37
by @aishatouuu
_Aishatou_
***
_________________
Aunty Mansura tayi zugum ɗaya bayan ɗaya take kallon kayan da Ramma ta kawo mata da sunan kayan sawar Husna, kayan Husnah dai tasu ƴar gidan Safiya Autar gidan su.
"Allahu Qadir."
Ta faɗa a bayyane kawai sai ta kama hannun akwatin ta rufe tana duban Ramma tace "sannu baiwar Allah, mungde sosai Allah ya biyaki, tunda muka shigo Husnah ke faɗa min kece Maman ta sai Aramma, mungde miki amma dan Allah wannan kayan ki tafi dasu kawai nasan baza a rasa wanda zaki bawa ba, babu matsala in munje gida sai a nema mata wasu."
Ramma tayi murmushi tace "to Maman Ma'u nice da godiya, amma zanye kewar Ma'u." Ta faɗa idan ta na cika da ƙwalla, matan Mai Gari suka hau bata haƙuri tunda sunsa ita bata da yara sai Ma'un.
Aunty Mansura ma haƙuri da godiya take ta mata, suna ta maida zance Husna ta fita da gudu babu wanda ya kula ta tafi tasha neman Mahaukacin yayanta, saida ta zagaye tashar tana neman sa amma bata ganshi ba, wajen Bahari ma taje baya nan, ta wuce Chioma a ƙofar shago tana mata magana amma hankalin ta yayi gaba bataji taba.
Ta daɗe a tsaye a tashar tana tunanin wanda zata bawa saƙo ya faɗa wa yayan ta Mami tazo tafiya da ita amma kowa ta kalla sai taji ta kasa faɗa masa komai, jikin ta a mugun sanyaye ta kamo hanyar barin tashar a hanya suka haɗu da headmaster ya tsuke ciki riga da wando yasa gilashi yana kallon mutane ɗai ɗai, Husna ta wuce shi tana masa kallon banza ta saki tsaki.
Dama tun daga randa taga yana ƙoƙarin dukan yayan ta ta tsane shi haka bata sake siyar masa da komai nata ba. Ko yace ta bashi akan idon sa zata ce bazan siyar maka ba, tun yana binta ta siyar masa da kayan siyarwar ta har ya haƙura ya daina tayawa.
A ƙofar gidan Mai gari ta samu Abdulyassar, Aramma da Aunty Mansura Aramma ne ya fara gano ta yace "yawwa gata nan ma, Asma'ullahi ina kika tafi? Kin barsu suna jiran ki."
Husna ta sunkuyar dakai tana murmushin jin daɗi.
Ramma ta fito, Mai gari ma ya fito Aunty Mansura ta ciro kuɗi masu yawa tabawa Mai gari ya karɓa yana ta zuba mata godiya, haka Ramma saida tayi mata alheri, yaran da suka zagaye Motar kuwa dubi daya ta basu tace suje su siyi alewa nan da nan suka watse suna murna.
Aramma ya dubi Husna da bakin ta yaƙi rufuwa yace "to Asma'ullahi Allah ya kiyaye hanya ki gaida Mamanki da yayanki kinji, ki gaishe min da Alhaji ƙarami, Allah ya raya ki yayi miki albarka."
"Amin Amin Aramma mun gode sosai Allah ya ƙara girma da lafiya." Aunty Mansura ta faɗa tana kama hannu Husna Ramma na danne kukan ta ita ma tace "Allah ya kiyaye hanya Ma'u sai wata ran." Ta faɗa tana barin wajen da sauri dan kuka ne ya ƙwace mata.
Husna kuwa taji babu daɗi sai dai murna ta hanata yin kuka dan Allah Allah take su tafi gani take kamar za'a ce an fasa tafiya da ita.
Harta juya zata shige mota sai kuma ta dawo da baya ta tsaya a gaban Aramma tana kallon sa tace "Aramma dan Allah sako zan baka ka faɗawa Yayana." Aramma ya tsaya yana kallon ta dan bai gane wanne yayan nata ba, ganin bai gane wa take nufi ba sai Husna tayi murmushi tace "Aramma Yayana fa wanda bashi da lafiya."
"Oho wai bawan Allah nan?"
Husna ta ɗaga masa kai tace "naje tasha kozan ganshi na faɗa masa zan tafi amma baya nan, dan Allah Aramma ka faɗa masa na tafi sai wata rana."
