SHI YA ISKANTANI

Fita ta 3

by @kwalisa

**
Wata tsuhuwa mai ruwan munafukai muka soma samu a tsakar gidan, tun lokacin da muka shiga cikin gidan ta kafeni da idanunta tana kallona, har muka qarasa gabanta bata xauke idanunta daga kaina ba.
Muna zuwa gabanta ya tsaya yana kallonta, ni da nake binsa a baya zugi-zugi kamar jela nima na tsaya shiru ya mamaye wajen na taqin lokaci kafin daga bisani ya buxa baki ya yi magana.
“Uwar tuwo, a nunawa baquwa xakinta a kuma haxa mata qayataccen ruwan wanka ta yi wanka zuwa anjima a kawo mun ita xakina” wacce aka kirawo uwar tuwo ta sake cira kai ta dube ni, ga mamakina sai naga fuskarta ta washe zuwa ga murmushi kafin ta buxe bakinta da ke cike da tuqar goro tace masa.
“An gama Alhaji” Ya gyaxa kai kamar qadangare kafin ya yi taku huxu gaba sannan ya juyo ya sake kallona da haxaxiyar fuska tamkar wacce aka sassaqo daga katako yace mun.
“Zata miki bayani da dokokin zaman gidanan” Ya sa kai ya yi gaba abinsa ya barni a tsaye tamkar falwaya.
Har ya yi mintina uku da barin wajen babu wanda ya yi magana tsakanina da uwar tuwo. Ganin shirun ya yi yawa na yi qarfin halin juyawa da zumar ficewa daga cikin gidan a lokacin kakkausar murya mata ta mun magana.
“Kul… kul kika aikata abinda zuciyarki take aiyana miki” Na ja na yi turus kamar wacce aka kafe da qusa, na juya na dubeta.
“To amman mene amfanin zamana a wannan wajen” Ta miqe a hankali ta tako zuwa gabana, sannan ta saka hannunta ta kamo nawa ta ja ni ya yin da ni kuma ban yi mata gardama ba na bita kamar raqumi da akala bamu tsaya ba sai cikin wani xaki.
“Nan ne xakin ki…” Ta kafe ni da idonta sannan ta sake jana zuwa wani wajen ta tura sannan na fahimci ashe banxaki ne “Nan za ki shiga ki yi wanka” Na zame hannuna daga cikin nata.
“Me yasa zan shiga na yi wanka?” Ta yi murmushi.
“Saboda yau a xakin Alhaji za ki kwana” Na murtuke fuska.
“Xakin Alhaji kuma Allah suturi buquyi, kuma kwalelen kura da hantar kare, duk iskancinsa sai dai ya gani ya qyale domin sama ta yiwa yaro nisa” Uwar tuwo ta sake yin murmushi kamar bata ji abinda na faxa ba a hankali tace mun.
“Ke sabuwar zuwa ce, wannan gidan ba shi da maraba da wajen bautar da mata, nan gaba kaxan za ki fahimci haka” Maganarta ta saukar mun da tsuro nan take a cikin zuciyata.
“Gidan bautar da mata kuma?” Ganin kalamanta sun samu matsuguni a zuciyata yasa ta sake matsowa kusa da ni.
“Ya sunanki?” Ta jeho mun tambayar kai tsaye.
“Zainab” Na bata amsa.
Ta miqa hannu ta zame gyalen dake jikina, ta zuba mun ido daga sama har qasa “Kin tava kusantar xa namiji?” Tambayar ta zo mun wata banbaraqwai, wannan wanne irin gidane? Wanne irin mutane ne su?
Ganin duk na shiga cikin damuwa yasa ta sake sassauta murya kafin tace mun.
“Ki amsa mun tambayoyina domin sune za su bani damar sanin wanne irin taimako zan yi miki” Jin haka sai ‘yar nutsuwa ta zo mun kaxan.
“Me kike son sani?”
“Kinji abinda na tambayeki ai xa zu, ko na sake maimaita miki tambayar?” Na girgiza kai kafin kai tsaye na bata amsar cewar “Bansa ma yadda ake yi ba” Ta kafe ni da ido.
Sannan ta ce mun “Hanyar fansar kai daga wannan gidan guda biyu ce, ta farko za a haxaki da wasu zaratan maza su kwanta da ke har ki samu ciki, bayan kin samu ciki kin haihu za ki mallaka xan da kika haifa ga Alhaji a matsayin kuxin fansar kai, shi kenan zai salame ki” Ta dakata tana kallona domin ganin ko maganar data faxa ta yi tasiri a kaina.
Tabbas ta yi kuwa, domin bama tasiri ba gigita ni tayi, wanda take wani gumi ya soma karyo mun, hakan ya saka ta kamo yatsun hannuna tana qoqarin saka mun nutsuwa.
“Akwai hanya ta biyu idan wannan ta yi wahala” Cike da razana nace mata.
“Wacce kuma ta biyun?”
“Idan kin aminta babu namijin da ya tava saduwa dake, to akwai manya mutanen da suke neman a kai musu macen da ba a tava kwanciya da ita ba, za su kwanta da ita su xebi maniyinta su baiwa mallaminsu ya yi musu sihiri… wannan ba shi ne matsalar ba babbar matsalar yawanci matan da suka zavi hanyar nan ta biyu yanzu suna xauke da cutar qanjamau”.
“Qanjamau kuma?” Cikin tsananin kaxuwa na tambayeta.
Tabbas ina cikin gagarumin tashin hankali, domin wannan shi ake cewa gaba tsini baya sayaki…
Mun xakin tsayin lokaci a cikin wannan yanayin babu wanda ya yi magana kafin daga bisani uwar tuwo ta sake yin magana a wannan lokacin cikin ruwan sanyi tace mun.
“Idan na ce a cikin biyun ki zavi xaya wanne za ki xauka?” Tambayar da ta mun yasa na tsayar da tunanin daya mamaye ni, na dubeta a nutse kafin na buxa baki na bata amsa kai tsaye da cewar.
“Idan zan aikata domin kuvutar da kaina daga wannan gidan to zan aikata laifi na biyu” Ta kafe ni da idanu.
“Na biyu fa kika ce?” Na gyaxa mata kai sannan na miqe ina kewaya cikin xakin sannan nace mata.
“Eh shi zai fi mun sauqi, haka kuma ko a banza ba qatan maza ne suka tara mun ba…” Jin haka yasa uwar tuwo yin murmushi, sannan ta nuna mun ban xaki “Ya kamata ki shiga ki watsa ruwa, zan sake dawowa zuwa amjima ta yiwu ki sauya shawara” Tana kammala faxin haka ta juya ta nufi hanyar fita har taje qofa nace mata.
“Bana sauya magana idan na faxa…” Ta juyo ta qare mun kallo sannan ta sa kai ta fita.