 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank

Shaidar biya👉 ***