Husna ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido, maganganun ta kuma suka bawa Aramma mamaki tare da jefa shi cikin kokonto, Husna bata tsaya jin me Aramma zaice ba ta juya ta shige cikin motar a baya ta zauna tana ɗagawa Aramma hannu Abdulyassar ya rufe ƙofar Aunty Mansura ta shiga gaba yaja motar suka tafi, Husna ta juyo baya tana dagawa Aramma hannu yana tsaye yana kallon su yana Murmushi har suka karya kwana.
*****Alokacin da motar su Husna ke daidaita zaman ta akan titi dan barin garin a dai-dai lokacin kuma mahaukacin yayanta na zaune a ƙasan bishiya can gaban rumfar Bahari bai daɗe da zuwa wajen ba, yana zama kuma ko minti biyar baiyi a wajen ba, mai mota ya sauke Bahari da jarkokin fetir ɗin sa daya siyo daga Doko, haka ta bayan shi motar su Husna tazo ta wuce, akace wai rashin sani wanda yafi dare duhu, yadda baƙin gilashin motar ke sawa na waje baya iya gane na ciki haka Husna dake barin garin su Mahaifin ta bata ganshi ba har suka yi nesa da garin.
A fili murna da wani irin farin cikin barin garin ne kwance akan fuskarta, ata can ƙasan zuciyar ta kuma wani irin kunci da rashin jin daɗi take ji duk lokacin da ta tuno da ta tafi ta bar shi a ciki garin da suke masa kallon mahaukaci sai taji kamar ta koma, sanda kuma ta dena hango garin su ta cikin gilashin idanun ta sai taji jikin ta ya saki wata irin kewa da damuwa na rufe gabobin jikin ta a hankali ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.
........Yana zaune a kasan bishiyar Dan Hajja ya zo ya wuce shi da sauri kamar zai tashi sama waya manne a kunnen sa yayi wajen Bahari dake zubawa headmaster mai a mota yana faɗin.
"Eh ina nan zaku ganni ta ƙarshen tasha ɗan gaba dame saida fetir bumburu tu."
"Eh yawwa daga shi saini shagona ne babban shago duk tashar, zaku ganshi ginin kwangiri, yawwa sai kunzo." Ya sauke wayar yana kashe ta yace "Bahari yimin full tank a mashin ɗina, yanzu Gambo zai kawo maka." Bahari ya gyaɗa masa kai yaci gaba da zuba fetir ɗin.
Dan Hajja kuma ya juya yana sake daga wata wayar yana zaune yazo ya sake wuce sa kaɗan sai kuma ya tsaya yana danna wayar shi Gambo ya iso inda yake tsaye yace "Yawwa ka kaiwa Bahari mashin ɗin yamin full tank, abokan aikina ne zasu zo oga ne zai bada sako a kawo min kasan yana gaf da sauka saura ƴan kwanaki, to sai ɗazu ya sanar mana zamu ɗan haɗu da wani yaron shi akwai sakon da zai bamu kan ya diro, na kira íla ma yace min tare zasu taho."
Gambo ya buga ihu yana faɗin "Yau muna da kuɗi Malam kut**** du*** eeee.....yau zamu baje ta."
"Hhhhh." Ɗan Hajja yayi dariyar nishaɗi.
"Ai zuwan Oga alkhairi ne tun kafin yazo sai yasa an jiƙa mana maƙoshi da Naira." Ɗan Hajja ya faɗa suka tafa da Gambo yayi shagon shi, shi kuma Gambo ya tafi wajen Bahari.
Ba'a dade da fitowa daga sallar azahar ba wata mota ƴar ƙurƙura ta tsaya a tsakiyar tasha, mutane huɗu dake bayan motar suka fara diddirgowa ƙasa kafin mutum biyun gaba su fito, gaba ɗayan su sun yi futu-futu da ƙura ƙafafun su sunyi fururu haka kawunan duka ƙafafun wandunan su a dage suke, rigunan jikin su kuwa duk sun koɗe da alama sunji jiki, slifas ne a kafafunsu harda wanda nasu ya tsinke suka daure da leda kana ganin su kaga ma'aikata da alama daga wajen aiki suke suka tsaya anan.
