Page 7&8
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _***_
Kuka Ahmad ke yi kamar ransa zai bar jikinsa yana kuma kiran mahaifiyar domin ceton sa, amma sam tak'i ko lek'owa. "Abbakar! Abbakar baza ka cece ni ba, Abbakar mutuwa zan yi, k'irjina ciwo yake yi Abbakar! Dan Allah ka kunce ni zan mutu!". Ahmad ya fad'a yana kuka saboda gaba d'aya nauyinsa k'irjin ya koma. Abubakar d'in shima kukan yake yi yana kallon Inna Murja da y'ay'an Sakina da Sameera suna dariya har da kyakyatawa. A mugun zuciye Abubakar ya isa wajen Ahmad d'in ya shiga k'ok'arin kwancesa, Inna Laadi ta zaburo tayo kansa tare da falla masa mari, amma Abbakar tsabar zuciyar da yayi ko jin zafin marin bai yi ba, sama saka hak'ori yayi yana jan igiyar ya soma sassauta d'aurin, Inna Murja kuwa ko ta ina duka take kai masa, shi kuma ganin ya kunce d'aurin sai ya saka hannun ya soma k'arisa warwarewa dai-dai lokacin da Inna Laadi ta fito daga d'aki ta d'auke shi da mari tare da jan hannunsa zuwa cikin d'akin tana masa fad'an don mai zai shiga abunda ba ruwan shi. Shikuwa Ahmad yana ganin hannunsa ya kwance yayi saurin warware sauran igiyar ya yar tare da kwanciya flat yana kallon sama yana wani irin nishi tare da danne hannunsa guda biyu a kan k'irji, can kuma ya fashe da kuka yana jujjuya kansa. Yafi k'arfin awa biyu kamin ya mik'e ya rarrafa ya shiga d'akin Inna Laadi wacce ke zaune a kan tabarma ita da su Abubakar suna cin d'an waken dawa, wani irin had'iyar miyau Ahmad d'in yayi, domin rabon shi da saka abinci a baki, tun karin safe da Inna Abu ta basa d'umamen tuwon masara da miyan kubewa bushasshe. "Innar mu zan ci d'an gaudan, nima yunwa nake ji tun safe ban karya ba!" Ya fad'i yana mai karyar da kansa. Wani harara ta galla masa tare da nuni da hannunta a waje, don ba k'aramin abu ke sakawa ta bud'e baki tayi masa magana ba, rabon da Ahmad yaji muryan mahaifiyar sa ta na magana dashi shekaru biyar kenan, ko yayi abunda za tayi magana dole, ko kallon in da yake bata yi, wani lokacin da gangan yake wani abu don ya samu yaji muryan ta tana magana dashi, amma sai tayi gum ko kuma ta bar wajen. Kuka Ahmad ya fara yi yana fad'in, "Haba Innar mu, haba Inna, ni mai na miki? Mai yasa ba kya sona ne? Ai ga su Abubakar nan, kina magana dasu kuma kina basu duk abunda suke so, ni mai yasa bakya sona to?" Ya fad'i yana kuka sosai. Tsam ta tsame hannun ta cikin d'an waken tare da ficewa daga d'akin ta bar masa ta koma tsakar gida, dama kuma haka take yi, idan ya shigo d'akin ta nuna masa hanyar fita yak'i fita, sai ta tashi ita ta fita daga d'akin kuma ko me take so da'ukowa daga d'akin bata tab'a shiga har sai ya fita, ko da kuwa manja ko mangyad'a aka zo saya ta gwammace tayi asara da ta shiga d'akin. Kuka ya fashe dashi tare da kallon Abubakar yana fad'in, "Abbakar mai nayi wa Innar mu bata so na? Ku kun ji dad'i, Inna na son ku". Sosai yake kuka, Abbakar ya dawo kusa dashi ya zauna tare da dafa shi yana fad'in, "Kayi hak'uri kaji Ahmadu, Innar mu na san ka kai ma, zan yi maka addu'a idan nayi sallah Allah ya sa ta dawo tana kula ka kamar mu. Ga d'an wake ka nan cikin roba, Inna ta zuba ta ajiye, kuma na san naka ne, kullum kana zuwa kana d'auka kaji! A ciki take zuba maka naka ta ajiye, idan baka zo ka d'auka ba kuma sai ta bawa Umar ya cinye. Kullum kake zuwa kana d'auka kaji?". Shuru Ahmad yayi yana tunanin kenan dama Innar tana ajiye masa abinci, magana ce baza ta iya masa ba ta ce ga abincin sa can yaje ya d'auka, kuma baza ta iya bawa su Umar su kawo masa ba! D'aukar plate d'in yayi tare da fitowa waje, har gaban Innar yaje ya duk'a tare da fad'in, "Innar mu nagode da d'an wake!" Ko kallonsa bata yi ba, sai ma mik'ewa tayi ta shige d'aki shikuwa ya fita kwar gida yana cin abinci yana kallon yaran dake wasa a k'ofar gidan.........
