Fita ta 3
by @kwalisa
BABI NA DA YA
Mafi akasarin xalibai ne suke shiga cikin makarantar, a yayin da wasu suke haramar fita daga cikin makarantar. A cikin xaliban da suke qoqarin fita daga cikin haraba makarantar har da xaliba mariya tana tafiya cikin kasala da nuna gajiya a rataye a kafaxarta jakar makaranta ce, da take xauke da litattafan xaukar darasi.
Duk wajen da ta wuce sai xalibai ‘yan uwanta sun waigo sun bi ta da kallo, idan da sabo mariya ta saba da irin wannan kallon da mutane suke yi mata, sau tari ta kan yi mamakin abin da jama’a suke kallo a gare ta domin ba ta ga abin kallo ga yoriki-yorikin tsumokaran kayan da suke jikinta ba wanda wasu saboda daxewa tana sa su har sun koxe. A haka ta ratsa haraba makarantar tana tafiya a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki a haka ta fita daga cikin makarantar a bakin titi ta tsaya ta yi shiru tana kallon tsayin hanya kafin ta ja dogon tsaki a hankali.
Wannnan tsayuwar da mariya ta yi tana son tuno abin da zai fisshe ta, saboda idan da sabo ta saba duk lokacin da ta fito daga makaranta sai ta tsaya a wajen ta yi tunanin abin da ya kamata ta yi kafin ta aiwatar da shi. Ba komai mariya take tsayawa tunani ba illah kuxin da za ta hau abin hawar da zai maida ita gida. Sau tari idan ta samu kuxin zuwa makarantar a motar haya to ba ta samu kuxin komawa sai dai ta taka da sayadarta ta qarasa zuwa gidansu.
Duk da ba wani nisan kirki ba ne tsa kanin su da makaranta amma ha kan ba qaramin qona mata zuciya yake ba, ganin kowa yana hawa abin hawa ya koma gida amma ita kullum cikin kame-kame take.
Wannan rayuwar ta zamar wa mariya qalubale.
Soyayyar mariya da karatu shi ya saka take daurewa,tana cijewa duk wata wahala da take fuskanta na ganin ta samu ilimi. Tana fatan wata rana wannan ilimin nata ya amfani al’umma. Ta yi saurin yanke tunanin da ta soma domin ba ta buqatar ba shi dama har ya yi galaba a gare ta gwara ta yi abin da zai fissheta.
Ba wai tashi aka yi daga makarantar ba, kawai wata azabar biya yunwa ce take damunta shi ya sa ta gwamace haqura da darasin na yanzu ta nufi gida ko za ta samu abin da za ta kai bakin salatin ta. Domin ta san ko da ta zauna a ajin to wannan yunwar da take ji ba za ta ba ta damar fahimtar darasin ba. Don haka ta saduda za ta koma gida ta samu hutu ko ta samu lokacin duba darasin da aka yi musu.
Ta gyara gyalenta da yake shirin zame mata daga kafaxa, a hankali ta motsa ta soma tafiya a hankali tana bin gefen titi da zummar daukar hanya don ragewa kanta tafiya.
A hankali ta ci gaba da bin gefen titin, kai ka ce duk duniya babu wani abu da yake damunta.lokaci zuwa lokaci ta kan xan xaga kanta ta kalli motocin da suke wucewa da gudu a cikin ranta ta kan yi tunanin da tana da kuxin hawa mota da ita ma yanzu ta kai waje kaza ko ta kusa zuwa gida a haka ta ci gaba da yin nisa da makaranta tana kusantar gidan su.
Wata jar mota qirar fa kanto ta saka sigina a hankali kamar ana tura ta da hannu ta samu waje gefen titi ta tsaya nesa kaxan da wajen da mariya take tunkara. Sannu a hankali qofar motar ta buxe wani saurayi dogo mai siririn saje da siririyar wushirya mai xauke da siraran lavan baki da manya dara-daran idanu ya fito daga cikin motar sannu a hankali ya jingina a jikin motar ya naxe hannuwan shi a qirjinsa yana kallon mariya da take tahowa.
Tun kafin ta qarasa wajen da yake tsaye wani daddaxan qamshin turarenshi ya soma ziyartar cikin hancinta. ‘Wannan qamshin da daxi yake’. Ta raya ha kan a cikin ranta kafin ta xaga idanunta suka kalli juna da saurayin karo na farko ta ji zuciyarta ta harba da qarfi a tsakiyar qirjinta.
Mariya ba ta san dalilin faruwar ha kan ba, cikin sauri ta kauda kanta. Ta ci gaba da tafiya a hankali tana qara tunkara wajen da yake yi tsaye yana kallon ta. Wannan kallon da yake mata duk sai ta ji kamar an yi wa qafarta takunkumi sai harxewa take yi ha kan ya sa saurinta ya ragu, ta qarasa wajen shi kamar daman ita yake jira ya yi mata Magana.
“Bai war Allah sannu dai”, Mariya ta ji shi amma ba ta buqatar tsayawa ha kan ya sa ta yi gaba abinta kamar ba ta ji abin da ya ce ba. Ganin ba ta tsaya ba ya saka ya bar jin motar ya biyo bayanta taku kaxan ya cin mata suka jera tare suna tafiya kamar daman can tare suka tawo, ganin haka ya sa ta ja ta tsaya tax ago idanunta ta kale shi.
“Don Allah kada kace na yi maka wulaqanci amma bana son ganin wani ya biyo ni” Ya yi murmushi.