A rumfar shagon Sunday suka zazzauna Chioma ce kaɗai a cikin shagon, ruwa me sanyi suka siya pure-water suka sha da lemo, sun ɗan jima a zaune a wajen kafin suka tashi Mutum ɗaya a cikin su ya tuka motar sauran kuma suka biyo shi a ƙafa a famfon masallaci suka tsaya suna wanke jikin su wanda yaja motar kuma ya tsaya a wajen Bahari ya fito yana kallon gaban shi yace "malam zoka ƙaramin mai rabin galon a motar nan." Ya ciro kuɗi yana tambayar shi nawa ne, Buhari ya faɗa masa kuɗin ya miƙa masa sannan yace yana zuwa kanya gama saka masa man, sai kuma y juya wajen abokan tafiyarsa yace "Kai in kun gama ku same ni shagon can na gaba naga kamar yana awu, bari na duba ko zan samu Ƙaura a wajen sa." Ya faɗa yana ɗaga wa abokan tafiyarsa hannu yayi gaba yabar motar a wajen Bahari.
Shagon Dan Hajja ya wuce yana ɗan dube dube, a waje ya tsaya Dan Hajja ya fito suna magana sauran mutum biyar ɗin suka taho wajen suna tafe suna hira.
Dukan su babu wanda ya zauna wanda ya iso wajen na karshe ne ya dubi Dan Hajja yana ƙarewa wajen kallo yace "ɗan hanya ne." Dan Hajja ya kalle shi da sauri sai kuma yayi murmushi yace "ba hanya." Sauran suka kwashe da dariyar gane su da yayi, wani mai ɗan jiki a cikin su da sai yanzu yayi magana yace "zaka karɓi saƙon ka yanzu lallai kana kwashe wa abokin hanya." Yana faɗin haka wanda ya fara zuwa wajen da farko ya ciro wani emblop mai ruwan ƙasa ya miƙa masa, ya karɓa ya bawa Dan Hajja sai kuma yaɗan bugi kafaɗun sa ƙasa ƙasa yace "kana ƙoƙari, ka huta da wannan sai mun haɗu gani na biyu."
Sai kuma yaɗan yi masa alama da hannu yace "ka kula."
Ya juya zai bar wajen ke nan ya ga mahaukaci zaune a ƙasan bishiyar da suke tsaye ya riƙe Sandar hannun sa ya cakata a kasa ƙafarsa ɗaya a miƙe daya a tanƙwashe da sauri ya juya ya kalli ɗan Hajja yace "wannan kuma daga ina?"
Ɗan Hajja yayi murmushi yace "ai mahaukaci ne yaɗan kwana biyu da zuwa nan."
"Kai amma baka da hankali ko? Ban faɗa muku duk wanda yazo gari inya wuce 24 hours ku faɗa min ba?"
Kafin Dan Hajja ya sake magana wanda yayi maganar har yayi gaba da sauri da nufin yabar wajen yana isowa inda Mahaukacin ke zaune kawai sai gani yayi ya miƙa hannun ya tare masa hanya, sauran abokan tafiyar da suke kamar yan rakiya a wajen mutumin daya tarewa hanyar da dantsen hannun sa sai suka taso masa suna fadin.
"Kai matsa mana a hanya mu wuce a ina ma kuka samu mahaukaci irin wannan?."
Wanda aka tarewa hanyar kuwa saida yaji wani mugun abu ya daki zuciyar sa dan babu abinda ya faɗo masa rai a lokacin sai kashe din da bokansa yayi masa, akan zuwa garin wannan nema yasa yayi badda kama yazo kuma a lokacin da bashi ya faɗawa yaran saba, amma tsabar rashin bada kai sai ya dubi Dan Hajja yace "kai zoka korar mana shi mu wuce."
Yanzu da asalin muryar sa yayi wa ɗan Hajja da mamakin mahaukacin ya cikawa zuciya magana, jin muryar mutumin ta asali kuma ɗan Hajja baisan sanda rudewa ta sashi faɗin "Ogan sama ba."
Saida ya kira sunan kuma saiya riƙe baki yana sake kallon mutumin.
Ogan sama ya yiwa ɗan Hajja wani mugun kallo da nufin zagaye Mahaukacin ya wuce, har yanzu yana a yadda yake ogan sama ya ɗaga ƙafa zai juya cikin wata dakakkiyar murya yaji mahaukacin yace
"You are too late ka riga ka shigo hannu Tasi Maro ko na kiraka da KACA da alama za kafi gane wannan sunan."
