SIRRIN ZUCIYA

Chapter seventeen

by @aysharano22

Shiru ta sakeyi tana sauraran me qawar tata ke cewa daga can bangaren, har snn kuma idonta na kanshi tana murmushi tace “wlh kyau da yana yawa ma shi kam nashi da ya kusa yawa…Nusaiba tunda nake ban taba ganin halitta me kyau kamar nashi ba, komai nashi fa me kyau ne musamman idanuwanshi”…shiru ta sakeyi tana sauraranta kafin can tace “wai so yake mu zama abokai”…ta sakeyin shiru for some secs before tace “gashi nan fa muna tare kinsan ai ba hausa yakeji ba balle yaji abunda nake fada…ni inaga class din Hindin nan ma daina zuwa zanyi yanzu tunda na samu aboki dan india saiya koyamin”…ta karasa mgn da dariyarta mai kyau da Ayaan ke jinta har cikin zuciyarshi.


In takaice muku dai haka Juwairiyya taita gulmarshi da hausa tana koda kyanshi wai ita duk a tunaninta baijin hausa shima kuma bai nuna mata ya gane me suke cewa ba har suka gama wayan…ta maidata cikin jaka snn ta sake juyowa tana dubanshi duk murmushi ya cika fuskanta tace “so friends right?”…ya gyada mata kai alamar yes, kawai sai gani yayi ta mika mashi hannun damanta alamar suyi shaking kuma tana cigaba da dubanshi da murmushi…hannun da take miqo mishi din ya kalla kafin ya dawo da kallon gareta irin ban gane abinda kike nufi ba..fahimtar hakan da tayi yasata sakin wani murmushin tana dan bugun shoulder dinshi tace “lets shake hands…as friends”…kallon hannun nata ya sakeyi before ya sake kallonta kmr bai fahimci abinda ta fada ba yace “oh!”…sai kuma ya kasa miqa mata hannun sbd baisan me zaiji ba idan hannunshi ya hadu da nata…ganin haka Juwairiyya taja hannun nashi tayi shaking da nata snn ta sakeshi tana cewa “now that we are friends can i ask for a favor?”…Ayaan da tunda hannunshi ya shiga cikin nata ya daskare yayi mutuwar zaune a wurin sai yanzu ya dago yana kallonta jin abinda tace, muryarshi na fita a hankali ya amsa mata da “anything”…tace “i want you to teach me how to speak Hindi”…tun bata rufe baki ba ya shiga gyada mata kanshi yana cewa “done”…wani murmushi ta saki kafin ta mike daga zaunen da take tana dubanshi tace “ok i need to go now..see you around, bye”.