“Me ya sa ba kya son wani ya biyo ki?” Ta juya tana kallon titi.
“Ni matar aure ce” Ya kalleta da mamaki.
“Matar aure kuma? Amma sam baki yi kama da matar aure ba, ina ganin duk wanda ya zo gare ki yana da manufa ta alheri idan haka ne bai kamata ki wulaqanta shi ba” A yanayin yadda yake Magana akwai wani sinadari dake sakawa mutum ya ji yana son jin muryar shi saboda lafuzan bakinsa suna da daxin saurare amma duk da haka ta gayato vacin rai ta saka a kan fuskarta.
Ganin haka shi kuma ya ci gaba da Magana “Ki yi haquri da tsare ki da na yi, ha kan ya faru ne saboda ba yadda zan yi. Kusan sati biyu ke nan da soma ganin ki amma na rasa hanyar da zan bi domin yi miki Magana amma yanzu na daure na tare ki ina son…” Ta xaga masa hannu wanda ha kan ya saka ya yi shiru yana jiran jin abin da za ta ce.
“Lokacinka ya cika, bana son jin qarashen abin da kake shirin faxa min, don Allah ka adona Kalmar ka xauke ta ka kai ta wajen da ya dace ka faxe shi ba wajena ba. Saboda ni da kake gani na daina so na daina soyayya, haka kuma duk wani da ya ce yana so na haushinsa nake ji” Maimakon maganar da ta faxa ta vata masa rai sai murmushi da ya yi mata ya ce mata.
“Ga shi kuma ni na faxa a cikin qaunar ki, sam na kasa samun sukuni a cikin rayuwata. Da gaske wannan abin da nake ji a game dake so ne irin son da maza basu cika samun kansu a cikinsa ba, wannan son da nake yi miki na musamma ne” Ta xaga kai ta kalle shi kamar za ta kuma yi masa Magana sai ta sunkuyar da kanta qasa ba tare da ta ce masa wani abu ba ta ci gaba da tafiyarta abinta, ganin haka shi ma ya kuma rufa mata baya suka ci gaba da tafiya shi bai kuma yi mata Magana ba haka itama ba ta ce masa kanzil ba. Maimakon haka sai ta gayyato wani tunani a cikin ranta tana fatan ta qarasa gida ta samu wani abu ta kai bakinta saboda yunwar da take rarakar cikinta.
Shi kuma ya ci gaba da tunanin hanyar da zai bi mafi sauqi da zai samu damar mallakarta. A haka suka xan yi tafiya mai xan nisa amma sam ba ta nuna alamar za ta tsaya ta saurare shi ba.
Ya daure ya ci gaba da bin ta har suka shiga unguwar su, tana qarasawa qofar gidan su ba ta waiwayo ta kalle shi ba bare ya sa ran za ta yi masa sallama kawai ta shigewarta cikin gida, ya tsaya a qofar gidan yana kallon ta cike da tsananin mamaki har ta shige.
Ya xan jima a tsaye a qofar ko yana tunanin za ta kuma fitowa ne? oho! Ganin ba ta da alamar fitowa ya saka ya haqura ya koma wajen da ya bar motar shi.
Mariya ta shiga cikin gidan da sallama kai tsaye xakin mahaifiyarta ta shiga ta same ta zaune ta yi shiru, ga alama tunanin rayuwa take yi a haka ta qarasa ta sunkuya tana gaida ita.
“Har kin dawo?” Ta ce mata lokacin da take gyara zamanta.
“Na dawo Umma”, Suka yi shiru na wani xan lokaci kamar ba kowa a wajen dukan su akwai abin da suke saqawa a cikin ransu zuwa can mariya ta yi Magana.
“Umma an dafa wani abu ne?, saboda yunwa nake ji” Maganar da ta yi ya saka mahaifiyarta ta xaga kai tana kallon ta cikin nuna tausayawa ta ce mata.
“Yadda kika fita kika barni ba ko taro a hannuna haka nake har yanzu, koda rowan da za a sha babu a cikin wannan gidan” Ta qarasa Magana cikin damuwa.
Maganar ta yi wa zuciyar mariya wata irin shiga ta yi sororo tana kallon mahaifiyarta wani irin takaici mafi girma ya shiga cikin ranta. Ita kam ba ta san wajen da za ta saka rayuwarta ba ta gujewa yunwa ta kuma zo ta tarar da ita, ta yi shiru ta ma rasa mene ne yake mata daxi a rayuwarta. Zaman xakin ya zamar mata babu daxi, don haka ta miqe a hankali ta qarasa tsakar gida ta xan tsaya jim kafin ta wuce cikin xakinta tana tura qofar xakin kamar za ta shiga sai kuma ta ja ta tsaya tana kallon cikin xakin ta zuba masa idanuwa, cikin tsananin takaici da yawaitar baqin ciki wani hawaye mai matuqar zafi ya kwaranyo mata.
Duniya kenan rawar ‘yan mata na gaba ya koma baya, rayuwa ta yi mata zuwan baza ta,ba a haka ta xauki rayuwa za ta zo mata ba, ta zo mata a baibai ba kamar yadda take zuwar wa sauran mutane ba.
Shirun da ta yi ha kan shi ne ya bai wa baqin cikin da yake a ranta tsawon lokaci ya riqa tasowa yana son tariyo abin da ya gaba ta a bayanta.
Hawayenta ya riqa qaruwa,baqin cikinta ya ci gaba da dawo mata cikin zuciyarta. Ha kan ya saka shasshaqar kukan nata ya soma fitowa.