Yana kai karshen maganar kuma cikin wani irin zafin nama ya miƙe tsaye yana wa ogan sama wani irin murmushin ka gama yawo sannan cikin jin isa ya sake ce masa "barkan mu da sake haɗu wa a karo na biyu kuma na ƙarshe."
Ya miƙa hannu da nufin riƙe shi ogan sama yayi wani tsalle yayi baya sai kuma ya kwashe da dariya yana tare da faɗin "ƙarya kake Ƙwaya, kai baka isa ka kama niba na wuce tunanin ka, ku kuma kowa yayi ta kanshi." Ya faɗa wa sauran yaransa a tsawace.
Kan suyi wani motsi sukaji ana dirowa daga saman bishiyar da suke tsaye, Sunday ne ya fara dirowa ya tsaya akan kafafunsa cikin Kananan kaya, headmaster ma ya diro, suka saka su Ogan sama a tsakiya ai gaba ɗaya sai suka rude kowa ya fara neman hanyar gudu, Ogan sama kuwa saiya ɗaga ƙafa zai bugata a ƙasa da nufin ya ɓace kamar yadda yake yi aduk sanda ya shiga hannu amma kanya sauke ta ƙasa MM yayi wata muguwar sufa ya daki ɗaya kafar shi yayi sama ya zube a ƙasa, sauran yaran da zasu watse danbe ya kware tsakanin su dasu Sunday.
Mutum biyu suka taka da gudun neman tsira zuwa wajen motar su dake wajen Bahari, ɗaya ya kama jikin motar zai haye yaji an doko shi ƙasa ya faɗo tim saida ya kurma uban ihun azaba dan hannun shi ya bugi ƙasa, sannan Buhari daya doko shi ƙasan da sauri ya naushi wata jijiya a gefan wuyansa take ya suma, wanda ya biyo shi ya juya zai gudu Bahari ya jefe shi a keya da wani mulmulallan ƙwallo take ya faɗi a wajen dafe da ƙeya yana son tashi amma ya kasa saida Bahari yasa musu handcup sannan ya taɓa wani abu kamar Bluetooth a kunne sa da sauri ya fara fadin.
"Operation MF5/1O-08 we are on duty, 1/07MM09 sun shigo hannu, na maimaita Operation MF5/1O-08 on duty masu laifi sun shigo hannu"
Saida ya maimaita yakai sau uku sannan ya kalli wajen ɗan Hajja inda su Sunday suke tuni suka sumar da mutum biyu suka saka musu handcup, MM kuma dambe suke zubawa shida ogan sama.
Bahari ne ya hango Mutum ɗaya daga cikin su yayi cikin tasha da gudu a tsiyace ya rufa masa baya nan fa hankalin mutane ya fara kawowa kansu cikin abinda bai cika minti ɗaya ba Bahari ya kurewa ɗayan gudu ya kama sa, tuni ya sumar dashi mutane suka zagaye sa cikin ɗinbin mamaki dan basu san meya haɗa suba saida sukaga ya zaro wata siririyar igiya ya ɗaure masa hannu sannan mutane suka fara ƙoƙarin tambayar sa meya faru.
Acan rumfar ɗan hajja kuwa Ogan sama ya ƙwaci kansa da ƙyar ya kwasa da gudu yayi cikin tasha headmaster da Sunday suka rufa masa baya, shi kuwa MM bai bisu a baya ba sai tsaiwar sa daya gyara yana kallon yadda Ogan sama yayi cikin tasha ta gudu saida ya gama ƙare masa kallo sannan cikin iyawa ya rarumin Sandar shi cikin zafin nama yayi wani irin jifa da ita cikin iya seti Sandar ta buɗe ta zama igiya take ta harɗe ƙafafun Ogan sama "tim." ya faɗi ƙasa a tsakiyar tashar ɗan nesa da Bahari kaɗan, sai kuma ya fara yunƙurin tashi danya gudu kafin mutane dasu Bahari su farga kaiwa sai ji kake.
"Tas....tas...tasss..." Karar bunduga ta sauka a kunne jama'ar tashar har wanda bai san me ke faruwa ba saida ya taso a tsoroce, ihun azaba Ogan sama ya kurma dan harbi ukun da MM yayi masa duka ya same sa a ƙafa ɗaya, su Sunday na ganin haka suka tsaya, cikin ƙarfin hali Ogan sama ya ɗaga ɗayar kafar zai gudu ji kake "Tauuuuu....."