Har ta juya zata tafi Ayaan da yaji kmr da wani bangare na jikinshi take kokarin tafiya yayi saurin dakatar da ita da cewa “can i at least have your number”…juyowa yaga tayi tana dan harararshi tace “i thought you were not going to ask”…ya saki murmushi yana shafa kanshi…haka dai ta bashi numberta ta tafi batasan yama haddace number nata ba kawai baison ya nuna mata hakan ne maybe tayi tunanin wani abu daban da zai iya sa wnn sabon friendship da suka fara ya samu tangarda…yasan indai suka zama friends zama boyfriend dinta bazai bashi wahala ba musamman yanzu daya fahimci batada wulakanci ko girman kai ko kadan kmr ba yarinyar masu kudi ba…haka suka rabu Ayaan na jinshi tamkar a Aljannar fiddausi don farin ciki…har yanzu ya kasa believing cewa wai yau shi da Juwairiyya ne a haka sai yaga kmr a mafarki ba gaske ba..soyayyarta yaji tana sake cika zuciyarshi ya nufi gida yanata babbaka dariyar zancenshi data dingayi da hausa batasan yanajin hausan ba.
Aikam tunda ya fahimci haka bazai nuna mata ya iya hausa ba yanzu, zaiyita enjoying kallo da kuma jinta tana zancenshi da friends dinta tana kodashi…shi duk baisan haka kyawunshi yake da kyau ba sai yau da yaji a bakinta..in takaice muku batu kmr tababbe haka ya dinga sakin dariya da murmushi at thesame time har ya isa gida. Lokacin was around 12:40 na rana shida ya fita tun 10 sai to 1 yake dawowa. Lee da bai dade da tashi daga bacci ba yana bathroom yana wanka Ayaan ya shigo, bai nemeshi ba don yaji motsinshi a bandaki Allah Allah kawai yake ya fito ya labarta mashi abunda ya faru tsakaninsu amma shiru shiru Lucas yaqi fitowa kmr yasan yanda yake a qage yayi mgn dashi…jikin kofar bathroom din Ayaan yaje ya tsaya yana dan bubbugawa a hankali yace “Lucas are you in there?”…shiru yaji ba mgn sai ya sake cewa “Lucas”…daga cikin bayin Lee ya amsa mashi da “meye?”..Ayaan yace “be fast plss i need to tell you something”…daga haka ya koma kan sofa ya zauna ya zaro waya yayi saving number dinta daya karba as Ju with a red heart emoji like this Ju❤️…yana gamawa ya ajiye wayar a gefe daidai nan Kuma Lee ya fito daga bathroom  kai tsaye ya nufi inda dressing mirrornsu yake yana ce mashi “what’s up dude?..you look excited”…cikeda zumudi Ayaan yace “yes bro am very very very excited, Lucas can you guess what happened today?”…kallonshi Lee dake shafa cream a jikinshi yace “kayi magana da Juwairiyya?”…da sauri Ayaan yace mishi “yes, and can you believe that ita ta fara yimin mgn?”…idanuwa Lee ya ware a kanshi cikeda mamaki jin itace ma ta fara mishi mgn yace “no way!”…da sauri Ayaan ya tashi daga inda yake ya koma kusada Lee din ya tsaya suna facing junansu yace “yes way bro..she just approached me and said ‘why are you stalking me?…kaai!, you need to see how i was shocked, guy i almost froze there…i was like oh my Goodness”…ya karasa mgn with so much excitement daya kasa boyuwa kan handsome face dinshi…shi kanshi Lucas zuwa yanzu excitement din ne kaca kaca kan fuskarshi kawai sai yaja da baya ya shiga taka rawa yana watsa hannayenshi exactly dai irin rawar yarbawa yana cewa “guy you be real man ooo…i swear to God it’s now that you proved to be a real man bro am happy for you…am so happy for you”…ya karasa mgn yana rungume Ayaan daya rasa inda zai tsoma kanshi don farin ciki…haka Lucas ya kama hannunshi bayan ya gama rawar suka zauna kan sofa yana cewa “give me the full gist abeg am eager to hear”…tiryan tiryan Ayaan ya shiga labarta mashi komai har saida ya gama…aiko Lee yasha dariyar jin wai tayi zancenshi da hausa batasan kila ma Ayaan ya fita jin hausa ba…saida suka gama dariyar Lee yace “kasan kai din ne wlh kana yankar mutane da yawa…ni kaina ranar dana fara ganinka ban taba kawoma raina cewa kama san meye hausa ba”…shima dariyar yakeyi yace “sai kuma kaji kaima na fika iyawa ba”…Lee yace”ah to dama ni hausan nawa dan zamana a kaduna nema na koya amma da ba abinda na iya”…haka dai sukaita hirarrakinsu Lee na sake karfafa masa guiwa kan cewa ai tunda sun zama friends shawo kanta abune mai sauqi a wurinshi…duk Lee ya fadi haka sai Ayaan yaji kmr an tsundumashi a aljanna ne don farin ciki.


Cikin lokaci qanqani Juwairiyya da Ayaan sukayi wani irin mugun sabo da ko yaya suka kwana ko suka yini basu hadu ba ita kanta Juwairiyyan sai taji tayi missing dinshi ballantana kuma shi da dama he’s head over heels for her…dukda ba class dinsu daya ba bama department dinsu daya ba kusan kullum suna tare a school har Nusaiba da Lucas…ranakun da ba school kuma suna haduwa yana koya mata Hindi kmr yanda yayi alqawari.


