RAI DA SO

Fita ta 2

by @kwalisa


               BASHIR 

 A hankali kamar maciji wata baqar mota ta sulalo ta samu matsuguni a harabar farfajiyar asibitin, bayan ta samu matsuguni tsayin wasu mintina kafin qofar motar ta buxe a hankali, wani matashi xan kwalisa ya sako qafafunsa waje kafin a hankali shima ya qarasa fitowa.
Fuskarsa tana sanye da wani baqin tabarau wanda ya taimaka wajen voye damuwar dake shimfixe akan fuskarsa.
Kai tsaye ya wuce cikin asibitin, bai tsaya a ko ina ba sai qofar ofishin likita, ya tura haxi da sallama ya shiga.
Wani dogo siriri kamar takanxa ya xago ya dube shi da motsatsiyar fuskarsa kamar an taka tunfafiya, ganin shigar Bashir ya saka bakinsa ya qara washe wa zuwa murmushi, kafin ya amsa sallamar da ya yi tare da miqa masa hannu suka gaisa cike da shauqin ganinsa.
“Kamar kasan kai nake zaman jira” Ya faxa masa har lokacin hannun Bashir yana cikin nasa.
“Cinkoson ababen hawa ne ya hanani qarasowa akan lokaci” Ya faxa yana zama.
Likitan ya gyaxa kai kamar qadangare sannan ya jawo wata takarda yana dubawa bayan wasu sakani ya xago qwayar idanunsa ya dubi Bashir yana xan yamutsa fuska, kamar ba zai yi magana ba.
“Har yanzu dai abinda muke son samu bamu same shi ba” Ya xan yi shiru yana kallon fuskar Bashir sannan ya miqa siraran ‘yan yatsun hannunsa ya xauko biro yana juya shi a tsakanin tsintsiyar hannunsa sannan ya ci gaba da magana.
“Yanzu ma kamar ko wane lokaci zan ci gaba da faxa maka cewar, yana da kyau ka sakawa zuciyarka dangana duk abinda Allah ya qaddara zai faru ya riga ya faru, ita mutuwa xaya ce kuma wanda ya mutu ba zai tava dawowa ba” Bashir ya xago a hankali ya dubi likitan sannan ya kauda kai zuwa gefe, idan da sabo wannan ba shi ne karo na farko da wannan motsatsen likitan ya ke faxa ma sa waxannan kalaman ba.
“Likita ba zan iya cire son Zainab daga cikin raina ba” Ya faxa a taqaice, bayan xan shiru ya ci gaba da magana cikin kwantar da murya.
“Bana iya barci sai na kuna kaset xin bikin mu na kalla, haka nan dana tashi daga barci bama samun nutsuwa sai na xauko kundin hotunanta na kalla, sau nawa zan faxa maka ba zan tava iya daina tunaninta ba” Dogon likitan ya saukar da ajiyar zuciya.
“Nima ba cewa na yi ka daina tunaninta ba, amman ka dubi irin halin daka shiga a rashinta, wannan ciwon naka dole sai ka daina sakawa ranka damuwa sannan za mu samu nasara akan samun lafiyarka” Bashir ya yi murmushi.
“Ba zan tava daina tunanin matata zainab ba”. Ya faxa yana xan buga tebur xin da xan yatsansa.
“Ni kaina nasan abu xaya ne zai saka na daina damuwa” Ya kalli idon likitan shima ya qura masa ido.
“Mene shi?” Likitan ya tambaya jin shirun yana neman yin yawa.
“Idan zaka iya bani maganin da zai dawo min da Zainab a raye” Cikin tsananin kaxuwa likitan ya dube shi baki buxe.