Ya sake harbin shi a ɗaya kafar, nan fa mutane suka rude tare da juye juyen neman ta inda harbin ya fito.
Mamaki da tsoro ya daskarar da mutane sanda suka yi Ido da wanda suka sani a matsayin mahaukaci yana tahowa hannun sa riƙe da bunduga ƴar ƙarama, cikin ainahin tafiyar sa ta kakkarfan Namiji maji karfin dantse da jarumta saf...saf....saf haka yake takowa da sarssarfa a ainahin MM ɗin sa, tun kan ya iso wajen Sunday ya aje masa benci a gaban Ogan sama dake kwance a tsakiyar tasha warwas yana ihun neman ceto, mutane kuwa tsoro da tu'ajjibi yasa kowa ya kame daga inda yake yana kallon ikon Allah.
"Sagir....."
MM Ya kira sunan da wata irin murya mai zurfi da faɗi.
"Yes Sir." Headmaster ya faɗa yana kame wa a gaban sa.
"Kaida Fasal ku ƙaraso da sauran mutanen nan." Yayi masa maganar cikin bada umarni, yana rufe bakin sa ya juya da sauri.
"Chike." Ya kira sunan, da sauri Sunday ya matso gaban shi ya zuge zif din gaban jallabiyar jikin sa take ta zame ta faɗi ƙasa, saiga wasu riga da wando bakake a jikin shi, baƙin abun daya saka a hannunsa ya zare take fararen sangalalin hannunsa suka bayyana da wasu irin murɗadɗun damatsa dakai ba sai an faɗa maka maisu ya tara ƙarfi ba.
Chioma dake tsaye a wajen tun ɗazu ta jefowa Sunday wata bakar jaka ya cafe, a ƙasa ya aje ta ya bude cikin ta saiga wasu takalma boot baƙake, ya tsugunna a gaban MM dake zaune akan bencin yana kallon ogan sama da wanda Bahari ya sumar, saida ya zare baƙin abun kafar sa sannan ya fara saka masa takalmin, asalin halittar kafarsa ta farar fata da kwantattun bakaken gashi suka bayyana, shi kuma sai yasa hannu ya ɗaye gemun daya cika masa fuska, gashin kansa ma ya cire hular asalin kammanin sa suka bayyana Blackrehy eyeglasses mai kyau Sunday ya miƙa masa yasa take mutane suka ƙara shiga mamaki.
Fuskar sa babu gashi ko kaɗan bashi da gemu haka bashi da gashin baki, girarsa a cike dake baƙa ƙirin, kasan kuwa kitsone guda huɗu all back jelar kitson an tufketa waje ɗaya.
Sunday yana gama daura masa takalmin daidai lokacin Bahari da headmaster suka gama kawo sauran mutum biyar ɗin nan, ya dube su ɗaya bayan ɗaya, yace "Kun ɗakko wancan Yaron a kofar shagon shi." Suka juya a tare suka tafi dakko ɗan hajja daya dade da suma.
"Victoria." Chioma ta bayyana a gaban sa, kallon ta kawai yayi ba tare da yayi magana ba tace "yes Sir."
Ta juya kan ogan sama daya fara galabaita ta fara ƙoƙarin cire masa bulet ɗin kafafun sa.
"Chike ina son ganin Garba da.....mene sunan ta?" Yayi maganar da na kusa da shi ne kawai zaiji dan ko haƙorin sa baya fitowa waje bare na nesa yayi tunanin magana yake, Bahari da isowar su wajen ke nan kuma yaji me MM yace sai yace "Ramma."
"Yes Inason ganin su yanzu, Faisal....!" Ya kira sunan da Babbar murya.
"Yes."
Minti biyar ne damu ta taho tare da....?" Ya ɗanyi shiru yana tauna sunan da zai faɗa.
"I understand." Bahari ya faɗa yana wani shegen murmushi sai kuma ya juya inda ya hango Aramma a tsaye, yana zuwa yace "Dan Allah Aramma muna son ganin Baba Ramma da Ma'u please bamu da lokaci." Bahari ya faɗa cikin girmamawa da roƙo.
Aramma ya rasa mema zaice masa, dan wallahi shi kansa ganin komai yake makar a mafarki.
