Chapter eighteen
by @aysharano22
Juwairiyya da taga babu sarki sai Allah batasan sanda ta fashe masa da kukan karya ba…da sauri ya bude idon yana kallonta ganin har snn yana rikeda ita ne yayi saurin sakinta yana cewa”am so sorry”…duka ta sake kai mashi a kirji tana cewa”you are very very very wicked”…rungumota yayi gaba daya a jikinshi ba tareda yasan lokacinda yayi hakan ba shi duk a tunaninshi kukan gaske takeyi yana shafa bayanta a hankali murya a tausashe kmr wanda ke mgn da baby yace”Juwairiyya i said am sorry, bansan zakiji zafi haka ba pls stop crying”…ba musu ta dakatar da kuka tana kokarin dagowa daga jikinshi ya sake mannata da chest dinshi…a hankali tace mishi”let me go Ayaan”…da sauri ya saketa yana komawa da baya don wlh baisan yaushe ya rungumeta a jikinshi ba…this is the first time da yakai hannunshi jikinta, bama ita kadai ba this is his first time touching a lady a rayuwarshi shiyasa duk yayi wani tsuru tsuru…kallon yanda duk ya koma kalar tausayi tayi kawai saiji yayi tace mishi”shall we go?”…a dan daburce ya dago ya kalleta kafin yace”oh yeah.. let’s go”…ba musu ta wuce gaba ya bita a baya yana kokarin tsaida musu da abun hawa tace”i want us to take a walk”…ba musu ya bar kokarin tsaidawa din snn yabita suka jera a tare suna tafiya ba wanda ke cewa wani abu kmr ba Juwairiyya da Ayaan ba…saida suka isa har wajen wani street food stall Juwairiyya ta zauna kan benchi dake wurin shi Kuma ya nufi cikin stall din don ya amso musu pani puri…kudi ya bayar aka zuba mishi ya karba ya tafi kan benchin da take shima ya zauna snn ya mika mata daya ya rike daya…harta karba zata faraci taji ya kira sunanta a hankali yace”Ju”…dagowa tayi ta kalleshi sai taga ya rike kunnuwanshi da hands dinshi ya wani jagwalgwale fuska yanda kasan dan yaye zai fara shagwaba har wani kikkifta blue eyes dinshi yakeyi yace mata”forgive me…please!”…tsabar yanda yayi da face da kuma lips dinshi batasan time data fashe da dariya ba tana cewa”you are just a baby Ayaan”…sake turo baki yayi yana langabe mata kanshi yace”stop calling me baby plssss”…tana cin pani puri dinta tace”oya tell me how old are you?”…tsuke baki yayi yaqi amsa mata, tace”ko baka fada ba nasan you are 20 ni kuma am 24, actually i think you should be calling me yaya”…Ayaan fa ya gama cika yayi taf don a duniya ya tsani tana kawo mgnr age din nan a tsakaninsu baisan tana sane tayi mishi haka don ta rama ba…saida ta bari ya gama cika da batsewarshi snn ta fashe da dariya tana dage mishi girarta tace”koba komai nima na rama”…ta karasa mgn tana mishi gwalo da tongue dinta kawai saiya tsinci kanshi yana dariya…wato shi dai everything tattare da ita murmushi yake sashi, dariya yake sashi, farin ciki yake sashi, shiyasa yakejin kmr duk ranar daya aureta ta zama mallakinshi ya zama complete…haka dai har suka gama cin pani puri suna tsokane tsokanensu, kmr yanda sukazo a kafa haka suka koma a kafa don ba wani nisa ke gare wurin ba saidai wnn karon suna tafe suna ’yar hira mai cikeda wasa da dariya.
Har gida Ayaan ya rakata yanata kallonta yanajin kmr kar su rabu sbd yanda bai taba gajiyawa da kallonta ba…Juwairiyya ta danyi hugging nashi for like one sec kafin ta dago tana dubanshi da murmushi sosai a fuskanta tace mashi”bye, see you tomorrow”…kai kawai ya iya gyada mata a hankali kafin yace”good night”…juyawa tayi ta shiga gidan shi kuma ya juya ya koma zuwa nasu gidan.
Washegari duk basu hadu ba kowa nacan yana fama lectures sbd sun kusa fara exams…Ayaan na gama lectures dinshi gaba daya ya nufi Cafeteria don tace acan zai sameta…ba tareda Lee suka taho ba don shi tun dazu ya wuce gida sbd baijin dadi…yana shiga cikin cafeterian ranshi ya koma bakikkirin fuskanshi ya wani tur6une sbd abinda ya gani…Juwairiyya ce zaune da wnn tsinannen ba’indiyen class mate dinta da dama ya tsaneshi tunba yanzu ba…karasawa table din da suke zaune yayi fuskan nan a tamke kmr bai taba dariya ba ya tsaya kyam a wurin yana kallonta kmr idanuwanshi zasu fadi qasa yace”waye wnn?”…kallon course mate din nata tayi kafin ta dawo da kallon gareshi itama da hausa yanda guy din bazai fahimci me suke cewa ba tace”ajinmu daya dashi mana…baka ganeshi bane?”…sake daure fuska yayi kafin yace”me yakeyi tareda ke a nan?”…dan karkatar da wuya tayi ganin yana nema ya kunyatata a gaban course mate dinta tace”Ayaan kar muzo nan wurin plss, karka taramin jama’a…besides meye ma tsakanina dakai da duk ka ganni tareda wani namiji saina fada maka waye shi?”…kallonta kawai Ayaan keyi cikeda takaici don saida yaji kmr ya tsinketa da mari a wurin amma dai ya daure ya hadiye wani yawu daya taru mishi a bakinshi yace”shikenan tashi mu tafi”…dauke kai tayi tareda rungume hannunta tace”kaje ni ba yanzu zan tafi ba”…murza forehead dinshi ya shigayi da karfi ganin yanda ta dage kan lallai sai ta sashi aikata abinda daga baya zai iya dana sani ba…bai sake ce mata tak ba kawai ya dauki bag dinta dake ajiye kan table snn ya kama hannunta da dayan hannunshi ya mikar da ita tsaye da dukkan karfinshi ya shiga janta suka fita daga cafeteria, sai tirjewa take tana ya saketa amma ko gezau baiyi ba kuma bai saketan ba har saida sukayi nisa snn ta daddage ta fizge hannun daga cikin nashi ta shiga binshi da wani kallo tana cewa”what is wrong with you Ayaan, what do you think you are doing?”…fuska a daure shima ya amsa mata da”am taking you home”…tace”who the fuck do you think you are to drag me out like that?…are you sick?”…bacin ranshi ne ya sake karuwa jin maganganun da take furta mashi yama kasa cewa komai…itama har snn nata ran a bacen yake tace”wai ma in tambayeka Ayaan, what makes you think that kanada right da zaka kafamin doka in bita?..do you think you are my boyfriend or something cox i don’t understand this insecurity really…i don’t get it so tell me meyasa bakaso ka ganni da wani namiji do you think we are dating?, or have you suddenly forgotten that you are just my friend not my boyfriend?”.
***.
Rano✨