Fita ta 5
by @kwalisa
**
Da dare tana zaune a xakinta bayan ta iddar da sallar isha’i ta ci gaba da laziminta a kan sallayar, a haka mahaifiyarta ta shiga ta same ta. Jin motsin an shiga ya saka ta xago kai suka kalli juna da mahaifiyarta.
“Ki je ana kira a waje” Mamaki ya bayyana a kan fuskarta maimakon ta nuna alamar za ta miqe sai ta kuma gyara zama ta ci gaba da laziminta, amma duk da haka a cikin ranta ta soma qoqarin tunano wanda ya zo wajenta. Ganin ba ta da alamar tashi ya sa mahaifiyarta ta yi mata Magana a karo na biyu.
“Wai ba za ki tashi kije wa jen kiran da aka yi miki ba?” Ta xago kai ta kalli mahaifiyarta kamar za ta ce wani abu sai kuma ta fasa, cikin kasala jiki kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta miqe ta soma naxe sallayar, ta wurga a kan katifar da take kwanciya, ta gyara hijabin da yake jikinta ba tare da ta ce da mahaifiyarta qala ba ta fita daga cikin xakin.
A waje ta same shi yana jingine da motarsa, wannan karon ya sauya kayan da suke jikinsa yana sanye da wani yadi mara nauyi kalar sararin samaniya,da hula a kansa daddaxan qamshin turarensa iska tana kaxa shi sashe zuwa sashe.
Ta qarasa wajen da yake fuska a xaure babu walwala kamar an aiko mata da saqon mutuwa.
Shi kuma ya kalle ta da murmushi, kafin ya kuma gyara tsayuwarsa. Shiru ya xan tsawaita a wajen ba tare da kowa ya yi Magana ba ganin ba ta da niyar gaida shi sai ya soma yi mata Magana.
“Ga ni na dawo gare ki, na dawo domin jin amsar maganar da na faxa miki xazu” Ya qarasa Magana yana kallon fuskarta da take sheqi a cikin matashin hasken farin watan da yake haskakka sararrin samaniya.
“Wacce Magana kenan?” Ta tambaye shi tana kallonsa.
Ya xauke idanunsa zuwa ga kallon wani vari na daban kafin ya ce mata.
“Ai daman na san ba za ki tuna ta ba, saboda ban samu shimfixar fuska ba daga gare ki ai ba a damu da sharar da ta kwaso ni ba. Amma kuma maso xan tsuntsu shi yake bin sa da jifa don haka zan kuma maimaita miki abin da na faxa miki xazun” Ya xan yi shiru yana jiran ko za ta ce wani abu amma ga mamakinsa ko alamar nuna alamar za ta yi Magana ba ta yi ba ha kan ya sa ya ci gaba da Magana.
“Na san ba za ki manta fuskarta ba, ni na tare ki xazu nace miki ina qaunarki, na faxa miki Kalmar har cikin raina. Da gaske ina son ki ina son neman auren ki, ni ba irin samarin nan ne masu zuwa da yaudara ba auren ki na zo yi don Allah ki ba ni dama” Ta girgiza kai gami da yi masa wani mugun kallo, sannan cikin fushi-fushi ta soma Magana.
“Bana jin zan kuma aminta da wani xa namiji a rayuwata. Ka yi haquri ka qyale rayuwata, a wannan lokacin bana gayyatar kowa cikin rayuwata ballantana har ta kai ga na goga masa kashin kaji” Mariya ta qarasa Magana tana kauda kai gefe a lokacin suka haxa idanu da shi yana zaune a kan wani tsohon benci da ya saba zama a kai, cikin zafin nama ta xauke kai.
“Ya kamata ki fahimci abin da na zo da shi” Da muryar tausayi ya ce mata.
Ta juyo ta kalleshi “Ba kuma zan fahimta ba” Bakinta ya faxa ba tare da ta shirya faxa bat a yi saurin sunkuyar da kanta qasa saboda ita kanta maganar ta yi mata nauyi.
Suka yi shiru su duka, amma daga alamar fuskar Ba shir ta nuna alamar sam bai ji daxin maganar da ta faxa masa ba, a duniya bai tava tsamanin akwai wata mace da zai tunkara da maganar soyayya ta watsa masa qasa a idanu ba. Ya daure cikin kwantar da murya ya ce mata.