"Please Aramma." Bahari ya sake faɗa da asalin muryar sa sai kuma ya juya yana duba inda Garba yake ba tare daya tsaya yaji amsar Aramma ba, can nesa ya hango sa, Garba yana ganin Bahari ya doso shi yuuuuuu mutane suka bisa da kallo Garba kuwa jikin sa saiya ɗuru ruwa ya fara fadin.
"Wallahi banyi lefin komai ba." Ya faɗa a mugun tsorace.
"Karka damu Boss ke son ganin ka, am sure babu abin da zai yi kama."
Bahari ya faɗa yana kamo hannun sa suka taho wajen tare.
Cikin abinda baifi minti biyu ba Chioma ta cire bulet ɗin jikin Ogan sama yana ihu yana komai babu kashe zafin ciwo babu tausaya ta cire su ta zuba wani ruwa a wajen take kafar ta fara rawar azaba jijin ya tsaya cak.
Ta cikin baƙin gilashin idon sa yake kallon komai harta gama.
"Wu...wu..wu...wu....."
Ƙarar jiragen sama masu saukar ungulu ta cika garin, dama gashi zancen mahaukaci ya kama Ɗan Hajja da wasu mutane a tasha tuni ya fara shiga cikin gari, ƙarar saukar jirage akan titin tsakiyar tasha kuma saiya sake jawo hankalin jama'ar garin, nan da nan tashar ta cika da mutane suka zagaye su kowa da abin da yake faɗa.
Helicopter na farko daya fara sauka a tsakiyar titin matasa biyu ne suka diro daga ciki, sanye da bakaken kaya ga bundugu a jikin su bayan su an rubuta SS, ɗaya jirgin kuma ɓaro ɓaro a jikin sa ga rubutun NDLEA nan da manyan harfa.
Su Bahari dake amsa sunan Faisal tuni suka zura takalma da jacket baƙake tuni ya yage gemu da sajen daya rufe masa fuska wasu kuma ja an subuta NDLEA a jikin ta.
Ogan sama daya dade da suman azaba aka fara sawa a Jirgi wasu suka shiga saida aka gama kwashe su duka sannan ya juyo ya kalli Garba dake tsaye jikin sa na rawa, dai-dai lokacin kuma Ramma ta iso wajen Aramma na binta a baya, Bahari yana hango ta ya tafi inda take mutane suka matsa ta shigo wajem yuuuuuuuu akan bisu da kallo.
Ƙasa ƙasa ya yiwa Bahari magana wanda shi kaɗai yaji me yace, Bahari ya daga masa kai ya dubi Garba yace "wajen da nake saida fetir yace an bar maka shi harda jarin gaba ɗaya." Garba ya ƙwalalo ido waje cikin ƙarfin hali yace "Uhm me kace Bahari?"
Bahari ya sake cewa "Eh ya ce an baka kyauta saboda ka taimaki Ma'u."
Bahari yana gama faɗin haka ya matsa ya bawa MM hanya ya matso gaban Ramma saida ya cire p-cap ɗin kansa alamar girmamawa sannan cikin maganar sa ta cikakkun Maza ya fara magana.
"Mama mun gode sosai da kula da ita da kikayi." Sai kuma ya juya wajen Aramma yace "Allah ya ƙara girma Aramma bamu da time amma zamu sake haɗuwa soon, Shagon Sunday Mama an baki kyauta duka kayan dake ciki naki ne saboda Alkhairin da kikayi mata."
Ya ɗanyi shiru yana rufe idanunsa ta ciki gilashin sai kuma ya buɗe, Bahari ya matso da wani envelope fari ya karɓa ya kama hannun Aramma yasa masa yace "Nagode sosai babu abinda zanma naji daɗi amma wannan ka samu wani ya rakaka dutse akwai komai aciki inama addu'ar yin Umrah me albarka, sai mun sake haɗuwa."
Ya karasa maganar da nufin juyawa Aramma ya riƙo hannun sa yana faɗin. "Asma'ullahi ta bar garin nan ɗazu Yayar Maman ta tazo ta tafi da ita, amma ta barmin sako tace na faɗawa yayanta ta tafi sai wata rana"
Aramma ya faɗa masa maganar yana ƙare masa kallo, saukar maganar a kunnan sa tasa yaji wani abu a ransa mara daɗi, dan yaso ya ganta yanzu amma sai ya dake cikin jarumta ya ɗagawa Aramma kai ya juya yaci gaba da tafiya ba tare daya sake juyowa ba.