RAI DA SO

Fita ta 1

by @kwalisa

                MARIYA

Wata tsohuwar motar tasi tana tafiya da qyar kamar wacce ake turawa da hannu tana tittilar da hayaqi ta salansal kamar ana gobara ta tsaya a qofar wani munafikin lungu, bata jima da tsayawa ba wata figaggiyar tsohuwa ta buxe qofar gaba na motar ta fito tana faman tsane gumi da wani yanqwananen tsuma.
A lokacin qofar baya na motar ya buxe wasu samari biyu suka buxe qofar gidan baya suna muzurai da idanunsu, basu yi wata-wata ba suka kamo qugun wani figagen matashi da yake faman fizge-fizge yana sambatu shi kaxai.
Figaggiyar tsohuwar ta buxe jakar dake hannunta ta zaro wata yanqwananiyar naira xari biyar ta miqawa mai motar cikin tsiwa tace masa.
“Malam yi maza ka bani canji, na bar wajen nan tun kafin mutane su soma xebo qasa suna yiwa motar atule” Ta zunvura baki gaba.
Direban ya yi gaggawar amsar xari biyar xin ya zaro wata naira hamsin ya miqa mata yana faxin.
“Dana san haka kuke da masifa ai babu abinda zai saka na xauko ku” Ta dube shi da motsatsiyar fuskarta mai kama da an taka tunfafiya cikin tsiwa tace masa.
“Dole ashe ana tsoron inna in ji ‘ya ‘yan mayya, kaxan ma ka gani malam maza ka janye mana wannan gidan biredin naka daga kan layi” Xan tasin ya zaro idanu ya soma qoqarin sakawa motar giya yana faxin.
“Allah ya haxani da jarrababiyar tsohuwa”.
“Ni ce ma alaqaqai qashin cikin tukunya, na qi shiga na qi fita, ai nan gani nan qyalewa haka za ka qare da wannan tsohuwar motar taka ita ce ajalinka” Shi dai ya soma tafiya yana faxin.
“Allah ba ki haquri” Ta bishi da ruwan bala’i.
“Haquri hatsin cikin tukunya ne, qarewa yake da wuri,ba dai ni ka ke cewa masifafiya ba ka je zaka ga masifa akan ka” Shi dai yaja motar ya yi gaba ya barta tana ruwan bala’i.
Ta nufi qofar shiga wani ruvavven gida ginin jar qasa,wanda yake barazanar faxowa kan mai tsautsayi a tsakar gida ta samu samarin biyu sun jingina saurayin da suka kamo, tun kafin ta qarasa shiga wata matashiyar mace ta fito daga cikin wani ruvaven xaki.
Kallo xaya zaka yi mata za ka fahimci tana cikin wahalar rayuwa, domin duk kayan da suke jikinta sun jeme sun koxe sun koma kamar jemamiyar fata, haka tsananin wahala yasa duk ta fita daga hayyacinta, cikin sauri ta qara so wajen matashin da aka jingina a jikin ginin jar qasar idanunta cike da qwalla.
“Har kun dawo…?” Bata qarasa magana ba tsohuwar nan ta yi saurin qarasawa wajen da take ta saka hannuwanta biyu masu kama da icen makara ta hankaxe ta,yaraf! Kamar yaron da citar shan inna ta kama ta faxi gefe a cikin wani dagwalon ruwa daya ke tsakar gidan.
“Kar ki tava min xana,tsinaniya matsiyaciya yau alqadarin ki ya karye, tunda yaron nan ya aure ki shi kenan ya tsiyace ya lalace” Ta dubi samarin dake tsaye carko-carko kamar zakaru sannan ta maido kallonta zuwa ga Mariya dake yashe a tsakar gidan.
“Ai yau kwanan ki na qarshe a cikin gidan nan kenan, mai farar qafa”.
Mariya dake yashe a tsakar gidan ta xago idanunta wanda suke cike da kwalla ta dubi masifafiyar tsohuwar, bata iya furta komai ba sauran hawayen da suke maqale akan fuskarta suka qarasa zubowa.
Tun tsawon lokaci take zaman haquri a gidan nan, ba daxin zaman auren take ji ba, saboda wannan matar ba qaramin quntatta rayuwarta ta yi ba. Kullum ta Allah sai ta aibata ta, ba ta da wani buri a rayuwa face ganin ta quntatta ma ta.
“Ki yi haquri Umma…” Ta xaga mata hannu.
“Ba maganar haquri, ina zan ci gaba da zama da mai farar qafa? Ai daman sai dana faxawa yaron nan kar ya sake ya aure ki, domin maza biyu kika aura amman ya kafe qarshe dai ga abinda ya jawowa kansa” Ta matsa kusa da shi tana laluba aljihunsa can ta xauko wata takarda ta jefawa Mariya.
“Ga takarda sakin ki nan matsiyaciya, sai ki koma gidan ku can wani mai rabon shan wahalar ya kwasa”.
Wani baqin ciki ya mamaye zuciyar Mariya damuwarta ta dawo sabuwa, sauran hawayen dake cikin kwarmin idanunta suka qarasa mamaye fuskarta, wannan rayuwar dame tayi kama? Ita kuma haka tatta qaddara ta ke?
Ta miqa hannunta cikin karkarwa kamar ana yi mata kixan gangi ta xauki takarda sannan ta rarrafa da jan gindi kamar mai koyon tafiya ta qarasa zuwa gabansa tana dubansa a hankali tace masa.
“Mijina wai ka sake ni?” Tana dubansa da idanunta.
Shiru ya biyo baya na taqin lokaci, bai bata amsa ba sai qura mata ido da ya yi kamar bai tava ganinta ba.
“Kaji min shaixaniyar ‘ya…” Ta zaburo kanta ta kuma kai mata duba qum! Ta yi mata wani dundu a gadon baya, Mariya ta saki qara domin ji data yi kamar an saka kofaton doki an bugar mata baya.
“Yau naga mayyar yarinya, to kai faxa mata cewar ka saketa” Tana kallon xan nata dake zaune kamar gunki.
Mariya dake zube a qasa tana dafe da gadon bayanta ta kuma taxowa cikin tsananin takaici, har lokacin hawaye suna ci gaba da zuba a idanunta.
“Ki yi haquri matata Mariya, zan rabu dake ba don ina son ki ba sai don mallamin da Inna ta kai ni wajen shi yace dole na rabu dake domin ke mace ce mai farar qafa… saboda na aure ki shi yasa na tsiyace haka… don haka na sake ki saki…” Mariya bata qarasa jin sauran bayanin nashi ba tayi saurin toshe kunnuwanta.
Amman duk da hakan data yi hakan bai hanata jin adadin sakin da ya yi mata ba.