Life was so good da har Ayaan keji kmr yayi stopping lokaci ya tsaya a haka cak don baya fatan zuwan duk wata qaddara daka iya yunkurin rabashi da ita…soyayyarta nata karuwa cikin zuciyarshi yayinda ita kuma ta daukeshi abokinta na qut da qut koma ince qaninta, dukda hakan na mishi ciwo bai taba nunawa ba.


Yau friday yana zaune daki yana karasa musu assignment shida Lucas da zasuyi submitting gobe yayinda shi kuma Lucas din ya tafi club tun wajen 8 na dare…ko gama assignment din baiyi ba kiran Juwairiyya ya shigo, ya saki murmushi ganin itace ya dauka, baikai ga yin mgn ba daga can bangaren yaji cikin sweetest voice dinta tace “hey you”…murmushi ne ya subuce mishi sbd jin muryanta da yayi yace “missing me already?”, don basu dade da rabuwa ba…koda baya ganinta yasan tale baki tayi kafin cikin Hindi da yake koya mata tace “haan, mein ne Aapko bohot miss kiya”(yes I miss you alot)…wani murmushin ya kara saki yana lumshe idanuwanshi yace”mein bhi”(me too)…da sauri tace”alright meet me downstairs”…yace”kya?”(what?)..tace”yeah, main bahar tumhara intizaar kar re ho”(am waiting for you outside)…mikewa yayi da sauri ya leqa ta window aikuwa ya hangota tsaye itama tana kallon windown nasu yace”Ju why did you come out by this time of the night?..you should have called me instead”…tace”its fine am here, dont keep me waiting”…da sauri ya kashe wayar ya zura slippers dinshi ya fita daga dakin ya sauka kasa…yana isa inda take ta kama hannunshi tana cewa”i want to eat pani puri, lets go get it”…zame hannunshi yayi daga cikin nata don duk jikinshi ya hadu da nata shi kadai yasan me yakeji yace”pani puri Ju, seriously a wnn daren ina zamu samu pani puri”…wara idanuwa tayi tana dubanshi cikeda mamaki tace”wait, did you just speak hausa?”…murmushi Ayaan yayi gamida shafa kai shaf ya manta ashefa har yanxu batasan yanajin hausa ba don haka yace”daidai kunnuwanki suka ji, hausa nayi”…hannu ta dora bisa kanta tanata rarraba ido a kanshi tsabar mamakin da ya bata na yanda hausan nashi yake fluent tasan ba wai rana tsaka ya koya ba tace”so you mean ka iya hausa amma duk tsahon wnn lokacin baka taba fadamin ba?”…kwantar da murya yayi yana ce mata”hey calm down…meye na dora hannu akai kmr kinga abun tsoro”…dawo da hannayen tayi bakinta jin ya sake yin wata cikakkiyar hausan kuma har snn bata bar mamaki ba tace”amma gsky kai munafiki ne Ayaan”…dariya mgnrta ya bashi amma yanayinta saiya hanashi dariyar ya gimtseta yana dubanta shima yace”Ju karki tara mana mutane mana”…ture hannunshi tayi wnn karon kmr zatasa kuka tace”kenan ranar duk mgnr da mukayi da Nusaiba kaji?”…murmushi yakeyi yace”ba ce mata kikayi inada kyau ba?…komai nawa me kyau ne musamman idanuwana?”…hannu bibbiyu ta shiga dukan chest dinshi dasu tana cewa”lallaima yaron nan ni kayi playing kou?”…hannayen nata ya kama ya rike gam kalmar yaron data fada na neman canxa mashi mood dinshi yace”ki bar cemin yaro”…tace”na fada din yaro or are you not a boy?”…janyota yayi jikinshi for the very first time tunda suka hadu ya matseta sosai har tana iya jin saukar numfashinshi a jikinta yakai bakinshi saitin kunnenta fuska babu alamun wasa yace”am old enough to be your man, so stop calling me a boy”…gum tayi tana rarraba ido as ba karamin zafi riqon yayi mata ba…shima bai damu tace din ba ya dawo da face din kusada nata snn ya hadesu waje daya yanajin yanda shauqinda yakeji ke neman sanyashi aikata abinda yafi haka.

***.




Rano✨