Soyayya ko Zalunci

Babi na 2

by @102565813543784586917

BAYAN AURE

Sati guda bayan ɗaurin aurensu, Fatima ta kira Yayarta Siyama a waya. Bayan sun gaisa tare da musayar barkwanci kamar yadda suka saba, Fatima ta yi murmushi tana sanar da ita wani albishir.

“Yaya Siyama, ina da labari mai daɗi.”

Siyama ta yi dariya.

“Toh, ina saurare. Ko dai kin fara kewarmu ne?”

“A’a,” Fatima ta amsa cikin annashuwa. “Ni da Muktar za mu tafi honeymoon na wata ɗaya kafin mu dawo Najeriya.”

“Masha Allah!” Siyama ta faɗa cikin farin ciki. “Wannan labari ne mai daɗi. Wace ƙasa za ku je?”

“Da farko za mu je Makkah mu yi sati biyu, daga nan kuma mu wuce Qatar.”

“Masha Allah, Allah Ya sanya albarka. This is a good news”

Fatima ta yi murmushi kafin ta ce da ɗan zolaya:

“Amma da kuke kushe shi.”

Siyama ta yi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce:

“Har yanzu bai min ba. Amma tunda ba ni ke auran shi ba chan ki karata ke da sh.”

“Yaya Siyama! Yana min albishir ke na fara kira na fadi maki amma sai ki gwashale ni.”

Dariya ta kubce wa Siyama.

“Shikenan, Yi haƙuri.”

Ta ɗan tsaya kafin ta sake tambaya.

“Yaushe za ku tafi?”

“Jibi da safe.”

“Toh Allah Ya tsare hanya, Ya dawo da ku lafiya. Kuma kar ki manta da mu a addu’a.”

“Ba zan manta ba, in shaa Allah.”


*********************************


Bayan Fatima da Muktar sun dawo daga tafiyarsu.

Da dawowarta ne ta fara fuskantar rayuwar da ba ta taɓa tsammani ba.

Gidan ya kasance gida ɗaya amma rayuwa daban-daban.

Habiba, uwargida, tana zaune a bene na ƙasa. Fatima kuma tana zaune a bene na tsakiya, yayin da Muktar ya ke da nasa sashe a bene na sama.

Tun ranar da Fatima ta shigo gidan, Habiba ba ta taɓa shiga sashenta ba. Haka ma Fatima ba ta shiga harkokin Habiba ba, musamman saboda Muktar ya sha gaya mata cewa ta nisanci Habiba.

A wannan rana, Fatima na zaune a falonta tana kallon wani shiri a Tv lokacin da aka buga ƙofa.

Ta rage sautin talabijin ɗin sannan ta ce:

“Waye?”

Daga wajen ƙofar wata sanyayyar murya ta amsa:

“Habiba ce.”

Fatima ta ɗan ɗaga gira cikin mamaki.

Me ya kawo ta?

Tun da ta zo gidan, Habiba ko kallonta ba ta cika yi ba, balle har ta zo sashenta.

Sai dai tarbiyyar da mahaifinta ya koya mata ta hana ta nuna mamakinta.

Ta miƙe ta buɗe ƙofar.

Habiba na tsaye cikin nutsuwa. Fuskar Fatima ta fara ɗaurewa na ɗan lokaci, amma sai ta tuna nasihohin mahaifinta game da kyautatawa mutane.

Ta yi murmushi.

“Bismillah, shigo.”

Habiba ta shiga a hankali. Idanunta suka fara yawo a cikin falon.

Ta kalli kayan ɗaki.

Ta kalli labulai.

Ta kalli yadda aka tsara komai cikin tsari da ƙayatarwa.

A fili ana iya ganin kuɗin da aka kashe wajen kawata wurin.

Fatima ta ce cikin karamci:

“Bari na kawo miki ruwa ko abin sha.”

Habiba ta girgiza kai.

“A’a. Ba na buƙata.”

Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu.

Fatima ta lura Habiba kamar tana son faɗin wani abu amma tana jinkirta shi.

Domin karya shirun, sai ta tambaya:

“Ina Raudah da sauran yaran?”

“Sun tafi Makaranta.” Inji Habiba,

sai ta ɗan gyara zamanta kafin ta cigaba:

“Amma ba wannan ya kawo ni ba.”