“Shi kenan ni zan tafi” Ba ta jira ta ce masa komai ba ta soma tafiya abinta kai tsaye wajen da Sani yake zaune ta nufa.
Ba shir ya saki baki yana kallon ta cike da mamaki, wajen wani ta tafi wani da ya fi shi matsayi saboda ya yi sa’ar mallakar zuciyarta. Wani kishi mafi girma ya lulluve masa zuciya saboda yadda ta nuna masa qarara ba ta son shi a kan wanda bai fi shi komai ba.
Lokaci guda kanshi ya yi wata irin sarawa ya yi amfani da hanayen shi wajen tare kansa. Baqin ciki ya ci gaba da qaruwa a cikin ransa duk sai ya ji layin ya gama gundurar sa domin ba zai iya jure baqin ciki ba cikin sauri ya juya ya buxa qofar motarsa ya shiga bai jira wata-wata ba ya tashi motar ya fisgeta a guje qura ta tashi a wajen.
Mariya dake tsaye a gaban sani ta juyo cikin sauri ta bi jar donjar motar Ba shir da take neman vacewa a cikin matashin duhun daren da ya yi wa kanshi wurin zama a cikin layin da kallo.
Sani ya bi ta da kallo shi ma kafin ya girgiza kansa ya kuma cewa da ita.
“Xazu na faxa miki wannan Kalmar cewar ba ki kyauta ba. Yanzu ma kin qara yi masa abin da kika yi masa xazun gaskiya mariya ban ji daxin abin da kika yi ba”
“Haba yaya Sani a wajenka abin da na yi ban kyauta ba? Kai yanzu ka goyi bayan na kuma aminta da wani xa namiji? kafi kowa sanin cewar zuciyata ta gama qonewa da tsanar duk wani namiji?..” Ya yi saurin xaga mata hannu yana harxe hannunsa a qirji kafin ya ce mata.
“Da quruciyarki da komai don haka aure ya zama dole a gare ki, idan haka ne ba zan tava goyon bayan ki wulaqanta duk wanda ya zo neman auren ki ba. Ki bai wa wannan saurayin dama ku sasanta kai ba ki san abin da Allah yake da nufin aiko miki wannan saurayin ba wata qila addu’ar mu ce ta amsu” Wannan maganar da ya faxa mata sam ba ta yi wa mariya daxi ba lokaci guda baqin ciki ya mamaye mata zuciya ta soma gyaxa kai cikin takaici.
“Haba yaya sani…Haba yaya sani, ka yi haquri bana jin zan kuma aminta da wani xa namiji balle kuma har na goga mishi kashin kaji kafi kowa sanin bala’in da yake bibiyar rayuwata” Sani ya miqe tsaye yana kallon ta da wani kallo na daban da ba ta tava ganin ya yi mata irin shi ba cikin fushi ya soma yi mata magana.
“Duk abin da ya faru a baya ya riga ya faru sai a gyara gaba. Don Allah ya jarrabe ka da wani iftila’i ba ha kan yana nufin idan kana addu’a Allah ba zai sauya maka da mafi alheri ba. Mariya ina ji a jikina wannan saurayin da ya zo wajenki yana tafe da alheri ba kamar sauran na bayan ne ba. Amma dai ki yi tunani a kan wannan maganar.” Yana kamala maganar bai bari ta kuma cewa da shi komai ba ya yi shigewarsa cikin gida ya bar ta a nan a tsaye.
Ta bi shi da kallo ba ta san lokacin da wasu baqin hawaye suka soma zubowa ta cikin idanunta ba. Takaicinta ya qaru sama da na xazu. A hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta juya ta nufi gidansu. Tana shiga ta faxa a kan katifarta mai kama da tabarma kaba ta soma fida sautin kuka da yake fita qasa-qasa.
Duk wahalar da ta sha a hannun namiji, duk baqin jinin da ta yi a wajen mutane, amma ba za a yi wa rayuwarta afuwa ba a qyale ta da abubuwan da suke faruwa da ita.
Ta ci gaba da kukanta ba tare da kowa ya zo ya lallashe ta ba.
**