Haka rayuwa ta cigaba, Ahmad kullum cikin k'unci, a madafi yake kwana domin Inna Laadi bata yarda ya kwana mata a d'aki ba, dama a d'akin Inna Abu yake kwana idan ba ranar kwananta bane, bai samu fuska wajen Daada ba balle yaje d'akin ta ya kwana, bai ma tab'a kwatanta hakan ba, a nan madafi yake kwana sauro da cinnaku na cizonsa. Yauwa ma ya tashi, ko kokon da zai saka a bakinsa babu, komai ya k'are, ko da ya shiga d'akin Innar tasa domin d'aukar kunu, sai ya tarar da kofin amma babu komai a ciki, "Innar mu ina nawa kunun?" Fad'in Ahmad dai-dai lokacin da ta shigo ba tare da sanin yana ciki ba. Saurin fita tayi daga d'akin tana jan dogon tsaki. Narai-narai Ahmad yayi da idanu zai yi kuka, Abbakar ya yi saurin k'arasawa wajen sa tare da fad'in, "Ahmadu kar kayi kuka, ai ban shanye nawa duka ba, gashi nan na rage maka, Umar ne ya ce bai k'oshi ba, shine Innar mu ta d'auka ta bashi naka da k'osan ka ya shanye". Girgiza kai Ahmadu yayi tare da k'ok'aro murmushi yana fad'in, "A'a Abbakar shanye kunun ka, idan naje makaranta zan sayi taliyar goma, ina da wata naira goma da ban kashe ba jiya". B'ata fuska Abbakar d'in yayi tare da fad'in, "Dan Allah ka shanye, Wallahi ni na k'oshi. Idan baka sha ba zan yi kuka". Kallon Abbakar yayi hawaye na cika idanunsa ya karb'i kofin ya kafa kai ya shanye yana hawaye. Cikin sauri ya goge bakinsa ya jawo ledar kayansa ya fiddo kayan makarantar sa ya saka, lokacin tuni su Abubakar sun fice daga d'akin. Bin bayansu yayi, a gaban Innar tasu ya gansu suna kukan a basu kud'in makaranta da na taara, ta d'auki d'ari bakwai ta basu, a kan su kai d'ari shidda kud'in makarantar su wanda ya kama kowa d'ari uku-uku, naira d'arin da ya hau kai kuma tace su raba hamsin-hamsin su saya wani abu a makarantar. Ahmad jiki a sanyaye ya k'arisa kusa da Innar yana fad'in, "Innar mu dan Allah ni ma ki bani, muma jarabawar muke yi, kuma ban yi kusan guda biyar ba, dan Allah ki bani kud'in makarantar ni ba sai kin ban ba taara ba dan Allah!" Kamar yanda yayi tsammani haka ce ta faru, tashi tayi ta bar masa wajen. Wasu zafafan hawaye suka zubo masa a fuska, Inna har ta kai k'ofar d'akin ta, sai ta juyo ta kalli su Abbakar tare da fad'in, "Kama hannun Umar ku wuce kar ku yi lattin zuwa makaranta". Abbakar ya kama hannun Umar suna waiwayen Ahmad har suka fice daga gidan. Ahmad kuwa d'akin Inna mu ya nufa, in da anan ne mahaifin sa yake, sai da yayi sallama sannan ya shiga, zaune ya samu mahaifin nasa shi da su Sakina suna cin waina da k'ashi kowa a tasa robar. Mal Bawa yana tsotsan k'ashi mara taunuwa ya kalli Ahmad tare da fad'in, "Uban menene kuma kazo ka wani tsuguna a gaba na ka zuba min idanuwa? Uwar ka ce ta turo ka?" Girgiza kai Ahmad yayi tare da fad'in "Baba dan Allah kud'in makaranta zaka bani, jarabawa muke yi kuma ko d'aya ban zana ba". "Toooo! Ita jarabawar? To kai Ahmadu ko na biya maka kud'in jarabawa, an fad'a maka zaka zama wani abu ne? Asarar kud'i na kawai zan yi, ni ban da ko sisi, kai ko da ina da shi ma ba zan baka ba, tashi ka wuce kaje kai ta d'umama benci". Kuka Ahmad ya fashe dashi tare da fita daga d'akin da gudu yayi hanyar waje ko jaka bai d'auka ba. Tafiya yake yi yana kuka da iya kacin k'arfin sa har da shasshek'a, yazo ta wani kango zai wuce, wani mutum wanda a k'alla zai yi sa'an mal Bawa ya yafito shi da hannu tare da fad'in, "Zo nan yaro mai aka maka kake kuka?" Ahmad d'in ya k'arasa yana shasshek'a tare da fad'in, "Kud'in makaranta Innar mu da baba su ka k'i biya min, kuma Innar mu na da kud'i don har k'annai na ta biya masu amma ni tak'i biya min, baba na kuma yace wai ko ya biya min bazan zama wani abu ba sabida haka ba zai yi asarar kud'in sa ba wai inje in d'umama benci". Kallon gefe da gefe mutumin yayi ya ga babu mai kallonsa, sai ya kama hannun Ahmad d'in ya shige dashi cikin kangon yana fad'in, "Dai na kuka, kwantar da hankalin ka, kai ne kuwa zaka zama wani abu a duniyan nan idan har kayi abunda nace maka kayi, zan baka kud'i masu yawa kaje ka biya kud'in makarantar ka kaji". Gyad'a kai Ahmadu yayi yana goge idanunsa da bayan hannunsa. Mutumin nan ya tub'e wandon shi tare da jawo Ahmad d'in jikinsa, waro idanuwa Ahmad yayi ganin babban mutum ba wando zai yi ihu, mutumin ya fiddo hanky ya toshe masa baki tare da saka d'aya hannunsa ya zaro y'ar k'aramar wuka ya nuna Ahmad d'in dashi tare da fad'in, "Kana yin ihu zan caka maka wannan wuk'ar a ciki ka mutu baza ka k'ara ganin kowa naka ba". Ahmad jikinsa babu inda baya rawa tsabar razana. Don tsananin rashin imani da tsoran Allah, haka mutumin nan ya cirewa Ahmad wando ya juya shi ta baya tare da toshe masa baki ya shiga amfani dashi ta duburarsa. Wani irin gurnani Ahmad ya soma yi yana jin wani irin azaba da tunda yake bai tab'a jin irinsa ba, gashi baki a toshe babu damar ihu, sai da mutumin nan ya samu natsuwa a jikin Ahmad wanda tuni ya sume, sannan ya goge jikinsa da hanky d'in ya mai da wandonsa ya lek'o yaga babu kowa ya gudu bayan ya ajiyewa Ahmad d'ari-d'ari guda hud'u.
*MATAR SAYYADEE* ✍️ [6/7, 12:14 PM] Matar Sayyadee: 🦜 *D'AN FAARI*🦜 ( _THE FIRST BORN_) *PAID BOOK*🤧 _TRUE LIFE STORY_
_Story and written_ *ZULFA'U SA'EED IBRAHIM* ( _MATAR SAYYADEE_)
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️ ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._
*_D'AN FAARI ISN'T FREE, PAY #600 NAIRA THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800, ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER ***_*