RAI DA SO

Fita ta 6

by @kwalisa

                       **
Da matuqar mamaki ya shiga cikin xakinsa ya zauna a kan kujera da take cikin xakin, ya yi shiru sam ya rasa abin da yake yi masa daxi. Idan ya ce baya son Mariya ya yi qarya saboda tun daga lokacin da ya soma ganinta wani irin azababen sonta ya keta qirjinsa ya shige cikin zuciyarsa.
Ya yi imani cewar yanzu kam yana cikin duniyar shagaltuwa da mayen begenta ha kan ya saka a zuciyarsa yanzu babu komai a ciki sau qaunar ta da kuma son kasancewa da ita. Ya yi shiru ya zuba wa xakinsa idanu kamar yana saka ran ganin mariya ta fito daga cikin xakin. Cikin sauri tunani ya xauki wani sashe na zuciyarsa ya cila can wani sashe na daban.
Abin da ke ba shi mamaki yadda wata mace take neman gara zuciyarsa, ba don komai ba sai don wani saurayinta. A tarihin rayuwarsa wani namiji bai tava cin nasara a kan shi ba idan kuma duniyar tarihi tana maimaita kai to wannan karon ma ba za a samu nasara a kan shi ba.
Amma kuma wannan wane saurayi ne mariya take qaunar shi kamar haka? Wacce hanya ya bi har ya yi dacen mallakar zuciyarta? Wane irin kalamai yake amfani da su da har kuxinsa da qimarsa ba su ruxe ta ta bi shi ba?.
Ya saurara yana son zuciyarsa ta ba shi amsar tambayar da take ta kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Maimakon samun amsa sai zuciyarsa ta xauko masa wani babi na dabam.
Tabbas! Idan ya mallaki mariya zai yi dace da mace, tsayayya mai ra’ayi guda xaya. Macen da arzikinsa sam! Bai qayatar da ita ba. Haka son abin duniya ba ya gabanta saboda kwana biyar ya yi yana kallon ta tana komawa gida a qafa daga makaranta zuwa gidan. Ya yi imani ba kowace mace ce za ta iya haka ba. Amma kuma me ya hana mariya ta so shi bayan ta san yana da kuxin da zai iya rufa musu asiri? Ya sauke hannunsa daga riqon da ya yi wa kansa, wannan amsar tambayar ba mai wahala ba ce domin ya san ba komai ya kawo ha kan ba illah son da take yi wa saurayin nan.
Wannan ita ce amsar da zuciyarsa ta ba shi, akwai aiki ja a gabansa matuqar yana son samun nasarar tattaro zuciyarta ya dawo da ita wajensa. Kamar yadda yake ji a ransa kuma ba ya jin zai iya daina sonta duk ruwa duk iska. A hankali ya koma ya kwanta a kan matokarin kujera ya lumshe idanunsa, kyakkyawar fuska mariya ta bayyana a hankali sai ya ji zuciyarsa tana yin sanyi.
Ba zan daina gwada sa’ata a kanta ba har sai lokacin da na samu nasara. Ya kuma gyara kwanciyarsa.

Ta gama shirinta tsaf!, amma sai ta kasa tashi ta fita, ta yi shiru cikin alamun kallo xaya za ka yi mata ka karanta damuwa bayyane a kan fuskarta. Sam! Ta rasa abin da yake yi mata daxi a duniya, ha kan ya sa ta ci gaba da zamanta a cikin xakin, sai dai ta saqa wannan ta kwance ta kamo wannan ta kuma saqawa tun daren jiya take abu xaya.
Duk irin wahalar da ta sha a rayuwa, da baqin tsautsayin da yake binta. Amma a haka za a kuma takura mata cewar ta kuma aminta da wani namiji?.
Hawayen da suka taru a idanunta suka kwaranyo saman kumatunta,takaicin da yake ranta ya kuma ruvanya na baya ba ta son buxa wannan shafin sam a rayuwarta ko a cikin mafarki ba ta son ta kuma yin mafarkin abubuwan da suka faru da ita.
Ha kan ya sa da sauri ta miqe ta qirqiri wani aikin da ba shi ya kamata ta yi ba, ta soma gyara xakinta don kada ma ta bai wa zuciyarta damar dawo mata da abin  da ya riga ya wuce a cikin shafin rayuwarta.
Sallamar da ta ji ta xauki hankalinta ha kan ya sa ta tsaya da yin aikin da ta soma, a hankali ta matsa ta xaga labulen xakin ta leqa wanda ta yi tsammai, shi xin ne ya shigo. Ya qarasa cikin tsakar xakin mahaifiyarta ya sunkuya har qasa yana gaida mahaifiyarta.
Da yake lokaci zuwa lokaci ya kan shiga su gaisa da ita, saboda itama ya xauke ta ne kamar mahaifiyarsa saboda irin zaman mutuncin da suka yi da mahaifiyarsa.
“Mutuniyar taka tana xaki” Ta jiyo murya mahaifiyarta tana cewa da shi.