Ta sake duban falon.

Sai kuma ta mayar da idanunta kan Fatima.

“Da ace mahaifinki ba mai kuɗi ba ne, da na ce kwaɗayi ne ya kawo ki nan.”

Fatima ta haɗe gira.

“Ban gane ba?”

Habiba ta yi murmushi mai cike da wani abu da Fatima ta kasa fassarawa.

“Za ki gane. Ba yanzu ba.”

Sai ta ƙara da cewa:

“Domin duk inda kwaɗayi ya shiga, wahala kan biyo bayansa kamar inuwa.”

Fatima ta ji wani irin sanyi ya ratsa ta.

“Me kike nufi?”

“Komai yana da lokacinsa.”

Habiba ta miƙe tsaye.

Fatima ma ta miƙe.

“Yaya za ki zo ki yi irin waɗannan maganganu sannan ki tafi ba tare da kin yi min bayani ba?”

Habiba ta gyara mayafinta.

“Na faɗi abin da ya kamata na faɗa.”

“Shawara ko Gargadi

Habiba ta yi murmushi.

“Wannan kuma sai ke da kanki ki tantance.”

Ta juya ta nufi ƙofa.

Kafin ta fita, sai ta waiwayo.

Idanunta suka sauka kan Fatima.

“A wannan karon hanyar ta bambanta…” ta faɗa cikin wata irin murya mai nauyi.

“Amma ki tabbata wurin saukar motar ɗaya ne.”

Daga nan ta fita.

Fatima ta tsaya cak tana kallon ƙofar da aka rufe.

Zuciyarta ta cika da tambayoyi.

Me Habiba take nufi?

Wane saƙo take ƙoƙarin isarwa?

Wane abu ne take son faɗa amma ta kasa faɗa kai tsaye?

Na kusan mintuna masu yawa Fatima tana zaune tana nazarin kalmomin Habiba.

Ta maimaita su sau da dama a zuciyarta.

Amma duk da haka ta kasa gano ma’anarsu.

Daga ƙarshe ta miƙe.

Ba ta iya haƙuri ba.

Ta sauko ƙasa zuwa sashen Habiba.

Bayan ta yi sallama, Habiba ta amsa cikin nutsuwa ba tare da ta ɗaga kai daga wayarta ba.

“Idan kin zo ne domin jin fassarar maganganuna, gara ki koma.”

Fatima ta tsaya tana kallonta.

Habiba ta ci gaba da cewa:

“Akwai wasu sirruka da ya fi kyau su kasance a rufe.”

Ta ɗan yi murmushi.

“Domin ba kowa ne idan ya shiga ruwa zai iya iyo ba. Wasu kuma idan suka shiga… nutsewa kawai za su yi.”

Ta maida hankalinta kan wayarta kamar babu wani abu mai muhimmanci da ta faɗa.

Fatima kuwa ta tsaya cikin ruɗani.

Kalaman suna ƙara rikita mata tunani maimakon su warware masa.

Ta buɗe baki za ta sake tambaya, amma sai ta fasa.

A hankali ta juya ta fita.

Da zarar ta fice daga falon, Habiba ta ɗaga kai tana kallon hanyar da ta bi.

Sai wani ɗan murmushi mai cike da ma’ana ya bayyana a fuskarta.

Ta girgiza kai a hankali.

“Soyayya…” ta furta a hankali.

“Wani lokaci ita ce mafi girman makanta.”

Sai ta yi tsaki tana komawa kan wayarta.




Wai, wai, wai! Laifin daɗi ƙarewa. 😩📖


Wannan shi ne ƙarshen free chapters. Sauran shafukan littafin na biya ne. 💖


🎉 Ina ba da rangwamen 50% ga masu karantawa a yanzu. Amma da zarar na kammala rubuta littafin, zan mayar da farashin yadda yake.


📚 Don haka ku yi ƙoƙarin karanta shi lokacin da nake ci gaba da rubuta labarin.


💃🏽wasa  farin girki, mu je zuwa! 😍🔥


❤️ Ku yi sharing, commenting, da kuma supporting domin ƙarfafa gwiwa. Allah ya saka da alheri. 🤗💕


— Meena Majeed ✍️📚❤️