Cike da damuwa Bashir ya baro wajen likitan ya na tafiya akan titi duk qwaqwalwarsa ta cika da tunani kala-kala shi kansa yasan tuqin kawai yake yi amman rabin hankalinsa baya kan titin. A haka ya zo daidai hanyar da zata kai shi unguwar Briged don haka sai ya saka sigina ya shiga daidai kwanar ‘yan kaji Mariya dake tafe hankalinta a tsananin tashe tafiya kawai take yi sam bata san wajen da take saka qafarta ba har ta hau tsakiyar titi sam bata sani ba.
Kamar daga sama Bashir yaga ta faxo tsakiyar titi, cikin tsananin razana yaja wani birki amman duk da haka sai daya xan tava ta, Mariya ta xago kai ta dube shi, shima yana daga cikin motar ya dubeta.
Kallon xaya daya yi mata yasan tana cikin tsananin tashin hankali, bata kuma bi ta kanshi ba sai ta yi gaba abinta.
Bashir ya bita da kallo cike da mamaki, ko ita kuma me yake damunta? Yasan dai banza bata kai zomo kasuwa, da ganinta tana cikin tashin hankali.
Bai kuma bi ta kanta ba ya sakawa motar giya ya soma tafiya yana yiwa Allah godiya da bai qaddara tsautsayin a kan shi yake ba. A haka har ya qaraso inda ya nufa wajen malaminsa da yake ba shi taimako game da harkokin kasuwancin sa.
A shagonsa ya same shi malam Yusuf matashin gardine xan kimanin shekara talatin, tun sanda matar Bashir ta rasu yake qoqari wajen yi masa rubutu yana ba shi duk a cikin qoqarin ganin ya mance da marigarya.
Amman duk da wannan qoqarin da yake yi sam babu wani ci gaba, domin kullum ta Allah akwai wani abu na daban da Bashir xin yake zuwar masa da shi.
A lokacin da Bashir xin ya qarasa qofar shagon ya samu waje ya yi fakin xin motar ya yi shiru yana kallon qofar shiga cikin shagon nan take wani tunani ya ziyarci zuciyarsa.

Wata rana sun tava zuwa wajen malam Yusuf da Zainab saboda matsala aljanu da suke damunta tana yawan fama da wasu munanan mafarke-mafarke harma ta riqa zabura a cikin barci, sai kuma wani tsananin ciwon kai mara sauka daya adabeta.
Hakan ya saka ya xaukota takanas ta kano ya kawota wajensa, lokacin da suka zo layin sai ta dubeshi cikin damuwa.
“Ni bana son unguwar nan” 
Bashir ya dubeta da murmushi.
“Me yasa?” Ta xan kalli gefe.
“Shi kenan dai”.
“Da kin faxi abinda yake ranki dai”.
“Ni dai kawai mu koma gida, kaina ya daina ciwon” Suka qarasa cikin layin ya tsaya a qofar shiga shagon.
“Sai da muka zo sannan za ki ce kin fasa, ki daure dai mu shiga kawai addu’a zai yi miki shi kenan” Zainab ta yi murmushi. 
“Mijina kenan, ai tunda na faxa maka ba zan shiga ba kasan ba zan tava shiga ba” Bashir ya xan yi shiru na taqin lokaci sannan ya ce mata.
“To bari na shiga wajensa na fito”.
“Dama hakan ya fi maka, ni dai ina nan zaune ina jiranka idan kuma ka daxe zaka dawo ka samu bana nan” Cikin sauri ya buxe motar ya fita.
Ko daya shiga wajen malam Yusuf sai ya same shi a zaune yana zane-zane akan rairayi, bayan sun gaisa sai ya dube shi ya yi murmushi tare da faxin.
“Ina uwar gidan kuma?” Bashir ya dube shi cike da mamaki domin bai faxa masa cewar za su zo ba, ganin ya na yi masa kallon mamaki sai ya qara cewa da shi.
“Ko ba kwana tayi tana ciwon kai ba?” Cikin sanyi jiki Bashir ya ba shi amsa.
“Haka ne”.
Sai ya qara yin murmushi ya ci gaba da zane-zanen shi sannan ya qara cewa da shi.
“Yanzu ma da kuka zo ai cewa tayi dakai ba zata shigo nan ba, daman ai ba za su barta ta shigo ba” Bashir ya dube shi cikin kaxuwa.
“Saboda me?”
“Aljanun ne suka hanata…”