Mariya ta saki labulen ta koma ta jingina a jikin bango xakin, Sani ya damu da ita yana tausayin rayuwarta, ta raya ha kan a cikin ranta. Ta lumshe idanunta a hankali a cikin ranta ta raya cewar. Ni ma Allah ya ba ni abin da zan samu damar saka masa da shi a kan kulawar da yake bai wa rayuwarta.
Murya shi ta ji tana cewa.
“Za mu gamu da ita,idan ta dawo daga makaranta” Cikin kwantar da lafazi ya ce.
Cikin takaici ta soma girgiza kai tabbas ta sani ba wai don baya son ganinta ba ne said an fushin da ya yi da ita saboda abin da abin da ta yi masa. Amma ya ta iya ba ta da wani zavi sama da wannan da ta xauka. Banda abinsa ta ya shima da kanshi zai goyi bayan ta kuma son wani xa namiji a cikin ranta, bayan shi ne mutumin da ya fi kowa sanin baqar wahalar da ta sha a hannunsu idan har ya tsaya a kan wannan maganar ta shi gaskiya ba ta jin ya yi mata adalci.
Sam! Bai so mata ta samu kwanciyar hankali a cikin rayuwarta ba, idan haka ne ya kamata ta same shi domin ta sanar da shi abin da ya manta, ta tuna masa illar abin da yake shirin sa ta ta aikata. Tana kammala wannan tunanin ta yiwo waje a azure ta yi sa a suka haxu suka tsaya suna fuskantar juna ta soma gaisar da shi kafin ta xora da cewa.
“Fushi kake yi da ni shi ya sa ba ka neme nib a?” Ya xan xaga idanu yana kallon ta kafin ya naxe hannunsa a kan qirjinsa.
“Ba fushi nake yi dake ba” Ya xan tsagaita sannan ya ci gaba da Magana “Sai dai kuma zan iya yin fushin dake nan gaba” Ta xago da kai cikin sauri tana kallonsa.
“Sabo da me za ka yi fushi da ni?” Ya sauke hannunsa.
“Idan kika qi bin abin da ya dace, saboda hujjar da kika riqa a matsayin makamin kariya ba gamsashiyar hujja ba ce” Mariya ta soma girgiza kai a hankali lokaci xaya idanunta suka soma kawo hawaye.
“Kada ka shiga cikin mutanen da suke fatan ganin rayuwata ta na ci gaba da zama a cikin tsautsayi, ni na zama mace mai wani tsautsayi a cikin rayuwata ka san komai sani ka san sirrina sama da kowa kada ka so na kuma zama silar shigar wani cikin halin qunci” Maganar da ta faxa ta daki zuciyar Sani ya ji wani tausayinta ya kama shi amma duk da haka ya haxiye damuwarsa yana kallon ta ido da ido, shi kam yana jin duk duniya babu wanda ya kai shi jin tausayin rayuwar da mariya take yi.
“Ki yi haquri mariya, ba na faxa miki haka a kan son raina ba ne, ni burina kullum naga kin zama cikin ‘yanci kuma ki xauka cewar duk waxan nan abubuwan da suka faru ba komai ba ne face camfe-camfe irin namu na Hausawa. Shi kuma camfi ba shi da kyau duk abin da ya samu bawa jaraba ce daga Allah” Cikin kwantar da murya ya ce mata.
Ta xago kwayar idanunta da suka soma tara hawaye ta kalli fuskarsa “Yin haka kana ganin zai zama adalci ga abin da ya faru ga mutanen baya? Maganin kar a yi kada a soma dai” Ya sunkuyar da kai qasa ya yi jim kaxan na wani lokaci kafin ya ce mata.
“Ita qaddara idan aka rubuta ta babu makawa sai ta faru ko da ke ko babu ke, irin wannan qaddara ta sha faruwa ana jingina ta a jikin mata. Amma sam ba haka ba ne, duk lokacin da mutum ya yi aure to ya kamata ya sani kashe kuxinsa zai qaru, haka hidima don haka idan ba ya tanadi yana lisafi wata rana zai wayi gari kuxin sun narke. Ni dai abin da zan faxa miki ki xauka duk abin da ya samu wani ba daga ke ba ne qaddara ce Allah ya kawo” Mariya ta girgiza kai.
“Shi kenan na ji, amma kuma ka yi haquri na gama yanke hukunci ba zan yi aure a rayuwata ba” Ya kalleta cikin sauri. Ya santa kamar yunwar cikinsa,idan tace tabbas shi xin take nufi ya kuma jin muryarta ta ce masa.
“Kayi haquri kuma ka daina fushi da ni” Ya jijjiga kai sam ya kasa cewa da ita komai saboda ta xaure shi da jijiyoyyin jikinsa. Ya juya abinsa ya fita daga cikin zauren ya bar ta a tsaye.
Ita fa ta rasa abin da yake nufi kuma me ya sa ya dage a kan lallai ta yi aure, idan haka ne  wa yake so ta aura? Tambayar ta zo mata cikin kwakwalwa. Shi yanzu yana da tabbacin wanda ya kawo mata zai iya tsare rayuwarta, ya kuma tsare mutuncinta ya kuma xauki haquri a lokacin da qaddara ta faxa masa? Ta san babu makawa sai qaddara ta faxawa duk wanda ya aureta saboda gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
Idan har za ta tsaya a kan aqidarta ha kan yana nuna cewar Sani zai ci gaba da yin fushi da ita.
Ita kuma ba ta fatan haka ya ci gaba da faruwa a tsa kanin su.