Fita ta 4
by @kwalisa
Jiyo kukan nata ya saka mahaifiyarta ta miqe da sauri ta fito waje a jingine a qofar shiga xakin ta ta sameta ta jingina jikinta a jikin katangar xakin nata a hankali ta qarasa wajen da take tsaye cikin kwantar da murya ta ce mata.
“Lafiya kike mariya?” Ta qarasa Magana tana kallon idanunta.
Ta kasa xago kai ta dubi mahaifiyarta, ta ci gaba da kukanta, ganin haka ya sa ta xan qara matsawa kusa da ita a hankali ta miqa hannu ta dafata cikin kwantar da murya ta ce mata.
“A ko wane lokaci ki zama mutum mai tawakali, domin duk bawan da kika gani a cikin wata qaddara ba wai don Allah ba ya qaunar shi ba ya jarrabe shi, ko xaya hasali ma ana jarraba ko wane bawa gwargwadon imaninsa ki daure ki ci jarrabawar da Allah yake miki” Mariya ta yi shiru da kukan da take yi, ta xago idanunta da suka kaxa suka yi jawur suka haxa idanu da mahaifiyarta kafin ta kauda kanta.
Mahaifiyarta ta ci gaba da Magana “Ki je gidan Habiba mai tuwo kice ta ba ki ba shin abinci, idan Allah ya kai mu zuwa anjima zan bayar a kawo mata” Mariya ta yi shiru ba tare da ta ce wani abu ba. Ta yi qoqarin done haushinta da yake damqe a cikin ranta. Kafin ta yi qoqarin barin wajen don zuwa aiken da mahaifiyarta ta yi mata.
Tana fita ta ganshi yana zaune a kan bencin da ya saba zama a qofar gidansu, idanun su suka kalli juna ta sunkuyar da kanta qasa.
Duk a unguwarsu babu wani mahaluki da ya san sirrin mariya kamar shi, saboda yawan kulawar da yake nunawa a gare ta. Ya soma yi mata murmushi ganin ta nufi wajen da yake zaune, kafin ta qarasa ta yi qoqarin kauda damuwar da take tattare da ita amma duk da yunqurinta na yin haka ta riga ta makara ya fahimci akwai abin da yake damun ta.
Ta qarasa ta gaida shi “Barka da hutawa” Ya kuma yi mata murmushi.
“Har an dawo daga makaranta kenan?” Ba ta ba shi amsa ba illa kawai xaga masa kai da ta yi.
Ya kuma kallon ta yana qara girman idanunsa kafin ya kuma cewa da ita.
“Me kuma yake faruwa?”
“Babu abin da ya faru” A taqaice ta ba shi amsa.
Ya xan shafi fuskarsa “Ina ga qarya ba ta dace da ke ba, saboda idan kika yi qarya ba ta yi miki kyau. Ko kin manta abokin kuka ba’a voye mishi mutuwa?” Ta sunkuyar da kai qasa ita dai ta san duk yadda suke da Sani ba za ta faxa masa yunwa take ji ba,ganin ta yi shiru ya sa ya yi murmushi kafin ya kuma cewa da ita.
“Ko saurayin da ya biyo ki ne ya vata miki rai?” Jin wannan maganar ya saka ta xago kai cikin sauri tana kallonsa ta xan yi jim kafin ta ce masa.
“Yaushe ka ga wucewarmu da wani?”
“Ina zaune a nan ina kallon ku, kina zuwa qofar gida kika shige kika bar shi” Ya xan yi shiru kafin ya kuma cewa da ita.
“Gaskiya ba ki kyauta ba” Ta tura baki gaba kafin ta ce masa.
“Shi ya sa wa kanshi rigar wahala, ka fi kowa sanin xa namiji ba ya gabana bare koma batun soyayyarsa bana jin zan kuma aminta da wani xa namijin don sun sha ni basilla na warke” Sani ya dube ta cikin mamaki.
“Mariya kin san abin da kike faxa kuwa?” Ta kalle shi da idanunta.
“Na san abin da nace mana” Ya girgiza kanshi kafin ya ci gaba da yi mata Magana, wannan karon ya kwantar da lafazinsa.
“Ita rayuwa duk abin da kika ga ya samu bawa to Allah ne yake son jarraba imaninsa, idan har ka zama xaya daga cikin bayin da aka jarraba ka yi qoqarin ganin ka samu damar cin jarrabawar da aka yi maka” Ta gyara tsayuwarta.
“Duk da haka da wahala na kuma aminta da soyayyar wani xa namiji, ni kam na haqura da duk wata alaqa da za ta shiga tsa kanin mu” Da qarfin guiwa ta qarashe lafazinta.
Sani ya yi murmushi.
“Mariya har yanzu yarinta tana xiban ki, amma ki sa ni duk yadda ka kai da baqin ciki wata rana za ka yi farin ciki bana jin bawa zai dauwama a cikin baqin ciki” Ta yi murmushi.
“Haka ne, amma kuma ni kam na yanke alaqa da soyayya ba zan kuma aminta da wani saurayi ba” Suka xanyi shiru ba don shi ba shi da abin da zai ce mata ba sai don ba ya son dawo mata da tsohon mikin da ya jima a cikin ranta ha kan ya sa ya sauya salon hirar ya ce mata.
“Mu shiga cikin gida ki samu abinci ki ci na san akwai sauran abinci a ciki” Ta xaga idanu tana kallon shi sam ba ta yi mamakin yadda aka yi ya gano tana jin yunwa ba don ba wannan shi ne karo na farko da suke haka da shi ba.
Ba ta yi masa musu ba ta bi shi suka shiga cikin gidan.