38
by @aishatouuu
Bahari ya bawa Ramma mukullan shagon Sunday ya juya da gudu ya haye Jirgin su, MM ne ƙarshen shiga nasu jirgin yana zama jirgin ya fara tashi mutane suka raka su da ido, dai-dai lokacin kuma Hajja da mugun labarin kama ɗan ta yaje mata ta iso tashar hankali tashe, saidai ina ta makara dan kuwa tuni harsun lula sama ta zube a wajen tana kurma uban ihu.
Mutanen garin kuwa sai suka fara maida yadda akayi, Aramma da Ramma suka bar wajen jikin su babu karfi, zance kuwa tuni ya zama on top topic ɗin da ake tattaunawa a ciki garin, wasu suce ƴan sanda ne wasu suce sojoji ne, kowa dai da labarin da yake bayar wa.
TO FAH!!!!
*Littafi MUTUWAR AURE na ɗaya kyauta ne, littafi na biyu na kuɗi ne zanyi a Telegram akan Naira ɗari biyar kacal, a Arewapen kuma zaizo muku a farashi mai rahusa, ku dai ku garzaya ba da labarin littafin MUTUWAR AURE labarin Husna da Mansur Mahmoud Mas'od Al-alfeey ba Andalus (Spain) ku sanar da wanda bai karanta ba da ya fara kar a barshi a baya. Ina da kyakyawan yakini akan abin da na rubuta kuma ina mai ba ku tabbacin za ku samu labarin nan fiye da hasashenku, In sha Allahu ba zan ba ku kunya ba*
AKWAI CAKWAKIYA A GABA...
_AMMA KAFIN NAN INADA TAMBAYA..._
SHIN HUSNA DA MAHAUKACIN YAYAN TA ZASU SAKE HAƊUWA?
KUNA GANIN HUSNA ZATA SAKE KOMAWA ZAMA GIDAN BABAN TA?
INTA KOMA YANZU WANNE IRIN ZAMA ZASUYI DA NANA?
TSAWAN SHEKARUN NAN DA HUSNA TAYI A ƘYAUYE ME YASA SAI YANZU RANA TSAKA DANGIN MAMANTA SUKA ZO DAUKAR TA?
INA LABARIN MAMAN HUSNA DA YAYAN TA BAFFA?
THANK YOU FOR SUPPORTING ME❤️