Bashir ya saukar da ajiyar zuciya, bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya shiga sannan a hankali ya buxe qofar motar ya zuro qafafunsa waje, ya jima a zaune qafarsa a qasa kafin ya fito daga cikin motar.
Ya nufi qofar shiga cikin shagon yana zuwa ya qwanqwasa tare da yin sallama, daga cikin shagon aka amsa masa tare da bashi izinin shiga cikin shagon, Bashir ya shiga tare da qara yin sallama ya samu Malam Yusuf a zaune akan wani buzu yana jan carbi.
Ya miqa masa hannu suka gaisa fuskarsa cike da fara’a ya samu waje ya zauna, malam Yusuf ya qarasa janye sauran ‘ya ‘yan carbin da suka rage sannan ya ajiye carbin.
“Malam Bashir ya qarin haquri?” 
“Haquri sai ma’aiki”.
“Allah ya ji qansa”.
“Allahuma amin” Suka yi shiru na taqin lokaci.
“Ya kasuwar taka kuma?” Bashir ya gyara zama.
“Kasuwa mun gode Allah, harkoki suna tafiya yadda ake so” Malam Yusuf ya jinjina kai.
“Haka ake so” Ya xan yi shiru sannan ya kuma xauko carbinsa yana xan juyawa a hannunsa sannan ya ci gaba da magana.
“Kana dai shan rubutun nan da nake bayarwa a kawo maka?” Bashir ya gyaxa kai.
“Eh ina sha amman har yanzu ban daina ganin zainab ba, har yanzu duk lokacin dana shiga falon mu sai naganta a zaune tana yi mun murmushi, haka ma idan na shiga wanka sai ta zo ta tayani, hakan nan tana zuwa ta tayani kwana” Malam Yusuf ya yi shiru kawai yana kallonsa cike da mamaki.
“Duka marigayar kake gani tana yi maka waxannan abubuwan?”
“Eh”
Malam Yusuf ya yi murmushi, tare da dafa hannun Bashir.
“Bashir wanda ya mutu ai ya riga ya mutu baya tava dawowa”.
“Nasan da haka, amman wallahi Zainab nake gani”. 
Malam Yusuf ya kalle shi cikin tausayawa, sannan cikin kwantar da murya ya ce masa.
“Bashir kana yin addu’o’in dana baka kuwa?”.
“Wane kenan?” Shima ya mayar masa da tambayar.
“Wacce da wacce na baka ma tukuna?”.
“Dana kwanciya barci dana tashi daga barci dana fita daga gida dana shiga abin hawa dana saka kaya da…” Ya xaga masa hannu.
“Ya isa haka” Ya faxa yana sauke wani numfashi.
“Amman kuma duk da haka baka daina gane-ganen marigaya ba?”
“Shakka-babu” Malam Yusuf ya miqa hannu ya jawo wani allo dake xauke da rairayi ya xan soma zane-zane zuwa wani xan sakani sannan ya furza da wani huci ya xago kai ya dubi Bashir.
“Kafin ka zo nan kun haxu da wata?” Bashir ya dubeshi cikin mamaki.
“Ban haxu da wata mace ba”.
Malam Yusuf ya yi murmushi, tare da ci gaba da zane-zanensa yana yin murmushi ya qara cewa da shi.
“Tuna dai tabbas kun haxu da wata, kamar tana cikin tashin hankali…” Bashir ya katse masa magana cikin sauri.
“Eh na kusa buge wata da mota, ga alama tana cikin tashin hankali”.
Malam Yusuf ya dakata da dubansa.
“Wannan ita ce maganin matsalar ka, ita zata saka mancewa da marigarya, sai dai matsalar xaya” Ya xago cikin jimami yana kallon fuskar Bashir sannan ya ci gaba da magana.
“Ta yi aure-aure har guda huxu”.
“Huxu!” Cikin ruxani Bashir ya tambaya.
“Eh” Ya tsuke fuska kamar an matse lemon tsami.
“Bashir an camfata da cewar farar qafa gareta”.
“Mene kuma farar qafa?” Ya tambaya cike da damuwa.
Ya xan yi murmushin gefen fuska “Baka san abinda ake nufi da cewar mace tana da farar qafa ba?” Ya xauki carbinsa yaci gaba da ja.
“Idan aka ce mace tana da farar qafa ma’ana duk wanda ta aura duk yawan dukiyarsa sai ya tsiyace ya koma kamar veran masalaci”.
Cike da damuwa Bashir ya dube shi.
“Malam mene maganin faruwar hakan?”
“Abu xaya ne zai hana faruwar hakan, ace ka koma cikin mahaifiyarka”.
Bashir ya yi mutuwar tsaye.